Showing 120001 words to 123000 words out of 124287 words
kai karshen maganar.
Baba Audu ya ce." Alhaji Habu kasan irin maganar da zaka dinga furtawa wannan maganar ba ta cancanta ba.
Shiru ya yi bai ce komai ba amma gabadaya yanayinsa ya sauya da bacin rai mai tsanani!
Ita kuwa Hajiya tunaninta gabadaya ya ta'allaka gurin ganin ta nemo masa magani, domin dai ita har ta yarda da maganarsa, kuma tana so kafin ta mutu ta sake ganin wasu daga cikin 'ya'yansa, halin da su Fatima suke ciki sam bai dame ta ba.
Shiru falon ya dauka kowa zuciyarsa babu dadi mussaman Baba Auta da tunda aka zauna be ce komai ba, ransa in banda zafi babu abinda yake, watakila yana ganin bacin rai da takaicin yaron shi zai zama ajalinsa, tunda duk 'yan kadarorinsa ya daga ya sayar, duk a kokarinsa na ganin malamai da bokaye sun shawo kansa ya mayar da 'yarsa gidansa, anan yake ganin zai fanshe! abinda ya lalatar, to sai dai abin mamaki! aikin ake ana zubar da jini amma a banza domin dai kullum yaron gaba yake arzikinsa yana ha'baka, duniya tana cigaba da suturtasa da rigar arziki. wannan tunane-tunane sune suka zautar da shi, ya yi tsiru a kan kujera sai zare ido yake.
Lokacin Shukura ta tashi ta buga wani uban tsale a tsakiyarsu, ta yi zaman 'yan bori! wasu abubuwa ta shiga yi tana furzar da yawu, tasa hannu ta cire d:ankwalin kanta tana walagigi a falon.
Gaba'daya hankalinsu ya ta shi. Baba Audu ya dinga yi mata tofi! amma kamar k'ara zugata! yake ta dinga yin iskanci samfur-samfur, don har na wannan lokacin ya fi na baya, duk ta hargitsa musu tunani, Hajiya Fatima sai kuka suke sunyi cirko-cirko a tsaye!
Duk yana zaune a kan kujera yana kallon abinda ke faruwa, cikin ransa ya ce yau ko sarkin aljanu ne akan yarinyar zai sauke mata shi.
Sama ya hau ya dauko wata murtukekiyar bulala! ya nado ta a hannunsa! yana zuwa ya fara zabga mata a jiki da dukkanin k'arfinsa!
Ihu! ta tsala! a guje! ta tayi yunk'urin ta shi ya mayar da ita ya cigaba da zabga mata yana fadin." Za ka yi magana ko ba za ka yi ba." Ya fada lokacin da ya lafta mata duka a gadon baya!..
Ta zabura! jiki na makyarkyata! ta ce" Daddy kayi hakuri don Allah wayyo Allah na shiga uku "
Ya k'ara zabga mata da cewa" Shukura ce ko ba ita ba?"
Tana wani irin kuka kamar za ta shid'e ta ce" Ni ce wallahi Daddy ni ce kayi hakuri."
Bai san lokacin da ya kifa mata wani lafiyayyan mari ba, wanda gabadaya ji da ganinta suka dauke, jini ya billo ta hancinta, sai kawai ta bingire! a gurin ta fadi ta suma.
Ba tare da ya ce komai ba ya jefar da blet din ya zauna kan kujera yana wani irin numfashi.
Hajiya Fatima jikinta duk ya yi la'asar, alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita.
Hajiya tare da su Baba Audu hankalinsu bai kwanta ba sai da Shukura ta dawo hankalinta sannan. falon ya yi tsit! sai sautin kukan Shukura dake fita a hankali a hankali.
Ya kallesu da fadin." Wannan shine abinda nake fad'a muku, na tabbatar da cewa; abinda yarinyar nan tayi da sanya hannun uwarta a ciki. ni na san wacece Fatima da halayenta" Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar yana sake jin tsanar Fatima a cikin ransa.
'Bangaranta kuwa tun ba a je ko'ina ba yanayinta a nu na cewa bata da gaskiya ta yi tsamo-tsamo!
Baba Audu ya ce " Shukura don Uwanki aljanu ki ke sha'awa! da har za ki dinga burgima kina tumami! da iface-iface! ashe baki da hankli dama ?"
Hajiya ta ce" Ga babbar mara hankali nan a zaune ai tunda duk abinda yake faruwa da sanya hannunta wallahi ni kaina nayi mamakin ganin Shukura tana iskokai, tunda a gaba ta girma bata ta'ba nuna wata alama ba sai da lamarin nan ya bijiro. amma Fatima kin bani kunya wallahi. wato ashe tuban muzuru! ki kayi? ni ina ta balo'ko'ko! a mayar dake ke kuma kin shirya mugun abu "
Shukura na kuka ta ce." Wallahi duk Mommy ce ta tsara mini komai. wai saboda ta lura Daddy yana sona ta ce mu gwada wannan hanyar ko za a dace ya mayar da ita nima na san watarana dole asirin mu zai tonu."
Sai ta fara borin kunya da fad'in" Kausasan! maganganu! Baba Auta ya fitar da hannu ya tsinka mata mari! zuciyarsa na tafarfasa! ya ce." Yi mini shiru munafukar banza da hofi."
Kallonsa ta yi tana mamakin furucinsa! yau ita yake kira da munafuka bayan duk abubuwan da suke faruwa da sanya hannunsa a ciki, yanzu da ya ga ta kwa'be shine zai cire kansa, wallahi don dai ubanta ne kawai amma da sai ta tona masa asiri.
Tana share hawaye ta dauki jakarta ta bar gidan tare da yanke shawara cewa; ko maza sun kare a duniya ta bar Dangaske har abadah.
Ko da ta fita babu wanda ya bi ta kanta illah shi da suke ta bawa hakuri, ita kanta Hajiyar nadama duk ta dabaibayeta ta ce." Ni damuwa ta wannan rashin lafiyar da ka ke fama da ita, kuma watakila son kudi ya sanya ka watsar da al'amarin baka neman magani." Tsakaninta da Allah take maganar tare da mayar da hankalinta kansa.
Sai ya bagarar da maganar ta hanyar fad'in" Babu Audu ina so ku zama sheda a wannan lokacin. na yankewa yarinyar nan hukuncin fito da mijin aure a cikin sati hudu kacal. idan ba ta tsayar ba, to wallahi nayi rantsuwa da Allah zan d'aura mata aure da duk wanda na yi ra'ayi.
Baba Auta ya ce." Wannan daidai ne abinda ka yi saboda haka ke Shukura kin ji abinda mahaifinki ya fada, kiyi kokarin fito da miji kafin cikar lokacin da ya gindaya miki.
Kukanta ya 'kara tsananta! gabadaya tunanin ya ta'allaka gurin hanyar da za ta bi domin warware matsalarta. a shekarun baya tayi samari kala-kala, kuma 'ya'yan manyan mutane, amma da yake babu auran a cikin ranta ta dinga wulakantasu har suka watse, yanzu dai shawarar da ta yanke za ta dinga binsu daya bayan daya tana kiransu a waya, idan anyi da ce sun dawo sai ta tantance wanda za ta aura.
***
Sai wajen tara da rabi na dare suka dawo gidan gabadaya har da Hajiya da duk ta shiga damuwa sakamakon lalurar dake damunsa domin dai ita duk a tunaninta da gaske ya ke, ba ta san da cewa; a daran ranar ma bai d'aga 'kafa ba, sai da ya sha shagali da bired'ensa hankalinsa kwance, lafiya ce da shi sosai, kuma cikin ikon Allah sam baya shaye-shayen magungunan k'arfi irin wanda mazan yanzu suke tu'ammali.
Abun mamaki da safe da na shiga gaishe da Hajiya ta amsa a sanyaye tana sunkuyar da kanta, yanda na lura kamar ba ta so mu had'a ido. har da tambayata baby Nanah.
mamaki na ya sake k'aruwa ganin Shukura ta zube a gabana tana gaisheni muryata na rawa take fadin." Antina don Allah ki yi hakuri da abubuwan da suka faru wallahi sharrin shaid'an ne."
Murmushi kawai na yi na ce" Ai babu komai Shukura dama can ni ban ri'ke ku a raina ba, wallahi na yafe Allah yafe mana bakid'aya."
Ita da Hajiyan suka amsa da "Ameen ameen. kafin na yi musu sallama na fita da tunanin al'amarin a cikin raina.
Ashe shine ya ce." Mutukar ta na so ya shirya da ita to lallai sai ta girmamani, kuma ta daukeni a matsayin uwarta, bayan haka kuma ta nemi afuwata. dole ta bi umarninsa domin samun nutsuwa da kwanciyar hankalinta.
****
Tun bayan faruwar al'amarin wata hatsaniya ba ta sake faruwa ba, muna zaune lafiya da juna duk da cewa; gurin kowa daban, amma duk lokacin da za mu had'u cikin girma da mutunci muke rabuwa. lokacin ita Shukuran ta tsayar da miji daga cikin masu sonta har an sanya rana wata uku, uban yana ta murna dalilin yaron da za ta auran d'an babban malami. shima kuma nasaba ya duba da nagarta ubanta ya sanya ya dawo har ya saurareta suka daidaita kansu.
Kafin zuwan lokacin Hajiya Fatima ta daure aure da wani balarabe a can saudia amma ba tare ba, wai sai bayan bikin 'yar za ta tare a can saudia din.
Hankalina ya kwanta ganin uwar da 'yar za su yi nesa da ni, dama sune matsalata kuma sune matsalar mijina.
****
Wattanin Nanah goma. tayi 'kafa gudu ko'ina, ga yarinyar tubarkallah. tana burge mutane da yawa saboda kyawunta, tayi gwibibi abin sha'awa, sai dai wasu lokotan idan na kalli yarinyar na kan ji zuciyata ta karye idan na tuna hanyar da aka samar da ita, ina jin tsoro kada a samu wani mara tsoron Allah ya fayyace mata komai, bayan mu muna iyakar bakin kokarinmu gurin nuna mata cewa; mu ne iyayanta.
***
Ubangiji yana tafiyar da al'amuransa cikin nutsuwa da hikima. abu uku suna tafiya akan ma'auni guda, Aure-Mutuwa- Haihuwa. dukkaninsu suna tafiya ne da hukuncin rabbil-izzati. abinda ya faru kenan ga rayuwata. lokacin da na cire tsammanin haihuwa na rungumi kaddara, domin dai tuntuni na sanya kaina a cikin jerin wadanda Allah ya jarabta sai kuma ya azurta ni a lokacin da ban yi zato ba, ciki har ya yi wata shida ba mu san da zamansa ba, dalili dama can tun ina budurwa na kan yi tsallaken wata ban yi al'ada ba, bayan haka kuma na yi ki'ba sosai shiyasa cikin ya bi jikina, sai dai 'kasan mara ta da ya d'an kumbura, amma ban kawo komai a raina ba, domin na fi tunanin cewa ko kibar da nayi ne, amma sa'i da lokacin na kan ji kasala da kwad'ayi! da motsi jefi-jefi a cikina. nan ma sai da al'amarin ya yi tsanani tukkuna na fad'a masa halin da ake ciki.
Ya kira likitansa domin ya turo likita mace ta dubani.
Wallahi lokacin da ta gama aune-aunenta result ya fito, gabadaya ni da shi rasa bakin magana mu ka yi, kawai naga idonsa ya ciko da ruwan hawaye! kamar zai fashe da kuka yake ta zabgawa likitar godiya. ta dinga dariya tana yi mana fatan alheri, anan gurin ya yi mata kyautar sabuwar mota tare da kujerar hajji, ta fita daga gidan da kwarin gwiwa tana godewa Allah. ashe tana da rabon sauke farali kafin ta mutu.
***
Na ga gata da kulawa ta kowanne fanni, domin Hajia kusan a sashena take wuni. hidima take mini ba kadan ba, cikin zuciyata na ce" Lallai babu wanda yake iyawa da d'an adam sai wanda ya halliceshi. kuma bahaushe ya ce." Mutum tara yake bai cika goma ba.
Har gida ake zuwa a duba ni tare da yi mini duk abinda ya kamata. scanning ya nuna tagwaye ne duk maza. 'Bangaransa kuwa godiya yake ga Allah da fadin." Ko d'aya ya samu ya yi godiya. domin bai sanya a ransa cewa biyun ne ba, saboda ya san babu wanda ya san gaibu sai Allah.
Haihuwa ta zo mini cikin sauk'i! a gida na haife yara maza biyu tare da taimakon Hajiya. wacce ta rasa ina zata tsoma kanta ta ji dad'i, ganin zaratan samari a gabanta suna ta tsala ihu! alamun suna cikin k'oshin lafiya.
Yanda suke farin ciki ita da maigidan abun sai da ya so ya bani tausayi, Allah kenan mai kyautar ban mamaki! shi yake bayar da abinda kud'i ba za su iya saya ba.
Bikin suna aka shirya gagarimi. daga can 'bangarena babu wanda bai samu damar halarta ba. domin motoci maigidan ya tura aka dinga jigilar dauko mutane wanda suke da sha'awar zuwa.
Komai ya gabata cikin walwala da karamci. jama'a duk suka koma gidajensu da abubuwan arziki tare da turmin atamfa.
To sai dai rainon 'yan biyu akwai k'alubale! wannan dalilin yasa duk na susuce! na rasa yanda zan yi ciwon kai na rashin bacci ya taru yana nema ya haifar mini da matsala ga garima, gefe guda kuma matsalar maigidan ta rashin ha'kuri ta nan, sai abinda ya yi gaba, domin tunda ya lura da cewa; na fara sallah. ya ma'kale mini sam bai bari ma nayi gyare-gyare ba, haka nan yake zuwa ya sauke bu'katarsa ba tare da ya nuna wata damuwa ba, a kullum maganarsa daya ba zai ta'ba gajiya da ni ba.
Sai da yaran su ka yi k'wari tukkuna na d'auki masu raino! sannan ne fa na fara gyara kaina wai ni nan zan cigaba da gayu! aikuwa tafiyar ba ta yi wani nisa ba, wani cikin ya samu! na shiga tashin hankali mai tsanani! ganin duka-duka Hassan da Hussani watansu bakwai a duniya ya za a yi na sake wata haihuwar. kuka na dinga yi sosai! da tunanin yanda zanyi da cikin, domin ina gudun kada yaran su samu matsala. gashi maigidan baya nan ya yi tafiya.
Haka dai na yi hakuri har ya dawo ya sameni na kod'e! ido duk ya zurma! saboda fargaba da tashin hankalin hankali, babu kwalliya babu kulawar da yake samu.
Ko da ya tambayeni abinda ke faruwa? rushewa nayi da kuka! na ce" Ciki ne da ni, kuma wallahi yanda nake jin motsi sosai ya yi 'kwari! yanzu ni ban san ya zanyi ba.
Ya zuba mini ido da yanayi na damuwa a tare da shi ya ce " Shine me ? don kina da ciki."
Na ce." Ban gane ba, ai ka san dole na damu tunda yaran nan ba su yi kwari ba watansu fa bakwai."
Ya daga mini hannu da cewa" Za ki butulcewa Allah kenan?" shiru nai ina kallonsa. ya cigaba da cewa; ban za ci haka daga gurinki ba wallahi. idan duk shekara za ki dinga haihuwa abin alfahari ne a gurina, domin ita muke nema ido rufe kuma ya ba mu mai ya kamata mu yi masa?"
Jikina ya yi sanyi na ce" Ni fa bana nufin wani abu kawai ina tunanin halin da yaran nan za su shiga"
Ya ce."Allah shi yake rayawa, da ikon Allah ba za su samu wata matsala ba." A sanyaye na ce" To shikkenn amma dai idan na haihu sai mu yi tsarin iyali saboda yaran su yi 'kwari."
Ya murtuke fuskarsa yana kallona! bacin rai na hango mai tsanani a fuskarsa!
Sai na sunkuyar da kaina gabana yana fad'uwa.
Ya ja tsaki! mai tsayi ya ta shi ya fita ya bar ni a zaune da tunanin mafita.
Da 'kyar na shanyo kansa ya ha'kura! amma ya yi mini gargadi cewa kada na sake yi masa maganar tsarin iyali, idan ba haka ba, to zai auri wacce take son had'a jini da shi. jin haka yasa na daina masa maganar saboda har ga Allah bana bukatar had'a miji da wata wani mugun so nake masa mussaman yanzu da muka zama abu d'aya zuria tana yawa a tsakaninmu.
****
Da jegon yarinyata Hamida wacce taci sunnan mamansa na je kano bikin Saliha da Jamila wanda ya kasance tsiran sati daya a tsakani, shiyasa na ji dadin hakan, domin dai na riga na san da cewa idan bikin ya rabe, bai zama lallai ya bar ni na je duka ba.
Sai dai yanda na ga unguwar ta sauya ya sanya na yi mamaki sosai. gabad'aya hanyoyin da suka lalace a tsakanin bakin titin da cikin lokon gidan Baba Asabe kwalta ce a shimfid'e, wanda ni dai tunda na ta so nake ganin gurin a haka da tudu da kwari kwatoci ko'ina da bola babu kyawun gani, amma tun daga bakin titi komai ya canza gwanin ban sha'awa.
Baba Asabe ce take sheda mini cewa; duk wani cigaba da unguwar ta samu daga mijina ne, kuma duk wanda yake makotaka da ita yana cin arziki, nan take fada mini jerin mutanan da ya bawa kyautar kujerar hajji daga cikin 'yan uwata, ashe duk lokacin da ya zo garin sai ya shiga unguwar ya gaisheta.
Cikin zuciyata na ce" Zai aikata fiye da haka, domin kyauta a jinin jikinsa take, babban burinsa ya samu ya bayar ga mabu'kata.
Dubu dari-dari na bawa Saliha da Jamila gudummawa, sosai na yi musu fatan alheri tare da tabbatuwar zaman lafiya a gidajen auransu, sai da yanda na ga Talatu ta lalace! al'amarin ya ta'ba mini zuciya, wallahi 'buya na yi na ti'ki kuka na k'oshi! wato dai shi dan adam ba a gama masa hallita har sai ya mutu, lafiyayyar macace, ta koma Zautacciya, yau da lafiya gobe babu, kullum tana rufe a daki tana zage-zage! duk gashin kanta ya gwaigwaye! saboda yanda take cizgarsa, idan abin ya yi tsamari! sai a mayar da ita asibiti a cigaba da bata magani. kai jama'a mu shuka alheri don girman Allah. za mu gama da duniya lafiya.
Haka na bar garin kano cike da alhini da tunanin yanayi na rayuwa.
*****
Kallonsa na yi a lokacin da yake 'ko'karin zama a kusa da ni, wanda fitowarsa kenan daga wanka daure da towel a jikinsa.
Yanayin kallon da yake mini ya sanya jikina yin la'asar! na ce" Na shirya maka abinci yana kan tevur na san kana jin yunwa ko?"
Girgiza kansa ya yi da cewa; ba wannan yunwar na ke ji ba" ya fada tare da riko hannuna. na zura masa ido domin sake nazartarsa duk da na riga na fahimci abinda yake da akwai. na ce" dawowarka kenan fa, na san akwai gajiya da yunwa a tare da kai. ya kamata ka ci abinci ka huta sannan komai sai ya biyo baya.
Ya girgiza kansa tare da matsowa jikina ya d'auki hannuna ya d'ora gabansa da cewa; damuwar wannan ta kori komai. bana jin wata yunwa domin na ci abinci a jirgi, ya kamata ki bani kulawa ta mussaman, idan kinyi la'akari da shud'ewar lokacin da mu ka yi ba mu had'u ba, wata uku fa, wallahi ni kadai na san irin wuyar dana sha, bayan haka kuma Hamida ta yi wayo, ina so yau na samar mata da mabiyi mace ko namiji, ke yau ma dai yanda nake jina din nan, biyu zan zuba"
Dariya ta su'bce mini na ce" Allah sarki! amma ka ba ni
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download