Showing 66001 words to 69000 words out of 124287 words
to ya akayi ban same ta cikakkiya ba, nan ta sheda min abinda suke yi da 'kawayenta (Madigo) hankalina ya tashi sosai! a lokacin, amma ban yi 'kasa a gwiwa ba, nayi mata nasiha mai ratsa jiki, ta ce min insha Allahu ba zata sake ba.
Saboda yanayin magungunan matan da take sha yasa kullum sai na neme ta, kuma bana iya ha'kura nayi sau d'aya sai nayi sau biyu zuwa uku sannan nake jin daidai, babu lefi ina jin dadin auratayya da ita sosai, saboda ta gama fahimtar abinda nake so.
Rayuwa tana tafiya da dad'i babu, haka muke zaune, amma duk wani hakki nata ina kokarin saukewa, to sai da tabbatar da cewa na saki jikina da ita sannan ta 'bullo da wata manufa, kullum bata yarda da na kwanta da ita sai na bata kud'i!
Ni kuma bani da hakuri ko kadan ta wannan 'bangaran, gashi na riga ba saba da ita bana iya kwanciya bacci sai nayi tara da ita, wannan dalilin yasa hankalina yake tashi a duk lokacin da bani da kudin da zan bata, domin sai an kai ruwa rana, take amincewa da b'ukata ta.
Cikin wannan halin ta samu ciki, sai ta tsiri nu'kufurci! 'bacin rai iri-iri! idan na tambayeta abinda ke damunta, sai ta ce min babu komai, ashe cikin ne bata so, ni kuma a lokacin farin ciki yasa na kasa hakuri na shedawa Mamana da Hajiyata, sunyi murna sosai! mussaman mahaifiyata da kullum idan naje gidan sai ta bani tsaraba irin ta masu ciki ta ce na kai mata.
Yanda na kai mata sak'on haka za ta bari su lalace! suyi funfuna, sai dai a zubar a shara, ga k'azanta domin ta daina komai a gidan, sai dai da safe kafin na fita aiki na gyara.
Ranar litinin 'Kawarta Jamila ta zo da sassafe! sam! bana 'kaunar yarinyar, dalili bata da kamun kai ko kad'an, shiyasa bana sakar mata fuska.
Ta same ni a d'aki ina shiryawa domin fita aiki, "Asibiti zan je." ta fad'a kamar bata so. na ce" Ai yana da kyau, dama tuntuni nake ce miki kije domin a duba lafiyarki, data baby, yanzu me kike bukata?"
"Ku zaka bani." a lokacin na dauki dubu biyu na bata, tayi wa kudin wani irin riko kafin ta ce"Dubu biyu me za tayi min gaskiya sai dai na fasa zuwa"
Na ce" Yau ban tashi da kudi ba, kiyi hakuri kiyi maleji mana"
"Gaskiya ba zan iya ba" tafad'a tare da ajiye min kud'in tana kokarin fita, sai na ce "Zo ga dubu daya na kara miki."
Ta ce" Dubu biyar zaka bani domin har scanning za ayi min."
Da yake ina so taje asibiti a lokacin, haka na dauki dubu biyar din na bata, ashe zubar da cikin suka tafi.
Ni dai na dawo gidan na ganta a galabaice, na ce" lafiya dai." sai ta ce" Gajiya ce kawa." Na ce" Ba kiyi girgi ba kenan? kai ta daga alamar eh! da kaina na shiga kicin din nayi mana shinkafa da wake.
Da daddare kafin mu kwanta nake tambayarta takardar scanning, sai ta ce" ai sakamakon bai fito ba." ban kawo komai a raina ba, na kwanta domin huta gajiya.
Sati biyu da faruwar al'amarin, sai naga ta warware! tana ta walwala babu alamun laulayi a tare da ita, al'amarin ya bani mamaki sosai, na ce" Da alama dai magungunan da na siyo miki suna da kyau, naga kwana biyu kin samu lafiya"
Ta'be bakinta tayi can kasan ma'koshi ta ce" Na dai rabu da jaraba." Na ce." Me kika ce?" shuru tayi bata tanka ba, sai nasha jinin jikina domin duk da tayi maganar a can k'asan mak'oshi, sai da na fahimta.
Na ce" Baki da gaskiya Fatima kin rabu da jaraba ko?"
Ta ce" Eh mana ni wallahi ba zan haihu yanzu ba."
Gabana na faduwa na ce" Me kike nufi kenan?"
"Zubar dashi nayi" ta fada hankalinta kwance!
Ban san sanda na kai mata wani mugun mari ba wanda yasa hancinta fitar da jini!
Jikina na rawa na ce" Cikin nawa ki ka zubar akan me?"
Ta tashi tsaye hannunta dafe da kumatunta ta ce" Saboda yana bani wahala kuma ban shirya haihuwa yanzu ba"
A zafafe! na sake zabga mata wani marin! na ce" Me na rage ki dashi a gidan nan? duk neman da nake akanki yake 'karewa, me yasa za kiyi min wannan wulakancin?"
Tana kuka take fadin" Kada ka sake mari na" na ce " Duka zanyi miki ma yanzu" da sauri na je na rufe kofar d'akin, na sanya blet na zane ta ciki da waje sai da na huce! fushina! sannan na kyale ta, na ce kuma lallai kada na dawo na sameta a gidana.
Tana kuka take fad'in"Ai dama ko baka fad'a ba, mugu azzalimi kawai" fita kawai nayi na k'yaleta domin idan ba hakan nayi ba, to zan iya kashe ta har lahira, saboda takaicin da ta 'kunsa min."
*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
73&74
'Bacin rai ne mai tsanani ya biyo bayan al'amarin da ya faru tsakanina da Fatima, domin zuwa tayi ta juya maganar, ta ce na rufe ta a daki nayi mata dukan tsiya! har sai da cikin jikinta ya zube! duk yanda naso da na kare kaina abin ya fassakara domin babu wanda ya tsaya ya saurareni, mussaman mahaifiyata da ta dauki fushi! mai tsanani! wanda ya d'aga min hankali mutu'ka! na dinga bata hakuri, amma fafur! taki saurarata, sai dai 'kyar na samu tayi min magana kan cewa; muddun ina so naga farin cikinta, to naje na bawa matata hakuri akan abinda na aikata, sannan na nemi gafarar Hajiya da shi kansa Baba Auta, to fushin Ummana yana da ala'ka da rashin kwanciyar hankalina, wannan dalilin yasa dole na sauke duk wani 'bacin raina, na je na samu Hajiya na bata hakuri, itama dai magana d'aya ce wato na je na bawa Baba Auta Hakuri da 'yarsa, haka nan, ba don raina yaso ba na nufi gidan, sai dai nasha wulakanci ba k'arami ba a gurin Baba Auta ya dinga nannago ba'kaken maganganu ya narka min, haka dai na daure na dinga bashi hakuri, kafin ya bari Fatima ta dawo gidana sai da ya kafa min sharad'ai! na ce na amince duk don samun zaman lafiya, da gujewa fushin mahaifiyata.
To koda ta dawo gidan, sai dana kai zuciyata nesa sannan na fara mu'amula da ita, amma na daina sakar mata fuska, kuma na sanya mata matakan tsaro sosai domin na hana duk wasu 'kawayenta zuwa gidan.
Da yake idan na fita tun safe bana dawowa gida sai wajejen sha biyu na dare, domin wani sa'in da daddare kasuwa tafi bud'ewa ga wad'anda basu da bukatar shiga gidan mai, sai su tsaya a gurina su saya, gefe guda kuma idan faci ko gyara ya samu ina yi duk domin asiri na ya rufu.
Tun safe na tashi da ciwon kai, na san hakan baya rasa nasaba da rashin samun wadataccen bacci, na daddafa na fita domin nasan ko na zauna a gidan don hutawa, 'bacin rai ne zai biyo baya gwara fitar tawa tafi alfanu.
Ina tsammanin ko rabin awa banyi da zama gurin aikin ba, na kasa jurewa domin saboda tsananin ciwon kai har jiri nake, sai na yanke shawarar komawa gida na samu nasha magani na kwanta
Sai dai me? tun daga nesa na hango 'katon 'kwado! a jikin kofar gidan, raina ya 'baci ainun! wato a duk sanda na sanya 'kafa na fita daga gidan, itama rufewa take ta tafi nata guri. Allah yasa ina da mukulli a hannuna kawai sai na bude gidan na shiga, yanda na fita na bar shi a hargitse babu gyara haka yake bata gyara ba.
Damuwa sosai na shiga da wannan abu da faru, kuma zuciyata ta dinga munanan tunane-tunane a kanta.
A takaice! dai Fatima bata dawo gidan ba sai bayan isha'i! tayi sallama ta shigo jikinta duk a sanyaye, lokacin ina kwance kan doguwar kujera na d'an ji dadin jikina, sakamakon magungunan dana sha, amma duk da haka sai da mai chamis din ya bani shawara cewa naje asibiti likita ya duba ni saboda yanda nake kuka da ciwon kai.
Ta zo ta tsaya a kaina tana wuri-wuri! tare da shirya karya da gaskiya, wai gidansu taje Mamanta bata da lafiya.
Na kalleta kafin na ce"Kin san dai ban yi kama da wanda zai yarda da wannan shirmen ba ko?"
"Wallahi tallahi ba 'karya nake yi ba ko za kaje ka tambaya ne" Tafad'a tana kokarin kare kanta
Zaune na mi'ke na d'aga mata hannu da fadin " Ki fad'a min gaskiya idan kina so ki tsira da lafiyarki, don wallahi tallahi rufe kofa zanyi naci ubanki sai dai duk abinda zai faru ya faru.''
"Ubana kake zagi?" ta fad'a tana nuna 'kirjinta.
Na ce" Ba shine yake daure miki gindi ba?"
Shuru tayi tana kallona .
Na ce" Na fi ki iya sharri! da mugunta! Fatima, duka zanyi miki na zubar miki da ha'kora! don ba zan yarda da munafurci ba, da aure na ki ke zuwa kina neman maza a waje"
Sai ta fashe! da kuka da fadin" Wallahi sai Allah ya saka min sharrin da kake min ni 'ban ta'ba kwanciya da wani namiji ba sai kai, amma kullum cikin zargi na kake.
Na ce" 'Karya ki ke yawon ta zubar ki ke zuwa bayan na fita dame na gaza miki? na d'auka ko bana son kwanciya dake sai kinyi min dole kuma haka nake 'kure miki gudu! amma shine zaki je ki kwaso mana cuta"
Ta tsuguna 'kasan 'kafafuna tana kuka da fadin "Ni dai don Allah ka daina jifa na da irin wannan munanan kalaman, wallahi bana zina, shima lesbian din tunda nayi aure ban sake yi ba, kuma zan gaya maka gaskiyar gurin da nake zuwa.
Na zuba mata ido ina kallonta ta ce" Gidan Jamila nake zuwa muna sana'ar dillanci, shine nake samun 'yan kud'i domin nima ina sha'awar na tsaya da k'afafuna, tunda dai kai baka da wata gwagwgwa'bar sana'a."
Raina ya 'baci mutu'ka na ce"Yanzu Fatima da 'kananun shekarunki ki ke wannan sana'ar? masifa kike so ki janyo mana ko me?" girgiza kanta tayi. Na ce" Kin ce bani da gwagwagwa'bar sana'a! shin na ta'ba barin ki, da yunwa?" kai ta girgiza. na cigaba da cewa; na gaza miki ta fannin ci dasha da suttura da lafiya da gurin kwanciya? " Ta ce" A'a." na ce" To mai zai sanya ki zubar min da mutunci?"
Hakuri ta dinga bani, Na ce" Wannan ya zama na farko da 'karshe kada ki sake fita bada izini na ba, sannan kuma na rabaki da Jamila har abada babu ke babu ita, zan je har gidanta na sameta da wannan maganar."
Kamar gaske ta ce" Shikkenan ba zan sake ba nayi alkawari, kuma na rabu da jamila har abada'' jin haka yasa hankalina ya dan kwanta na sassauta mata.
To ashe tsugune! bata 'kare ba, domin dai Fatima ha'inata take ta kowanni, idan na siyo kayan abinci na wata guda sai ta kwashe rabi ta siyar, abin ya dinga bani mamaki! ganin cewa mu biyu ne kacal! amma 'karamin buhun shinkafa baya wata d'aya haka nan kwalin taliya ma, mangyada da manja jarka-jarka nake saya da ledar maggi, amma basa kwana goma zuwa sati biyu sun 'kare, sosai na sanya mata ido, anan na gane cewa kwashewa take ta siyarwa da wani mai kanti, dake bayan layinmu, duk na samu wannan hujjojin ne daga gurin al'majirin da yake mana aike-aike! tunda na gane haka sai na daina siyan komai ina aje wa, sai dai kullum idan zan fita zan bata dubu daya ko dari bakwai, tayi awo da cefane!
Sai ta shiga damuwa! kullum cikin 'korafi! cewa; kudin da nake bata basa isa komai yayi tsada! shareta kawai nake na kan ce ta cigaba da yi min addu'a idan na samu kudi zan cigaba da siyo mata komai da yawa.
Wata da'bi'a da ta tsira kuma shine, duk sanda na dawo gida na cire rigata na shiga wanka sai tayi min binkice ta dauki dubu daya ko biyu a cikin abinda na samu, da yake bana lissafi a can sai na dawo gida shiyasa ban gane ba, sai watarana dana shiga wanka sai naga babu sabulu, na fito kawai sai naga tana zazzage min kudin cikin aljihu tana lissafawa, nan naga ta dauki dubu uku ta daure a bakin zaninta, tashi tayi da sauri zata mayar da rigar sai kawai muka had'a ido! duk sai ta gigice! ta fara wuri-wuri! na daga mata hannu da fadin" Bani kudi na" babu kunya ba tsoron Allah ta kwanto kudin ta bani. Na ce" Tun yaushe ki ke min sata?"
"Wallahi yau ne kawai" Tafada muryarta na rawa"
Na juya na rufe dakin da sakata na ce" Zaki fada min gaskiya ko sai naci ubanki"
Ganin ina kokarin dukanta yasa ta fara kuka da fadin" Ka tsaya don Allah kada ka doke ni zan fad'a maka wallahi wannan shine karo na bakwai ."
"Iya adadin nawa ki ka dauka?" na fad'a zuciyata a 'kuntacce!
"Dubu goma sha shida kenan" Tafad'a tana yin nesa dani.
Na ce" Me za kiyi da kudin?"
"Ankon bikin Abulle zan saya dubu talatin da biyar ne, na san idan na fad'a maka ba iya saya min za kayi ba."
Wani kuttun bakin ciki ya tokare min wuya.Na ce" Ya akayi ki ka yanke min hukunci bayan baki fad'a min kin ji ta bakina ba"
"Dubu talatin fa duka-duka jarin naka guda nawa yake wallahi ba zaka iya say......." Wani bahagon mari na kwada mata, jikina na rawa na ce" Don ubanki da kudin wa za ki saya yanzu?" tayi shuru tana kallona hannunta dafe a kumatu.
Na cigaba da cewa; ina jin yanzu har kin had'a dubu goma sha biyar da kudina wanda duk sanda ki ka tashi magana zaki ce bani da jari, ko kuma gwagwgwabar sana'a wannan din kudin ubanki?"
Kuka take sosai! na ce" Fito min da kud'ina ko na lahira ya fi ki jin dadi yanzu.
Tana kuka ta ce" Ai na riga na bayar dasu na ce zan ciko sauran, don Allah kayi hakuri ka saya min"
Na ce"Ai baki biyo hanya ba, wallahi da kin fad'a min cikin mutunci ni mai iya saya miki ne, amma tunda ta wannan hanyar ki ka biyo shikkenan, gobe da wurwuri ki je ki kar'bo min kud'ina idan ba haka ba, ni dake ke ne"
Zubewa tayi a kasan dakin tana kuka, ni kuma nasa rigata na fita domin sayo sabulun wanka.
Sai da ta kar'bo min kud'ina sannan na 'kyaleta ta sha'ki iska.
Kwana biyar da faruwar al'amarin, na dawo gida naga babu kujeru a falo. na tambayeta suna ina? kai tsaye tace ta sayar dasu, domin ta sharewa kanta hawaye! tunda dai nata ne.
na ce to shikkenan, mutukar kuwa ta fita zuwa gurin bikin nan, a bakin auranta.
Ko a jikinta, biki na zuwa ta dinga zurga-zurga duk ina kallonta ban ce mata komai ba, sai da suka gama bikin tukkuna, da safe ta kwaso wanki za tayi, da zan fita na bata takarda saki, nace" wannan ita ce shedar sakin da nayi mata idan ta manta to na tuna cewa muddun ta fita da niyyar zuwa gidan biki 'kawarta a bakin auranta.
Kuka sosai ta dinga yi tana bani hakuri, ban ko saurareta ba nasa 'kafata na fita daga gidan.
Wannan abun dana aikata sai da nayi nadama! domin shine silar kwanciyar mamana 'bacin rai da tashin hankali ya janyo mata mutuwar 'barin jiki! kuka sosai nayi da idanuwana ganin mahaifiyata magashiyan rai a hannun Allah, nayi tur! da auran Fatima da kuma 'bakar zuciyata, duk da nasan duk abinda nake yi akan gaskiyata nake domin na kare darajar aure na.
Har Mamana ta gama zama a asibiti babu wanda ya taka kafa ya je domin dubata, gabad'aya 'yan uwan mahaifina da ita kanta Hajiyar sun dauki laifi sun d'ora mata cewa; da umarninta nake aikata komai, saboda haka babu su babu ita.
Nayi nadama sosai! kuma na zubar da hawayena ganin yanda 'bacin rai da damuwa suka haifarwa da Ummana matsala, 'bari guda na jikinta ya daina aiki, sai an taimaka mata! haka Sadiya take kula da ita, ni kuma ina yi da jikina da aljihuna, kuma nayi mata alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba, sosai tayi min fad'a ta kuma nuna min kuskuran abinda na aikata, cewa saurin saki ba shi da fa'ida ko don gaba kada na sake, tunda yanzu saura igiya daya to nayi kokarin ri'ke ta da kyau muddun raina! har cikin raina nayi nadama na kuma yi mata al'kawari cewa duk abinda Fatima za ta aikata ba zan 'kara daukar matakin sakinta ba. tana daga kwance ta dinga yi min kyawawan addu'o ina amsawa da "Ameen"
****
Bayan wasu
'yan wattani da
faruwar al'amarin. zamana da Fatima babu yabo babu fallasa, idan rikicin ya ratso mu nayi sosai! kuma ina ladabtar da ita yanda ya kamata don bana daukar wargi, amma ban sake yun'kurin sakinta ba duk irin 'bacin ran da zata sanya ni a ciki ina hakuri, don ko da naga magungunan planning (tsarin iyali) cikin kayanta, ban yi mamaki ba, saboda na san zata aikata abinda ya fi haka, kawai sai na d'auke! maganin na zuba a cikin masai! (shaddah) da yake bata da gaskiya ba ta tambayeni ba, sai dai kawai naga tana ta dube-dube a dakin.
A tsakankanin lokacin nake ta shirye-shiryen aurar da Sadiya domin tuntuni aka sanya ranar auran ana d'agawa, saboda yanayi na rayuwa komai ni nake na hidimar auran, cikin 'yan uwan mahaifina babu wanda ya tambayeni
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download