Showing 78001 words to 81000 words out of 124287 words

Chapter 27 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16693

ba dutse ka ajiye a gidanka ba ko?"

Shuru nayi tare da tsira mata ido! ta cigaba da cewa" Tsayin sati hudu da kwanaki baka kula ni ballantana ka bani hakkina na aure, to gaskiya ni dai wallahi na gaji, idan ba zaka iya ba ka sake ni na fita na samu wanda zai d'ebi min kewa"

Zama nayi ina fuskantarta na ce" Zinaru lafiya ta ki ke bu'kata ko?"

"Ban gane ba?" tafad'a tana ta'be baki.

Na ce" Kwanana nawa a kwance ina jinyya wanda kece sanadi amma baki duba ni ba, ballanatana kiyi min sannu, yanzu Allah ya bani lafiya kin zo kina min wata maganar banza.

Shuru tayi tare da sunkuyar da kanta.

Na ce" Kin yi min abubuwa masu muni! amma na ajiye su a gefe ba don komai ba, sai don ina duba wani abu, kada ki dauka kin fi k'arfi na, ko kuma tsoro ya hana ni, d'aukar mataki a kanki, ko d'aya, ina da yanda zanyi dake wallahi ina duba wani abu ne amma da ba don haka ba, zaki san asalin waye Saddi'ku"


"Ka ga nifa ban nemi wata magana ba, ni fa dole akayi min na aureka amma wallahi na fi jin dad'in zama a haka, idan namiji nake bu'kata akwai su kala-kala sai wanda nayi ra'ayi.

Cike da takaici nake kallonta kafin na ce" Ki ji tsoron Allah wallahi, kuma ki bi duniya a sannu idan ba haka ba zaki yi nadama a rayuwarki, menene abin tunk'aho gurin aikata zina? menene abin burgewa? da har ki ke tutiya da aikata alfasha! kina ta 'kama da kyau! da surar jiki ko? to ki sa ni lokaci guda ubangiji na iya juya hallitarki, ki zama abar tsoro abar 'kyama, a gurin mazan dake bibiyarki, su guje ki, babu abun burgewa a gurin aikata abinda Allah ya haramta don haka wallahi kiyi hattara"

Lokacin jikinta yayi sanyi, da alama nasiha ta, ta ratsa mata jiki.

Na cigaba da cewa" Kada ki sake kiran Shukura da shegiya domin yin hakan, zai sa ni dake mu sa kafar wando d'aya domin ita kad'ai gare ni, kuma ni ne ubanta.

Ta ce" To ai nima 'kawata ce ta fad'a min cewa; sun zauna d'aki d'aya da Fatiman a saudia kuma ta tabbatar min da cewa Fatiman 'yar iska ce tana bin maza."

Takaici ya cika min zuciyata, na ce" To 'karya take miki, lokacin dana rabu da Fatima tana tare da ciki na, idan kin duba sosai za ki ga kama a tsakanina da Shukura don haka kada na sake jin wannan maganar ta fito daga bakin ki."

Ta ce" To na ji ni dai gaskiya idan kana so mu samu zaman lafiya ka cigaba da bani hakkina, domin shine dalilin da yasa zuciyata take zafi wani lokacin.

Na ce"Babu damuwa in dai wannan ne, zanyi kokarin sauke hakkinki da yake kaina." lokaci 'kan'kani ta saki fuskarta har tana bani labarai, ni dai jin ta kawai nake cikin zuciyata nake mamakin halayenta, wani sa'in ina gazgata maganar d'an uwanta, lallai tana da matsalar mutanan 'boye!


*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*

82&83
Haka na cigaba da zama da Zinaru da dad'i ba dad'i nake ha'kuri da halayen ta ina kawar da kaina gudun 'bacin rai da rikice domin duk ranar dana dau'ki mataki akan rashin arzi'kin da take a gidan, iskokai! take tayarwa ta yini ta nayi wani sa'in har kwana take tana buge-buge da birgima! duk abinda ya zo hannunta d'auka take ta kai min duka dashi!Zinaru ta yi min rauni a jikina wanda ba zai lissafu ba, damuwa da fargaba gami da tashin hankali yasa ciwona ya ke tashi akai-aikai, wanda kusan duk sati sai na ga likita ya duba ni tare da bani shawarwari! wasu al'amuran nawa duk sun tsaya sakamakon masifar da nake ciki, gashi a lokacin Allah ya bud'e min 'kofafin samu ta ko'ina, bayan kamfanin shinkafa da Alhaji Harazimi ya bani kyautarsa, cikin hukuncin Allah na bud'e wani kamfanin amma na sumunti, sai gonaki uku da na saya nake noma wake da alkama da kuma gero, harkoki na sun bud'e sosai! kuma ina samun alheri fiye da tunaninki, a lokacin abokina Alhaji Faruk yake tsokana ta da fad'in "Zinaru ita ce matar arziki na taurarinmu sun zo d'aya, wai tunda na aure ta nake samun d'aukaka da cigaba, murmushi kawai nayi a lokacin na tabbatar masa da cewa; ni ban yarda da wannan hasashen ba, na fi yarda da cewa; Ubangiji ne kawai yake saukar da ikonsa akaina, domin shi yake bayar wa, kuma shi yake hana wa, sai kuma tasirin addu'ar iyaye na dake bibiyar rayuwarta.

Hajiya na mutu'kar ha'kurin zama da Zinaru domin rashin kunya take mata sosai! bata shakkar zaginta a ko'ina, ga gori kala-kala! duk ranar da Shukura tayi gangancin mayar mata da martani, to babu zaman lafiya a gidan, domin dukan tsiya take mata har sai ta fitar da mata da jini, 'karfi ne da ita sosai! wanda na tabbata da cewa; aljanun da take tare da ita ne suke tunzurata aikata munanan ayyuka! domin wasu lokutan na sha farkawa daga bacci na ganta a tsaye a kaina da wu'ka! sai nayi namijin 'ko'kari! nake fita daga dakin, wannan dalilin ya sa na daina kwana a d'akinta, sai dai duk ranar da take da wata bu'kata sai kawo kanta d'aki na.


Ranar Asabar ban fita ba saboda ba na jin dadi, cikin baccin da nake na dinga jin hayaniya! a firgice! na tashi zaune, ina kiran sunan Allah. can na ji muryarta tana d'urawa Hajiya zagi! rai na a 'bace! na tashi na fita sai na same ta tsaye a kan Hajiyan tana nu na ta da yatsa sai rashin mutunci take mata, Hajiyan kanta a sunkuye sai share hawaye take, raina ya 'baci mutuk'a! mari na tsinka mata tare da yin ball da ita gurin! Hajiya ta rirri'ke ni tana bani hak'uri! ina sake kai mata duka da 'kafata! ji nake kamar na fashe da kuka saboda ba'kin ciki, tabbas auran Zinaru bai 'kare ni da komai ba sai tozarci!

kai na tayo tana kuka ta ci kwalar riga ta ta dinga zagi na tana kuka wai dole sai na sake ta, ko kuma ta kashe ni.

Nayi-nayi na k'wace! daga hannunta na kasa saboda ri'kon kamar ba nata ba, zagi na take ta uwa ta uba, bakinta duk ya tara wata irin kumfa! a lokacin na tsorata! sosai sai kawai na dinga karanta mata ayatul-kursiyu ina tofa mata a fuska! hakan yasa ta sassaura ri'kon da tayi min, na finkice! da sauri na nufi d'aki na.

Kafin nayi wani yun'kuri! ta shigo dakin, ta buga 'kofar da k'arfi ta rufe! tayo kaina! da kokawa sosai ta kama ni! mu dinga bi kusurwa-kusurwa da ita, nayi mamakin 'karfinta dan ban samu galaba a kanta ba, da 'kyar! na samu na rarrashe ta na ce ta zauna muyi magana ta fahimta, ta ce itafa ba zata zauna ba sai na rubuta mata takardar saki. na ce ni ba zan sake ta ba har abada domin al'kawari nayi wa d'an uwanta. nan ta tabbatar min da cewa; wallahi sai ta kashe ni mutu'kar ban rabu da ita ba. jin haka sai jikina yayi sanyi na kalle ta tare da fad'in" Zaki iya kashe ni Zinaru? ta ce" 'Kwarai kuwa mutukar baka rubuta min takardar saki ba. na ce to shikkenan kiyi hakuri zanyi shawara ki bani kwana biyu. jin haka yasa ta sakar min wuyan riga ta fita daga d'akin tana numfarfashi!

Kwana nayi ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin nayi wa tufkar hanci, tabbas Zinaru tana iya kashe ni tunda ta furta to hakan yake a zuciyarta, maslaha kawai na samu d'an uwanta da maganar domin mu tattauna.

Alhaji Harazimi bai yi mamakin jin haka daga gare ni ba, ya ce." Abinda ya fi haka Zinaru za ta aikata, shiyasa na ce maka wasu lokotan ba ita take aikatawa wasu abubuwan ba, mutanan da suke tare da ita ne, amma ina 'kara neman alfarma a gurinka, wannan ita ce ta 'karshe idan abin ya ci tura to na baka wu'ka da nama ka sake ta domin ba zan bari ta cutar da kai ba.

Na ce" Alhaji wace alfarma ce wannan?" Ya ce" Za mu d'auko malamai su yi mata ru'kiya idan Allah yasa an dace iskokin sun rabu da ita shikkenan, domin dana ta'ba tuntu'bar wani malami da maganar, nan yake tabbatar min da cewa; iskokin da suke tare da ita da wuya su rabu da ita saboda na gado ne, wallahi tun daga lokacin jikina yayi sanyi, domin ba zan manta ba, Mahaifiyarmu ma haka tayi ta fama dasu a lokotan baya, don dai ita tana da rik'o da addini ne shiyasa basa wahalar da ita sosai.

Ajiyar zuciya na sauke na ce"Shikkenan Alhaji yanda ka ce hakan za 'ayi ina rokon Allah yasa ayi asa'a, domin ni kaina ina tausaya mata wallahi, gabad'aya daga ni har ita muna cikin tashin hankali da damuwa."


To malamai uku ne suka rufu a kan Zinaru suna ta karatu har sai da suka sauke al'kur'ani mai girma kana suka fara karatun ru'kiya! a lokacin bacci ne ya kwashe ta wanda ta d'auki tsayin kwana uku ta nayi, domin ni har na tsorata da al'amarin, sai da na kira d'aya daga cikin malaman ya kwantar min da hankali, tare da fad'in" Insha Allahu za ta tashi.

Washe gari kwana hud'u kenan, ta tashi idonta cike da kwansa! fuskarta duk ta zurma! gabad'aya ta fita daga hayyacinta, sosai ta bani tausayi don da kaina na had'a mata ruwan wanka na ri'ke hannunta muka shiga band'akin tare na taimaka mata tayi wankan.

Kwanciya tayi kan gado bayan ta shirya jikinta tayi lamo! tare da tsirawa rufin d'akin ido, na ce" Kina jin yunwa ko?" kai ta d'aga min alamar Eh, na fita da sauri, na umarci Shukura ta shirya abinci ta kai mata, tare suka shiga da Hajiya suka duba jikinta kafin su fito jikinsu duk a sanyaye! domin duk wanda ya ga Zinaru a lokacin sai ya tausaya mata duba da yanda hallitun ta suka sauya.

Sati biyu da faruwar al'amarin. ta warware sosai! kuma muna zaman lafiya domin wata hatsaniya bata sake faruwa ba, tsakaninta da Hajiya ma babu wata matsala. hakan ya sa hankali na ya kwanta, sosai na dinga godewa Allah. na cigaba da gudanar da harkokina na yau da gobe.

Ranar talata ya kama kwana ashirin da biyar da yi mata Ru'kiyar muka nema ta muka rasa a gidan. hankali na a tashe na kira wayarta ina tambayarta. kai tsaye ta ce min ta na Swaziland ('kasar waje) gabana na fad'uwa na ce" Me ki ka je yi a can?" Ta ce" Aure za tayi tare da tsohon saurayinta wanda yake aiki a can.'' wani kuttun! bakin ciki ya tokare min a wuya, na ce "Zinaru da aure na za ki auri wani?" ta ce" Eh man, yanzu ai ka sake ni don dole! bana k'aunarka munafiki macuci kawai."

Kashe wayar nayi sai kwai na zube a gurin tare da dafe kaina. "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! ka kawai na kira, har na samu sassauci! na dauki waya na kira d'an uwanta na sheda masa halin da ake ciki. cikin 'bacin rai ya ce." Saddiku yanzu na tabbatar da cewa; idan da akwai iska a tare da Zinaru, to akwai hali, wallahi nayi iyakar bakin 'ko'kari na don haka na gaji, na gode sosai da alfarmar da kayi min, saboda haka ka rubuta takardar sakin yarinyar nan ka aiko min da ita, dama ni ne na tilas taka auranta duk da na san da cewa; ba ta dace da kamilin mutum irinka ba, wallahi don ka saki Zinaru hakan ba zai yi min ciwo ba."

Cike da tausayinsa cikin raina, na ce" Alhaji kayi hakuri don Allah kada kasa damuwa a cikin ranka har wani ciwo ya kama ka, hakika ina tausaya maka wannan jarabawa da Allah ya dora mana, sannan kuma ka daina cewa; ka gaji, ka cigaba da yi mata addu'a babu abinda ya gagari Ubangiji."
Fashewa! yayi da kuka a lokacin tsabar bakin ciki ya kasa cewa komai! kawai sai ya kashe wayar ya bar ni cikin tsananin damuwa!

Wannan shine abinda ya faru tsakanina da Zinaru, har Alhaji Harazimi ya rasu ban iya furta kalmar saki ga Zinaru ba, har hazar yau, saboda ina ganin idan na aikata hakan, kamar na so kaina kuma nayi rashin adalci, sosai nake k'aunar mutumin, nake kuma tausaya masa da irin jarrabawar da Allah ya d'ora masa, tunda Zinaru ta bar gari, har yau ba ta dawo ba, sai dai ina samun labari a gurin iyalin Alhaji Harazimi cewa; tana can Swaziland din tayi aure akan aure har da 'ya'ya biyu.

Bayan rabuwar mu, hankali na ya kwanta na cigaba da bun'kasa harkokin kasuwanci na, cikin ikon Allah nayi suna a 'kasata da duniya, yanzu haka ina da gidajen mai biyar, tare da kamfanoni da dama, sannan ina harkar sufari ina da jirage uku tare da manyan motoci na daukar kaya, alhamdulillhi, Ubangiji ya azurta ni, da dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba, kuma daidai gwargwado ina 'kokarin ganin na sauke hakkin Allah dake kaina, domi duk wanda Ubangiji ya bashi dukiya kamar ya d'ora masa babban nauyi ne, wanda dole sai yayi takatsantsan! ina kokarin ganin na taimaki 'yan uwa da abokanan arziki tare da jama'ar gari da duk wani ma'bukaci.

Wannan shine abinda ya faru, shine kuma dalilin da yasa na shirya shiga cikin unguwanni domin neman matar aure, na kuma sauya kammani na zuwa mahaukaci, don kin san a wannan zamanin ba kowace mace ce zata yarda ta auri garma-garma! (mai ta'bin hankali) irina ba, tun lokacin da na fara ganinki na ji kin kwanta min a raina, sai a ka ci sa'a kema kina tausaya min, tun daga lokacin na sanya ki, a raina nake addu'a akan Allah ya tabbatar min dake a matsayin matata, domin ni lalurar ki, sam bata dame ni ba, abubuwa da yawa suka ja hankali na a kan ki, saboda haka ki kwantar da hankali, insha Allah zan nuna miki soyayya fiye da wacce ki ke tunanin mahaukacin nan zai yi miki.'' Ya 'kare maganar da lallausan murmushi a kwance a fuskarsa.

Kallon sa kawai nake ina mamakin yanda ya sha gwagwarmaya, zahirin gaskiya ba shi da laifi don ya aikata hakan, domin neman matar aure, na farko wata macen za ta aure shi ne saboda dukiyarsa, mafi akasari abinda yake faruwa kenan, auran kud'i! amma yanzu da yayi hakan ya tabbatar da son gaskiya, kuma yayi abinda duk 'kwa'kwar mutum ba zai gane ba.

Hannuwa na ya ri'ke tare da sassauta murya ya ce." Kin yi shiru ba ki ce komai ba.

Murmushin ya'ke nayi na ce." Ni kam ba ni da abinda cewa domin har yanzu ina kokwanto akan ka."

Shiru yayi na minti uku kafin ya kalle ni da fad'in"Ta shi mu je na nuna miki wani abu wanda zai sake tabbatar miki da gaskiya ta."

Ban yi jayayya da shi ba, na tashi kamar yanda ya umarce ni, sai ya ri'ke hannuna muka fita harabar gidan...


*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*


_THE UNKNOWN RICH MAN_
84&85
Ni dai bin sa nake duk in da ya ajiye 'kafarsa nan nake ajiye tawa, har muka isa wata 'kofa dake wani d'an korido, tsoro na ji ganin gurin yayi duhu da yawa! na ja na tsaya ina 'kokarin cire hannuna dake cikin nasa. a nutse ya kalle ni da fad'in" Menene?" na ce" Wannan d'akin fa?" murmushi yayi kafin ya ce." 'Dakina ne, da nake ajiye muhimman abubuwa, kada ki ji komai ba zan cutar dake ba."

Nayi shiru ina kallonsa tare da tunanin wani abu a cikin raina. na ji mutane na fad'in yawanci masu kud'in da sukayi shura a duniya suna da wani 'boyayyan sirri wanda suke aikatawa na sa'bon Allah! haka kawai zuciya bata amince da shi ba, duba da yanayin gurin da ya kawo ni, wani irin d'aki a cikin ciyayi! da wata doguwar 'kofa zururu! gabana na fad'uwa! na ce" Ni dai ba zan shiga ba."

Kallona yayi da mamaki a tare da shi ya ce." Saboda me? ko har yanzu ba ki amince da ni ba?"

Baki na ta'be da fad'in" A'a kawai ina zargin d'akin ne watak'ila ba abin arzi'ki ne a ciki ba"

Yanayinsa ne ya sauya don na fad'in

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login