Showing 75001 words to 78000 words out of 124287 words

Chapter 26 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16700

baka da aure, na samu labari a bakin abokinka Faruk, wannan dalilin yasa na nemi wannan alfarmar a gurinka.

Wato Faruk ne ya fad'a masa cewa; bani da aure, amma gaskiya ban ji dad'in abinda yayi min ba domin kwata-kwata babu maganar aure a tare dani, amma tunda al'amarin ya kasance haka, dole nayi hakuri, domin ba zan iya jayayya da wanda ya rufa min asiri ba.


Na ce" Alhaji Na gode da wannan kyauta da kayi min, tabbas hakane, bani da aure a yanzu, amma shekarun baya na auri 'yar uwata har da rabo a tsakaninmu."

Ya ce" Ma sha Allah. ai duk Faruk ya fad'a min komai. amma idan kana ganin da akwai matsala sai na janye.

Na ce" Haba Alhaji ai kafi 'karfin komai a guri na wallahi, zan auri 'kanwarka kamar yanda ka bu'kata"


Ya ce" Na gode sosai Saddiku da wannan rufin asirin da kayi min, sai dai kuma hanzari ba gudu ba"

Shuru yayi fuskarsa da alamun damuwa.

Na ce" Alhaji da akwai matsala kenan?"

Ya gyad'a kansa da fad'in" 'Kwarai kuwa Saddiku ba zan munafurce ka ba, yarinyar nan ta d'an yi yawo gaskiyar magana kenan, bana tsammanin za a samu budurci a tare da ita, bayan haka kuma tana da aljanu, wanda muke tunanin sune suke sanyata aikata munanan ayyuka"

Gabad'aya jikina ya mutu! cikin zuciyata nake tasbihi ga Ubangiji duba da irin kaddarar da take wanzuwa a tattare dani, ba zan ta'ba bijirewa umarnin Alhaji Harazimi ba, domin yayi min abinda ba zan manta ba.


Na ce" Alhaji kada ka damu. auran Zinaru a gare ni, kamar jahadi ne, mutukar tayi istibura'i zan aureta na kuma zauna da ita da zuciya d'aya, maganar aljanu kuma, ba su fi k'arfin Allah ba, insha Allahu zanyi iyakar bakin kokarina akan hakan.

Nan da nan, ya saki fuskarsa cikin jin dadin lafazi na, ya ce" Na gode sosai Saddiku Allah ya saka maka da alheri, hakika ka rufa min asiri a lokacin da nake bukatar hakan, a duniya bani da matsalar komai, sai ta Zinaru, 'kanwata ce, mu biyu iyayenmu suka haifa, asali mutumin Nijar ne, cikin zinder aka haife ni, neman kudi ya kawo ni Najeria, har nayi aure na tara iyali na, bayan rasuwar iyayenmu, Zinaru ta dawo hannuna, wallahi tunda ta zama cikakkiyar budurwa ta gagare ni, babu irin dukan da ban yi mata ba, amma k'arshe sai ta tattara kayanta ta gudu, sai tayi wata uku hud'u sannan zata dawo gida, wannan dalilin yasa na daina dukanta, sai na tsananta da addu'a tare da sanya matakan tsaro a gidana, amma duk da hakan, sai ta fita yawo, maza na d'aukarta a mota su tafi uwa duniya, wannan shine dalilin da yasa na yanke shawarar yi mata aure, ko Allah zai sanya ta shiryu.

Cikin damuwa na ce" Ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, duk abinda yayi farko, yana da 'karshe! ni nayi maka al'kawarin ri'ke yarinyar nan amana, zanyi iyakar bakin 'kok'ari na insha Allahu.

Sosai ya dinga yi min godiya har sai da ya bani tausayi.

Wallahi Shahida idan kin ga Zinaru, sai ki dauka ita tayi kanta saboda tsananin kyau! domin ta ko'ina tayi, cikakkiyar mace kyakykyawa, tana da duk abinda namiji yake bukata, dama na fad'a miki asalinsu, 'yan nijar ne, buzaye ne gashinta har baya gata da kyau! sai dai rashin kyawun hali.

Amma kin san wani abu, wallahi kwata-kwata ni ba ta kwanta min a raina ba, kawai dai na aureta ne saboda d'an uwanta, dama can a tsari na bana son auran kyakykyawar mace, saboda wasu dalilai nawa.

Zuwa na gurinta sau d'aya aka d'aura aure ta tare a gidana, washe garin ranar d'aurin auran Alhaji Harazimi yayi min kyautar d'aya daga cikin kamfaninsa na shinkafa! sosai al'amarin ya bani tsoro mutu'ka! na kalle shi a lokacin da yake bani takardun kamfanin, na ce"Alhaji kada muyi haka da kai, don Allah ka janye wannan kyautar, wallahi ban auri yarinyar nan don abun hannunka ba, na aureta ne tsakani da Allah, da kuma darajarka, amma ban aureta don ka bani wani abu ba.

Murmushi yayi tare da cewa" Saddiku ba ka ji bahaushe yana fad'in" Yaba kyauta tukwici ba, wallahi zan iya mallaka maka duk kadarorina, saboda rufamin asiri da kayi, ka auri 'yar uwata ba tare da ka 'kyamace ta ba, a wannan zamanin da kowane uba yake kokarin samawa 'ya'yansa uwa ta gari, sannan ba kowa ne zai yarda ya auri mace irin Zinaru ba, ai ni ka gama yi min komai, saboda haka kyauta nayi maka, kuma babu mai canza ta, ina bukatar ka tsaya da k'afafunka saboda nauyin iyali, tunda akwai yaran da su kayi iya aiki ta dalilinka, to za su cigaba da zama a 'kar'kashina, amma kai na 'yantaka insha Allahu.


Gabadaya sai jikina yayi sanyi da kalamansa, hannu biyu nasa na 'karbi takardun ina godiya. Ya ce" Zaka cigaba da gudanar da komai na kamfanin, domin ya riga ya bar hannuna, kuma na tara duk ma'aikatan dake karkashin kamfanin na sheda mu su komai, saboda haka kanka tsaye, zaka cigaba da gabatar da komai."

Na ce" Na gode sosai Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara suttura duniya da lahira, Allah ya amfani zuria" ya amsa da "amen ya Allah tare da mi'ko min hannu mu kayi sallama.


Abota ta da Alhaji Faruk babu ganin 'kyashi, ya taya ni murna sosai, kuma ya taimaka min ta hanyoyi da dama, har kawowa yanzu muna tare muna gudanar da harkokinmu.

Hajiya tayi farin cikin alherin da ya same ni tare da duk wani mai k'aunata, amma a zahiri ina ganin masu yi min hassada! sai dai tsakani na dasu addu'a ce.

Zama na da Zinaru da farkon fari, yayi dad'i sosai, don har na dinga k'ok'arin sanyata cikin zuciyata domin a lokacin ina ganin kamar tayi hankali ta nutsu ta shiryu kamar yanda muke bu'kata, don tun da na fahimci cewa; tana cikin jerin jarababbun mata nake kokarin ganin na kawar mata da sha'awarta a duk lokacin da ta bukaci hakan daga gare ni, sai dai ashe duka aikin banza nake, domin duk kokarin da nake akanta fita take yi tabi abokan shashancinta da aurena a kanta.

Hajiya ce ta tare ni da maganar ranar litinin da sassafe na fito da shirin fita ta ce" Saddiku ina son magana da kai."

Yanayin fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa maganar da za tayi tana da muhimmanci, duk da sauri nake a lokacin, sai na nemi guri na zauna tare da fadin" To Hajiya ina sauraranki.

Ta ce" Duk dai shiga tsakanin ma'aurata babu kyau, amma ni gaskiya abinda ake a gidan nan, ya fara damuna.

Na ce" Hajiya wani abu yana faruwa ne?" Shuru tayi tana girgiza kai kafin ta ce" Matarka bata da gaskiya Saddiku, domin tana aikata abubuwa marasa kyau!
Gabana ya fadi jin abinda tace, da saurin na ce" Me take aikatawa?"

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Kullum bata zama a gida, ka na fita take ficewa, kuma bata dawowa sai dare, sannan duk san da take gida wani mutum kullum sai ya zo gurinta su shiga daki, na ta'ba tambayarta shin wanane shi? sai tace ai d'an uwanta ne, ban yarda ba domin kwata-kwata basa kama da juna, wannan dalilin yasa nake zarginta."



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*_MAJANUNI!_*
_*The Unknown Rich Man*_
80&81
Kafin nayi magana sai ga ta fito, kamar wacce take la'be, ta tsaya 'kerere! a kan mu, ta nuna Hajiya da yatsa tare da fad'in'' To magulmaciya tsohuwa mai zuwa lahira da 'ko'kon dambu, duk na ji abinda ki ke fad'a masa sharri za kiyi min Allah ya isa tsakani na dake." tana wata irin girgiza irin ta rashin mutunci take maganar.

Kaina ya d'aure mutu'ka! na kalli Hajiya dake zaune idanuwanta sun ciko da ruwan hawaye sakamakon cin mutuncin da Zinaru ke mata, zuciyata ta cika da tausayinta, na kalle ta har yanzu tana tsaye a kan mu babu alamun risina a tare da ita, raina a 'bace na tashi tare da tsinka mata mari a fuskarta, cikin takaici da bak'in cikin abinda ta aikata na ce" Hajiyar tawa ki ke kira da magulmaciya saboda baki da mutunci."

"To idan ba magulmaciya ba mai zai sanya ta zaunar da kai tana shirya maka magana wallahi duk abinda ta fad'a sharri tayi min" Ta karasa maganar cikin k'okarin kare kanta.

Na ce" Wallahi ki iya bakin ki, muddun kina bukatar zama da ni to dole ne sai kin daraja Hajiyata mutu'kar kuwa ba haka ba, to zamu sa kafar wando daya dake.

"To sai me ? tafad'a tana buga cinya kafin ta cigaba da cewa; kai bari ka ji wallahi ba zan zauna kana taka ni ba, al halin na san da dukiyar d'an uwana kake fankama, akan me? wannan tsohuwar zata sanya min ido a gida har tana fada maka cewa; ina fita yawo to 'karya take munafuka ce"

Jikina na tsuma! na sake kai mata wani marin, ta kauce ban same ta ba, Hajiya ta tashi ta rirri'ke ni tana hana ni dukanta, ganin haka yasa tayi mana kallon banza tare da jan dogon tsaki! ta shiga daki ta bugo kofar da karfin gaske!

Zubewa nayi kan kujera tare da dafe kaina zuciyata in ban da zafi babu abinda take, Hajiya ita ta dinga tausar zuciyata har na samu sukunin tafiya ofis, amma duk da haka da 'bacin rai na yini, har sai da abokina Alhaji Faruk ya fahimci ina da damuwa. ya matsanta min sai na sanar dashi halin da ake ciki.

Ya ce" Ban yi mamakin faruwar wannan abu ba, domin dama can yarinyar bata da mutunci, sai dai shawarar da zan baka shine ka kula sosai, kuma ka sanya matakan tsaro a cikin gidanka, gudun kada ta je ta dauko wani ciwo ta kawo maka gida, ko kuma ta d'auko cikin wani ta kawo maka.

Na ce" Aboki na wallahi ni duk a tunanina yarinyar nan, ta shiryu ta daina duk wasu halaye marasa kyau! wannan dalilin ne ma ya sanya na saki jikina da ita har nake mu'amular aure da ita, ashe yaudarata take, tana ha'inta ta.

"Kayi hakuri abokina kaddara kowa da irin tasa amma ni kaina ina jajanta maka auran Zinaru, sai dai nayi maka alkawari insha Allahu, zan sanya ka cikin addu'ata, Allah ya kawo maka mafita.

Jikina a sanyaye na amsa da "ameen suma ameen abokina.


Gabad'aya daina shiga sabgar ta nayi, sannan kuma na saka matakan tsaro sosai a gidan, duk a k'okarin na ganin na kare martabar aurena.

Hakan da nayi sai ya sanya ta cikin damuwa mai tsanani, ashe kullum idan na fita zuwa take har d'akin Hajiya ta ci mata mutunci iya son ranta, watarana dai Shukura ta kasa daurewa ta mayar mata da martani, tunda a lokacin yarinyar tana da shekara goma sha biyu, ta fara sanin ciwon kanta.

Aikuwa kamar jira take, sai ta zari wayar redio ta kama yarinyar ta dinga dukanta kamar wacce Allah ya aiko, Hajiya tayi-tayi ta 'kwace yarinyar daga hannunta ta kasa, k'arshe ma ta dinga had'awa da ita tana duka.


Sosai ta farfasawa yarinyar jiki, da wayar redio, amma abin mamaki! ina dawowa gidan ta same ni tana kuka tare da fadin" Shukura tayi mata rashin kunya har da zagi, na tambayeta dalili sai ta fara kame-kame, ganin haka yasa na ce ta je zan d'auki mataki akan hakan.

Lokacin da Hajiya take yi min bayanin abinda ya faru. sai ta fito ta zauna duk abinda Hajiyar ta fad'a sai tace 'karya ne ba haka bane, na kalle ta da tsananin b'acin rai a tare dani na ce" Zinaru idan na sake jin maganarki sai ranki ya 'baci." shuru tayi tana zabgawa Hajiyar Harara.

Hajiya ta gama yi min bayanin duk abinda ya faru, raina ya 'baci sosai tunda na fahimci cewa babu laifin tsaye bare na zaune ta kama yarinyar da duka har sai da shatin waya ya fito a jikinta, na ce" Wallahi Zinaru, duk sanda ki ka sake dukan yarinyar nan sai na rama mata, domin ita d'in ba jakarki ba ce, da zaki kama duka sai kace an aiko ki, ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe.

'Budar bakinta sai ta ce" A wai! to ai 'yar taka ba cikakkiya bace, domin ita da shegiya ba su da maraba, duk ina da labarin komai, tsohuwar matarka ta je yawo can saudia ta d'auko cikin shege, ta haife ta kawo maka, saboda kai shakatafe ne kazo kana murna, wannan yarinyar duk ina da labarin komai a kanta"

Hajiya ta fashe da kuka tana fadin" Ki ji tsoron Allah Zinaru, ki bi duniya a sannu."

Tsaki ta ja mana kafin ta tashi ta shige daki ta bar mu cikin damuwa da tashin hankali.

Hajiya da Shukura kuka suke, ni kam! gabad'aya ma na rasa tunanin me nake, Shukura na tabbata jinina ce amma a gaban idona ana sheganta min ita, a lokacin idanuwana suka ciko da 'kwallah, babu shakka Fatima tayi mana gi'bi a rayuwarmu.


Gabad'aya gidan haka muka kwana da b'acin rai! in ka cire ita wacce ta haddasa mana damuwar kwana tayi tana shaye-shaye! na tabbatar da hakan ne, lokacin dana shiga d'akinta domin na nuna mata kuskuran da ta aikata.

Wallahi numfashi kasa sha'ka nayi sakamakon mugun warin da ya cika dakin, kwayoyi ne da kwala'ben kayan maye har da guntayen sigari wanda ta sha, tana kwance a kasan kafet tana ta sharar bacci.

Hankali a tashe na je ofis na kasa katabus! tunani da damuwa sunyi min katutu! ashe ba iyakar bin maza Zinaru keyi ba har da shaye-shaye? wannan abu ya tsaya min a rai sosai da sosai.


Bala'i ne ya faru bayan fita ta, domin Fatima ce ta je gidan, bayan dawowarta daga dubai! da yake kasuwanci take sosai, to duk sanda ta samu sukuni tana zuwa ta gaishe da Hajiya sannan ta duba Shukura, sai ta same su cikin damuwa! domin ita bata san ma nayi aure ba a lokacin, 'bacin rai da kishi suka rufe mata ido, lokacin da Hajiya take kuka tana fad'a mata abubuwan dake faruwa.

Ta duba jikin Shukura ta ga shatin duka a ko'ina, mayafi ta cire kawai ta nufi dakin Zinaru domin d'aukar fansa.

Fad'a da zage-zage su kayi sosai a d'akin, kafin su fito falo, nan ma suka cigaba da cin mutuncin junansu, tare da jifan kansu da munanan kalmomi.

Zinaru ita ta fara d'auko makami (wu'ka) wai sai ta kashe Fatima sai ta ga wanda ya tsaya mata.

Hajiya Hankalinta ya tashi sosai, gudun kada suyi aika-aika, yasa ta umarci Shukura ta kira ni da wayar mamanta, tana kuka take sheda min abinda yake faruwa.


Taimakon Allah ne kawai ya kawo ni gidan, lokacin dana shiga na samu Fatima a ruwan cikin Zinaru! sai dukanta take, don Allah ne ya bata sa'a ta 'kwace wukar, ta samu galaba a kanta.

Da 'kyar na iya janye Fatima na juya ina yi mata fad'a, kawai sai saukar wu'ka na ji a baya na, Zinaru ta soke ni da ita, lokaci guda jini ya jika riga ta yana d'iga a gurin. da gudu ta shiga dak'i ta kulle 'kofa!

Hankali a tashe suka rirrik'e ni suna kuka, ni kam ni kad'ai na san azabar na da nake ji, sosai wu'kar ta hud'a jikina.

Asibiti muka nufa. Emagency su ka bani taimakon gaggawa, sai dana na kwana tukkuna na dawo gida da tarin magunguna, bayana nannad'e da bandaji.

Ban iya fad'awa Alhaji Harazimi komai ba, kawai dai na ce dashi tsautsayi ne ya ritsa ni wani mai babur ya buge ni lokacin dana fito daga mota ta. Bayan tafiyarsa abokina Alhaji Faruk! Ya ce" Gaskiya ka bani mamaki Alhaji Saddiku mai zai sanya ka rufa mata asiri, wallahi bari na fada maka da yarinyar nan da ta samu nasara a kanka kashe ka za tayi, to mai yasa za ka cigaba da zama da ita, tunda ta zama annoba, kamata yayi ka shedawa d'an uwanta halin da ake ciki, cewa; tunda akayi auran nan baka samu kwanciyar hankali ba.


Girgiza kaina nayi na ce" Ba zan iya fad'awa Alhaji Harazimi wannan al'amari ba, domin ni nayi masa al'kawari cewa; zan jure zanyi hakuri da halayen 'yar uwarsa, kuma idan ka duba akwai shekaru a tare dashi, wanda ya kamata a ce yana samun nutsuwa da kwanciyar hankali a irin wannan lokacin, wallahi da bakinsa ya sheda min cewa, a duniya bashi da damuwar kowa sai ta Zinaru, ita kad'ai ce matsalarsa, to mai zai sanya na fad'a masa abinda zai d'aga masa hankali, wallahi ko yarinyar nan, zata kashe ni ba zan fad'a masa abunda zai d'aga masa hankali ba, zan cigaba da bashi amsa d'aya a duk lokacin da ya tambaye ni zan ce masa muna zaune lafiya.

Shuru yayi yana jinjina kai! na san yana mamakin karfin hali na, wanda ba kowa ne zai iya jurar wannan al'amari ba.


To har na 'karaci jinyyata Zinaru ba ta ce min sannu ba, sai dai duk san da ta ji muryar Fatima a gidan, za ta fito daga d'akinta ta nemi fitina, ni nake tsawatarwa da Fatima, a lokacin zata ci mutuncinta sosai tare da fad'in sai dai gani daga nesa amma Saddiku ya fi 'karfinta, wani lokacin Fatima har kuka take saboda takaici da 'bacin rai!

Tsayin sati hud'u bana kula ta, don gabad'aya na ajiye ta a gefe guda, sabgogin gabana kawai nake, sai ta same ni a daki bayan na dawo daga ofis, ta nemi guri ta zauna tana kallona.

Na ce" Kina bukatar wani abu ne?"

"Eh ina da magana da kai" tafada tare da tsira min ido, lokacin na karanci abinda yake damunta.

Babu walwala a tare dani na ce" Ina sauraranki.

"Ka san dai

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login