Showing 93001 words to 96000 words out of 124287 words

Chapter 32 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16690

mai tsafta sannan ta ce"Alhaji shigo daga ciki."

Ya shiga da wata sallamar a bakinsa, 'kamshin turaransa ya cika gidan. takalmansa ya cire kafin ya zauna kan tabarmar ya saki fuska sosai yana gaisheta amma da muryar Baban- baba yayi hakan ne domin ya samu saukin fahimtar da ita abinda yake tafe dashi.
Itama gabanta ne ya fadi jin muryar mahaukacin nan mijin jikarta da kullum take mafarkinta sai kawai ta zuba masa ido gabanta na dukan uku-uku!

Abin mamaki! sai ga Saliha ta fito cikin kwalliya tana 'kamshin turare ta tsuguna tana gaishe shi, ya amsa yana murmushi tare da cewa; Ke ce Saliha ko?" da sauri ta daga kanta tana wasa da yatsun hannunta, ya sake wani murmushin kafin ya ce." Shahida tana gaisheki."

Gabad'aya sai suka kalleshi da mamakin jin furucinsa.

Baba Asabe za tayi magana kenan. Kawu ya shigo a fujajan! yana fadin" Wai me yake faruwa ne a waje! jama'a sun cika sai hayaniya suk.....maganar ce ta ma'kale a bakinsa ganin wanda yake zaune, duk da babu wadataccen haske a tsakar gidan sai da ya sheda wanene a gurin, haba ashe shiyasa ya ga dan'kareriyar mota a fake a kofar gidan.

Takalmansa ya cire da sauri ya mi'ka masa hannu da fadin"Yallabai barka da dare ?"


Ya rike hannunsa da kyau! kafin ya ce."Barka dai Kawu kayi mamakin magani na ko?"

Kawu ya ce."Kwarai kuwa Yallabai Allah dai yasa ba wani gagarimin lefi mu kayi ba."

Murmushi yayi wanda yake kara masa haiba da kwarjini ya ce." Ni nayi muku lefi Kawu, amma yanzu na zo gareku ne domin ku gafarce ni."


Kawu ya nemi guri ya zauna da al'ajabin abun a tare dashi ya ce."Ranka ya dade lefi kuma? wane iri kenan?"

Ita kuwa Baba Asabe kasa magana tayi kawai dai tana zaune ta zubawa sarautar Allah ido tana dai jinsa har ya fara basu labarin abinda yake faruwa, kamar yanda yayi musu bayanin asalinsa da farko yanzu ma sai da ya sake jadadda musu, sannan ya fahimtar dasu dalilin da yasa ya sauya kammani domin neman matar aure, tabbas hakan na iya faruwa mussaman idan anyi duba da irin gwagwarmayar da ya sha a baya, ba lefi bane don ya nemi matar aure ta wannan sigar, ya sake yi musu cikkaken bayanin kansa cewa; Shine Alhaji Habu, wanda jama'a suka fi saninsa da 'Dangaske, kuma shine Baban-baba wannan mahaukacin da yazo ya auri 'yarsu cikin talauci da rangwamin gata.

Baba Asabe ta dinga tasbihi ga Ubangiji tana kad'aita shi! wannan al'amari ya bata tsoro mutu'ka wato dai shi Ubangiji ba a yi masa wayo kuma ba a yi masa dubara, tayi kuka sosai a lokacin da ta rabu da yarinyar, kuma duk sanda ta tuna cewa; wanda ta aura bashi da cikakken galihu tana shiga tashin hankali mai tsanani! ba komai take tunawa ba sai mahaifiyar yarinyar da kuma lalurar da take tare dashi, amma sai ta fawwalawa Allah ta bar abin cikin ranta, sai dai duk daran duniya tana tashi tayi wa yarinyar adduar samu kwanciyar hankali da rayuwa mai kyau! sai gashi adduarta ta kar'bu! ashe wanda yarinyar ta aura nagartaccen mutum ne irin wanda yake wahalar samu, hakika ha'kuri da tawakkali yayi wa Shahida rana wannan shine matakin nasara, babu wani abu da ake samunsa kai tsaye ba tare da an fuskanci kalubale ba, Yarinyar tasha gwagwarmaya ta rayuwa, amma da tayi hakuri ta fawwalawa Allah sai gashi yayi mata alheri mafifici.


Gabad'aya suka kasance cikin walwala da farin ciki idan ka cire Saliha daga cikinsu,kasancewa tayi cikin k'unci da bakin ciki, ido cike taf da hawaye ta tashi ta shiga daki ta kwanta sai kawai ta rushe! da kukan takaici! yanzu ace wai kamar Shahida kurma ita ce ta mallaki hamsha'kin mutum mai daraja wanda duniya tasan dashi ta sanya masa rigar arziki shine mijinta to ita kuma wa zata aura ? bayan ta san tafi Shahidan kyau nesa ba kusa ba, kuma duk samarin dake zuwa gurinta talakawa ne, domin saurayinta na farko da a ka sanya musu ranar aure, saboda bashi da gidan kansa tace ba zata aureshi ba, babu yanda ba a yi da ita ba ta bijire sai mayar masa da kudinsa akai, a halin yanzu kuma babu wanda yake zuwa gurinta da maganar aure! dole hankalinta ya tashi da jin wannan al'amari! a ce yarinyar da takewa dariya muskiniya wai ita ce ta auri d'aya daga cikin attajiran da ake ji dasu a duniya. kuka sosai ta dinga yi tana shar'ben majina.

Yayin da su Baba suke kwasar garar alheri daga gurin dattijo mai halin dattako mutumin da ya dauki kansa dai-dai da kowa duk kuwa da cewa; Ubangiji yayi masa baiwar ilimi dukiya nutsuwa wadatar zuci hankali da kuma hangen nesa da sanin ya kamata, hakan bai sanya ya ajiye kansa a wani bigire na daban ba, ko da yaushe mu'amula yake dai-dai da mutane, ya ajiye hakan a ransa cewa shima ba kowa bane a wannan duniyar, tunda tun kafin zuwansa anyi ire-irensa da yawa, akwai wad'anda suka wanye lafiya kafin mutuwarsu, akwai kuma wad'anda su kayi mutuwar wulakanci bayan Allah ya 'kwace damar da ya basu saboda sun d'auki kansu wata tsiya har suna jin kai isa da izzah! uwa uba girman kai! duk mutumin da Ubangiji ya azurta da dukiya ba wai ya azurta shi ne saboda ya fi sonsa a cikin bayi ba, a'a jarrabawa ce daga gareshi, daga lokacin da ya ga kana ta'kama da izzah! tare da nuna kamar kai kayi wa kanka da wulakanta mutane sai yayi maka kwaf d'aya! zai iya saukar da ibtila'i akan dukiyar taka sai ka wayi gari baka da ko kwabo. karshe wanda ka ke wulakantawa ya zama shi yake taimakonka. to wannan dalilan yasa D'angaske baya d'aukar kansa wata tsiya, kuma bai ta'ba sanyawa a ransa cewa; zai dawwama da dukiyarsa ba, watakila kafin mutuwarsa Ubangiji ya kar'ba ya bawa waninsa.


Kyautar kudi masu kauri yayi musu, sannan ya roki alfarmar Baba Asabe ta daina sayar da abinci, duk abinda take bukata na rayuwa yayi al'kawarin d'auke mata! kana yayi wa Kawu Al'kawarin bashi jari mai kauri domin ha'baka kasuwancinsa.

Wannan gida kuma da Baba ke ciki za a rushe a gina na zamani gobe za a fara aikin.

Baba Asabe kasa daurewa tayi ta dinga kuka tana godiya tare da yi masa fatan alheri da gamawa da duniya lafiya.

Cikin jin dadi da farin ciki yake amsawa domin ya ji dadin yanda suka fahimce shi, sai suka 'kara martaba a idonsa yayi musu godiya mai yawa ya kuma ce su zauna a shirye cikin 'yan uwa ga duk wanda yake da bukatar zuwa gidanshi zai turo da motaci a d'aukesu, hakan ya 'karawa Baba Asabe kwarin gwiwa, In sha Allah gobe da wuri za ta fita domin ta shedawa 'yan uwa da abokanan arziki abinda yake faruwa.

Cikin mutunci da karrama juna su kayi sallama. Kawu ya take masa baya abin mamaki! suna fitowa waje sukayi arba da cincirindon mutane har sun fi na da yawa. ganin Fitowarsa gurin ya hautsine, ya dinga d'aga musu hannu yana godiya yayin da Kawu ke kokarin kare shi da hannuwansa ganin yanda wasu daga cikin mutanan ke ja masa babbar rigar jikinsa wai ya taimaka musu. suna da yawa sosai! babu halin ya tsaya ya saurari Uzurinsu, sai da ya samu nasarar shiga mota tukkuna ya ce da Sule ya bawa mutanan hak'uri amma duk mai bukatar ganinsa ya je gidansa dake giginyu ya same shi amma sai 'karshen wata domin gobe da wuri yake so ya tashi.

Sule ya sheda musu abinda mai-gidansa ya ce sannan fa aka samu sau'ki suka fara watsewa daga gurin, wannan ya bawa Sule da escorts dinsa damar shiga motar. Sule ya tashi motar Kawu ya daga masa hannu da fadin" A sauka kafiya Yallabai mungode sosai Allah ya 'kara girma." Shima hannun ya daga masa yana godiya kafin ya sauke gilashin. lokacin motar ta fara 'kokarin fita daga layin. hakan ya bawa jama'ar da su kayi saura a gurin damar bin bayan motar suna ta bambad'anci mussaman matasan da basu da aikin yi duk a 'kokarinsu na ya za a yi su samu wani taimako daga gurinsa.
102&103
Ganin tunda ta hau sama bata sauko ba yasa Hajiya yanke shawarar bin bayanta, hakika itama ta ji takaicin abinda akayi mata na rashin kyautawa, zahirin gaskiya zaman Hajiya Fatima a gidan ba zai haifar da alheri ba domin duk ta fahimci abinda take nufi wato tana so ta dawo gidan su had'a kai da 'yarta su cizgunawa yarinyar mutane to gaskiya ba zata yarda da wannan al'amarin ba.

Ina kwance kan kujera abin duniya ya yi min yawa Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta.

Zaune na tashi tare da kokarin daidaita yanayin fuskata.

Gefe na ta zauna fuskarta babu yabo babu fallasa!

Nima nayi 'kokarin kawar da damuwata. na sake gaisheta a karo na biyu ta amsa cikin kulawa kafin ta d'ora da fad'in abinda ya shigo da ita.


Murmushin takaici kawai nayi zuciyata na wani irin turiri! domin a lokacin idan nayi magana zan iya fashewa da kuka saboda b'acin rai!


Ta ce" Don Allah kiyi hakuri kin ji ko, in sha Allahu za a yi wa tufkar hanci! idan mijinki ya dawo duk zan sheda masa abubuwan da suka faru domin ita kanta Fatiman idan bakya bukatar ta a gidanki to dole ta daina zuwa tunda ba alheri ne yake kawo ta ba.


Da mamakin maganarta na kalleta na ce"Hajiya ya za ayi na raba zumuncin dake tsakaninsu? 'yar uwarsa ce fa, kuma uwar 'yarsa tilo d'a yake da ita a duniya, ni kuma wacece da zan hana ta shigowa gidan nan."

Tayi murmushi da cewa" Duk dan a samu zaman lafiya yasa nayi wannan maganar, Fatima jika ta ce, domin ni na haifi Ubanta to amma bana 'kaunar halayenta saboda bata da kirki! wannan dalilin yasa na yanke shawara cewa; idan mijinki ya dawo ya tsawatar mata! sannan itama Shukura dole ta fuskanci hukunci akan abinda tayi miki, ai duk 'kan'kantar ki a matsayin uwa ki ke a gurinta tunda kina auran ubanta."


Girgiza kaina nayi tare da cewa; A'a Hajiya kada kiyi haka don Allah! domin ba naso daga zuwa na gidan nan wata matsala ta faru mara dad'i! wallahi gabad'aya idan sun fahimce ni to zamu zauna lafiya da juna, domin bana son tashin hankali! kawai ki bar maganar kada ki fada masa da kaina idan ya dawo zan masa bayani sai yayi wa tufkar hanci."

Ta ce"To shikkenan tunda kin ce haka, amma don Allah ki 'kara hakuri kuma ki saki jikinki gidanki ne babu wanda zai nuna iko domin ni ba zan yarda a had'a baki da ni a cutar da ke ba."

Cikin jin dadin furucinta na ce"In sha Allahu Hajiya Na gode sosai da kulawa kuma nayi miki alk'awarin cewa zan yi iyakar bakin k'okarina a gidan nan, Allah ya kawar da sa'bani a tsakaninmu.'

Ta amsa da ''Ameen suma ameen sannan ta ce" Ai tuntuni mijin naki ya kira wayar Shukura ya ce" Ta fada miki cewa ba zai samu damar dawowa yau ba saboda wani dalili sai dai gobe idan Allah ya nufa.


Duk da ban ji dadin hakan a raina ba. amma ban nuna a fuskata ba na ce"To shikkenan Allah ya dawo dashi lafiya ai da yau da goben duk d'aya ne."

Tare muka sauka 'kasa nan muka same su a zaune sun yi baja-baja da kaya da alama ta kwance jaka ne Shukura sai duba dogwayen riguna take.

Da saurin gaske na d'auke kaina kai tsaye gurin cin abinci na nufa, ita kuma Hajiyan ta je ta zauna kan kujera tana kallonsu.


Abincin na zuba daidai cikina na ci na k'oshi ban sake bi takansu ba har na kammala. na ta shi a nutse na isa gurin da Hajiya take zaune nayi mata sallama.

Kai tsaye sama na nufa kawai na ji muryarta a bayana tana kiran sunana. "Anti Shahida."

Na tsaya ina kallonta da mamaki! sosai a tare dani kamar ba ita ce ta gama d'ura min ashar d'azu ba.

Ta miko min wata leda da fadin "Wai gashi in ji Mommy tsarabarki ce."


Na bi ledar da kallo ina nazari.

Ta ce"Ki kar'ba don Allah kuma kiyi hakuri akan abinda ya faru d'azu tsautsayi ne ba zan sake ba."


Na sa hannu na 'karba da cewa"Kada ki damu ni dama ban ajiye abin raina ba ballanatana ya dame ni, Na gode sosai Allah ya bamu hakurin zama da juna."

Da farin ciki a fuskarta ta amsa da "Ameen Anti."

Da ledar a hannuna na isa gurin da hamsha'kiyar ke zaune tana waya, sai da ta kammala tukkuna ta kalle ni, babu yabo babu fallasa na ce"Shukura ta kawo min tsaraba duk da ban duba ba ina godiya kwarai Allah ya kara arziki."


Ta amsa da murmushi a fuskarta kafin ta kai hannu ta dauki d'aya wayar dake gefenta wacce take ta kuwwa! ganin tana amsa waya yasa na sake yi wa Hajiya sallama a karo na biyu na hau sama da tunanin abubuwa da yawa a raina.


Sai da ta gama wayar tukkuna Hajiya ta kalle ta da fadin"Yanzu hakan ai ya fi alheri da mutunci. wannan yarinyar dai a haife kin haifeta domin duka bata fi Shukura a shekaru ba, amma tana da hankali da nutsuwa irin na masu yawan shekaru, don Allah ki zauna lafiya a gidan nan har ki gama kwanakin da za ki yi ki tafi tunda dai kin 'ki aure kin fi bukatar zamanki a haka"

Shiru kawai tayi mata ba tace komai ba sai wani irin murmushi dake fuskarta shi ba na farin ciki ba, shi ba na bakin ciki ba.

***
Kwata-kwata ban yi tsammanin dawowarsa da wuri ba, shiyasa dana yi sallar asubahi na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'auke ni.

Mafarki nake ko a gaske ne? yanda dai al'amarin yake ratsa min jiki da k'okarin tayar min da hankali yasa na tsorata! na zabura! da sauri na bud'e idona jin nauyi a kaina tare da jin ana tatta'ba wasu guraran na jikina uwa uba k'amshin turaransa da ya cika min hanci, wannan ya tabbatar min da cewa; ba mafarki bane. idona na bud'e da saurin gaske! fuskarsa daf da tawa yana kokarin had'a bakina dana shi. a tsorace! na ture shi ya fad'i saman gadon yana bina da wani gigitaccen kallo.

Ni kuwa gabad'aya hankalina a tashe yake kallonsa kawai nake sai kace majanunin! (mahaukacin!) gaske. da suffar Baban-baba ya dawo gare ni.

Ya tashi zaune yana murmushi har ila yau da muryar Baban-baba ya ce."Meye abin firgita! ni ne fa mijinki majanuni! na dawo da bege da kwad'ayi tare da ishirwarki! ki taimaka min a cikin wannan yanayi."

Kukan takaici ne yake kokarin 'kwace min. na ce"Wallahi ka d'auki alhakina! ka bani tsoro me yasa zaka shigo min da wannan suffar! ka cire wannan yagaggiyar rigar ta jikinka, da kuma wannan fuska da kasa domin ba kayi kyau ba."
Tsakani da Allah nake maganar hawaye na kwaranya daga idona.

Hankalinsa a kwance ya ce."Kefa ki ka ce kin fi bu'katata a haka. ashe dan na zo miki da wannan suffar da ki ke so ba wani abu bane a gurinki, tunda dama a haka ki ka aure ni."

Rintse idona nayi na ce"To yanzu na ce bana bu'kata! zahirinka nake so da 'kauna."

Ya 'kara nutsuwa a cikin kogin kaunarta, yarinyar ta riga ta gama kamashi dumu-dumu! tunda bata jin nauyin fad'a masa abinda ke cikin zuciyarta.


"To na ji bu'de fuskarki ki ga wani abu."

Jin haka yasa na bud'e fuskata ina kallonsa yasa hannuna ya tattago fuskar dake cike da gashi mai furfura! duzaza! babu kyawun gani ya cire ya ajiye asalin fuskarta ta bayyana! ajiyar zuciya ya sauke ya sauko daga gadon, nan na dinga bin ilahirin jikinsa da kallo, fatarsa a bushe duk tayi duhu tayi wani irin kamar dai lokacin da ya shud'e! ya kama hannuna muka shiga bandaki a tare ina tsaye ina kallonsa ya had'a ruwan d'umi! ya cire yagaggiyar rigar jikinsa ya rataye kafin ya fara kokarin cire gajeran wandon jikinsa, da sauri na kama kofar band'akin zan fita, ya sha gabana da cewe; babu inda za ki sai kin tsaya kin kalli zahirin mijinki domin a yau ina so ki san waye Abubakar Saddiku".

Gabana na fad'uwa na ce"Wane irin sani kuma bayan wanda nayi maka"

"Ina so ki fita daga cikin zargi ne, ki san cewa; na sauya hallitata ne saboda ke, domin takanas ta kano na je india nayi tsayin sati hud'u domin shirya yanda al'amarin zai kasance."


Na ce"Wallahi na amince da hojjojinka domin babu wani sauran zargi a tare dani tunda dai yanzu na ga zahiri don haka ka rabu dani kawai na fita sai kayi wankan."


Ya girgiza kansa yana lumshe ido ya ce."So nake na wanke jikina da ruwa a gabanki domin ki sake gazagata waye ni? dan har yanzu akwai sauran abinda baki sani ba.

Kokarin magana nake kawai naga zura sakata kuma tsawo na ba zai kai ba ballanatana na bud'e, ina kallo ya fara cire wandon jikinsa na juya bayana gabana sai fad'uwa yake lallai mutumin nan bashi da ta ido.

Motsin ruwa na fara ji hakan ya tabbatar min da cewa; ya fara wankan, na sauke ajiyar zuciya ko kusa ban yi gangancin juyawa na kalle shi ba har sanda na daina jin motsin ruwan. Ba zato na ji ya kinkime ni kuma babu komai a jikinsa, gabad'aya ya manne ni a kirjinsa ruwan daya kwanta kan gashin kirjinsa ya ji'ka ni! tsigar jikina ta tashi. ture shi nake ina kokarin sauka yana sake talfe ni har sai da ya tsunduma ni cikin kwamin wankan dake cike da ruwan d'umi! sannan hankalinsa ya kwanta. na rufe idona

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login