Showing 3001 words to 6000 words out of 87761 words

Chapter 2 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6105

dai shi ba wai dare ne yayi ba, to amma ban saba ba, tun aurenmu sau ɗaya ya taɓa kaiwa bayan isha'i a waje, shima kuma dalilin hatsarin da ya samu ne, shiyasa ko yanzu nake ta jin kaman da akwai wata matsalar, sai dai ina ta kore mugun saƙe saƙen da zuciya ke min.
Mayafi na yafa na fita, mai gadi na hangoni ya taso da sauri ganin na fito a furgice, gabana ya russina yana tambayar lafiya, da ƙyar na daure na haɗiye kukana nace masa.

"Tun da Hubbi ya fita bai dawo ba ne?".

Mamakin tambayar tawa ya bayyana ƙarara a irin kallon da yake min, na san mamakin bai wuci ace ni da za'a tambayi fita da dawowar mijina ba amma wai ni ce ke tambayar.
Cikin girmamawa yace da ni,"Hajiya ai bai jima da fita masallaci ba, amma dai da mota ya fita inaga ba masallacin nan kusa ya tsaya ba".

Wani ƙunci naji ya ziyarci zuciyata, na kawar da ɓacin raina da damuwata nace,"ok". Abin da na iya faɗa kenan na wuce na bar wajen, don idan nace zanyi doguwar magana tabbas sai ta tsarƙe da kukan da nake dannewa.

Ina komawa ciki na shiga bedroom nasa na ƙasa, ya daɗe da dawowa kam daga yanayin yanda ɗakin ya nuna. Abin da ya bani mamaki matuƙa shi ne sabon ƙamshin turaren da ban san da shi ba, turarensa ɗaya na sani a duniya wanda tun kafin muyi aure da na taɓa basa kyautarsa shikenan ya riƙe shi bai taɓa canjawa ba sai a yau, kuma yanzu da nake ganin sabuwar kwalba akan madubi bayan ga waccen kwalbar bata ƙare ba.

Ɗakin na bi da kallo, idona ya kai kan warm coolers ɗin da ke ƙasa guda uku, wani abu naji ya soke ni kaman sukar mashi. Ƙafafuna na rawa na isa gabansu da sauri na buɗe, ƙamshin lafiyayyan abincin ciki ya doki hancina, babu tantama abincin wata ƙwararriyar chef ɗin ne. Na bar ganina daga kai ina kallon kan gadon da kayansa ke zube waɗanda ya cire, sai naji kamar ana jana zuwa bakin wadrobe, jikina duk na rawa na buɗe ɓangaren da jallabiyunsa su ke, kaf guda goma sha ukun da yake da su suna nan ciki rataye a hanger babu ɗaya da ya saka ya wuce masallaci kamar yanda ya saba.

Lokaci ɗaya naji yawun bakina ya bushe gaba ɗaya, cikin rasa makamar abin yi na rarumi wayata na shiga kiran lambarsa, farko not available su ka ce min, na biyo kuma ringing ɗin bai je ko'ina ba aka danna user busy, na kalli agogo naga lokacin sallar isha'i ya wuce, hakan yasa na ƙara danna kiran, amma har sau huɗu abu guda ake faɗa min user busy ni kuma ƙara kiran nake yi.

Zuciya da bata da ƙashi tuni ta fara ƙissima min tunanin wasu lamura, har tana haska min hoton hakan a cikin idanuwana, babu shiri na rumtse ido gam ina girgiza kaina, ban san lokaci da na sami mazauni a gefen gadon ba ina damƙe zanin gado, wani abu ya soki ƙirjina, cikin raina faɗi nake ina ƙara maimaitawa ba yanda za'ai Hubbi yayi min abin da zuciyata ke rayawa, ko da komai ya canja shi ba zai taɓa sauyawa daga mutumin kirki ba, nagartaccen namiji mai wuyar samu, ba ɗan kuka na aura ba, duk tsanani Hubbi ba zai taɓa juya min baya ba, ba zai taɓa cin zarafina ta irin wannan hanyar ba, matsayin da nake da shi a zuciyarsa ya wuci gaban yaci mutuncina ta irin haka, yana tsanin sona na sani, kowa kuma shaida ne.

Kaman daga sama na jiyo ana kwaɗa sallama a parlo, na miƙe da sauri ina saita natsuwata na fita da sassarfa, da zumuɗin da na fita inci karo da Hubbi nah a asalin Hubbin da mu kayi aure cike da so da ƙauna gami da kwanciyar hankali a zamanmu na baya.

Sai dai me! Ina isa falo gabana ya faɗi ras sakamakon tozalin da nayi, duk sai na daburce ina neman rasa ina zanyi kuma mai ya kamata inyi. Yayar Hubbi ce ta zo Maijidda wadda muke cewa Yaya, daga ƙanne har ƴaƴa da ƴan uwa kowa Yaya yake ce mata, ita ce babbar su wadda ta zamar musu tamkar uwa, kowa na sonta haka kuma kowa na tsoronta, sai abin da tace ayi haka kuma idan ta faɗa ta zauna, ko mahaifiyarsu bata fiya yanke hukunci ba sai dai ta bata wuƙa da nama, haka duk abin da za'a yi sai da shawararta, ba'a taɓa yin abu ba tare da masaniyarta ba, ana girmamata sosai da mata biyayya, kuma itama tana mutunta kowa, ba zan ce bata da kirki ba idan na faɗi haka na zalunceta, macece mai ƙaunar nata, duk abin da ta tattaro na ahalinta ne, burinta taga kowa cikin farin ciki, haka kuma kowa ya tashi kai kukansa ita yake kaiwa, kowa Yaya komai Yaya, sai dai tana da zafi, bata ɗaukar raini, idan ta tashi faɗanta da masifarta shafar kowa yake yi, shisa kowa ke kiyaye abin da zai haɗosa da ita.

Kaf cikin matan ƙannenta tafi sona babu ya ni a wurinta, ba wai don su ɗin bata son su ba, a'a nima albarkacin tsananin soyayyar da take ma Hubbi ne yasa na zama ta gaban goshinta, yanda take nan nan da ni kamar ƴarta Shatu wacce mubke sa'anni, amma duk wannan tarin soyayyar tata da kulawarta gareni sun rushe cikin ƴan watanni, halinta da ɗabi'unta sun sauya, ban san laifin me na mata ba haka kawai ta ɗora dukkan fushinta da karan tsanarta a kaina, ko bikin da aka yi watan da ya wuce cewa tayi kowa ya zauna ya huta ni a tattara min duka ayyuka, haka na zama kamar wata ƴar aiki ko baiwa, nayi ta fama da uban wanke wanken kwanukan taron biki, shara kuwa har sai da na ranƙwafa saboda mugun riƙewar da bayana yay, da an tashi rabon abincin zata kira sunana ta yarfo min zagi tace in ɗauka in bi mutane in raba musu, ban da damar zama ko na sakanni, hatta kashin ƴaƴa da wankan yaran baƙin kunya duk ni ce, haka tasa aka wareni a gefe wai banda amfani, ta mayarni kaman wata jaɓa, na sha baƙin ciki da takaici a bikin nan, har sai da na dinƙa jin kaman in gudu gidanmu, sai dai ban isa ba YaShaik tsab zai takeni idan yaji cewar nayi yaji.

Su kan su ƴan bikin sai da suka ɗinka tausaya min wasu na cewa ya kamata a barni in huta, in huta tunda surukan gidan gamu nan fal, to amma ban isa ba, zaman hutawata daidai yake da zaman hutu a gidan iyayena tun da har Yaya na fushi da ni. To ni kam yanzu mugun tsoron Yaya nake yi, Wallahi a baya da zarar ta ganni take washe baki ta buɗe min hannaye in tafi jikinta ta rungume ni, amma yanzu har gwara naga hukuma su ce kamani suka zo yi akan ganinta, ganin ma ace a gidana.
Harar da ta banka min ita tasa na razana na ƙarasa gaban kujera cike da furgicin ganin fuskarta babu annuri. haka na rakuɓe tsugune kamar an jijjiga ɓera a buta, ji nayi gaba ɗaya ta cika falon saboda irin matan nan ne zabga zabga masu ƙiba, duk da idona a ƙasa yake amma ina jin irin banzan kallon da take jifana da shi, tana aikin kyaɓe baki kamar taga amai, ganin na buɗe baki cikin fusata ta katse ni.

"Lumɓu-lumɓu wutar ƙaiƙayi, tsiga tsiyau kazar matsiyata, wato saboda ba ki da mutunci, ba ki da tarbiya, ba ki da ɗa'a, ba ki san darajar na gaba da ke ba, ni kike jira in gaishe ki...me kika taka da har kike ganinki daidai da ni?, ko saboda an ɗauko ki daga tsiya an rufa asirinki cikin daula shiyasa kike ganin kinfi kowa?, aikin banza shafa lalle a ɗuwawu uban me ma kika aje a gidan da har za ki gadara. to ko shi me gidan yayi kaɗan in zo gidansa ya wulaƙanta ni wallahi, ke ga ƴar iska kina so ki nuna min dangin mijinki mutanen banza ne a wurinki, shiyasa har kina ji ina kwaɗa sallama ki ka barni a shanye, wato in gaji in bushe in kama gabana, to idan ba ki sani ba ki sani, ni mai sakawa ya sallameki ne kuma kin sallamu wallahi, ko idan danginki ne za ki wulaƙanta su har haka?, wato sai ni Yayar mijinki ƴar banza tazo miki gida ba za ki amsa sallamarta ba ko?".

Jiki na rawa na girgiza mata kai alamar a'a ina faɗin,"duk ba haka ba ne Yaya, don Allah don Annabi kiyi haƙuri, wallahi sam banji sallamar ba ina aiki...".

Daka min tsawa tayi tana katse sauran maganata, cikin faɗa sosai take cewa,"dalla rufe min baki munafuka algunguma makira mara tsoron Allah, aikin uban me kike yi a gidan nan banda kici ki kwanta, to idan ma aikin ne fina yayi da ba za ki iya katse kome ne ba, ballantana babu aikin da kike kina kwance sharaf kaman kayan tsinuwa, rashin mutunci dai irin na matan yau shi ya hanaki fitowa".

Na haɗiye abin da ke tokare a maƙoshina ina karanto hasbunallahu, cikin sadda kai ƙasa nace,"don Allah kiyi haƙuri hakan ba zai ƙara faruwa ba in sha Allahu, ki yafe min Yaya don Allah".

Sai na miƙe tsaye jiki babu ƙwarin kirki na shiga gyara kan kujerar da yake a gyaransa nace,"Bismilla Yaya ki zauna".

Ta maimaita,"in zauna?...Sa'ida saboda raini da cin fuska ni kike kallo kina ce min in zauna saboda ga jarababba ta isheki da hayaniya, Yo Sa'ida har wacece ke a gidan nan da sai kin ban izini akan abu, ko tunaninki umarninki nake jira shiyasa nake tsaye har wa yanzu?, Ehh lallai yarinyar nan kin riƙa, wuyanki ya isa a yanka, raini da cin fuska mai muni har haka?, ina Yayar mijinki za ki wulaƙanta ni?, to uwar me kike gadara da shi a cikin gidan nan?, tun da aka auro ki wacce tsiyar kika aje?, shekara takwas babu ɓatan wata balle ɓari, kin kasa ajiye ko tsinke sai aikin ci da kasayarwa, kuma a hakan kike neman gadara da gida, to ke a wa?".

Sai tayi shiru tana bin ko ina na cikin falon da kallo,"ina Nazifin yake?".

"Ya fita".
"Ya fita ina?, Ƙarya za ki min, shi dama yana fita ne ya wannan lokacin?"

Nace,"ai in ya fita magriba sai anyi isha'i yake dawowa, kuma yauma da mota ya fita ba lallai nan kusa zai dawo ba".

Zagayowa tayi ta zauna kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza su, tana ta kaɗa kai. Na wuce kitchen na ɗauko ruwa da lemu na kawo mata, a kofi na tsiyaya ina ce mata ga shi, na duƙa gefen ƙafafunta, cikin taushin murya nace da ita.

"Yaya don Allah ina neman afuwar laifin da nayi".

Ba ta dai ce min komai ba har wucewar wasu sakanni, kafin ta kalle ni cikin zafin rai tace,"wallahil azim idan ba ki bar min magana ba zan zabga miki maruka a wannan damammiyar fuskar taki da ta zame mana musiba cikin ahali, kuma ki kwashe kayanki tun da ban ce miki a yunwace nake ba".

Ni dai ban ko motsa ba kaina na ƙasa ina ta biya kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Yayin da ita kuma na ke jinta tana ci gaba da faɗin,"haba wannan wacce kalar annoba ce, yarinya sa'annin aurenku duk sun haihu daga masu ƴaƴa biyu sai uku, amma ke kina zaune sai dai a ciyar da ke ki cikawa mutane masai da kashi, aure shekara takwas babu wani labari, ai wallahi da sake a wannan lamarin, dole a duba".

Furucin nata yasa na ɗago da sauri na kalleta, ta ƙara jefa min wani matsiyacin kallon tace,"ƙarya na miki?, ko sharri na miki?. to ki kira min mijinki duk inda yake ya dawo ina son magana da shi, yazo ayiwa tufkar hanci, ba zai yiwu yayta ɗawainiya da ke yana faman hidimta miki amma kin kasa biyansa da ƙyanƙyasar ƙwai ko guda, gida har gida kamar wannan ace babu ƴaƴa, wa zai gaji uban dukiyar da aka tara?, to idan shi baida hankalin tunani da lura mu ƴan uwansa da muka san ciwonsa zamu nemi mafita. Yazo ya ɗauke ki a daren nan kuje asibiti ayi miki gwajin haihuwa, idan haihuwar ce ba kya yi muji, idan kuma irinku ne masu dogon jinkiri shima muji, ke idan ma da gayya kika hana haihuwar zamu ji ai, don ni nafi tunanin mugunta ce irin ta ɗiyar talakawa, bai wuci zuwa kika yi aka sa miki tsarin iyali ba. Yo me ma ake da ƙarin aure da ba zai yi ba ya ke ta zama da baƙar aniya, ai wallahi muddin ɗaya cikin abin da na lissafa ba za'a shafe wata guda curr ba sai ya ƙara aure tunda ke ba abar mora ba ce, gwara auren wadda ahali za suyi alfahari da ita, waye ba ya so yaga zuri'arsa?, yo wannan ma ai cutarwa ce ace yana zaune da macen da bata haihuwa, me amfanin auren?, Ai ko ma'aiki cewa yay kuyi aure ku hayayyafa domin in alfahari da ku ranar gobe ƙiyama...don haka Maza maza tashi kira min shi a waya, kuskurena ne ma da ban zo da tawa ba, ki kirasa yazo kuje asibiti yanzu yanzu, wallahi ko haihuwa ko ƙarin aure, ba za'a ci gaba da zama a yanda ake ba".

Maganganunta duk sun saka jikina ɓari, cikin kaina babu abin da ke nanatuwa sai kalmar rashin haihuwa da ƙarin aure, wato duk a baya basu san da matsalar rashin haihuwar ba sai a yanzu. Kuma har tana da bakin kirana ƴar talaka, ehh lallai ciki mai manta kyautar jiya, saurin share hawayena nayi ina ƙoƙarin daidaita yanayina, domin kuwa tun da har na gano manufarsu ta tsangwamata to ba zan taɓa bari suga raunina ba, ballatana su ƙara samun damar cin zarafina yanda suke so.

"Ba kiji me nace miki ba ne, ki tashi ki kira min shi a waya, ni ba wajenki na zo ba balle ki sani a gaba da kirsa".

Hmmm ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali, dama ai shi gwano ba ya jin warin jikinsa, ban da haka mancewa tayi ƴarta ta fari har yanzu bata haihu ba, shekararta goma sha shida da aure shiru babu labari, kuma babu wanda ya tsangwameta ƙarshe ma ɗa aka samu a dangi aka bata, sai ni da ban ko rufe shekara goma ba zata ƙwazzafe ni, ta ɗaga min hankali, ita ba ɗanta nake aure ba, yo ko ɗanta na ke aure irin rayuwar da na yi da shi ai ta shafa min lafiya.

Ji nayi ba zan iya yin shiru ba da zage zagen da take ta yarfo min, hakan yasa murya a hankali nace,"Yaya dama wannan shi ne kuskuren nawa wanda yasa duk ku ka juya min baya?, soyayya ta koma ƙiyayya?, akan abin da bani na ɗorawa kaina ba, akan lamarin da yake na ubangiji shi ne ake tsangwamata haka. Yaya haihuwa fa ta Allah ce na san kin sani, haka duk wanda ya haihu ba shi ya bawa kansa ba, kuma duk wanda aka haifa ba shi ya haifi kansa ba. in har ace ina da iko da haihuwa ai da tuni wani labarin ake, domin nima ina so na ganni da zuri'ata, na ga yau na kafa nawa ahalin".

Muryata ce ta raunana a daidai wannan gaɓar, sai dai ban bari ko kusa ta fahimci cewa kuka nake so nayi ba, tabbas ba zan juri wulaƙanci ba matsawar akan wannan matsalar ce, ai bani kaɗai zan haihun ba, dole sai da ɗan uwan nasu, don haka muddin za'a duba lafiyata akan rashin haihuwata to shima sai an duba tasa. Maganarta naji a tsakiyar kaina tana faɗin,"kin gama min wankin babban bargon?, Nace kin gama zagin nawa?".

Na kasa danne abin da nake ji a ƙirjina na ɗago kaina ina kallonta, lokacin ta miƙe tsaye tana gyara yafen mayafinta, na rumtse ido nace.

"Ki haƙuri ban faɗa miki komai da rashin kunya ba, iya gaskiyata na faɗa, haihuwa ba ni zan bawa kaina ita ba Allah ne mai bayarwa, kuma mafi aksarin jinkiri alkhairi ne, bamu san mai Allah ya shirya mana ba, da haihuwar yuyuyu gwara haihuwar babu, rayuwar nan ba'a ƙareta ba duk da bamu san gawar fari ba, amma ni ina da yaƙinin ba zamu kai ga kushewa ba sai Allah ya azurtamu da haihuwa, sai Allah ya bamu mai jin ƙanmu da alfaharinmu. Kar ki tafi zan kirasa a waya muje asibitin yanzu a duba ni, amma don darajar Allah kar ku yanke hukuncin ƙarin aure, don Allah kar ku saka ya ƙara aure, ba don bana sonsa naƙi haihuwa ba, Allah ne bai kawo lokacinta ba ki duba min Yaya, nayi ƙaranta ace za'a min kishiya yanzu".

"Mtswwww". Taja wani dogon tsaki mai muni wanda yay duka har tsakiyar ƙwaƙwalwata. tasa ƙafa tayi fatali da teburin gabanta, lemu da ruwan da suke kai suka zube akan carpet.

"Sa'ida kici min mutunci ki tsammaci za ki ci gaba da rayuwa ke ɗaya a wannan tamfatsetsen gidan, kice ke ɗaya za ki mori dukiyar Nazifi?, Bayan kin tauye masa hakki kin hana shi ƴaƴa kice ba zai auro mace mai lafiya ba, ai ƙarya kike wallahi...ni bani hanya na wuce ko in bi ta kanki, banza juya kawai marar amfani".

Juya! Kalmar tayi wani tsallen maimaituwa a ƙoƙon kaina, na ɗaga idanuwana nabi ta da kallo har ta fice ta bar parlon. Juya! Juya! Juya!, kalma mafi ciwo da raɗaɗi a duk cikin kalaman da ta gaggaya min, wannan hanyar da suka ɓullo da ita tabbas zata zama hanyar karayata, bana jin zan jurewa gorin haihuwa, duk haƙurina ba zan ɗauki wannan ɓangaren ba.
Idanuwana naji su na zugi, duk da ban kallesu ba na san sunyi jajur, sai dai ko kusa ko alama hawaye sun kasa zuba daga cikinsu. Plate da kofunan da ta kifar na tattara na kai kitchen, na dawo ɗauke da tsumma na goge lemun da ya zube kan carpet, ac na ƙaro saboda wurin yay saurin bushewa gudun kar yay ɗoyi.

Cikin ƙarfafawa kaina gwiwa na wuce ɗakin barcin Hubbi, ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login