Showing 48001 words to 51000 words out of 124287 words

Chapter 17 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16705

yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa.


Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita!

Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua.

'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana.


Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci.

*Littafi na daya yana daf da 'karewa, ina fatan masoya za ku goya mini baya gurin sayan littafi na biyu domin cigaba da tafiyar tare. hanyar da za a biya kudin mai sauki ce Normal group #500 Vip group posting sau biyu a rana 1k za a tura kudin ta wannan asusun. 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku tura dala dari Vip jakka daya katin airtel za ku turo min dashi ta lambata. Allah ya yassare*

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*Dubbun Godiya zuwa ga:*
*Hajiya Hadija Marad'i (Nijar) Ina godiya da abin alheri Hajjaju??????*

49&50
'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta ke yi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda su na yi.


Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya.

Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Saliha kuwa sai dariya take mata addua take a zuciyarta Allah yasa mahaukacin ya nuna mata tumasanci!


Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa domin ita Hadiza ma yawon gantali ta tafi da saurayinta.

Da magariba Hujaj ya shigo gidan; 'kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba.

A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba."

Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na."

Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam."

Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai."

'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa.

A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai."

D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya!


Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba Asabe. ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki.

Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna.

Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba.

Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa.

Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido.

Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min."

Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba.

Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye."

Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito."

Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa".

Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri.

Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki."

Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a."

Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce."

Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.''

Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki."

Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya ba mu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa.


Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta.

Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri."

Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua."

Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri."

Sosai suka rungume juna suna ta kuka!

Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba.

Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita.

****
To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta.

Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta.

Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya mutu! ta gaji sosai! sai addua take Allah ya sa su sauka lafiya! ko ta samu ta mi'ke k'afafunta!

Matar dake kusa da ita ta bata pure water "Kar'bi ruwa 'yan mata naga kamar kin gaji."

Ba ta ji maganarta ba kawai dai ta ga tana mi'ko mata ruwa.

Da sauri tasa hannu ta kar'ba ta bud'e baki za tayi magana, ya juyo daga mazauninsa wata muguwar harara ya daka mata fuskarsa a mugun had'e!

Sai tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na wani irin fad'uwa ta mayarwa da matar ruwan da sauri! jikinta sai rawa yake.

Matar ta bi ta da kallon mamaki! sai kuma ta ta'be bakinta ta ajiye ruwanta da fadin."Kin yi wa kan ki."


A galabaice suka isa abuja! yanda ta fahimta kamar tafi kowa galabaita watakila saboda rashin sabo ne.


Ya riga ta fita daga motar yana tsaye yana jiranta ta fito. a gajiye likis ta fito, nan ta ga yanda ya sa bakin gilashi a idonsa tare da rufe kansa da bakar hular sanyi. ta dan tsaya a gefansa tana bin tashar da kallo! ga rana ta k'wallare! jama'a kowa na gabatar da abinda yake gabansa.

Hannunta ya ri'ke! ya jata suka nufi wata rumfar kwano gurin wata mai sayar da abinci bayerabiya. cikin harshen turanci suka gaisa kafin ya shedawa matar cewa ga ajiyar yarinya ya kawo mata ta bata abincin da zai isheta anjima zai turo a d'auke ta, wanda zai zo ya d'auke ta sunansa Sule."

Ta Amsa da "to
kafin kalle ta da fad'in." Zo ki zauna." tana nuna mata wata kujera.

Gabanta ya dinga duka yana daka! hawaye suka ciko idonta! ita dai ba ta ji abinda suke cewa ba amma ta fahimci kamar barin ta zai yi a gurin ganin yanda matar ke kallonta tana nuna mata gurin zama.


Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai! wasu zafafan! hawaye suka kufce mata.

Saurin d'auke kansa yayi ya cire hannunsa daga nata ya kalli matar da fad'in." Tana da matsalar kunne ba sosai take ji ba."

Da kansa ya ja hannunta ya kai ta ya ajiye a kan kujera, fuska a murtuke ya ce" Zan je wani guri ne shiyasa na kawo ki anan na ajiye amma zan turo a dauke ki kada ki damu."

Bai jira tace wani abu ba yayi saurin barin gurin ko waiwayenta be yi ba.


Duk kyawun abincin bai bata sha'awa ba, gabadaya ma ba ta cikin nutsuwarta, tsoro da fargaba sunyi mata dabaibaiyi, tunani ma ta rasa wane kala za tayi, sa'i da lokaci ta ke share hawaye tana bin tashar da kallo da nazarin wace rayuwa za ta fuskanta a nan gaba.

Ekeke matar dake sayar da abincin kenan, ta kalleta a karon da ba zai lissafu ba, domin tun tana lallabata ta ci abincin har ta gaji ta zuba mata ido! sai dai haka kawai take tausaya mata idan ta tuna cewa kurma ce ba ta ji sosai, ta yi tunanin abubuwa da yawa akan yarinyar, ta tunanin mutumin yayi kawalcinta ne domin ya dinga biyan buk'atarsa!


Sai daf da magariba Sule ya je domin d'aukarta!

Ko kusa ko alama bai gane ta ba ballantana yayi tunanin wani abu, ko da yake can baya da ya je binkice lokacin da abin ya faru duhun dare ya shigo da kuma cikowa ta mutane shine dalili.

Su ka gaisa da Ekeke kafin ya sheda mata shine Sule ya zo tafiya da yarinyar."

Ta ce." To kud'in abinci dubu biyu sai kudin jira dubu uku, duk da ba taci abincin ba ita wannan ba damuwarta bane. Sule bai ja doguwar magana ba ya ciri kudinta ya bata.


Jiki a sanyaye take binsa tana ta addua a cikin zuciyarta. ba ta 'kara firgita ba sai da ta ga shirgegiyar motar da ya bude mata wai ta shiga.

Ai sai hawaye suka fara zuba kuka sosai take! tana waiwaye a gurin, ta tsorata don gani take kamar sa ce za ayi."

Yayi -yayi da ita ta shiga amma fafur! ta' ki shiga sai kuka take tana nema ta tara musu mutane a gurin.

Wayarsa ya fito da ita ya kira maigidan nasa ya sheda masa halin da ake ciki.

Ya ce ya bata wayar su yi magana.

Nan ma da kyar ta karbi wayar jikinta sai rawa yake.

Da muryar da ya aro yayi mata magana da k'arfi yanda za ta ji. "Shahida ki shiga mota Sule zai kawo ki gidan da nake aiki wato gidan maigidana kamar yanda nayi miki bayani a can baya. zamu zauna a gidan ne a wani sashe da aka ba mu, ina nan ina jiran zuwanki."

Hankalinta ya kwanta jin muryarsa, a sanyaye ta ce." To." ta mika masa wayar tana godiya a cikin ranta domin wallahi tayi tunanin Sule sace ta zai yi.

*Normal group #500 Vip group 1k via 0542382124..Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262...Mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel. Vip gruop jakka daya.*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE??*
_Akwai ingantaccan maganin???? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci????_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

51&52
Girman gidan da tsaruwarsa ya firgitata sosai, sai ta 'kara shiga rud'ani zuciyarta ta cigaba da yi mata tunane-tunane marasa kyau! wani 'bangaran na zuciyarta na nuna mata cewa Baban- Baba mutumin arziki ne ba zai cutar da ita ba.

Tafiya mai tsayi su kayi a cikin gidan domin kwalta ce a shimfid'e har sai da suka kusa kai wa karshen gidan, sannan taga yayi parking, sai ta dinga kalle-kalle a gurin, tsit! sai shuke-shuke da kukan tsintsayen dake sauka a kan ciyayi gabanta ya cigaba da fad'uwa, cikin zuciyarta take ta nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya bud'e mata 'kofar motar, alama yayi mata ta fito da hannunsa.

'Kin fitowa tayi ido jawur! take kallonsa kafin ta bud'e baki cikin yanayin maganarta tace." Ina ne nan din.?

Ya ce." Gurin da zaki zauna ne maigida ne ya ce a kawo ki nan"

Sai ta kasa fahimtar inda maganarsa ta dosa. kawai dai ta zuba masa ido tana ayyanawa abubuwa da yawa aran ta.

Cikin wayo da dubara ya ce." Ai yana ciki yana jiranki kamar yanda ya fad'a miki a waya." shima ya fadi maganar ne kawai! ba tare da ya san abinda ke faruwa ba.

Jin abinda ya ce yasa ta d'an ji 'kwari a

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login