Showing 15001 words to 18000 words out of 87761 words

Chapter 6 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6112

ne?".

"A'a yana ɗakin Iyam, yanzu na fito a ɗakin nima ina jiransa ne zamu tafi".

"bari na leƙa ai ban san kun zo ba, ina nemansa dama".

Ta faɗi hakan tana min wani kallon hadarin kaji. ɗakin Iyam ta wuce ta barni da bin bayanta da kallo, miƙewa nayi na nufi ɗakin Gwaggoje, tana kwance bacci har ya fara ɗibarta jin maganata yasa tayi saurin tashi tana min sannu da zuwa. na zauna muna ta hirarmu da ita, har tana tsokanata wai bamu iya zuwa ba sai dare kamar wasu korarru, ko da ike wataƙila tuwon gidan muka biyo, ni dai dariya kawai na ke yi. sai kuma ta hau min hirar zuwa ƙauyen da zata yi ƙarshen wannan watan, tana cewa ƙila ma tare zamu je tun da su Asama'u suma duk za su je, mijin Aina'u ne dai boɗararre ya hanata. shirin siyasar kano da aka fara yasa ta maida hankalinta ga radiyon, aifa nan ta fara tsinewa shuwaganni, idan na ce ta daina sai ta ƙara tunzura tana akan me ba zata tsine musu ba duk sun sanya talakawa cikin wani hali, yanda ta haƙiƙance yasa nayi shiru ina dariya ƙasa ƙasa.

Sallamar su Iyam ce ta katse maganar da muke yi muka ɗago idanuwanmu kansu. Iyam ta shigo tana cewa da mahaifiyar tata,"ai kamar na sani nace bara in leƙo ba lallai kin saki net ba".

Gwaggoje ta ɓata fuska bata ce da ita komai ba, Iyam kuma ta shiga sauke mata net ɗin. Hubbi ya zauna suna gaisawa, har yana tambayarta ita babu wata matsala a ɗakin nata, ta ce da shi babu matsalar komai, ta faɗa tana saka masa albarka.

Wajen ƙarfe goma muka yi haramar tafiya, lokacin ne kuma Iyam ke cewa da Hubbi.

"Ka kuwa ji haihuwar matar Nasiru?".

"Ahh matar Nasiru ta ƙara haihuwa, lallai ne amma kuwa kinga bai kira ni ba wallahi, Allah ya raya".

Ta ce,"wallahi dai kaga su matansu sai haihuwa suke yi, ga su nan kowanne da yara uku biyu, kai ne dai shiru har yanzu, ban san menene matsalar ba, kai ɗin dai lafiyayye ne na san ɗan da na haifa, amma ya kamata ita ka kaita asibiti a dubata, ai ba a zauna shiru haka ba ayita zuba ido wa tsammanin da ba tabbas".

a hankali yace,"haka ne zamu je ɗin in sha Allah".

Da sauri ta cafe,"Shalele ba fa batun wani in sha Allah ba, da zafifi ake bugun ice, in ba'a san abin yi ba yanzu shin sai yaushe?, rayuwar nan fa tafiya take tayi, girma ne ya ke daɗa kamaka, kana so ka mutu ne baka bar ɗan da zai ke maka adu'a ba, haba ai ka samu ganin jininka ma a duniya rahma ne".

Sai kuma ta juyo gare ni tana cewa,"kuma ke Sa'ida ba ki sha wani abu ba da zai hanaki ɗaukar ciki ba?".

Kaina a ƙasa nace,"ban sha komai ba Iyam, amma ai mun je...".

Hubbi yay saurin tarar maganata da cewa,"Iyam bari mu wuce na bar baƙo zai zo ga kiransa naga yana shigowa".

Wani kallo tayi masa da cewa,"tana magana kuma ka katseta, ko wani abun ne baka so na sani?".

kansa ƙasa yace,"a'a fa ita ai tana maganar mun je wajen wani me magani ɗazu to bamu sami ganinsa ba, dama ina so sai mun gansa ɗin sai kiji komai".

"To ai shikenan Allah ya kyauta, sai ku daure ku ƙara zuwa amma kuje da wuri tun da irin su jama'a yawa suke musu. Gwara idan haihuwar ce bata yi muji da wuri ai ba'a ta zama haka ba, sa'anninka dai duk gasu nan da ƴaƴansu, kuma in jin daɗin rayuwar nan ne dai ai ka fisu, dukiya gata nan bata wasa ba, kaima in kana ganin yaronka ai sai kafi farin ciki da kwanciyar hankali, ga shi nan yanzu naga duk ka rame, kuma na san ba zai wuci damuwar rashin haihuwar kasawa ranka ba".

ta fuskanto ni ta ce,"ko cikin danginku akwai masu matsalar haihuwa ne Sa'ida irin wanda basu taɓa haihuwa ba haka?, kin san akan yi gado, kuma auren irin waɗannan cuturwa ce ga namiji ba kaɗan ba tun da an yaudare shi ba'a faɗa masa ba, amma dai ko me ke nan ki samu ki faɗawa iyayen naki a nema miki magani ba'a ta zama haka ba, kinga shi mijin naki hidindimu sun masa yawa ba ya ta fama da na magani ba tun da babu tabbas ɗin ma za'a sami abin da ake so, dole dai iyayen na ki sai sun miƙe tsaye sun taimaka miki, abubuwa sun masa yawa shi kam, ga hidimarmu ga taki ta yau da kullum...kuyi magana da Ummar taki, nima ƴaƴan gabana yawa gare su da sai inji da ke, to ba zaune na ke ba kullum cikin nemar musu taimako na ke yi duk da su lafiya ƙalau su ke suna haihuwa abin su...ko Malam dai kina ganin yacca yake rubuce su da ayoyin qur'ani, ya kamata gaskiya dai a duba miki rashin haihuwa ai bala'i ne, ga shi ni Allah ya sani ina ta so inga ƴaƴan Nazifi wallahi, Allah yaji ya gani bana so na mutu banga jikokina daga gare shi ba".

nasa hannu na goge hawayen da ya sakko min ba tare da na bari ta lura ba. ban iya cewa komai ba, haka ta rakomu har waje tana ta ƴan maganganu. kan hanyarmu ta komawa gida babu yacca banyi ba ya faɗa min sakamakon gwajin da aka yi min amma kamar ba muminin da na ke ta haɗawa da ubangijinsa ba, ƙememe ma yaƙi min magana.

Muna zuwa gida kowa ya wuce ɗakinsa, ni dai ko da na shiga kan gado kawai na faɗa ko hijabin ma na kasa cirewa, kukan zuci na ke yi domin kuwa ruwan hawaye yaƙi sakko min. Ina cikin duniyar tunani wayata tayi ringing, na ɗaga ganin shi ne yake kirana. a taƙaice ya ce da ni,"ki zo ina nemanki".

Da damuwa fal a muryana na ce,"me zan maka Hubbi?".

"Me za ki min! Kina tambayan mijinki haka!, lafiyarki?".

Shiru nayi na ƙi cemasa komai. kiran wayar sai tafiya yake yi, can yay nisa ya ce,"ai kin ji abin da na ce ko?, to ki taso yanzu kar ki ragen lokacin bacci, in kin zo kya ga me za ki min".

da faɗar hakan ya kashe wayarsa, tashi nayi na shiga banɗaki na wanko fuskata, ban cire kayan jikina ba haka na fita don karma na sanya kayan bacci ya tsammaci ko ina jiran kaɗan ne.
Ina shiga na iske har yay kwanciyarsa ma, na zauna gefen gadon ina kallonsa ta cikin ɗan hasken duhun ɗakin, a hankali nace masa,"gani, ko kayi bacci?".

zaune ya miƙe ya fuskance ni sosai, ya sauke numfashi sannan ya kira sunana. sai da na ɗora idona a saman fuskarsa tukunna na amsa saboda yacca naji yanayin sautin muryar tamkar ba nasa ba.

"Ina da bukatar haihuwa Sa'ida, so na ke na ganni ɗa".

nayi wani guntun murmushi mai ciwo, hannuna bisa kafaɗarsa, cikin tausashshiyar murya na kwantarwa da mutum hankali da sanya natsuwa na ce,"to Hubbi mu ci gaba da faɗawa Allah, shi zai bamu ba wani ba, haihuwa a wurinsa kaɗai take ba ga wani mutum ba, damuwarmu ba ita zata sa mu samu ba, ƙosawarmu ba zata bamu ba, haƙuri da jiran lokaci Hubbi".

"kina nufin ke ba za ki iya haihuwar ba kenan?...".

Na katse cewarsa da,"Subhanallah, baka ji abin da nace ba ne kake ambaton ni ba zan iya bawa kaina ba. Haba Hubbi kar son wani abu yasa ka yi saɓo, ai ba zancen ba zan iya ba, idan Allah ya kawo mai zai hana kuwa in haifa maka ƴaƴa, in bai kawo ba ina da ikon bawa kaina ne?, haƙurin nan dai da muka saba shi zamu ci gaba da yi, komai lokaci ne, watarana sai ƙalubalen jinkirin kaga ya zama alkhairi mafi girma".

aikuwa furucin nawa ya fusata shi, nan ya hau banbami yana faɗin,"fina sanin daidai kika yi da za ki dinga tsara min kalamai, sai anyi magana ki nuna kin fi kowa sanin Allah. to ni dai na faɗa miki ina son haihuwa, so na ke na ganni da ƴaƴa, idan ba za ki haifa min ba kuma ki sanar da ni. kullum burina ne inji an kira ni da Baban wane, na dawo gida inga ɗana ya tarbe ni, to kar ki sa nima na fara zargin wani abun kika sha saboda kar ki haihu, in ba ki haifa yanzu da ƙuruciyarki ba sai kin tsufa kenan?, wannan ai ni kikawa mugunta ba kanki ba, shekara nawa haba".

Na ɗago a gigice ina kallonsa, cikin sarƙewar murya na shiga ce masa,"haba Hubbi! haba!, ta ya kaima zaka shiga sahun masu tuhumata akan rashin haihuwa, kar ka fita daga imaninka mana, kar ka zama me shiga hurumin ubangiji, Hubbi akan me zan maka mugunta in sha wani magani saboda dai kar na ɗauki ciki?, cikinka fa Hubbi, shin ka manta irin tsananin son da na ke maka ne".

Na tsagaita yayin da na ke goge hawayena, zuwa lokacin kuma kuka yaci ƙarfina, kallonsa na ke yi ta ruwan hawayen da ya taru a idona.

"bayan iyayena kafi kowa sanin wace ni, kai zaka bayar da shaidar yanda na ke son yara, tun farkon aurenmu ka san da cewa ina bala'in son ace na haihu, na san kaima yanda ka ke son ƴaƴa tun kafin aurenmu, Hubbi in ace da yanda zan yi in sanya cikin da zan haife maka a cikina wallahi tallahi da duk in da ake samo ciki sai na samo na saka, to amma ya zan yi, lokacina ne bai yi ba...".

nayi shiru ina ɗago ido na kalle shi, ba ni ya ke kallo ba, idonsa na manne a ƙasan tiles, hannunsa dunƙule a gefen bakinsa, yanayinsa na nuni da cewar hankalinsa sam bama akaina ya ke ba, ya nutsa ne can cikin tunanin wani abun.

na daɗa matsowa kusa da shi, kaina na kwantar a kafaɗarsa, hawayen idona ya sauka ta gefe ya tsarga ta cikin rigarsa, na danne kukana, muryana ya washe wajen ce masa,"na san ɗazu da muka je asibiti gwajin haihuwa aka yi min, sun kuma bamu sakamakon gwajin nan, Hubbi don me yasa ba zaka faɗa min ba domin in san menene matsalatar, idan ta neman magani ce sai mu nema kaman yanda Iyam ta ce, idan ma wata mafitar za'a nema sai a nema, ba zan taɓa ɗaga hankalina ba domin na san komai nufin ilahu ne".

Bai ce da ni komai ba, har tsawon wani lokaci duk mun yi jungum jungum, janye jikinsa yay ya miƙe akan gadon. lokacin nima na tashi jiki a sanyaye, har ga Allah ina son kusantuwa ga mijina, nayi kewarsa da soyayyarsa.

"Hubbi". Na kira sunan nasa murya a hankali.

"Ina jinki".

hannu na kai na kamo nasa ina cewa,"Hubbi mu da muke son haihuwa kuma mu ke raba makawanci, mu ka sani ko rabon samun cikin na a dararen da muka tsallakewa".

Muskutawa yay ya gyara kwanciyarsa da cewa,"ba'a ɗau ciki a darare kusan dubu uku ba sai a dare ɗaya?, mtssww ni bani da matsala da rashin kusantarki haka kema na san ba ki da matsala za ki iya riƙe kanki, me amfanin mu'amalar da ba za'a ɗau ciki a haifa maka ba...mun gama maganar zan yi bacci".

Miƙewa nayi zan bar ɗakin ya ce,"ina kuma za ki?".

"zan je in kwanta ne".

"nan ba wurin kwanciya ba ne?".

na waigo na kalle shi ban ce komai ba. cikin muryar ɓacin rai ya ce,"Malama kar ki buɗe min ƙofar ɗaki".

numfashi na sauke, nayi tattaki gaban wadrobe na buɗe na ɗauko kayan baccinsa riga da wando na saka, gadon na hau na kwanta nesa da shi, ina jinsa yana tofemu da adu'a kafin yaja bargo ya rufe mu gaba ɗaya.

washegari da asuba muna cikin karatun ƙur'ani ni da shi, wayarsa da ke kan gado tayi ƙara, na yunƙura na miƙe naje na ɗauko masa, sai dai ganin sunan Yaya a jiki nayi mamaki matuƙa da tambayar kaina kiran ko na lafiya da farar asuba haka.
tun bayan sallamarta da ya amsa da gaisheta da yay naji yay shiru bai ƙara cewa komai ba, sai dai ina iya jiyo sautin maganarta amma bana ce ga abin da take cewa ba, tayi kusan minti biyu tana magana can naji ya ce da ita.

"ehh mun je, bamu dawo da wuri ba ne sai dare, sai na fito zan biyo ta nan ɗin".

yay shiru kafin ya ƙara cewa. "sai na zo ɗin dai Yaya". ya ƙara yin shiru na ƴan sakanni kana ya ce,"tom shikenan ba matsala. Allah ya ƙara lafiya, a gaida yaran".

ba don karatun ƙur'ani mu ke ba bana tunanin zan iya ci gaba da zama, saboda yacca lokaci ɗaya naji gabana na faɗuwa tun gama wayar tasu, to gwarama in ci gaba da karatun ko ba komai damuwa da ɗacin ƙasan zuciyata sa wanke.
da yake yau asabar ban koma baccin safe ba kasancewar akwai tahfeez, ƙarfe tara mu ke tafiya sai ƙarfe ɗaya, kuma bana tafiya sai na girka na rana na ajiye masa, ga shi yau ɗin ya ce kunu da ƙosai yake son ci, bayan ya san bamu da garin kunu da ƙosai a ajiye, ya dai ɓata min lokaci da rai kawai, saboda haka yana gama min ƙarin karatu na shiga kitchen.

sai a lokacin na jiƙa gero, sannan na shiga gyaran waken ƙosai, Allah yasa ma akwai bilenda ban da haka da ba ƙaramin lokaci zan ɗauka ba kafin in gama, kuma rashin gamawar da wuri ya zamar min ɓacin rai tun da shi ƙa'ida ne cin abincin safensa kafin ƙarfe takwas, in har kuwa ya wuce haka sai in ba lafiya ko kuma wani ƙwaƙwƙwaran dalili.
sauri sauri na ke tayi na gama ganin takwas ta doso, ga shi ko abincin ranar ma ban samu na ɗora ba, dole haka zan bari sai na dawo tun da kunu da ƙosan da yawa kuma zai riƙe masa ciki har in dawo. na kwashi kayan abincin na kai ɗakinsa na ajiye, tashinsa nayi na sanar masa sannan na koma ɗakina, wanka nayi na shirya cikin uniform din makarantata, ganin yanda lokaci ya ƙure na sakko a gaggauce.

ina komawa ɗakinsa na tarar har ya gama karyawa, nima yunwar na ke ji sai dai ina tunanin zama in ci gudun ƙara ɓata lokaci. tun da na shigo bai ɗago ido ya kalle ni ba, zama nayi na zuba kaɗan na ci, ina kammalawa na dube shi na ce,"Hubbi na gama".

kallona ya tsaya yi da tambayar,"ina za ki je?". mamakin tambayar yasa na kalli jikina don in ga ko bai lura da yunifom ɗin da na saka ba ne, tambayar ta shi ta rainin hankali ce, kawai lurar da nayi so yake ya ce ba zanje ba, ko kuma ya tabbatar min da na daina zuwa makarantar, kuma take tsoron hakan ya kama ni.

fuskata a narke na ce masa,"makaranta mana Hubbi, yau fa asabar".

idonsa ya mayar kan waya yana faɗin,"ohh na sha'afa ne. ki ɗauki kuɗin mota yau ba zan sami damar kai ki ba".

hakan ma ya wadatar ni kam a wajena, ai da ya hana ni zuwa gwara bai kai ni ɗin ba tun da duk tsiya dai zan iya zuwa da kaina. kawai dai nayi mamakin rashin kai ni ɗin. tashi nayi na je na ɗauki wallet ɗinsa, na buɗe ina cewa.

"nawa zan ɗauka?".

"nawa ne kuɗin motar dama?".

"ba na ce ba tun da kaga ban taɓa zuwa daga nan ba".

"ɗauki ɗari biyar".

na san kuɗin ya wuce haka zuwa dai da dawowa, kuma shi ɗin ma ya sa ni, amma ban ce komai ba na ɗauka ina godiya. na sanya hijabina na ɗaura liƙab, yay min adawo lafiya, sai da zan fita a ɗakin na tuna ban fa bar masa abincin rana ba. a ɗarɗarce na juyo ina cewa,"Hubbi kaga saboda naga na makara ban samu na girka maka na rana ba amma..."

ban kai ga ƙarasawa ba ya ɗaga min hannu,"kuma a hakan kike tunanin za ki fita, makarantar fin mijinki muhimmanci tayi ko me?. to dawo babu in da za ki je sai kin yi duk abin da kika saba kafin ki fita, in kuma ba haka ba ki haƙura da zuwan gaba ɗaya kyaje gobe".

sai kuma can yay gajeran tsaki ya ce,"ke bama za kije ko ina ba, yau na soke zuwan".

cikin sadda kai na ce,"don Allah kayi haƙuri Hubbi, wallahi bana so nayi fashin zuwa, bari nayi sauri na dafa maka, me zan ɗora?".

na faɗa ina kallon agogon da ya kaɗa ƙarfe tara har da minti goma, to yanzu ko da ace ma fitar nayi kafin in je makarantar ai tara da rabi ta wuce, kuma a dokan makaranta minti biyar ka ƙara ba zaka shiga aji ba, kuma ba za'a barka ka dawo gida ba sai dai ka zauna a waje har lokacin tashi, don ma matan aure ne mu ba yanda su ka iya wajen duka. haƙura kawai nayi na cire hijabina na ajiye, na je na mayar masa da kuɗin da na ɗauka.

"dashishi za ki dafa da rana, akwai tsakin alkamar ko?".

"ehh akwai".
"to ki dafa da yawa saboda akwai baƙi".

na amsa masa da,"to". zan fita a ɗakin ya dakatar da ni da cewa,"ki gyara ɗakin kusa da ke na sama, Rumana da Atika za su dawo wajenmu, anjima za'a kawo su ko idan na fita in ɗauko su. na sa a kawo musu gado, ban san lokacin da za su kawo ba idan ina nan shikenan, in bana nan sai ki kula".

tamkar an kafe ni haka nayi ƙyam a tsaye da jin furucinsa, Rumana da Atika!, za su dawo gidan nan da zama?. anya kuwa?, Hubbin da ya ce ba zai taɓa riƙe ɗan wani ba saboda mahaifiyarsa ta riƙe bata ji da daɗi ba, don haka shi ma matarsa ba zata riƙi ɗan kowa ba saboda sanin halin ɗan ruƙo da ke da wuyar sha'ani. to amma ta ya akai farat ɗaya haka ya ce yaran za su dawo gidan nan?.

ya katse min tunani da cewa,"kika kafe ni da ido, Rumana ce ƴar gidan Yaya sai Atika ƴar Anty Aisha, cikinsu wa ye baƙon fuska a wajen ki?".

a rauna ne na ce,"duk ba baƙuwar fuska, amma Hubbi gaba ɗaya gidan nan za su dawo ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login