Showing 51001 words to 54000 words out of 124287 words

Chapter 18 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16684

jikinta, ta fito daga motar, yayi mata jagora zuwa wani ke'bantaccen sashe, ya bude mata ta shiga da bisimillah a bakinta! tare da jin fad'uwa gaba a tare da ita.

Tana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe da key. ya bar gurin da saurin gaske.


Shuru falon babu alamun motsi! sai dai tsaf ko'ina a tsare babu datti a ko'ina.

Falo ne mai girma da kujeru masu kyau da labulaye! sai dak'in bacci guda biyu da kicin da bandaki duk a falon. a hankali ta zauna kan kujera mai cin mutum d'aya tana sake nazarin falon, gefe guda kuma zuciyarta sai bugawa take, shin ko daga ina mijin nata zai fito oho!


"Yallabai komai ya kammala, yarinyar tana wannan sashen daka umarce ni dana ajiye ta."
Sule ne ke wannan maganar lokacin da yake zaune a gabansa.

Ya cire farin gilashin dake sakaye a idonsa ya kalleshi sosai kafin ya ce."Matata ce Shahida."

Da sauri Sule ya kalle shi da dumbun mamaki a tare dashi ya ce." Matarka Yallabai?"

Yayi murmushi da fadin."Kwarai kuwa a jiya nan aka daura min aure da ita, itace yarinyar mutumin nan da nasa kayi min binkice a kansa."


Sule ya dinga jinjina al'amarin ya ce." Wallahi Yallabai ban gane komai ba, ita kanta yarinyar ban gane ta ba, sai dai nayi ta mamakin dalilin da yasa ka 'kebance ta a gidanka, sai na ce to ko da wani abu ne wanda kake shiryawa."


Ya ce." K'warai kuwa Sule kai din yaro na ne amintacce wanda na yarda dashi, nasan cewa ba zaka mance wahalhalun da nasha a can baya ba, auren farko ban yi dace ba, na biyu ma haka, wannan dalilin yasa gabad'aya nake tsoron duk wata 'ya mace saboda kaidi da sharrinsu, da yawa 'yan uwa da abokanan arziki suna fad'in ai ba duka suke da mugun hali ba, bahaushe yace wanda maciji ya sara idan ya ga bakin tsumma dole ya razana! a cikin zuciyata na cire aure gabad'aya daga raina! sabida samun zaman lafiya na, daga baya surutai na jama'a yayi yawa a kaina cewa ba girma na bane na zauna babu aure! wannan dalilin yasa na janye kudirina, auran wannan yarinyar nayi shi ne da manufofi da yawa. saboda haka kai kad'ai ne a gidan nan kasan wannan yarinyar matata ce, akwai wani shiri da nake akan lamarin duk don na gwada ta, da tarbiyarta." numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Matata ce, amma za ta zauna a matsayin matarka na d'an wani lokaci, ina nufin ko da wani daga cikin iyali na zai tambaye ka sai ka amsa da cewar matarka ce, shikkenan, amma babu ruwanka da zuwa sashen, sai dai idan ni na aike ka gurinta."

Sule ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, a sanyaye ya ce." To shikkenan Alhaji Allah ya sa a dace da tagari, ina yi maka fatan alheri ubangiji Allah yasa anyi kenan."

Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina Sule za ka iya tafiya sai na neme ka."

Godiya yayi sosai kafin ya tashi ya tafi cike da mamaki a tare dashi, ko da yake bai ga laifin maigidan nasa ba, duba da cewa a can baya mata sun wahalar dashi don yayi hakan ba laifi bane.


Kuka taci sosai! ganin duhu dare ya shigo gashi babu haske a falon, ko'ina yayi duhu! sai labulan tagogin dake falon ta janye haske ya shigo, hakan yasa iskar sanyi ta dinga shigowa, jikinta ya dinga kyarma! da sauri ta takure jikinta akan kujera tsoro na sake kanainaye ta, bud'e tagogin da tayi sai idanunta ya dinga yi mata gizo ta dinga ganin gilmawar abubuwa da yawa. da sauri ta je ta sauke labulayen ta koma ta zauna, babu abinda ya fi damunta irin sallar magariba da isha'i! ga yunwar da take mugun sasakarta!

Jin motsi kamar ana ta'ba 'kofa ya sa gabanta ya tsananta fad'uwa! ta tsirawa kofar ido! duk da bata da tabbacin ganin fuskarsa saboda duhu amma a jikinta take jin shine zai shigo.


Ya shigo da sallama ciki-ciki. ba ta ji ba amma ta ga inuwarsa.

Tsaye ta mi'ke! har yanzu jikinta bai dawo daidai ba.

Ya kunna hasken 'karamar wayarsa, nan ya hangeta a tsaye ta tsura masa ido, lokaci guda ya fahimci firgici da tsoro a tare da ita.

Sunanta ya kira babu walwala a fuskarsa.

Ta amsa cikin rawar murya.

Ya ce." Zo ki kar'bi wannan ledojin kayanki ne a ciki."

A sanyaye ta 'karasa kusa dashi tasa hannu ta kar'bi manyan ledejojin dake hanunsa.

Bayansa ta bi ganin ya nufi d'aya daga cikin d'akunan dake falon.

Ya juyo ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya ce." Nan d'akina ne kuma ina bukatar sirri! ki d'auki wancan dakin ya zama naki." ya fada yana nuna mata d'aya dakin. Yana gama maganarsa ya bud'e ya shiga ya barta a tsaye da ledoji a hannu.

Ta jima a tsaye a bakin kofar dakin tana tunane-tunane! daga bisani ta fara laluben hanya tunda ya shige dakinsa da hasken sai falon ya dawo inda yake duhu sosa! ta nemi kan kujera ta zauna ba tare da tayi tunanin shiga dakin ba, saboda tsoro take ji tana ganin gwara ta zauna a falon shi yafi mata alheri, amma haki'kanin gaskiya Baban-Baba yayi mata bazata! ba ta ta'ba tunanin zai mata wannan wulakacin ba, hawaye masu tsananin zafi suka shiga kwaranya a saman fuskarta.

Fitowa yayi daga d'akin ya ji shashshekar kukanta!

Tausayi ta bashi amma bai nuna ba, ya d'aga muryarsa sosai!" Ke menene? ki ke wa mutune kuka"

A zabure! ta juyo tana kallonsa! sai kuma ta sunkuyar da kanta amma ba ta fasa zubar da hawaye ba.

Ya ja tsaki! da fad'in." Ko yunwa ki ke ji ?"

Kai ta daga masa alamun hakane sannan tayi namijin 'kokarin fad'in." Ina so nayi sallar magariba da isha'i."

Ya ce." To waye ya hana ki? da duk zaman da ki ke a gidan ba kiyi sallar ba?"

Ta ce." Duhu ko'ina babu haske."

Ya ce." Ki bud'e wannan ledojin da akwai fitila da batiri a ciki sai ki kunna."

Da sauri ta fara dubawa, ya kunna mata hasken wayarsa har ta saita fitilar ta kama, sannan ya kashe wayarsa, ya kama hanyar fita, ta bishi da wani irin kallo zuciyarta sai bugawa take.

Tana d'aura alwala a bandakin dake cikin falon ta dinga jin motsinsa kamar yana shigowa da abu, sai da ta fito ne ta fahimci cewa kayan abinci ne.

Nan falon ta gabatar da sallolinta, ta jingina jikin kujera tana kallon shiga da ficensa tsakanin kicin da dakinsa.

Gani tayi ya zo ya zauna a daya daga cikin kujerun dake falon, ido ya zuba mata, sai ta kasa jure hada ido dashi, domin yanzu gabadaya tsoro yake bata, ya sauya sosai! ya dawo Baban-baba na asali wanda ta san shi a lokacin da yake kwanciya a 'kasan mota!

Gyaran murya yayi kafin ya kira sunanta yanda za ta ji.''

Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba.


Ya ce." Nan ne gurin da maigidana ya bani domin na zauna da iyalina. bayan haka kuma sa'i da lokaci za ki dinga zuwa kina gaisawa da kakarsa wacce take zaune a cikin gidan, za ki dinga taimaka mata da wasu abubuwa duk da cewa akwai masu aiki amma kema zaki shiga sahun su, akwai kayan abinci a kicin komai da komai na bukata maigidana ya bani kudi nayi miki sayayya! a cikin ledojin nan akwai kayan sawarki kala hud'u da mai na shafawa da sabulun wanka da wanki da sauran tarkacen ku na mata, abinda babu kada kiyi 'kwaron baki sai ki sanar dani, amma ina so ki zauna da masu gidan nan lafiya! mussaman maigidana domin shi ya mayar dani cikakken mutum kamar kowa, wannan dalilin yasa nake so kiyi masa biyayya kamar yanda za kiyi min, duk wani abu da yake bukata kiyi masa.''


A sanyaye ta ce." Insha Allahu zanyi iyakar bakin kokari na, ni dai buri na ka ri'ke ni amana kamar yanda kayi alkawari!

Tsaki ya ja kafin ya mi'ke tsaye ya ce." Wace amana kuma? ki daina wannan maganar, domin kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, saboda haka ki daina wannan maganar."

Wani irin kallo take masa tana jin maganganunsa na amsa kuwwa! a kunnanta "Kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, don haka ki daina maganar amana." Wannan magana ta jima tana yi mata yawo a k'wa'kwalwarta.



Jin yunwa na nema ta halaka ta yasa babu shiri ta dauki fitila ta nemi hanyar kicin ta je tana laluben abinci, aikuwa ta samu fulas cike da dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i! ga ledojin ruwa nan pure water ta dauka ta fito da fulas din abincin a hannunta.
*BINTU*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


53&54
A ta'kaice dai Shahida ita kad'ai ta kwana, domin tun da yayi fitar nan, bai dawo ba, tun tana jin tsoro har ta hak'ura ta barwa Allah al'amarin, sai dai bakinta bai daina addu'a ba har san da bacci 'barawo ya sace ta.

Motsin shigowarsa da asubah ya tashe ta, sai ta mik'e zaune da sauri tana laluben fitilar da gurin bacci ta fad'i a gurin, batiran duk suka watse

Shigowarsa yayi daidai da lokacin da ta gama gyara fitilar haske ya mamaye falon.

Ya kalle ta babu walwala a tattare dashi ya ce." A nan ki ka kwanta ne?"

Kanta ta daga masa alamar ."Eh." ya kama hanyar d'akinsa ba tare da ya sake wata magana ba, wannan ya sake tabbatar mata da cewa ba a gidan ya kwana ba.

Jiki a sanyaye tayi alwala ta fito anan falon dai ta gabatar da sallah, ta jima tana addu'a tana kuka sosai take neman sassauci a gurin mai duka domin ba ta ta'ba tunanin cewa zata fuskanci irin wannan matsala ba.

Sai da gari ya waye sosai ya fito cikin shiri ya d'ora rigar sanyi babbah da sabuwar hula irin ta sanyi ya rufe kunnuwansa sannan ya rufe idonsa da gilashi b'aki, tsira masa ido tayi domin gani tayi kamar yayi haske ba kamar can baya ba sai dai har yanzu wannan k'asumbar tana nan duguzaza! tare da tsalli-tsallin furfura.

Ganin yanda take kallonsa sai ya sha kunu! ya ce." Na zama tibi ne?"

Ba ta ji abinda ya fad'a ba amma yanayin yanda ya yi maganar yana tsatstare ta da ido ta fahimci cewa ransa a 'bace! sai ta d'auke kanta tana mamakinsa a cikin zuciyarta.

Gyaran murya yayi sosai ya bud'e ta domin ta ji abinda zai fad'a mata.

"Zan tafi can kudu wani aiki kamar yanda maigidana ya umarce ni, don haka za ki cigaba da zama anan babu wata matsala tunda akwai ci dasha saboda haka ki kwantar da hankalinki, amma ban amince ki je ko'ina na ba, abinda na aminta dashi zuwa gaishe da kakar maigidan kamar yanda na fad'a miki da farko.

Tsoro ta cire a ranta ta kalle shi sosai kafin ta ce." Shi maigidan naka bai san cewa kai ango bane zai tura ka wata uwa duniya, kada fa ka manta amana ka d'auko ni a gaban iyaye na mai yasa tun kafin tafiya tayi nisa ka sauya hali, wallahi ban yi tunanin haka daga gare ka ba."


Hannu ya d'aga mata da fad'in." Za kiyi min rashin kunya ne?" ta girgiza kanta. ya cigaba da cewa; idan na zauna a gidan me zanyi miki da har ki ke wannan maganar."

Sunkuyar da kanta tayi tana mamakinsa.

Ya cigaba da cewa'' Ai ban ta'ba ganin makwad'aicin uba irin naki ba, wanda bai san k'ima da mutumcin 'ya'yansa ba. domin ya ba ni auranki ne a matsayin fansa a gare shi, ke da bakinki kuma ki kayi al'kawarin girmama maigidana saboda alherin da yayi miki keda mahaifinki, amma har kina da bakin fad'in wata magana a kansa, to ki iya bakinki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan 'baci!

Kuka take sosai! ta ce." Yanzu mai ya kawo wannan maganar? wato ka naso ka nuna min cewa maigidan ka ya fi ni kenan, kada fa kamanta bani da kowa a wannan gari sai kai, ban san ko'ina ba, sannan akwai rashin sabo wannan shine dalilina na fad'in wannan maganar amma bada cin mutunci ba.

Tsaye ya mi'ke tare da fad'in" Ni dai na fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa.


Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?"

Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema."

Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo"

Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata."

Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa.


Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya.

Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba.

Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta.


Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi.


Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu.

Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne.

Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan.

Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escorts dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! "Wannan ai shahararran attajirin nan ne da ake nuna fuskarsa a tibi." sake kallonsa tayi a karo na biyu cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara ya nad'a farin rawani a saman hular. as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an.


Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya k'araso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta.

Bai amsa ba sai dai ya yi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa.

Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya.

Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi ciyayi! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske.

A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta.

Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata.

A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta,

Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba.

Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya."

Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login