Showing 108001 words to 111000 words out of 124287 words

Chapter 37 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16699

yi da ni,

Allah yasa babu kowa a falon, hakan yasa duk nauyi na ya d'auke ni muka hau sama yana ta yi min kalamai! ni kuwa ina sane nake kuka da sangarta lallai sai na bi su tamkar k'aramar yarinyar haka na zama, ya zaunar da ni kan gado duk ya rikice! fad'i yake " Yanzu ki ke so ayi?"

Shiru nayi kuma ban fasa kukan ba don hawaye ne jaga-jaga a fuskata! wani sa'in ina jin dad'in yanda yake biye min idan ina irin haka duk sai ya shiga damuwa! komai nasa sai ya tsaya, baya samun nutsuwa har sai ya ga na warware ina dariya sannan zai kwantar da hankalinsa.
Yanzu ma kwantar da ni ya yi a gadon yana ta shanye hawayen fuskata yana jijjigani tamkar 'yar goye! ganin yanayinsa ya fara sauyawa yana wasu abubuwa yasa da sauri na tashi daga jikinsa, aikuwa yace bai san wannan ba! sauka zanyi daga gadon, ya kamo ni ya kwantar! danne ni ya yi ya d'ora min nauyinsa, lokacin na shiga nutsuwata! na fara dana sanin abinda na aikata, aikuwa dai bai sake ni ba sai da nayi kuka mai dalili da ro'ko da bada hakuri sannan ya sauka na tashi jikina duk ya yi tsami.



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*

122&123
Rayuwa tana tafiya sannu a hankali, da dad'i babu dad'i haka ake hak'uri, dama ba dole d'an adam ya samu abinda yake so d'ari bisa d'ari ba, sosai na samu kwanciyar hankali fiye da lokacin baya ba, amma wani lokacin na kan 'buya a d'aki na zubar da hawaye a duk lokacin dana tuna cewa ko 'batan wata ban ta'ba yi ba wanda ya yanzu watanni goma kenan da auranmu, kuma iyakar bakin k'okari yana yi idan yana gari babu d'aga kafa kullum maganarsa na samu ciki na haihu amma babu labari, na shiga damuwa sosai, lokacin da watarana na farka daga bacci na ganshi gurfane! gaban Ubangiji yana addua kamar zai fashe da kuka! wasu hawaye masu rad'ad'i suka ciko idona da sauri nasa hannu na rufe bakina gudun kada sautin kukan da nake ya fito fili, rufe fuskata nayi da bargo hawaye na ta kwaranya watakila ba zan haihu ba, abinda nake rayawa kenan a cikin zuciyata, idan Allah ya kaddara mini hakan dole na bashi goyon bayan auran wacce zata haihu, ko kuma tilas ko baya so ya dawo da uwargidansa domin samun zuria tunda Allah ya bashi dukiyar dashi kansa bai san adadinta ba.
Tunanin da nakeyi kenan wanda ya haddasa min karyewar zuciya kukan dai da nake boye wa sai da ya fito fili, na rungume! filo a jikina tare da kiran innalillhi-wa'ina ilaihi raji'un!

Cikin tashin hankali ya zauna kusa dani yana birkitoni ina sake kudindine jikina! kuka mai sauti ne yake fita kuma ban fasa kiran sunan Allah ba.

Damuwa mai tsanani! ya shiga ya rungume ni tsam! a jikinsa yana rarrashina domin na fad'a masa damuwata.

Murya a dashe! na ce" Wata'kila bani da rabon haihuwa a duniya."

Gabansa ya fad'i jin abinda ta ce. da sauri ya ce." Saboda me zaki fadi wannan maganar? ko kina da masaniyar abinda Allah ya rufe?"

Hannunsa na ri'ke da kyau na ce" Wata goma kenan ina lissafi ban ta'ba 'batan wata ba, duk da cewa kana iyakar bakin 'ko'karinka, amma babu wani alamu da ya nuna zan samu ciki, ina jin tsoron halin da zamu shiga idan Allah ya kaddaro ni a matsayin juya mara haihuwa."


Ya ce." Wace irin magana ce wannan?" yafad'a cikin 'kunar zuciya.

Girgiza kaina kawai nayi ban ce masa komai ba. sai ya cigaba da cewa" Ashe kin manta Allah shi yake bayarwa kuma shi yake hanawa, me zai sanya kiyi wannan furucin bayan kina cikakkiyar musulma, idan kin kasance d'aya daga cikin mata marasa haihuwa menene? ko kina tunanin zan rabu dake saboda wannan matsalar? wannan ba hujja ba ce domin banga abinda damuwa da tashin hankali ba, wata goma kacal ba shi zai tabbatar da abinda ki ke zargi ba, akwai ma'auranta da suka fi shekara goma da aure basu haihu ba, amma basu cire tsammani ba, domin wani rabonsa yana nesa mutukar an barwa Allah lamarin sai ya kawo d'auki a lokacin da ba ayi tunani ba, don haka kada ki sake damuwa da wannan komai lokaci ne.


A sanyaye na ce" Ba zan iya jurewa ba, domin a yanzu babban burina na haihu mussaman dana fahimci abinda kafi bukata kenan! yana da kyau a duba ni ko ni ce nake da matsalar mahaifa" Cikin rauni da sarewa nayi maganar.


Shiru yayi na minti biyu kafin ya ce." Za a yi hakan in sha Allahu. amma abinda nake so dake shine; ki samu nutsuwa kada ki sake kuka akan wannan dalilin komai na Allah ne, kuma in sha Allahu zaki haifa min yara da yawa."


Ajiyar zuciya na sauke a sanyaye na ce" Amin ya Allah. Rabbi ya bamu masu albarka.

Ya amsa da "Ameen tare da rungumeni tsam! a jikinsa.


To koda likita ya dubani bai ci karo da wata matsala ba, kyakykawan sakamako ya fito cewa; cikin kowane lokaci zan iya d'aukar ciki, kawai lokacin ne beyi ba, amma likitan ya ba shi shawara cewa; ya d'an dinga d'aga k'afa saboda wani sa'in! cikin yana iya shiga amma yawan wannan abu na sanya maniyin ya tsinke cikin ya fita ba tare da an lura ba.

Wannan dokar tasa shi a damuwa mai tsanani domin da ya riga ya saba mutukar yana gida yana manne dani, nima har na saba da lamarin, haka dai ya yi hakuri tare da 'kokarin bin dokar amma wani lokacin idan lamarin ya bijiro masa haka zai zo ya yi kwance a gado! yana nishi! hanyoyin dana san yana so nake yi masa duk don ya samu gamsuwa, hakan baya samuwa domin baya iya samun satisfied a haka sai ya shiga wannan guri, don haka baya ma neman shawarar kowa a lokacin yake mantawa da dokar likita ya haye kaina kuma baya sauka sai ya zubar da duk abinda ke damunsa.

Haka muka cigaba da tafiya dokar likita ta tashi a banza domin babu abinda ya fasa, a cewarsa idan Allah yaso zartar da hukuncinsa babu wanda ya isa ya hana, duk yanda naso na fahimtar da shi, ya'ki saurara ta, wani lokaci idan na furje! na ce ban yarda ba, sai mu kwana mu yini bai kulani ba, idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare! ganin haka yasa na ha'kura na kyaleshi yana yin yanda yake so.

A cikin tsukin muka je umara gabad'ayan mu har da Shukura! sati biyu mukayi muka dawo gida. kamar wacce ta dawo da ciwo a ranar haka na kwana da wani irin ciwon ciki mai tsanani! na galabaita sosai! sai gefin asubahi! jinin yazo! nayi mamaki sosai! ganin cewa duka ban fi kwana goma da yin wanka ba, amma jinin ya dawo mini, wanda ban ta'ba haka ba tunda nake lafiya lau yake zuwa ya tafi bana ciwon mara bare na 'kafa! kuma jinin ya sha bam-bam! da irin na haila, wannan mai kauri ne!

Likita yasa aka turo daga babban asibiti, tazo har gida ta dubani! to itama dai shawarwari ta bani, sannan tace watakila na samu ciki ne ya lalace! sai ta bani magunguna wanda zasu taimaka min.

Bayan likitan ta tafi na kalleshi da cewa; Itama kaji abinda ta fada ko? ka bar mutum da aikinsa da kuma abinda ya sa ni, don Allah kayi hakuri kana d'aga kafa kada mu dinga asarar 'kwai'kwayanmu a banza.

Maganata ma dariya ta ba shi sai da ya dara tukkuna ya ce." Tom zan yi kokarin yin hakan."

Cike da jin dadi na ce "Yawwa to ko kai fa." Kallona ya yi tare da murmushi ya tashi ya nufi band'aki sai na bi shi da kallo ina tunanin abubuwa da yawa a tare dashi.
Mutum ne shi mai kawaici da kawar dakai! na karanci halayensa! sosai yana da sauki kai da fahimta, amma duk abinda yake akan lamarin na lura cewa dauriya ce, abin yana damu sa, kawai yana dannewa ne gudun kada na shiga damuwa.


Matsalar da ta kunno kai a gidan ita ce ta rushe duk wani farin cikina, sai ya kasance! kullum ina sama sai kace tsuntsuwa! bani da damar na sauko k'asa nayi walwala da mutan gidan, sai 'bakar magana daga Hajiya. gabad'aya ta sauya mini kullum maganarta d'aya ban haihu ba, amma na kankane! gida na hana a dawo da mai haihuwa! da sauti mai k'arfi take maganar a duk lokacin dana gifta ta kusa da ita sai ta san irin munanan maganganun data fad'a mini har cewa take na zama bijima! na samu duniya sai narka uwar 'kiba nake ina kasayarwa, amma na gagara! daukar ciki! kuka nake sosai a duk lokacin da bakin ciki ya ishe ni, gashi mai-gidan baya gari ya je ghana duba wasu ma'aikatu da zai saya! shi da kansa yake fad'a min cewa" Allah ya had'a arzikimu domin tunda ya aure ni yake ganin bud'i da d'aukaka! domin dai har sarauta a ka ba shi wato maji dad'in Katsina saboda irin gudumawar da yake bayarwa yasa sarki ya bashi wannan sarautar, bayan haka kuma dukiyarsa sai kara yawaita take dalilin samun nutsuwa da ni matsalar dai itace wannan dake 'kokarin kassara farin cikinmu.

Na san ina da hakuri sosai! amma idan nazo iya wuya ina da wuyar sarrafuwa! domin idona rufewa yake duk sai na amayar da abinda yake damuna.

Abinda ya faru kenan tsakanina da Hajiya na sauko da zummar shiga kicin, ta fara farfad'a min magangunu kamar yanda ta saba sai na gaza hakuri na dawo da baya na tsaya, lokacin Shukura tana zaune kan kujera da wayarta a hannu uffan ba tace ba, domin itama tun bayan tafiyar mahaifinta take min wani gani-gani.

Na ce" Wai shin Hajiya haihuwar waye yake bada ita ne?"


Kallona tayi kafin ta ce.'' Rashin kunya za ki yi min ne fitsararriya ai ba banza ba Allah ya hallice ki haka."

Wasu hawaye masu zafi suka ciko idona, ban bari sun zuba ba na ce" Har da kushe hallitar Ubangiji kuma? ke ma dai baki wuya komai a gurin Allah ba, domin ba a gamawa dan adam hallita har sai ranar da ya mutu. Hajiya a she dama duk kulawar da ki ke min ta ganin ido ce? me nayi miki da zaki tsawwalawa rayuwata, ke kanki kin san cewa'' Allah shine mai bayarwa kuma shine mai hanawa."


"Kin ga yi min shiru munafukar banza da wofi." Tafada tana zazzare min ido! raina ya sake 'baci! na ce"Hajiya munafurcin me nayi miki?"

Tsaki tayi kafin ta ce " Duk abinki sai Fatima ta dawo d'akinta, idan kuma bata dawo ba to babu shakka sai an kawo mai haihuwa tunda ke ba zaki haihu ba."

Hawayen da nake dannewa suka subce suka fara gudana a saman fuskata! na ce" Maganar dawowar Fatima d'akinta Allah ya gani nayi iyakar bakin k'ok'arina hakan bai yuwu ba, aure kuma ko baki fad'a ba da kaina zan sanya shi ya yi, domin samun zuria kamar yanda kuke buk'ata, idan yaso duk lokacin da Allah ya bani sai ki kashe shi."


Shukura ta ce" Lallai wannan baki da mutunci Hajiyar ki ke fad'awa wannan maganar?"

Ko kallonta ban yi ba naja tsaki! na bar gurin zuciyata a masifar k'untacce!


Ashe bayan na bar gurin kiransa sukayi a waya Hajiyan tana kuka take sheda masa cewa; na yi mata rashin kunya harda zagi!

Bai ji dadin faruwar al'amarin ba, shiyasa ba kasafai yake so yayi tafiya mai nisa ba saboda gudun faruwar matsala irin wannan, amma ba zai yanke hukunci ba tukkuna sai ya koma gidan.


Sai da ya dawo na lura da sauyi a tare da shi, tunda dai lami lafiya mukayi sallama da juna ya tafi, amma kuma ya dawo babu walwala.

Duk abinda yake bukata na gabatarsa masa, ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya kafin ya zauna gurin hutarsa na kai masa abinci, na had'a masa komai har ya kammala cin abincin bai ce min uffan ba, nima banyi masa magana ba kawai na zuba masa ido ne nasan lallai ruwa baya tsami banza.

"Me ya had'a ki da Hajiya har kina kiranta da munafuka yaushe ki ka lalace kema?"
Ya yi maganar ne a lokacin da ya kammala cin abincin yana goge bakinsa da tissue.

Shiru nayi ina kallonsa da jin takaicinsa a raina, har kullum idan matsala zata faru baya binkice akai zai zo ya turke ni.

Ganin nayi shiru ina kallonsa yasa ya ce." Ko ba kya ji ne ki bani amsar dana tambayeki."

Ajiyar zuciya na sauke da cewa; Ni bani da wata amsa da zan baka."


Ya 'bata rai da cewa" Kin raina ni ko? shiyasa ki ka samu sararin cin zarafin Hajiya saboda kina ganin hakan shine daidai a gurinki ashe kema mutuniyar banza ce."


Kuka ne ya kufce min na ce" Wallahi na gaji da wannan masifa! na gaji! kawai ka sake ni! idan yaso sai ka auri mai haihuwa ai Allah shi yake bada haihuwa ba wani mahalu'ki ba."


Zuba min idonsa ya yi a lokacin da nake maganar ina rusa kuka! tabbacin abin yana mugun damuna! na tashi naje na kwanta kan gado hawaye na zuba kamar an kwance famfo!


Ya zo ya zauna kusa da ni yana kokarin ri'ke min hannu na fizge da fadin." Ko da yaushe idan matsala ta faru baka binkice zaka d'auki lefi ka d'ora mini, to na gaji da wannan abu, a k'yale ni na samu nutsuwar zuciya haka.

Ya ce." Ni ki kewa tsawa?" d'auke kaina nayi daga kallonsa naja bargo na rufe fuskata! kukan dai na cigaba da yi tare da nemo hanyar warware matsalata.

Gadon ya hau ya tayar dani zaune, da alamar sassauci a fuskarsa ya ce." Na yi kuskure! kuma na kar'ba, amma mai yasa zaki biyewa Hajiya har ki fad'a mata maganar da bata dace ba, kin san da cewa dole raina ya 'baci idan na ji hakan.


Hannu nasa na share fuskata na ce" Yanda ka kira ni da mutuniyar banza shine ya 'bata min rai! amma wallahi ban zagi hajiya ba ballanatana na fada mata mummunar kalma, nasan dai tun bayan tafiyarka ta hura min wuta a gidan nan, cin mutuncin yau daban na gobe daban....duk na kwashe abinda yake faruwa na fad'a masa!

Ya ce." Ki yi hakuri watarana sai labari, abinda yake damun Hajiya shine yake damuna yake kuma damunki, amma dukkaninmu bamu isa mu bawa kanmu farin ciki ba face sai Allah ya bamu. babu shakka haihuwa rabo ce ga wanda rabbi ya so, muna sanya rai muna daga cikin wad'anda ilahi zai azurtamu da zuria masu yawa da albarka. tuntuni na barwa Allah ikonsa domin duk yanda naso idan lokaci beyi ba dole nayi hakuri, amma idan abinda ya dame ni nakan zubar da hawaye tare da tsananta roko a gurin Ubangiji." Cikin tsantsar damuwa ya kai karshen maganar.

Na ce" Ga shawara idan zaka d'auka zata amfane mu duka."

Kallona ya yi kafin ya ce." Ina sauraranki.

"Don darajar Allah da Annabi ka dawo da Fatima idan kuma hakan ba zai yuwu ba to kayi aure, dalili shekaru sun fara hawa kanka ya kamata a ce yanzu kana da yara masu yawa. ni ba zan tauye ka ba, duk da cewa; shekarar mu guda da aure amma ba zan damu ba don ka auro wata wata'kila nima na samu rabona ta dalilin hakan."


Fuskarsa ya had'e ya ce." Zanyi shawara a kan haka." Bai sake magana ba ya sauka daga gadon. lamarin da ya janyo mini 'bacin rai! domin dai daina shiga hurumina ya yi duk 'kwa'kwarsa da sha'awarsa ajiyesu ya yi a gefe ya shiga sabgar gabansa, sai ya zama gaisuwa ce kawai take had'amu da kuma sannu da zuwa a duk lokacin da ya dawo.

Ni na neme shi da maslaha domin na tsani irin wannan zaman a rayuwata! shi kuma b'acin ransa akan me zan ce ya yi aure! a lokacin ya sake jaddada min cewa; zai ha'kuri da yanda Allah ya tsara masa rayuwarsa, zai kuma zauna tare da ni a yanda Allah ya halliceni. sosai na yabawa k'o'karinsa da sadaukarsa kuma ya cika d'an halak! kamar yanda yake fad'a mini a koda yaushe cewa zai yi mini hallaci fiye da yanda nayi masa to naga zahiri gashinan, Allah ya riga ya gama yi masa komai na daga jin dadin duniya yana da ikon ajiye mata hudu a gidansa ba tare da wata matsala ba, rabbi ya wadata shi da lafiyar da ba kowane namiji ba, uwa uba kuma zahiri ya nuna matsalar rashin haihuwa daga gareni ne, tunda shi dai ga sheda nan budurwar 'yarsa Shukura! amma hakan bai sanya ya yi yun'kurin kawo wacce zata tara masa iyali ba kamar yanda yake da buri, sai ya sadaukar da farin cikinsa saboda ni, ban san wane irin so yake mini ba.


*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login