Showing 9001 words to 12000 words out of 124287 words
lalitar dake rataye a wuyanta, tace."Hohoho! Haladu ba dai son dad'i ba ina jin dai kana adalci a gidanka ma'ana kana yi musu kyakykyawan cefa ne."
Gemunsa ya sosa cikin inda-inda ya ce."Sosai nake musu cefane mai kyau amma shashashan babu abunda suka iya sai rage kudin cefane gabad'aya babu wacce ta iya abinci a cikinsu shiyasa nake zuwa nake cin kud'ina anan."
Tana 'yar dariya ta ce." To Allah ya rufa asiri me zaka siya shinkafa ko gurasa da miya?"
Ya ce."Shinkafa da miya da rabin kaza."
Da yake da dan 'karfi yayi maganar yasa tayi saurin kallonsa tana girgiza kai dama haushinsa ta ke ji ta san abinda za tayi masa.
Baba Asabe ta had'a masa komai ya juya bayansa yana ta kai loma.
Saliha ce kad'ai ta lura da fitarta to da yake ba magana suke da juna ba shiyasa bata tambayeta ina za ta je ba.
Minti biyar ta dawo ta cigaba da aikinta, ba tare da damuwar komai ba.
Lokacin da Haladu yake ya gar cinyar kaza lokacin suka shigo gidan hayaniyarsu tasa cinyar kazar ta su'bce ta fad'i kasan gurin, ya lashi 'kasan bakinsa yana bin su da kallo.
Indo Uwar gidansa tabi cinyar kazar da kallo kafin ta kalleshi sai muzurai yake kamar kace kyat ya ruga a guje alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare dashi.
Lubabata amaryarsa ta sunkuya ta d'auki cinyar kazar tana nuna masa da fadin." Ashe abinda kake kenan a bayan fage Haladu wai me yasa kai azzalimi ne? Kullum sai kace mana kasuwa babu ciniki ashe nan kake zuwa ka baje kolinka mu ka barmu da wahalar yara da da'wainiya dasu.
Indo tayi 'kwafa tana girgiza kai tace."Yau Allah ya tona maka asiri Haladu daga nan gidan sai gidanmu dama na gaji da zaman wahalar nan."
Baba Asabe tace." Haba Indo ai ba za'ayi haka ba idan rai ya 'baci hankali ake sawa ya duba shi kiyi hak........"Ke kin ga dakata Asabe!"
Lubabatu ce ta katseta tana hura hanci ta ce."Ai dole ki fadi haka mana tunda kullum ke yake zuwa ya yi wa ciniki saboda haka kawai ki ja bakinki kiyi shuru.
Baba Asabe ta rike baki da fadin." Lubabatu rashin kunya zaki min daka gyara kayanka sai ba'kar magana.
Cikin borin kunya ya ce."Ki rabu dasu Uwar towo duk in da za su je su tafi dama meye amfaninsu ku tafi din, amma ku aje min yara na domin ina da yanda zanyi dasu kudi kuma dole na ci abuna tunda ba uwar uban wani ne ya nema min ba."
Fadin wannan magana da ya yi sai ya fusata! su suka shiga ci masa mutunci da gore-gore! Baba Asabe hankalinta ya tashi mutuka tsoronta Allah tsoronta Annabi kada Haladu ya saki matansa akan wannan dalilin.
Da kyar ta rarrashesu suka fita daga gidan, shi kuwa Haladu har bayan magariba yana gidan ya kasa tafiya ashe duk fuffukar 'karya yake ya aika yara har biyu domin su duba masa sai su dawo suce gidan a bude yake Indo da Lubabatu suna nan babu inda su ka je
Jikinsa yayi masifar sanyi fargabarsa d'aya kada ya shiga gidan su ci 'kwal ubansa dama kansu a had'e yake duk kisan mummu'ken da yake musu basa fad'a da junansu k'o'karinsu ya za'ayi su rufawa kansu asiri.
Tsaki ya ja ya cire hularsa ya ajiye ya cigaba da zare ido akan jama'ar dake shige da fice a gidan.
Sai da jama'a su ka yi sauki kana ta kalleshi da fadin." Haladu kayi jugum! ka tashi kaje gida komai yayi zafi maganinsa Allah amma don Allah ka sauya halinka ban ji dadin abinda ya faru ba kaga yanzu ni kaina a cikin zargi nake tunda a gabanka matarka Lubabatu take nuna ni da ya tsaya tana so ta dauki laifin kacokan ta dora min alhalin ni ban san abinda kake aikatawa ba na san dai kullum babu fashi za ka zo ka sayi abinci a gurina wannan shine abinda na sani."
Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki hularsa yasa a sanyaye ya kama hanyar fita jikinsa duk a sa'bule, Shahida kamar ta fashe da dariya duk suka bi shi da kallo yana tafiya zugwi-zugwi kamar wanda k'wai ya tashewa a ciki.
Bayan fitarsa dariyar da take boyewa ta sub'ce a fili ta ce."Karshen munafiki jin kunya."
Saliha ta kalleta kamar za ta yi magana sai kuma ta ja bakinta tayi shuru tana girgiza kai.
Ita kuwa Baba Asabe surutai take ita kad'ai akan maza masu irin wannan hali ko meye abin burgewa a gurin mazan dake ganin k'yashin ciyar da iyalinsu oho!
****
Bayan kwana biyu ta fakaici idon Baba Asabe tasa hijibi ta fita, kai tsaye bakin titi ta nufa, idonta a gurin zamansa babu shi babu dalilinsa sai tarkacen kwaran-kwacamansa! ta jima a bakin titin tana kalle-kalle gabad'aya jikinta ya mutu saboda rashin ganinsa idanuwanta suka cika da ruwan hawaye.
Wani yaro dake tafiya ta tsayar dashi tana tambayarsa.
Yaron yayi mata wani irin kallo kafin ya ce."Ni ina ruwana da wani Baban- Baba ki je ki tambayi 'yan uwansa mahaukata" Yana gama maganarsa ya shige ya barta a gurin, taji kamar ta janyoshi ta gaura masa mari ta tsani a dangantashi da mahaukaci domin ita a ganinta ba taga haukan da yake ba tunda baya doke-doke.
Wani kuttun! abu yazo ya tsaya mata a wuya ta juya domin komawa gida tamkar mara jini a jika haka take tafiya salo-salo! har ta isa gidan bata daina tunane-tunane a kansa ba.
Kai tsaye uwar daki ta shige ta kwanta kan gado kai tasa a cikin hijabi ta fara zubda hawaye.
Baba Asabe dake kokarin hura wuta ta ce."Saliha tunda ta dawo daga gantalin jeki ce tazo tayi wannan wanke-wanken.
Saliha ta amsa da "To." Kai tsaye dakin ta shiga ta tsaya a kanta, "Ke! ki je ki kiyi wanke-wanke inji Baba."
Tana jinta tayi mata banza, Tasa hannu tana kokarin fizge hijab din data rufe fuskarta dashi, Cikin zafin nama ta doke hannun! har sai da yayi 'kara.
Saliha ta fita da hannu a sage! murya na rawa tace." Baba tana jina sai magana nake tayi min banza 'karshe ma hannuna ta buge duba sai zafi yake min."
Tace."Rabu da ita zan shiga dakin na sameta." Saliha ta koma ta zauna da fadin." Wallahi Baba akwai ranar da zan sanya bulala na zane ' Yar iskar yarinyar nan na gaji da abinda take min."
Tana kokarin fitowa daga kicin din tace."Idan kina ganin zaki iya da ita bisimillah ni babu ruwana to ka ji."
'Dakin ta shiga sai kawai taji shashshekar kukanta
A sanyaye tace."Saboda na ce kizo kiyi wanke-wanke shine kike kuka?"
Shuru tayi mata, Baba ta sake daga murya gami da maimaita maganarta.
Ba tare data bude fuskarta ba tace." Me yasa kullum ni nake wanke-wanke a gidan nan idan gaskiya ne itama Saliha tayi saboda kinfi sonta shine kika bata aiki mai sauki ni kika bani aiki mai wahala ni wallahi na gaji haka kawai sanyi ya kamani idan gaskiya ne ki dauki 'yar aiki mana."
Baba Asabe ta ji kanta yana juyawa da ita a gurin al'amarin ya bata mamaki mutu'ka. Ta ce."Shahida ni kike fad'awa wannan maganganun yaushe kika lalace?"
Tana kuka tace."Ni kuskuranki nake so na nuna miki abinda kike ba daidai bane."
Baba Asabe ta fashe da kuka da fadin." Mariya kin tafi kin bar baya da k'ura ni na haifeki a cikina amma baki tozartani kamar yanda 'yarki take tozartani ba, ni ba zan hofintar da zuriarki ba koda kuwa yarinyar nan zata dauko abin duka ta dake ni ba zan damu ba duniya ce ta ishi bagaruwa jima."
Kuka take sosai wanda ya sanya Saliha ta shigo dakin hankalinta ya tashi sosai! sai rarrashinta take, A fusace! ta fita daga dakin, Ashe Kawu Musa ta kira a waya, ta sheda masa abinda yake faruwa, yace." Gashinan kan hanya.
Baba Asabe na raku'be a jikin gado tana kuka da fyace hanci ita kuma Saliha tana tsaye a tsakiyar dakin sai Zaginta take da gore-gore! "Shegiya ai idan ba ki yi haka ba to ba ki cika 'yar gado ba, wannan mahaifin naki ai butulu ne masu ba'kin hali wai ace matar dake tallafarki ita kike wa rashin kunya ai yau zaki gane baki da wayo!
Baba ta daga mata hannu da fadin." Saliha yi shuru da bakinki Ni tayi wa rashin kunya bake ba kada na kara jin maganarki.
Gefe ta koma tana huci!
Shi kuwa Kawu Musa yana zuwa ai bai yi wata-wata ba ya zari wayar redio ya fara lafta mata yana d'ura mata ashar! ,Fadi yake." Wallahi ba'kin cikinki ba zai kashe min uwa ba don ubanki yau sai kin bar gidan nan domin dama hakkin ri'ke ki ba a hannunmu yake ba.
Da 'karfi yake maganar yana dukanta.
Baba Asabe ta rike wayar tana janye shi daga gurin, "Ka daina dukanta kada kaji mata ciwo." Ita kuwa
Fad'i take." Ki k'yale shi ya cigaba da dukana ya kasheni Kawu Musa idan baka kasheni ba wallahi baka cika dan halak ba."
Maganar ta dinga yi masa kuwwa! a kunne! Ya nuna kirjinsa da hannu! " Ni kike fadawa haka?
Tana kuka tace."Me yasa kake nuna min 'kiyayya! me yasa baka 'kaunata? me yasa kake fifita 'yarka a kaina? duk abinda kake min ina fahinta baka kaunata kullum idan kazo gidan nan cikin zuga Baba kake akan ta mayar dani gaban ubana, duk da ba naji sosai watarana na kan tsinkayi abinda kake fad'a akaina saboda haka nima bana sonka tunda baka kaunata."
Kawu Musa jikinsa yayi sanyi, ya jefar da wayar redion ya kama hanya ya fita daga dakin kunyar duniya ta ishe shi.
Ita kanta Salihan ganin yanda jikin babanta yayi sanyi yasa ta kasa daga kai ta kalleta simi-simi ta fita daga dakin.
Tana kuka ta fara hada kayanta, Baba Asabe da sauri taje ta rufe sif din da mukkuli ta fita daga dakin.......Gabadaya haka suka kwana suka wuni cikin bacin rai mai tsanani, kuma tun daga ranar Baba Asabe take takatsantsan! da yarinyar bata tilasta mata kan cewa dole sai tayi mata aiki, Ita da kanta take tashi tayi abinda ba'a rasa ba amma ta daina aikin ruwa saboda tana gudun sanyi ya kamata, dama tayi wannan boran ne don ta samu sassaucin aikin ruwan da ake sanyata kullum ta Allah.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*Fejin na yau na ku ne 'kannena biyu??*
_Jamila Jamy 'Yar kankia_
Tare da:
_Ummu-Hanifa_
Kuna da matsayi mai girma a gurina??
*11&12*
*WAIWAYE*
Shekarun baya da suka wuce Baba Asabe da mijinta Malam Almu sunyi zama na mutunta juna gami da girmama juna, haihuwarsu biyu mace da namiji Musa shine babba tsakaninsa da 'yar uwarsa Mariya akwai tazara amma ba mai tsayi ba, A lokacin da Baba Asabe ta auri Malam Almu ya tsufa sosai bai ta'ba haihuwa ba har ya fitar da rai sai gashi cikin ikon Allah yana auranta Allah ya azurtashi da zuria, yayi farin ciki sosai ya dauki son duniya ya dorawa yaran ashe ba zai jima tare dasu ba Allah ya dauki rayuwarsa.
Uwargidansa dama bata haihu ba wannan dalilin yasa ana raba gado ta tattara kayanta ta tafi garinsu.
Gida ya rage Baba Asabe da 'ya'yanta, Tun daga lokacin ta kafa sana'ar sayar da abinci wanda da yawa mutane da dama suka dinga ganin rashin hankalinta a ganinsu ai bata wuce aure ba amma zata zauna ta lalata 'kuruciyarta a banza a wofi, To Duk zantukan dake yawo a gari suna dawowa kunanta, tayi banza da surutan mutane ta cigaba da sabgarta da kula da yaranta.
Da yawa wasu mazan da biyu suke zuwa sayan abinci gurinta domin su kafa gwamnatinsu, cikin ikon Allah Alhaji Haruna ya samu shiga a gurinta ta kudiri aniyar auransa domin tana yi masa kallon nagartaccen mutum ashe kallon kitse takewa rogo auran beje ko'ina ba ya lalace a sakamakon nuna kyara! da hantara! da yake akan 'ya'yanta. Da farko ta nuna masa kuskuransa akan abinda yake ta kuma gargad'eshi ya daina.
Sai shi kuma yayi kunnan uwar shegu da maganarta duk sanda yazo gidan to fa yaran basu da walwala sun dinga takurewa kenan gabadaya sun tsorata dashi domin kuwa wani sa'in har fakaitar idonta yake ya doke su, mahaifinsu kuwa dake karkashin 'kasa yana shan zagi! Sosai Alhaji Haruna yake *(Kishin kushewa)* akan yaran.
Baba Asabe data gaji da iya shegen da yake mata sai kawai ta fito masa a mutum tayi masa wankin babban bargo, 'Karshe tace dashi babu lallai babu dole idan ba zai juri zama da 'ya'yanta ba to ya saketa domin kuwa ba zai zo har gida yana cin arzikin yara ya takura musu ba.''
Alhaji Haruna ya fusata! ransa ya baci a ganinsa babu amfanin auran macen dake da 'ya'ya tunda duk tsiya watarana sai ta tuna ubansu kuma soyayyar da take nunawa yaran ai kamar ubansu take nunawa, kawai sai ya yanke shawarar sakinta domin dai shi yana kishin ya budi ido yaga yaran a matsayin 'ya'yan wani ba nasa ba, Sai kawai ya rubuta mata saki biyu ya kama gabansa.
Baba Asabe ranta ya baci sosai tayi kuka?? mai yawa ta share hawaye ta barwa Allah lamarinsa, amma a zahirin gaskiya abin ya jima yana cin ranta ace wai shikkenan daga zarar mijin mace ya mutu ko kuma mace ta rabu da mijinta kan wani dalili shikkenan ita da 'ya'yanta sun zama abun 'kyama da wulakantawa a gurin wasu mazan, wannan ba daidai bane wallahi maza kuji tsoron Allah ku tausayawa mata mutukar mace zata sadaukar da rayuwarta a kanka da 'ya'yanka meye abin gudu a tare da ita, 'Ya'ya ne abin gudu kai ma kana dasu, kuma ba dole akace ka rike 'ya'yan da ba naka ba, *(Maza idan zaku auri bazawara to kuyi adalci kada kuso zuciyarku kan wani dalili shi aure na mutum biyu ne yarda da aminci shike janyo har a kulla auratayya amma sai kuga wasu mazan suna gudun mace mai 'ya'ya sai kace ance dole suyi wa yaran d'awainiya da d'an mutum da dukiya ba ai musu mugunta kuma ita rayuwa juyawa take wanda kake gudu sai ya taimake ka watarana)*
Tun daga wannan lokaci Baba Asabe ta cire rai da aure kawai ta cigaba da neman kudinta, Allah kuwa ya shiga cikin al'amarinta tafi karfin yau da gobe da duk wani abunda ba za'a rasa ba.
*******
Manyan mutane masu mutunci da dattako suka dinga turereniya gurin zuwa neman auran Mariya amma funfurus! ta shafawa idonta toka ta kore su, al'amarin daya fusata! Baba Asabe kenan ta rufeta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ta cigaba da cewa"Shi wanda kike kulafuci shin kina da tabbacin zai aureki? Babu wanda be san halin Jamilu ba gurin yaudarar yaran mutane me zakiyi da Jamilu manyan mutane masu mutunci suna tururrubi akanki! Ko kin dauka kinfi karfinsu ne? to bari kiji bayan kyawun jikin da kike dashi to baki da komai sai tarin muni duk ga 'yan mata nan masu kyau a gari wanda suka fiki komai basu dauki kansu wata tsiya ba sai ke to mutukar ni na haifeki ba zaki auri Jamilu ba."
Da jin wannan magana sai ta dora hannu aka ta kurma ihu! tana kiran ta shiga uku ta lalace! Makota suka shigo suna tambayar ba'asi.
Takaici da bakin ciki yasa Baba Asabe kasa magana ta koma ta zauna tana me cigaba da sabgoginta.
Mariya ihu! take tana fadin." Ban ta'ba yi miki rashin kunya Baba ban ta'ba bijirewa umarninki ba duk abunda kike so shi nake so, ke kika zama gatana ban taso da ubana ba amma kin share min hawayen maraicin uba ina so kiyi min adalci a rayuwata kiyi hakuri na auri wanda nake so Jamilu shine rayuwata!"
Jama'ar dake tsaye a gurin suka shiga mamakin al'amarin, Baba tace."Kun dai ji da kunnuwanku abunda take fada, Shin kuna da tabbacin Jamilu auranta zaiyi ko kuma yaudararta yazo yayi sanin kanku ne kafin yazo gurinta ya yaudari 'yan mata da yawa a cikin unguwar nan to me zai sanya ina ganin kashi da rana na taka auran Jamilu bashi da fa'ida tunda shi bashi da hali uwa uba kuma bashi da sana'a"
D'aya daga cikinsu mai suna Huwaila tace."Ki yi hakuri ki barwa Allah al'amarin domin kuwa shi aure nufi ne na Allah kuma naji kina maganar Jamilu bashi da sana'a Aa yana da sana'a domin shago guda ne dashi a kasuwar wambai kawai dai aure ne be yi ba ya tsaya shiririta amma ki bari ni nayi miki alkwarin zuwa gidansu domin mu tattauna da mahaifiyarsa idan da gaske yake to ya fito ayi magana idan yana yaudaran yaran mutane to mu ba zai yaudare mu ba."
Baba Asabe ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Huwaila Na gode Allah ya jishshemu alkairi." Huwaila ta amsa da ameen kafin ta rungume Mariya tana rarrashinta.
Koda Huwaila ta samu mahaifiyar Jamilu da maganar kai tsaye tace ita sam bata ma san da maganar ba, amma idan ya dawo zata tambayeshi duk yanda ake ciki zata zo har gida tayi mata bayani.
Bayan sunyi maganar da mahaifiyarsa ya nuna mata shi sam be san da wata Mariya ba ballantana ya je neman auranta saboda haka ta daina yarda da jita jitan mutane akansa aure nufi ne na Allah idan lokacinsa yayi to ko yana so ko baya so sai yayi.
Sai jikinta ya mutu tace."Anya Jamilu ba zaka nemi maganin baki ba kuwa na fahimci cewar mutanan unguwar nan sun sanya maka ido."
Dariya kawai yayi ya shashantar da maganar.
Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin ya zauna yayi dogon tunani akan al'amarin a zahirin gaskiya Mariya bata da wani kyawun azo a gani amma kyawun jikinta yana mutukar rud'arsa yana masifar son cikakkiyar mace amma kuma yana so ya dawo gida yaga kyakykyawar fuska nayi masa sannu da zuwa.
Murmushi yayi lokacin da ya tuna ai Ubangiji Allah ya hallata masa auran mace fiye da d'aya saboda haka zai auri Mariya saboda kyawun jikinta nan gaba kuma idan ya samu fara kyakykyawa sai ya aura ya samu ta shiga cikin taron jama'a wacce zai sanya a gaban mota
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download