Showing 114001 words to 117000 words out of 124287 words

Chapter 39 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16695

mugun zafi suka shiga gararanba a farfajiyar fuskata!

Jamila kuka take tana fadin." Shikkenan Hadiza ta mutu! shikkenan ta mutu ta bar maka duniyar Baba! ba ka yi mana adalci ba." Kamar zautacciya haka take sakin maganganu! nayi saurin toshe bakinta ina girgiza mata kai.
Shiru tayi amma fa hawaye sai shatata suke.

Sosai nayi ta nanata addua a fili da zucci har na samu k'warin gwiwa na d'auko waya ta, lambar babanmu na kira. yana d'agawa na mi'kawa Jamila wayar. hannu na rawa ta 'karba cikin kuka ta sheda masa abinda yake faruwa, ta kashe wayar ta mi'ko min.
Na nemi lambar wayar Saliha nan ma Jamila ta kar'bi wayar ta sheda musu abinda yake faruwa. da karshe na kira maigidana shima na fad'a masa.
Na kalleta sai kuka take tana girgiza kanta, na ce" Jamila ki kira dangin mamanku suma ki sheda musu, sannan ki dai na yi wa Hadiza kuka tayi shahada Allah yasa ta mu ta yi kyau."

Ta ce."Anti Shahida wane irin Shahada kuma? ki dubi akan tafarkin da mutu, haihuwar shege fa, me zata fad'awa mahallicinta.

Raina ya 'baci ainun! na ce" Wai ke yaushe za ki yi hankali ne Jamila? ko so ki ke ki tona masa asiri a cikin asibitin nan, ina ruwanki da tsakaninta da Ubangijinta? to mutu'kar kina so mu shirya kada ki sake tayar da magana irin wannan. mu dai fatanmu anan shine Allah ya kar'bi shahadarta ya kuma raya abinda ta bari.''

A sanyaye ta amsa da " Ameen." Tana ta jan majina kuka duk ta rasa yanda za ta yi.


To kafin gari ya waye jama'a da yawa sun sami labarin mutuwar Hadiza, kowa dai da abinda yake fad'a akan lamarin. domin shi kansa Babanmu da yake jin haushinta sai da mutuwar ta doke shi! kuka sosai ya yi a gaban gawarta yana nema mata rahama, Jamila kuwa faduwa ta yi a gurin tana iskokai! wanda tunda muke da ita ba mu ta'ba sanin tana dasu ba.
Haka aka yi jana'izar Hadiza Talatu na can gidan mahaukata sai dai a nema mata sauki daga Allah. amma kuma 'yan uwanta cika su ka yi a gidan a kayi duk abinda ya cancanta da su.

Har yamma muna tare da Baba Asabe domin har da ita a cikin masu wanke Hadiza da shiryata zuwa gidanta na gaskiya.
A nan nake sheda mata kyautar jaririyar da marigayiyar ta yi min

Ta ce" Shahida kina ganin hakan ba zai janyo miki matsala ba kuwa?"

Girgiza kaina na yi murya na rawa na ce" Babu wata matsala Baba, dama nema muke ni da mijina ni kuma yanzu ga shi mun samu, in sha Allahu za mu rike yarinyar kamar mu muka haife ta.

Ta ce." Shikkenan Allah ya taya riko, kema Ubangiji ya baki naki rabon masu albarka.
Na amsa da amin suma amin.

To ganin yanda jama'a suke ta turareniyar zuwa gaisuwa ya sanya na sha jinin jikina, domin dai da yawa idan sun zo gaisuwar ba sa tafiya sai sun ce aba su baby su ga ni, ashe gari ya d'auka cewa; Jaririya tana nan kyakykyawa kamar 'yar larabawa, to wannan shine dalilin da yasa mutane basa tafiya sai sun gazgata abinda suke ji a gari.

Hakan ya sanya ranar da a kayi adduar uku. na shirya tafiya gida domin bana jin dadin irin kallon da jama'ar gari sukewa jaririyar da bata san komai ba.
Tsaf na kammala shiryawa, dama kuma tun safe nayi sallama da Baba Asabe domin da ita a ka gabatar da adduar uku kafin ta tafi.

Muna zaune tare da Jamila a d'aki ina tsammanin zuwa Sule a lokacin, tunda nasa an kira shi a waya ya ce gashinan a kan hanya. na kalleta a nutse na ce"Wai Jamila ina saurayinki ne wanda a kayi muku baiko?"

Shiru ta yi na minti biyu kafin ta ce." Bayan dawowar Hadiza da abin kunya, da kuma aika-aikan da Talatu ta dinga tabkawa ya sanya ya janye aurena, dama kuma can iyayensa basa so a cewarsa Babanmu bashi da kirki dan bariki ne, Shine ya ma'kale dole sai ya aureni, ganin haka yasa iyayen nasa suka ha'kura, amma sakamakon faruwar wannan al'amarin sai ya daina zuwa kona kiransa a waya baya d'auka, daga karshe ma wakilansa suka zo suka kar'bi kudin da suka kawo na zance."

Sosai na tausaya mata domin yanda take maganar na fahimci cewa; ta ji ciwon abin. na ce." Kiyi hakuri in sha Allahu. Ubangiji zai baki wanda ya fi shi.
Ta ce" Allah ya yarda."

Rufe bakinta ke da wuya Walida ta shigo tana cewa" Anti Shahida ga wata mata tazo gaisuwa anti Murja ta ce na fada muku.

Tare muka fita tsakar gidan, matar babbar macace daka ga ni kuma ta ga jiya da yau! ha'koran makka sama da 'kasa! ga wani ubansu less da yake jikinta da wani dan'kareran mayafi, sai k'amshi turare! take.

Cikin rashin fahimta muka gaisa ta ce" Na san baki gane ni ba ko?"

Na ce"Eh gaskiya kuwa.".

Ta ce" Sunana Hajiya Zaliha 'kawar Hajiya Fatima tsohuwar matar 'Dangaske ina nufin mijinki, tare muka zauna da ita a saudia."


Na ce" Ayyo! Allah sarki ya a kayi ki ka san gidanmu."

Murmushi ta yi da cewa." 'Kawata ce ta yi min kwatance sai na ga ashe ma muna kusa da juna, shine na ce bari na shigo na yi miki gaisuwa kafin ki tafi, duk da yake nima cikin satin nan nake koma saudiya.

Jin haka yasa na gazgata abinda nake zargi, wato a gurinta Hajiya Fatima ta samu labarin komai, wanda ta samu damar cin zarafin mahaifinta.

Shiru na yi mata ban ce komai ba, amma na lura fakaice take yi min wani irin kallo.
Wanda ya sanya gabad'aya na tsargu! 'bata fuskata na yi nayi bala'in shan kunu! don gabadaya matar bata kwanta min a rai ba.

Sai ta yi 'yar dariya da cewa; Allah sarki Hadiza Allah ya gafarta mata ya raya abinda ta bari."
Na amsa da ameen'' kamar na gaura mata mari saboda takaicin abinda take.

Ta mik'e tare da d'aukar jakarta da cewa; to Allah ya kara hakuri." Anti Murja ta ce" Ameen ya rabbi Allah ya bada lada."
Tana 'kokarin sanya takalminta take amsawa.
Tana fita na ja tsaki da fadin." Anti na lura da yawa mutane gulma ce take kawo su wallahi. wannan shine dalilin da ya sanya yau-yau din nan zan bar garin nan wallahi".
Ta ce" To ya za a yi da sha'anin mutane! kin san yanzu jama'a sun fi zuzuta! sharri! a kan alheri Allah dai ya rufa asiri."

Na amsa da "Amen dai Allah ya sa mu dace."

****
Cikin gajiya na fito daga cikin motar, lokacin ana ta kiran sallar magariba. Walida ta fito goye da babyn a bayanta wacce muka mayar mata da sunan mamanta sai muka yanke shawarar kiranta da Nanah! lokacin da na shirya tafiya ne na nemi alfarma gurin Babanmu ya ba ni Walida. ba don komai ba sai dan ta d'ebe min kewa ta kuma taimaka mini da rainon yarinyar. haka nan ba don ransa ya so ba ya amince ne kawai saboda baya son 'bacin rai na, amma maganar kyautar da Hadiza ta yi mini ta tafasa bai ce ba balle ki sauke, kawai ya ja bakinsa ya yi shiru, yanda na fahimta ma kamar hakan ya yi masa dad'i yarinyar tayi nesa da shi.


Da sallama muka shiga falon, Shukura ce kawai a zaune da waya a hannunta

Wani irin kallo take mana na san tana mamakin ganin Walida ne da kuma yarinyar dake goye a bayanta tana tsala ihu!

Na daure na yi mata magana da cewa" Shukura ya gida? ina Hajiya?"

Da k'yar ta bani amsa da cewa" Ta shiga sallah.

Ban sake wata magana ba na fara hawa saman domin babu abinda na fi bu'kata a yanzu kamar na watsawa jikina ruwa.

Walida ta biyo bayana tana jijjiga yarinyar dake wani irin kuka da alama dai akwai abinda ke damunta .


Hajiya ta fito d'aga daki tana fadin" Kukan jarirai na ke ji a cikin gidan nan".

Shukara ta bata amsa da cewa" Eh mana matar gidan ce ta dawo ina jin ta je gidan marayu ta dauk'o mana jangwam!

Ta zauna kan kujera da fadin" A'a to ba a gidan nan ba, domin mafi akasari duk yaran da suke gidan marayu shegu ne an rasa yanda za a yi da su aka kai su can aka aje."


Shukura dai ta'be bakinta ta yi ta cigaba da danna wayarta ita dai babban burinta mamanta ta dawo gidan.

Ina 'ko'karin shiga wanka kawai na ga mace ta shigo dakin. fuskarta kawai na kalla na gane cewa; ba alheri ne ya shigo da ita ba.

Na ce" Hajiya sannu da gida, na dawo ai Shukura ta ce mini kina sallah.

Ta shiga bin Walida da kallo wacce take kokarin cirewa babyn pampas.

"Wannan jaririyar fa?" ta fada idonta a tsaye a kaina.

Na ce." 'Yar gidan Hadiza ce, na san kuna da labarin mutuwarta ko?"

Ta ce" A'a mu ba mu da labari. to yanzu da ki ka dau'ko ta kina da nonon da za ki bata ne?"

Na ce" Hajiya wannan ai duk mai sauki ne akwai madara da likita ya dora ta akai.

Wani irin kallo ta yi mini kafin ta ce." Kin d'auko nauyi kin kawo mana cikin gida ita kuma wannan fa?" ta fad'a tana nuna Walida dake zaune.

Na danne 'bacin raina na ce" 'Kanwata ce ita ce 'karama a cikinmu."

Tsaki! mai tsayi ta ja kafin ta ce" Allah ya kyauta! ai na d'auka gidan marayu ki ka je ki ka d'auko mana jaraba! domin dai duk shege ne a gidan."

Gabana ya fad'i da jin abinda ta ce. ina jin tsoron ta san asalin yarinyar ban san wane irin tashin hankali ne zai faru ba.

Na yi namijin 'kokarin fadin." A'a Hajiya ba duka suke shegu ba, don Allah ka da kiyi wa al'amarin mummunar fahimta, domin wasu kaddara ce take kai su gidan, kuma shegen da ki ke magana a kai ai yana da uba, domin dai mace ita kadai bata iya haihuwa, kuma dukkansu Allah ya kaddara hallitarsu ta wannan hanyar.

Uffan ba ta ce mini ba, sai mummunan tsaki da ta ja min ta kama hanya ta fita.

Ajiyar zuciya na sauke tare da shiga band'akin da tunanin abinda zai je ya dawo.

A gurguje na yi wankan na fito, dalilin kukan da yarinyar take tsalawa, dama kwana biyu abinda ke damunta kenan koke-koke! rashin kwanciyar hankali ya sa ba mu kaita asibiti an dubata ba.

Walida na tsaye da ita a kafadarta tana jijjigata ta ce." Anti anya ba wani abun ne yake damun yarinyar nan ba, ina kokarin sanya rigata na ce." Na fi tunanin cikinta ne ya kumbura tunda kinga tunda aka haifeta ba ta yi kashi ba, tun bayan wanda suke a ranar da aka haife su''

Cike da alhini ta ce."To anti yanzu ya za a yi?"

Hannu nasa na kar'be ta da cewa; Kada ki damu in sha Allah likita zai zo har gida ya duba ta, ke dai je ki yi wanka ki d'auro alwala ki fito.

Ta amsa da ''To" ta ta shi ta nufi band'akin!

Iskar bakina na dinga hura mata a kunne har Allah ya sa tayi shiru jikinta ya saki alamun baccin ya dau'keta, a hankali na kwantar da ita. na hau kan dadduma na gabatar da sallah.


Sai da ta idar da sallah tukkuna na kalleta da fadin."Kina jin yunwa ko Walida?"

Murmushi ta yi da cewa" Ba sosai ba, amma Anti ina da tambaya idan babu matsala."

Ido na tsira mata ina sauraranta.
Ta ce" Da alama ba kya jin dadin zama da mutanan gidan nan, duba da irin kallon banza da su kai mana, maganganun da matar nan ta yi, sun tsaya min a rai."

Murmushi na yi na ce" Walida al'amarin sai dai addua kawai, amma na ajiye abinda yake faruwa a matsayin ibada, kin san shi aure hakuri ya fi rinjaye, ke ma ina so ki kawar da kanki a kan dukkanin abinda za ki ga yana faruwa a gidan nan."

A sanyaye ta ce" Shikkenan Anti Allah ya ba ki hakurin da juria." na amsa da "ameen" kafin mu sauka kasan domin nu na mata masaukinta

Akwatin kayanta na
can a jiye a bakin kofa! na ce." Ki dauko kayan ki biyo ni."
Dakin dake kusa da Shukura na nufa. da mukkuli a jikin kofar ina murzawa ya bude, muka shiga tare, komai a akwai a dakin, sai dai ya yi datti! yana bukatar gyara, na ce'' Ki gyara abinda ya sawwaka idan ya so da safe sai ki 'karasa. amma ki fito min da kayan Nanah dake cikin akwatinki."
Ta ce"To shikkenan Anti." fita na yi daga d'akin cike da tunani a cikin raina.

To a daran na tura masa text na bayanin duk abinda yake faruwa, na ba shi tabbacin cewa mun dawo gida amma yarinyar tana bukatar ganin likita.

Washe gari da sassafe sai ga likita mace ta zo. na sauk'a kasa da yarinyar a hannuna na shiryata tsaf! muka gaisa da juna, ta kar'be ta na dubata, nan na yi mata duk bayanin da ya dace.
Ta ce." Watakila madarar da ake bata ce bata kar'be ta ba, amma za a sauya mata wata in sha Allahu. sannan akwai magunguna da za a dinga bata za su taimaka mata."
Na ce" Na gode sosai 'yar uwa. yanzu za ku je da Sule sai ki hada masa duk abinda ya dace."
Ta ce"To shikkenan hakan ya yi Allah ya bata lafiya."
Cike da kulawa na amsa da "Amen."

To cikin ikon Allah yarinyar ta samu lafiya sakamakon madarar da aka sauya mata da kuma magungunan da nake bata a kan ka'ida, ta dai na kuka yini take tana bacci, sai dare ya yi ta hana ni yin nawa, k'arshe k'asa na sauko na tare a masaukin Walida muna renon tare.
Wani lokacin kuma Baba Marka ta kan taimaka mana domin idan ta kammala ayyukanta, yini yarinyar take a bayanta, a lokacin muke samun dama rama bashin baccin da muka tara.
Hajiya kuwa kallonmu kawai take duk d'auki ba dad'in dake faruwa ci kanku ba ta ce ba.

Cikin wannan halin
Hajiya Fatima ta dira a gidan, tun bayan abubuwan da suka faru ba ta sake zuwa gidan ba sai wannan lokacin. sama-sama muka gaisa, sai dai gani na, ina hidima da jaririya ya sanya ta dinga yi min wani irin kallo wanda sai da na sha jinin jikina, kuma na tabbatar da cewa; sai wani abu ya faru na tashin hankali.


128&129
Aikuwa dai ina fitowa daga kicin na riske su suna mayar da yanda akayi gani na ya sanya Hajiya
cewa" Shahida ashe wannan yarinyar ta hannunki shegiya ce shine ki ka d'auko najasa ki ka kawo mana gida?"

Na ce" Lallai duk wanda ya fad'a miki wannan magana ya cika ma'karyaci."
Na fad'i hakan ne saboda Fatima domin ina da tabbacin ita ta zo da maganar, tunda ta tura k'awarta ne domin ta d'auko mata rahoto!

Kallona ta yi da cewa'' Ke kada ki mayar da mutane shashashai mana, ko kin d'auka ba mu da labarin abinda ke faruwa? idan Hajiya ba ta san komai ba, to ni a tafin hannuna ki ke?''

Na ce." Oh! shiyasa ki ka tura 'kawarki mai suffar karuwai."

Kallona ta yi kafin ta yi murmushi da cewa" Hajiya Zaliha dai ba ta ta'ba ajiye d'an shege ba ballanatana ki goranta mata, tsiya da fasadi ya tattara a zuriarku masu mugun abun fad'a."
Karaf a kunnan Walida Fatima ta kai karshen maganarta, dama can Walida ba kanwar lasa ba ce, jin irin cin mutuncin da Fatima ke yi ya sanya ta dakatar da ita ta hanyar fad'in" Ga ki nan karuwa! mai bilitin da suffar 'yan wuta!"
Shukura ta zabura! ta mike tsaye tana d'urawa Walida ashar da fadin"Lallai yau sai ta bar gidan."

Na ce" Walida kada ki sake wata magana ki k'yalesu koma meye dai ba zan mayar da yarinya ba tunda gidan mijina ne da kuma amincewarsa komai ya ke faruwa."

Hajiya ta ce" Aikuwa ni zan bar miki gidan. domin kuwa ba zan zauna da najasa a gida d'aya ba."

Shiru na yi mata ban ce uffan ba, na ja hannun Walida muka shiga daki.

Na ce" Walida wallahi akan wannan yarinyar zan iya barin gidan nan, bari maigidan ya dawo na ga ji da wannan masifar."

Cike da alhini ta ce" Anti gaskiya mutanan nan sun matsanta miki da yawa, ke da gidanki sun zo suna takura miki mussaman waccer tsohuwar wallahi na tsaneta.

Na ce" Walida ki bari kawai! ni kadai na san irin takaicin da nake k:unsa a gidan nan, amma Allah zai yi min maganinsu.''

Ta ce" Shiyasa fa wasu basa son auran masu kud'i saboda gudun matsala irin wannan, ga dai jin dadin amma babu kwanciyar hankali."

"Ni ba ni da matsala da mijina domin yana sona mutu'ka, matsalar kakarsa ne da tsohuwar matarsa sune suka addabi rayuwata.'

Ta ce" Anti ki yi hakuri amma ki tsananta da addua in sha Allahu. komai zan wuce."


To a can falo kuwa Hajiya ta sa a kira mata maigidan a waya. ta rushe da kuka da cewa" Babu shakka Alhaji Habu ka kalalace, yanzu a ce da goyon bayanka matarka ta d'auko najasa ta kawo mana gida, to wallahi zan tattara kayana na bar maka gidanka muddin ba za ka d'auki mataki ba.

Sai ya kasa gane inda maganarta ta dosa ya ce." Hajiya wace irin najasa kuma? don Allah ki yi hakuri kina sasautawa yarinyar nan, abinda ke faruwa a tsakaninku baya yi min dadi."

Ta ce" Dama ai da gadara take fad'in gidanta ne kuma miji na ta ne, sai yanda ta yi, to ai babu lefi tunda kai ka bada goyon baya kuma baka hango kuskure hakan ba, zan tattara kaya na bar maka gidanka tunda dai haka ku ke so.

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce." Ki yi hakuri in sha Allahi gobe i war haka ina gida sai mu tattauna maganar."

Ta ce." To shikkenan Allah ya kawo ka lafiya."

Wayarsa ya kashe yana girgiza kansa, ya rasa abinda yake damun Hajiya, dama bahaushe ya ce." Idan ka shekara ba ka ga mutum ba, to duk lokacin da ku ka had'u ka tambaye shi halinsa, a lokacin zamansa da Zinaru har tausaya Hajiyan yake, amma da yake

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login