Showing 81001 words to 84000 words out of 124287 words

Chapter 28 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16687

wannan maganar, jikinsa duk yayi sanyi kawai sai ya tsira min ido! ya d'an ban tausayi, amma ban nuna a zahiri ba, sai kawai ma na tafi na bar shi a tsaye a gurin.

Sosai ransa ya 'baci da abinda yarinyar take masa, gabad'aya ya rasa gane abinda take nufi, yanayin kallon da take masa shi kad'ai ke damunsa, ya riga ya gama sanya ta a cikin ransa, domin wani irin so yake mata wanda ba zai fasaltu ba, amma yana ganin sai ya sha wahala kafin ya samu kanta, don ganin irin kallon da take masa kamar wanda yayi mata gagarimun laifi.

Bai sake tunkarar inda take ba sai wajejan goma da rabi na dare ya shiga gurun da take cikin kayan bacci masu taushi, yana 'kamshin azababben turaransa.


Salamarsa kawai na amsa na sunkuyar da kaina don ban yi tsammanin zai shigo ba shiyasa na zauna da vest tare da siket wanda ya tsaya iya gwiwa! da sauri na d'auki dankwalina na yafa a jikina na d'an ture plate din da na ci abinci gefe na had'e jikina guri guda.


Zama yayi yana fuskanta ta, yayin da 'kamshin turaransa ya addabeni yana neman ya kashe min jiki. ganin yanda ya tsura min ido yasa duk na tsargu! sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce." Haka ki ke zaune a cikin duhu?" shima ya fad'i maganar ne kawai saboda ya ji dad'in bakinsa, waye ya ajiye ta a duhun idan bashi ba.

Shuru kawai nayi masa saboda raina ne ma ya 'baci da maganar tasa, wacce tayi kama da ta rainin hankali. Shirun nawa shi ya bashi amsa da kuma yanayin fuskata don 'kiris ya rage na fashe da kuka!

"Babu gaisuwa ko?" Ya fad'a yana haske ni da fitilar wayarsa.

Hannu nasa na kare fuskata, babu fara'a na ce" Ina wuni?"

Ya amsa babu yabo babu fallasa kafin ya d'ora da fad'in." Kin ci abinci?"

Kaina na d'aga masa.

Falon yayi shuru na 'yan mintina kafin ya sake wata maganar da ta sanya nayi saurin kallonsa.

Ya ce." 'Kwarai kuwa ina da bu'katar matata a wannan daran, ai nayi ma 'kokari kusan watanni uku ina kallonki ban yi komai ba, kada ki manta a cikin labarina na sheda miki cewa; ina da yawan bu'kata! saboda haka sai ki shirya domin ina so ki zama jaruma! mai d'aukar d'awainiyata."

Kuka ne ya 'kwace! min da sauri na ce" Ni wallahi ban shirya wannan al'amari da kai ba, domin dai ni ba kai nake so ba, saboda haka ka ajiye wannan maganar ni kawai ka dauke ni ka mayar wa da iyayena"

Murmushi yayi mai ciwo kafin ya ce." Ai kin shigo hannun Saddiku dattijon nan mai furfura! babu rabuwa a tsakanina dake yarinya sai dai mutuwa."

Tashi nayi da gudu na shige d'aki na kwanta a kan gado ina kuka! ni gaskiya ba zan iya bashi kaina ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma ban shirya zaman aure dashi ba.


Gadon ya hayo ya janyo ni jikinsa yana so ya rungume ni ina turjewa tare da fizge-fizge! sai kawai yasa min 'karfi ya matse ni tsam! a jikinsa yana ta jijjigani tare da shafa gashin kaina! rarrashina yake tamkar 'yar goye yana ta fad'a min kalaman soyayya a cikin kunnena har ya samu nasarar kashe min jiki ta hanyar fad'in" Da wasa yake babu abunda zai yi min. jin haka yasa nayi shuru, tare da gyara kwanciyata a jikinsa.


Cikin wata murya na ji maganarsa a kunne na. ya ce. "Me yasa ki ke tunani mara kyau a kaina?"

Shiru nayi ban bashi amsa ba. Ya cigaba da cewa; ba zan gaji da fad'a miki cewa ni ba zan cutar dake ba, kuma duk abinda ya faru, akwai dalili wanda na sheda miki, amma ban yi tunanin haka daga gare ki ba don Allah kiyi hakuri mu zauna domin mu raya sunnar ma'aiki tare."

Jin yanda yake had'a ni da Allah yasa jikina ya mutu! na ce" Ni fa muddin kana so na zauna da kai domin yin rayuwar aure sai ka kasance yanda na sanka a farko, domin ni fi bukatarka a haka."

Ya ce." Hakan ba zai yuwu ba, ki so zahiri na, shine abinda na fi buk'ata, amma wancan da ki ke so duk gaibu ne, shiri ne, nayi domin cimma wata manufa kuma Alhamdulillhi na samu nasara, amma ba zan zauna cikin yagaggun kaya da 'kazanta ba, wannan zai janyo min wani abu daban."

Na ce" Ni kam na fi bu'katar ka a haka, tunda kana ganin hakan ba zai yuwu ba shikkenan."

Murmushi kawai yayi bai sake magana ba. ganin haka yasa na tashi daga jikinsa na matsa can 'karshen gado! na ja bargo na rufe jikina.

Bacci ne mai nauyi ya d'auke ni, ko da na tashi da asubah! baya d'akin, ban damu ba, kawai na tashi na shiga band'aki da tunani mai yawa a cikin raina.

Sai da na shirya tsaf sannan na nufi cikin gidan don gaishe da Hajiya.
Da sallama a bakina na shiga falon, Hajiya da Shukura suna zaune a gurin cin abinci. na 'karasa a nutse na tsuguna har kasa na gaishe ta, ta amsa da fara'a mai yawa a fuskarta.

Cikin wani irin yanayi mara dad'i Shukura ta gaishe ni kamar anyi mata dole. nima na amsa babu yabo babu fallasa.

Hajiya ta ce" Ki zauna ki karya kummalo mana.

Na ce" Hajiya na ci abinci a guri na kafin na fito.

"Allah sarki." Ta fad'a kafin ta d'ora da fad'in." Mijin naki ai tun asubah ya tafi can garin mu jibia da yake duk 'karshen wata yana zuwa, ina fatan kunyi sallama da juna?"

Da sauri na ce" Eh Hajiya ya fad'a min, Allah ya dawo dashi lafiya"

Ta amsa da "Ameen ya Allah."

Tsaye na mi'ke tare da fad'in" Hajiya zan koma guri na sai an jima.

Ta ce"To shikkenan mu jima da yawa."

Tana fita Shukura ta kalli Hajiya da fad'in "Wai Daddy ya rasa wacce zai aura sai kurma! wallahi Hajiya abin yayi min ciwo sosai! tuntuni Mommyna take so ya dawo da ita ya'ki ya je ya kwaso wannan k'azamar."


Hajiya ta ce" Ke dai ki iya bakin ki Shukura bana son tashin hankali don Allah. domin abin farin ciki ne a guri na da Allah yasa yayi auran ina raye, maganar babarki kuma ki ajiye ta, a gefe domin da zai dawo da ita da tuntuni anyi an gama, saboda haka ki d'auki matar babanki a matsayin uwarki, kin fi kowa sanin halin mahaifinki, don haka kada ki ga kuna sa'anni da yarinyar nan, ki raina ta, duk 'kan'kantar ta uwarki ce, tunda tana auran mahaifinki."

Kawai sai ta buga tevur d'in cin abinci tare da fad'in" ba zai yuwu ba wallahi." hanyar d'akinta ta shiga tana surutai! Hajiya tabi ta da kallon mamaki!

"Mommy kina da labarin Daddyna yayi aure kuwa?" ta fad'a cikin ba'kin ciki da takaici!

Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Aure? yaushe yayi babu labari?"

Nan duk ta kwashe komai ta sheda mata.

Ta ce" Amma gaskiya 'Dan-gaske ya ba ni kunya, duk diddigin nasa anan ya tsaya? auran kurma wacce take da nakasu, mtsww! kada ki damu idan na dawo zan zo gidan, ai ko yana so ko baya so sai ya mayar dani d'aki na, ko kuma na hana shi kwanciyar hankali da matar tasa.

Ta ce."Mommy ni na rasa wace irin zuciya ce da Daddy, ke fa 'yar uwarsa ce, yana kallon yanda ki ke katangala! kiyi nan kiyi can, duk saboda shi amma ya 'ki ya saurareki, gaskiya Momy kiyi wani abu akai, domin ba zan iya bud'e idona na kalli kucakar yarinyar can a matsayin matar mahaifina ba, wai har Hajiya tana fad'in" Dole sai nayi mata biyayya"

Hajiya Fatima ta ja tsaki tare da cewa; ki rabu da Hajiya Saude tuntuni na fahimci cewa; ba ta son lefinsa, saboda yana da kud'i! babu yanda ban yi da ita ba, akan tasa baki ya mayar dani, amma ta'ki, saboda haka idan na dawo daga dubai, a gidan zan sauka duk sai na rikirkita musu lissafi tunda abin ya kasance haka."

Ta ce." Yawwa Mommy Allah ya dawo dake lafiya." Ta amsa da "Ameen kafin ta kashe wayar zuciyarta a 'kuntacce!


*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*


_THE UNKNOWN RICH MAN_
86&87
Ranar na yini cikin zullumi da tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na yi zaman aure da shi kamar yanda yake bu'kata, gaskiyar magana ba shi da wata makusa ta kowane fanni yana da kyawun hali, uwa uba kyawun zuciya tare da nagartar da ba kowa ne mai arzi'ki ne yake da ita ba, yanda na fahimce shi, bai d'auki kansa wata tsiya ba, irin yanda masu kud'i da mulki sukeyi, ya ajiye kansa dai-dai yake da kowa, kuma arzikinsa bai rufe masa ido ba, yana alheri sosai, tunda ni ganau ce, domin duk sati ranar juma'a kenan, gidan cika yake yi da bil-adam yara da manya dattijai da matasa har da mata masu buk'ata, kuma da kansa yake fitowa ya gaisa da kowane sashi kafin ya zauna ya fara robon kayan abinci da kud'i! shiyasa a kullum bakin gate d'in gidansa baka raba shi da al'majirai kala-kala, daga wata uwa duniya ma zuwa suke kuma duk yawansu sai ya faranta mu su rai, mutuk'ar kaga sawun 'kafa ya d'auke a gidansa, to ka tabbata cewa; baya gari yayi tafiya, amma duk da haka dai ba'a fasa aikin alherin ba, al'majirai irin na tsangayu suna zuwa kar'bar sadakar abinci mai rai da lafiya, wanda ya bada umarin cewa; ko baya gari kada a sauke tukunyar abincin sadaka.


Maganar shekaru, gaskiya ya kwana biyu a duniya domin ya wuce shekaru ar'ba'in da biyar don a 'kalla zai yi shakara hamsin, amma saboda yanda yake kula da kansa shekarun basu nuna ba, bayan haka kuma yana da kyawun jiki, dogo ne amma bashi da ki'ba mai muni! sai dai kowace ga'ba a jikinsa a bud'e take, wannan ya samo asali ne, sakamakon atisayen da yake a duk ranakun karshen ma'ko, yana da kyau! daidai gwargwado don bashi da muni! ya fi ni kyau! nesa ba kusa ba, gashi da gayu da tsafta! kowace mace ta same shi a matsayin miji ta more! amma ni har yanzu zuciyata ta kasa aminta da shi, domin na zauna nayi rayuwar aure dashi, kuma na rasa a wane matsayi zan ajiye shi a cikin raina.

Da wannan tunanin na yini, don sai bayan magariba ma na shiga kicin na dafa taliya fara tunda na kan yi miya ta kwana biyu zuwa uku, don na kori yunwa na zauna na tuttura abincin ba don baki na yana so ba.

Wanka nayi na sanya doguwar rigar bacci ma dan taushi, saboda yanayin garin ana zafi, falo na fito, kafin na zauna sai dana zuge labule domin haske ya shigo, tunda harabar gidan, da fitilu ko ina, gurina ne, kawai babu fitila, to idan na bud'e labule haske yana shigowa, don tun ina jin tsoro har na saba.

Zama nayi ina sa'ka wasik'ar jaki, har lokacin da na ji agogo ya buga goma daidai na dare, na sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyata kan dugowar kujera, ina tunanin Baba Asabe da sauran 'yan uwa da mahaifi na, hawaye ne suka zubo min nasa hannu na goge wasu na na sake zubowa, cikin wannan yanayin ya shigo ya same ni, nayi saurin juya fuskata baya ina rintse idona.

Sallama yayi bata amsa ba, kuma ya ga sanda ta juya baya a lokacin da ya shigo.

Bai ajiye abin a ransa ba, ballananta ya dame shi, kawai abinda yake nazari shine, yarinyar ta samu dama a kansa ne, tunda ta fahimci irin azababben son da yake mata, dama kuma ta'kidin mata ne hakan, mutu'kar sun fahimci namiji na k'aunarsu shikkenan iskanci iri-iri zai biyo baya.

Ya zauna a gefan ta tare da riko hannunta kafin ya 'bud'e muryarsa yanda za ta ji ya ce" Na zama dodo abin gudu ko Shahida?"

Shiru ba tayi magana ba, sai ya d'ora da fad'in." Ki tashi mu tafi can cikin gidan, na gaji da zaman ki anan gurin, tunda wasan kwaikwayon ya 'kare."

Ta shi nayi ina kallonsa shima ya tsira min nasa idon, wanda nake hango tsantsar gajiya a ciki.

Na ce" A'a ka bar ni anan tunda dai kai ka ajiye ni kuma nan d'in kaga ya fi cancanta da ni.''

Ya ce." Ba zai yuwu ba dole zaki koma cikin gidanki da zama kiyi rayuwa mai kyau kamar yanda ko wace mace take a gidan auranta."


Cikin rauni! na ce" Ka da ka manta fa, da bakinka ka ke fad'in kud'i ka bayar aka baka ni, to mai zai sanya ka ajiye ni a guri mai kyau?"

Shiru yayi yana kallona, na goge hawayen dake zubo min na ce, idan ka manta ni ban manta ba, babu irin cin mutuncin da ba kayi wa mahaifina ba duk da na san halinsa ne ya janyo masa cin zarafi, saboda haka ni me zanyi a cikin gidanka domin ni wannan auran har yanzu wasan kwaikwayo na d'aukashi''


Ransa a 'bace ya ce." Kada ki sake kiran auranmu da wasan kwaikwayo kin ji ko."

Kaina na d'auke tare da fad'in" Ai kai ka shirya kuma kai ka bada umarnin sunan shirin film din naka wasan kwaikwayo." Na sake maimaitawa duk da ya nuna baya so ban ji shakka ba.

Shiru falon yayi ni da shi kowa da nazarin da yake, ganin kawai ya tisa ni a gaba yana kallo yasa na yun'kura zan tashi, sai ya ri'ke min hannu, still idonsa yana kaina, gabadaya jikina ya mutu! domin bana iya jurar wannan kallon nasa.

Ya ce" Na je jibia ban fad'a miki ba, duk suna gaishe ki, za kiyi 'bakuwa cikin satin Sadiya za ta zo ku gaisa."

Shiru nayi masa. ya sake rintse hannuna dake cikin nasa, kafin ya ce." Ina ganin dai har yanzu wahalata ba ta 'kare ba, zan cigaba da addu'a tare da fara dubawa daga cikin masu rubibi na."

Kallonsa nayi tare da jin fad'uwar gaba, duk da cikin zaurance yayi maganar na fahimci abinda yake nufi, duk sai na ji rashin dadin furucinsa, amma ban nuna a fuskata ba, nayi saurin d'auke kaina.

Ya mi'ke tsaye tare da zuba hannuwansa cikin aljihu, ya ce" Na tafi ko na zauna na taya ki kwana?"

Da sauri na ce" Ka je kawai."

Yayi tsayiwar minti biyu kafin ya kama hanyar fita, na bishi da kallo! zuciyata na wani irin tunani akan kalamansa.


Washe gari na tashi sukuku! babu kuzari ko kad'an a jikina, dalilin mafarkin da nayi, haka dai na gudanar da komai cikin rashin nutsuwa! na gama uzurirrika na sannan na zauna karya kummalo kana na sa hijabi a jikina, kamar dai ko da yaushe na nufi cikin gidan.

Lokacin dana shiga falon shiru babu kowa, jikina a sanyaye na sake wata sallamar a karo na uku, babu wanda ya amsa, sai jikina ya 'kara mutuwa! cikin zuciyata nake addu'ar cewa; Allah yasa lafiya.

Motsi na ji can saman bene in da ya kasance turakar mai-gidan, da sauri na d'aga kaina ina kallon gurin, Hajiya ce take saukowa daga benan idanuwanta jawur! da alama kuka tayi. gabana ya yanke ya fad'i! cikin rawar baki na gaishe ta amsa a sanyaye kafin ta ce" Ki hau sama mai-gidan naki bashi da lafiya jiya da daddare ciwonsa ya tashi ba mu rintsa ba"

'Kafafuna suka shiga rawa! na kasa gaba na kasa baya kawai na zuba mata ido, k'walla duk ta cika kwarmin idona.

Ta ce" Kiyi wa Allah da Annabi ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki bawa mijinki kulawa, wallahi ba mu da mummunan nufi! a kanki, bana raba d'aya biyu 'bacin ran ki ne, ya haddasa ciwonsa ya tashi.

Da sauri na ce" Wallahi ba haka bane Hajiya, ni kuma me nayi masa da har ciwonsa zai tashi a kaina, kada fa ki manta manya irinsu, dole ba zaki raba su da cututtuka ba, bayan haka kuma abubuwa sunyi masa yawa, na harkokin yau, da gobe, amma kada ki ala'kanta ciwonsa da damuwata."

Murmushi takaici tayi kafin ta ce." Duk abubuwan dake faruwa a tsakaninku ina da labari, domin Saddiku baya b'oye min komai, ki sani cewa; a gurinki ne kad'ai muke sanya rai za mu samu nutsuwa, gashi ke kuma kina yi mana wani irin kallo na rashin yarda, wannan ce babbar damuwarsa, gashi ya sanya ki a ransa sosai, ki duba irin 'kaunar da yake miki don Allah ki zauna dashi."

Duk yanda na so dana daure abun ya gagara, hawayen da nake 'boyewa suka su'bce! na ce" Hajia wallahi bani da laifi zuciyata ce, amma insha Allahu zanyi 'ko'karin ganin na kawar da komai na zauna tare da ku kamar yanda kuke bu'kata."

Ta saki fuskarta tare da fad'in" To shikkenan Allah ya baki iko." na amsa da "ameen" kafin na fara hawa 'kafar benan cikin sassarfa.


Zaune a kusa dashi na samu Shukura tana kuka tare da rungume hannunsa a 'kirjinta fuskarta ji'ke da hawaye! sai duk suka bani tausayi ita da shi, mafarkin da nayi yana nema ya tabbata.

A sanyaye na 'karasa bakin gadon, wanda tun da na shiga d'akin yake kallona, kuma bai daina ba har na zauna a kusa da shi.

Ta kalle ni a banza ce kafin ta ja tsaki! mai tsayi wanda duk

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login