Showing 105001 words to 108000 words out of 124287 words
a kanta, babu irin masifar da ban shiga ba ta dalilinta, karshe ta zama sanadiyar mutuwar mahaifiyata, tabbas mutum baya kashe mutum face kwanansa bai kare ba, to amma wani yana iya zama sanadin wani, ni daku duk mun sheda cewa itace sanadin uwata dalilin zubar min da ciki da tayi ta dauka a leda taje ta dire a gabanta hakan yasa zuciyarta ta buga. babu imani bare tsoron Allah
Ta tsallake tayi tafiyarta, a lokacin Ubangiji ya nuna mata ishara! tazo min da yarinya a matsayin tawa, wanda idan naso a lokacin zan bijire na nuna rashin amincewata, tunda bani da tabbas a kanta, amma ganin yanda yarinyar take kama da ni ya sanya na cire kokwanto bayan munje asibiti an gwada jini an tabbatar min da gaskiya lamari, wannan yasa na kwantar da hankalina na kar'bi yarinyar.
Bayan haka abubuwa da yawa sun faru marasa da dadi da Fatima lokacin da take kasuwanci 'kasa-'kasa take zuwa, ta tara kudi masu nauyi ta sayi gida ta zauna ita kadai a ciki, wannan ya janyo ce-ce ku-ce na jama'a a kanta da yawa wasu na zarginta da harkokin banza, hankalina ya tashi da labari ya sameni, Hajiya tayi min maganar domin itama tana tsoron 'bacin suna a duniya, da kaina na sameta da maganar cewa; ta rufe gidan nan, amma ban hana ta kasuwancin taba, sai dai a duk lokacin da ta dawo yawonta ta sauka a gidana domin hakan shine rufin asirinta tunda taki aure, nayi hakan ne domin zumunci da kare mutuncinmu bakid'aya, sai kuma ta samu hanyar lalata min zamantakewar gida, ta d'auki karan tsana ta d'ora a kan matata, tashin hankalin yau na gobe daban, wannan yasa na ce lallai ta fitar da miji tai aure idan ba haka ba ta fice min daga gida. wannan shine abinda na san ya faru tsakanina da ita, sannan ina kara jaddada muku cewa; ba zan iya zama da Fatima ba saboda wasu dalilai! kuyi hakuri! ba wai na'ki bin umarninku bane, bana son abinda zai biyo baya na bacin rai, Fatima ta samu miji tayi aure ni zan shige mata gaba."
Baba Audu ya ce." Hakane kana da gaskiya lamarin aure babu tursasawa! a ciki mussaman idan anyi ba a ji dad'i ba, saboda haka ni daga 'bangarena ina muku fatan alheri dukkaninku."
Fatima na kuka Shukara na kuka yayin da Baba Auta ke marairaicewa! gabad'aya ya koma kalar tausayi! ya rasa wane kalar rarrashi zai yi a mayar da 'Yarsa.
Itama Hajiya yanda na fahimta jikinta duk ya yi sanyi, ita kanta ta san idan Fatima ta sake shiga rayuwarsa a karo na biyu komai zai dagule! tunda dai har yanzu bata sauya hali ba.
Jikina ya mutu murus! don wallahi a lokacin na tausaya mata sosai ganin yanda take zubar da hawaye! ba shakka tayi nadama! kuma yana da kyau! idan mutum ya tuba a kar'bi tubansa.
Na kalleshi yana zaune fuskarsa kadaran kadahan! na ce"Duk da cewa; maganar bata shafe ni ba amma ina neman alfarma a gurinka."
Gabad'aya duk sai suka zuba min ido har ita Fatiman ni take kallo idanuwanta ya yi fululu! saboda tsabar kuka da takaici.
[1/29, 10:49 PM]
*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*
_THE UNKNOWN RICH MAN_
120&201
Idona a tsaye a kansa na ce." Idan da yuwuwar Fatima ta dawo dakinta don Allah kayi hakuri komai ya wuce a tsakaninku, babu d'an adam d'in da baya kuskure! kuma tayi nadama ta nemi afuwa yana da kyau ka yafe mata, domin Annabi SAW yana son masu hakuri, wallahi nayi alkawarin zama da ita lafiya mutu'kar zata zauna da ni tsakani da Allah to ba ni da matsala."
Falon ya yi shiru bayan gama maganata, duka suka zuba min ido, mussaman shi da gabad'aya bakinsa ya mutu, Sadiya kuwa wani irin kallo take min na rashin wayo da dubara.
Sunkuyar da kaina nayi tare da k'o'karin daidaita yanayina domin dai nima k'arfin hali nayi gurin yin wannan maganar domin na tabbatar da cewa; ba shine gaskiyar abinda yake zuciyata ba, nayi hakan ne domin na goge zargin da suke min, to ya zanyi? ina bukatar zama dasu lafiya tunda ina son mijina, dole na nemi hanyoyin da zan samu nutsuwa da zaman lafiya da 'yan uwansa, amma har ga Allah ina jin tsoron ya amince da maganata ban san iya adadin tashin hankalin da zan shiga ba.
A nasa 'bangaran kuwa gabad'aya yarinyar ta gama kashe masa jiki da kalamanta, a yanzu dai ba shi da wani furuci da zai yi wanda zai gamsar da su, tunda ta riga ta watsa masa tsakuwa a ido! sai kawai ya sauke ajiyar zuciya da fad'in" Shikkenan zan yi shawara a kan hakan, duk hukuncin dana yanke in sha Allahu zamu sake zama makamancin wannan."
Jin abinda ya ce sai farin ciki ya baibayesu mussaman Hajiya da bakinta ya kasa rufuwa albarka kawai take sanya min. Dukkaninsu
Suka kasance cikin walwala da farin ciki, Sadiya ma ta ara ta yafa ta shiga murna amma in zaka tona zuciyarta tafi kowa 'kin al'amarin, dalili ta san da cewa ba za a wanye lafiya ba.
Ni kam damuwa mai tsanani! na shiga a lokacin da na ji yayi furucin, sai na fara hasaso irin zaman da za mu yi, wasu hawaye masu zafi suka ciko idona, babu yanda zanyi shiyasa na yanke wannan hukuncin domin samun maslaha a tsakaninsu tunda naga hakan na nema ya lalata zumuncinsu, wanda ni kuma ba zan so hakan ba, kuma ina so na cigaba da zaman lafiya da Hajiyar kamar yanda muka dauko.
Bayan la'asar muka shirya tafiya bayan mun ci abinci kowa ya samu nutsuwa a tsakaninsu idan ka cire ni da shi da muke cikin damuwa, domin tun bayan da nayi masa wannan maganar ban sake ganin dariyarsa ba, kuma bai min wata magana ba, har muka shiga jirgi babu abinda ya ce min, sai dai jefi jefi idan su Hajiya suna hira na kan sanya musu baki. Amma yanda ya watsar da ni abin ya mini ciwo sosai daurewa kawai nake har muka sauka.
Ina shiga d'akin na kwanta kan gado, kukan dake cin raina ya kufce! na rufe fuskata da tafukan hannuwana ina ta risgar kuka! zuciyata na wani irin zafi!
Maganarsa na ji a kunnena na bud'e ido ina kallonsa har yanzu fuskarsa babu sassauci! ya ce." Kukan me ki keyi kuma?"
Shiru nai ban ce komai ba.
Ya ce." Kin 'bata min rai sosai wallahi, kin fi kowa sanin cewa; bani da wannan ra'ayin mai zai sanya kiyi wannan furucin a gabansu, idan ke kad'ai ce ba kya bukatar zamanki a haka sai na auri wata amma babu Fatima a cikin tsarin rayuwata a halin yanzu."
Hawaye na goge wasu na sake zuba na ce" Ya kake so nayi? dukansu fa suna min wani irin kallo tare da zargin kamar da sanya hannuna cikin faruwar al'amarin, ni kuma wallahi babu mugun nufi a zuciyata, hakika ina sonka mutuka, kuma ina da burin na zauna ni kadai babu kishiya sai dai na san hakan ba zai yuwu ba saboda tsakanin ni da kai babu wanda ya isa ya tsarawa kansa rayuwa face wacce Allah ya tsara masa, duk 'kin ka da Fatima idan akwai shauran zama a tsakaninku dole sai ta dawo gidanka, ni ban isa na hana ba, amma nayi hakan ne domin na wanke kaina a gurin iyayenka da Hajiya wacce lokaci guda ta sauya min, ta daina sakar min fuska ko na gaisheta da 'kyar take amsawa, ni kuma ina sonka tare da k'aunar zama da kai, dole kuma na nemi zaman lafiya da 'yan uwanka."
Wani irin tausayi da k'aunarta ya sake nunkuwa a zuciyarsa, tabbas yanda yarinyar ke k'aunarsa tare da sadaukar da farin cikinta a kansa, ya zama dole ya nuna mata cewa shima d'an halak ne.
Ya ce." Kiyi hakuri ki share hawayenki kuma ki cigaba da addua Allah ya za'ba min abinda yafi alheri a rayuwata, in sha Allahu kuma zan yi miki hallaci fiye da yanda ki kayi min, zaki zauna ke kad'ai kamar yanda ki ke bukata.
Hannunsa na rike da cewa" Maganar Fatiman fa?"
"Zan yi istahara a kai kada ki damu ke dai kiyi mana addua."
A sanyaye na ce" Allah yayi mana za'bi na alheri."
Ya amsa da "Ameen ya Allahu."
KANO
To an nemi Talatu an rasa a garin Kano, anyi cigiya gidajen tv da redio har yanzu ba a samu labarinta ba, 'Yan uwanta sun shiga damuwa sosai tare da 'ya'yanta, abu biyu ya damesu, dawowar Hadiza gida da cikin shege wanda ya janyo Hujaj d'in ya yi mata dukan mutuwa! har sai da ya yi mata targad'e a hannu saboda ta'ki fad'ar wanda yayi mata cikin, sai da aka tsananta mata da tijira da duka sannan ta ce ita ba zata tantance wanda ya yi mata ciki ba tunda mazan da suke nemanta suna da yawa cikinsu babu wanda zata nuna tace shine ya yi mata.
Hujaj ya kasa daure zuciyarsa kuka wurjajan! ya dinga ti'ka! domin da shi a ganinsa yarinyar ta gama keta masa rigar mutunci, duk da yana jin irin surutan da jama'a sukeyi cewa; abinda ya aikata ne ya waiwayo! amma ai shi duk yawon bariki da ya yi, bai ta'ba yin zina ba, ya san dai yana kashewa mata kudi a can baya yana d'an tattaba jikinsu, amma bai ta'ba yi wa yar wani ciki ba.
Takaicinsa shine a yanzu da duniya ta sheda tuban sa ta sanya masa rigar mutunci, tare da azurtashi da suruki nagari, wannan matsalar ta kunno masa a rayuwarsa dole da yawa mutane suyi masa wani irin kallo. bayan haka kuma duniya ta tabbatar da cewa; Talatu 'bauraniya ce! domin har gida aka zo nemanta da zummar binkice a kanta a lokacin da wani yaro ya ga lokacin da take satar tufafin mamansa da mai wanki ya shanya a baranda, wannan shine mummunan aikin da ta aikata na 'karshe ! wanda kuma yanzu bata cikin hayyancinta sakamakon abinda ta shuka ta ke girba.
Hakanan Hujaj ya yi ha'kuri da k'addara! ya kar'bi Hadiza da cikin dake jikinta wanda aka rasa waye ubansa, sai dai ya zubar da hawaye sosai! na bakin ciki tare da nadamar hada zuria da Talatu, amma yanzu ya yi sa'a matar da ya aura mutuniyar kirki ce, kuma tana da ilimin addini, itace take tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, kuma ta bashi shawarar dawo da yaran gabansa, sannan kuma tayi alkawarin rike su da amana, domin dai d'a duka na kowa ne.
To wannan shine dalilin da yasa su Hadizan suka dawo gaban mahaifinsu da zama, kuma Murja matar Hujaj din dai-dai gwargwado tana iyakar bakin 'ko'karinta a kan su mussaman Hadiza dake d'auke da juna biyu.
Ba a tashi ganin Talatu ba sai a Damaturu, cikin wani k'auye lokacin duk ta fice daga hayyacinta, don an samu wasu 'bata garin ma sun kwanta da ita ba'a adadi! gabanta sai ciwo yake mata yana zubar da wani irin ruwa mai wari! domin ko lokacin daka d'aukota haukata take tu'kuru! tana soshe-soshe! jiddin hannunta a gabanta tana karta! cikin surutan da take na hauka ta dinga tonawa kanta asiri kan abubuwan da ta aikata tun daga kan Mariya har zuwa kan 'yarta data tafi ta bari.
Kai tsaye gidan mahaukata aka nufa da ita domin bata taimakon gaggawa!
****
ABUJA
Sati biyu da faruwar al'amarin, zamantakewar gidan tayi kyau! dalili Hajiya da Shukura duk sun kwantar da hankalinsu sakamakon furucin da nayi akan dawowar Fatima gidan, sun saki jikinsu sosai! muna mu'amular arziki, Sosai Shukura take bani girma, wanda hakan yake faranta min rai mutuka.
Bangaran mijina ma sai godiyar Allah zama muke na mutunci da girmama juna, idan soyayya ta zo muyi kamar zamu cinye junanmu, yawan shekarunsa bai sanya ya tauye kansa ba, abubuwan da yake min na soyayya har mamaki nake! lallai na yarda da cewa; dattijai sun fi iya kula da mace da tarairaya ba kamar matasa irin na yanzu ba, sosai muka samu fahimtar juna, kuma muna kokarin kyautata kanmu ta hanyoyi da yawa, mussaman ni da na riga na fahimci abinda yake so, sai na rike hakan hannu biyu, na kuma sanya juria a cikin raina, amma duk da haka ban zauna ba, ina 'ko'karin gyara jikina da sha da kuma cin abubuwan da zasu saukar min da ni'ima duk domin ya samu yanda yake so idan bu'katarsa ta tashi.
Hankali ya kwanta sosai! wata irin ki'ba nake narkawa ta 'kasa, nono na ya ciko sosai ya 'kara girma! kwankwasona ya bud'e! da yawa duk kayan da nake sanyawa sunyi min kad'an, sai wasu aka din'ka, ga wani irin haske da nayi fatata tayi kyau! ainun! lokacin sai ka rantse da Allah cewa; Yaron ciki ne da ni duba da yanda suffofina suka sauya ta ko'ina.
Shi kansa mai-gidan tsokanata yake wai na zama 'yar lukuta! ko dai na samu ciki ne nake 'boye masa! dariya kawai na kan yi a duk lokacin da ya yi irin wannan maganar sai na ce" Sai na fi kowa farin cikin samun ciki a yanzu kuma in sha Allah da 'yan tagwaye zan fara."
Kalamai na suna faranta masa rai mutu'ka! addua yake tare da burin tabbatuwar furucin bakina.
Watana biyar a gidan 'yan uwana suka zo kaf! Baba Asabe da tawagarta Babana ma tare da 'yan uwansa maza da mata. sosai na yi farin cikin ganinsu, kuma sun samu tar'ba mai kyau daga gurin mai-gidan, don lokaci guda ya ware ya zauna tare dasu suka gaisa cikin girmamawa, hakan ya faranta min rai sosai yanda ya karrama dangina itama Hajiya bata nuna wani abu ba yabo na ta dinga yi a gabansu tana fad'in alheri na.
Baba Asabe ta dinga jin dad'i tana kallona na san mamaki take ganin yanda gabad'aya na sauya bakinta ya'ki rufuwa duk inda na gifta sai ta bini da kallo. shi kansa Babanmu na lura da yanda yake kallona sa'i da lokaci sai dai yayi murmushi ya girgiza kansa.
Saliha kuwa har sai da na gaji na tambayata kallon me take min, domin tamkar tv na zama a gurinta, ajiyar zuciya kawai ta sauke ba tace min komai ba ta d'auke kanta, sai kawai nayi murmushi cikin zuciyata na ce Saliha kenan har yanzu hali yana nan, dama can haka take min ko yaya na samu cigaba a rayuwata sai naga wani canji a tare da ita, ban san abinda yake damunta ba.
Na ce." Baba ban ga Talatu da Hadiza ba me yasa basu zo ba?"
Jamila ce ta kalle ni sai naga idonta ya ciko da ruwan hawaye!
Jikina ya yi sanyi na dafa kafadarta da fadin." Menene?"
Sai kawai ta fashe da kuka tare da rungume ni!
Nima nan take na ji hawaye ya ciko idona!
Na kalleshi da cewa; Allah yasa lafiya?"
Shiru ya yi yana girgiza kansa.
"Anti Murja matarsa ta ce" Sai hakuri da rayuwa! kaddara kuma bata wuce kan kowa ba."
A sanyaye na ce"Anti Murja me ya faru? ko mutuwa su kayi ?"
Ta ce" Duk suna raye sai dai suna cikin wani hali wanda addua ita kad'ai ce magani."
Hawaye suka zubo min. na ce"Rayuwa kenan! Ubangiji Allah yasa muyi kyakykyawan karshe yanda yanayin ku ya nuna tabbas al'amarin babu dad'i, amma duk rashin dad'insa ina da bukatar na sani ko da taimakon da zanyi a kan hakan."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya warware min duk abinda ya faru! gabad'aya kasa daurewa nayi hawaye masu tsananin zafi suka shiga sauka a fuskata, na gagara! cewa komai tsabar yanda nake jin wani irin takaici a cikin raina
Hannu nasa na share hawayen fuska da cewa; Allah ya bata lafiya, ita kuma Hadiza Allah ya sauketa lafiya, amma hakika na tausaya mu su sosai! Allah yasa mu fi karfin zuciyoyinmu."
Gabad'aya suka amsa da "Ameen ameen. Duk cikin alhini da damuwa!
Kwanansu biyu suka shirya tafiya, shatara ta arziki mai-gidan ya yi musu, sannan ya yi musu kyautar kujerar Hajji su Uku Babana Baba Asabe da Anti Murja! To basu ba ni kaina sai da na taya su godiya, sai ya nuna babu wannan a tsakaninmu, duk abinda ya yi min riba ce a gurinsa ba fad'uwa ba.
Da zasu tafi nayi Wa Saliha da su Jamila kyautar zannuwa da mayafai tare da kayan kwalliya da turaruka masu tsada! duk abinda na san zai faranta musu rai! sai da na d'auka na ba su, muka rabu cike da kewar juna! sai da suka shiga mota sannan kuma zuciyata tayi rauni! kuka ne yake so ya 'kwace min ina hana shi, amma ban samu nasara ba, motar tana fita daga gidan, nasa hannu na rufe fuskata da sauri na juya domin komawa cikin gidan, ya rungumo ni jikinsa yana rarrashina sai kawai na fashe da kuka! tare da kwanciya a jikinsa a haka muka shiga falon, duk ya rasa yanda zai
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download