Showing 12001 words to 15000 words out of 124287 words
yana zagaya gari da ita.
Ya shedawa mahaifiyarsa shawarar da ya yanke kan cewa taje ta shedawa Huwaila cewa Eh tabbas da gaske yake zai auri Mariya domin ma yanzu ma shirye-shiryen kawo kudin aure yake.
Farin ciki ya lullubeta aikuwa ba taja dogon lokaci ba taje ta shedawa Huwaila halin da ake ciki Huwaila cike da farin ciki ta yafa mayafi domin zuwa ta shedawa Baba Asabe abinda yake wakana.
Baba Asabe addua kawai tayi ta barwa Allah amma daga can 'bangaran 'yan uwan Malam Almu an dan samu matsala domin sun so su hana faruwar al'amarin mussaman da sukayi binkice suka tabbatar da munanan halin Jamilu wanda ya zama abun gudu ga ko wane managarcin mutum.
Jamilu yana ganin haka sai ya shiga musu facaka da kudi lokaci guda ya toshe musu baki.
Kuma ba'aja dogon lokaci ba akayi komai a ka gama. amarya ta tare a gidanta dake unguwar ja'in.
Jamilu ya ga fa'idar auran Mariya domin daga sanda aka daura auransa da ita k'ofofin samu suka bude daga gareshi Allah ya albarkaci kasuwancinsa, a maimakon ya nutsu ya yi abinda zai taimaki rayuwarsa ai sai kawai ya hau shiririta da shirme, burni yake sosai ya sayi sabuwar mota kana kuma duk bayan wata biyu yake fitar da tufafinsa ya zuba wasu takalma da huluna gami da agogona kamar hauka a dakinsa, turare kam be yarda da mai arha ba mai tsada yake fesawa, Mariya tana ganin ikon Allah domin duk irin shawarar da take bashi baya dauka idan ta matsanta masa sai ya rufeta da fada da fadin kudinta ne ko nasa! Haka ta naji tana kallo ta zuba masa ido sai dai labarin duk abinda yake aikatawa a gari yana dawowa kunnanta tana da labarin yanda yake kashewa matan bariki kudi.
Sosai al'amarin yake cin ranta gashi har sunyi shekara da aure amma babu labarin haihuwa ta fahimci kuma shi sam abun bai dameshi ba harkar gabansa kawai yake.
Ta sameshi da maganar tana so ita dashi suje asibiti a dubasu domin a tabbatar musu da lafiyarsu.
Yayi funfurus! ya ce shi babu inda za shi lafiyarsa lau don haka kada ta 'kara yi masa maganar zuwa asibiti.
A ranar taci kuka ta koshi kuma yanzu ta fara nadamar auranta dashi dama wannan badakalar mahaifiyarta take guje mata, yanzu da kunya ta tunkareta da maganar domin kuwa tun farko itace ta za'bi auransa dole tayi hakurin zama da mugun halinsa.
Haka ta cigaba da hakuri yau fari goma baki don ma dai yana kokari ta fannin ci da sha daba don haka ba da ba zata ganu ba.
Tana kokarin warware matsalarta sai wata ta matsalar ta shigo domin kuwa mijin nata aure ya rakito ashe tuntuni har an kai kudi dasa rana bata sani ba sai ana saura kwana biyu daurin aure yazo ya ajiye mata leda viva da kayan fadar kishiya a ciki.
A ranar kwanan kuka tayi ta kudiri aniyar gari na waye wa zata tafi gidansu domin kuwa ba zata iya ganin wannan ba'kin cikin ba.
Yana d'akinsa yana shirin fita kasuwa ta fita daga gidan, koda ya fito yaga bata nan be wani damu ba dama yayi tsammanin faruwar haka, aure zai yi babu wanda ya isa ya hana shi.
Baba Asabe ta rufe idonta tace sam! bata yarda ba don haka tayi maza ta tashi ta koma dakinta ai duk wanda ya sayi rariya ya san zata zubda ruwa don haka ita bata da gurin kwana.
Haka nan tana ji tana gani ta koma gidan Jamilu koda ya dawo ya sameta a gidan, a maimakon ya rarrasheta ai sai ya tsiri gaba da ita ya dai nai mata magana har aka daura auran baya kulata.
Ta sake shiga halin ni 'yasu ta ko'ina babu sassauci sai ta mayar da hankalinta gurin ibadah da ro'kon sauk:i daga rabbis-samawati.
Jamilu da amaryarsa suka dinga sheka amarci ayi wanka tare aci abinci a tare sannan kullum da daddare idan ya dawo daga kasuwa ya sata a gaban mota su tafi su zaga gari ko ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba.
Amarya Hafsa ta dinga jiji da kai a gidan tana zubar da habaici ita ga matar da akeso, ita kuwa Mariya ta tattara komai ta barwa Allah ta zuba musu ido.
Aikuwa tafiyar ba tayi nisa ba amarya ta samu ciki, yana fahimtar haka sai yaje ya samo mata maganin zubar da ciki ya tsaya a kanta sai da tasha. A daran ranan cikin ya zube. Taci kuka ta koshi domin ita taso ta haihu ko don tayi wa Mariya gadara da hujja.
Koda ya fahimci amaryarsa tana da saurin da'ukar ciki sai ya daina kusantarta kai tsaye sai yasa kwaroron roba(condem) sannan yake auratayya da ita, Hafsa amarya ranta ya b'aci mutuka sai ta daina amincewa dashi, aikuwa be ji kunyar ci mata mutunci ba domin tsakar gida ya fito ya dinga zazzaga mata tujara da fadin." Dama lalurace tasa ya aureta ba wani gamsar dashi take ba ta dubi matarsa Mariya cikakkiyar macace me zai yi da ita idan ba kaddara ba.
Hafsa ta dinga kuka tana mamakin halin d:a namiji.
Ita kuwa Mariya ba tayi mamaki ba domin ta san abunda yafi haka zai iya aikatawa ita tafi kowa sanin halinsa
Tun daga ranar ya mak'ale mata ya dinga rarrashinta da kalamai masu dadi har da fadin kaddarace ta sa shi aure amma me zaiyi da wata bayan yana da ita.
Ita dai jinsa kawai take ta san ba komai yakewa dadin baki ba sai ni'imar da Allah yayi mata duk daran duniya baya iya hakuri sai ya kusanceta.
Tsayin wata biyar haka rayuwar take tafiya Jamilu ya watsar da amaryarsa kamar bashi ya ajiyeta ba, sai kawai ta tunkareshi domin taji matsayinta, ya kalleta sama da kasa kafin yaja mugun tsaki ya ce."Wallahi ban san dalilin da yasa na aureki ba dubeki don Allah guntuwa dake hanci k'ato in banda farar fata baki da komai."
Hafsa ta fusata! ta daga masa hannu da fadin." Kaga ya isa haka ka fada min matsayina a gidanka dama ai kafin na aureka sai da aka fada min halinka amma tsautsayi yasa na aureka.
Ya sosa gemunsa yana mata wani irin kallo ya ce."Kwad'ayin abun duniya ne yasa kika aure ni ai tun kafin naje neman auranki na gane ke din mayyar kudi ce shiyasa na rud'eki dasu kuma na samu nasara, saboda haka yanzu baki da wani amfani a gurina kije na sakeki saki biyu."
Hawaye suka k'wace mata ta ce."Sai Allah ya saka min wallahi kuma abunda kayi min sai anyi wa 'yarka."
Ko a jikinsa ya rubuta mata saki a takarda ya bata harda kudi dubu biyar akan takardar, a fusace! ta watsa masa kudinsa ta fita daga d'akin tana kukan bakin ciki.
*TAFIYAR TANA DA TSAYI??*
Ku karanta littafin a sannu a hankali, amma kada ku manta na fada muku cewa nayi amfani da salo biyu gurin rubuta littafin, sai a nan gaba za ku fahimta
*BINTA UMAR ABBALE*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi Join domin samun damar karanta littafi na daya
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*13&14*
Ya hujaj! bayan ya rabu da amaryarsa da wata uku sai ya hango wata 'yar dumur-dumur! mai cikar kirji fara tas da ita amma ba ta cika kyau a fuska ba dan Mariya ma ta fita kyawun fuska, to da yake yana da kudi a hannu bai sha wahala gurin siye zuciyar Talatu ba, dama ubanta talaka ne basu da komai koda yaje neman auranta basu wani tsananta binkice ba suka dauki 'yarsu suka bashi.
Wannan karon ba'kin cikin da Mariya ta had'iya yafi wanda ta had'iya a lokacin da ya auri Hafsatu, Talatu fitinanniya ce ta ajin karshe gabad'aya ta kanainaiye shi ta hanashi gane fari da baki ita kadai yake gani a gabansa, iskanci iri - iri suke a gidan, Sai ya kasance Mariya ta zama 'yar kallo domin tunda Talatu ta shigo gidan shikkenan ta kar'be girki da mijin gabadaya tsayin wata shida itake juya gidan sai abinda take so za'ayi.
Sai dai abinda Talatu bata sani ba shine duk ranar da ta tafi Unguwa shi kuma a lokacin yake samun damar shiga dakin Mariya yayi abinda yake bukata domin duk gigin da yake akanta ba wani cikakkiyar gamsuwa yake samu da ita ba, Yafi samun gamsuwar da yake bukata da Mariya.
Cikin ikon Allah ciki ya samu kuma bai bayyana kanshi ba sai da yayi wata biyar, ita Mariyar ta san da zaman cikin a jikinta. kawai tayi masa shuru ne saboda tana gudun ta fada masa ya zubar dashi tunda tana ganin irin k'wayoyin da yake dubgawa matayensa.
Aikuwa bala'i ne ya tashi a lokacin da Talatu ta farga da cikin tana kuka tana fadin." Ashe dama yaudararta yake yana kusantar Mariya gashinan har yayi mata ciki amma ita saboda mugunta duk sanda ta samu ciki sai ya bata magani cikin ya zube to dan haka wallahi ba zata yarda ba sai an zubar da cikin Mariya.
Budar bakinsa sai yace."Ta kwantar da hankalinta shi wannan ciki ba nasa bane domin shi rabon da ya hada shimfida da Mariya har ya manta.
Mariya tana share hawaye ta fito daga dakinta tana kallonsu a tsaye a tsakar gidan sai rarrashinta yake, Tace."Jamilu kaji tsoron Allah kaji tsoron ranar haduwar ka dashi, kai ka san wannan cikin na jikina kai ne ubansa amma ka ke shegenta shi.
Ya nuna ta da yatsa da fadin." Rufe min baki munafurka Allah ta'ala har yaushe na kwanta dake da zanyi miki ciki ban yarda ba tun wuri kije ki nemi uban danki."
Wani irin hawaye masu tsananin zafi suka shiga zuba a saman fuskata, ta dinga kokarin magana amma tsabar bacin rai ya hanata furta komai, a daddafe ta shiga dakinta, tasa hijabi ta fito.
Ya kalleta ya watsar da fadin." Duk in da zaki tafi kije domin kuwa ba zan yarda da wannan cikin ba.
Talatu zuciyarta tayi wasai dama babban burinta Mariya ta fita ta bar mata gidan ita kad'ai.
Tsakanin Baba Asabe da Hujaj! rigima aka tafka ba kad'an ba! domin kuwa Baba Asabe cewa ita ba zata yarda da wannan 'kazafin ba sai ta maka! shi a kotu a maimako ya risina ya bata hakuri domin su samu daidaito a tsakaninsu, sai ya k'ara fusata yace idan kotun k'oli zata kai k'ararsa taje ta kai babu abunda ya dame shi.
Baba Asabe kai tsaye kotun musulunci ta nufa ta d'auki lauya ya tsaya mata suka fara bugawa, da yake ita gaskiya duk inda take sai ta nuna kanta a take asirin Hujaj! ya tonu domin kuwa duk wanda zai bud'i baki a gurin ba zai fadi alkairinsa ba sai sharrinsa.
Alk'ali ya tabbatar da shedu daga bakunan jama'a a take ya yanke hukunci kan cewa dole Hujaj! ya amince da wannan ciki domin addinin musulunci ne ya amince da hakan, koda bashi yayi cikin ba tunda har ya kasance a gidanshi a ka sameshi dole ya dauki d'an da za'a haifa a matsayin d'ansa, bayan haka kuma dole ya cigaba da kula da matarsa da cikin da take dauke dashi, Ci da sha da kula da lafiyarsu duk yana rataye a wuyansa.
Mai sharia ya gama yanke hukunci ya buga katako alamun hukuncin ya tabbata, ya mi'ke. kotu ta tashi kowa na fadin albarkacin bakinsa.
Bayan kwana uku ya samu takarda da biro ba tare da tunani da tsinkaye ba ya rubuta saki har uku da kansa yaje ya har gidan ya bada takadar ya futo abunsa.
Baba Asabe ba ta iya karatun hausa ba, ita Mariyar ita ta karanta takardar a take a lokacin ta fadi a gurin, hankalin Baba Asabe ya tashi a wahalce aka kaita asibiti taimakon gaggawa akayi a kanta domin kuwa jininta ya kai k'ololowa gurin hawa.
Haka Baba Asabe ta dinga kai kawo ita kad'ai dan ma dai tana da kudi a ajiye shiyasa ta samu saukin wasu al'amuran.
A takaice sai da Mariya tayi sati uku a kwance a asibiti ta samu sauki likita ya dora ta akan magani tare da sharad'ai masu tsauri domin kuwa. hawan jini ga mace mai ciki babban matsala ne.
Baba Asabe ta sake yun'kurin shigar da kara kotu domin tun sanda alkali ya yanke hukunci Hujaj! bai ta'ba zuwa ya kawo naira biyar a cikin abunda alkali ya yanke masa ba.
Kawu Musa d'anta shine ya hanata yace ta bar maganar kawai su barshi da Allah domun duk yanda take tunanin Hujaj! ya wuce haka shaid'anin mutum ne, Sharia dashi bata da amfani.
Baba Asabe ta hakura ta bar maganar suka kyaleshi da mugun halinsa, Bangaran Mariya kuwa sai addua domin ita kadai ta san irin kuncin da take ciki bata ta'ba tsammanin Jamilu zai tozartata irin hakaba.
Allah al-musauwiru wanda bashi da tamka, ya fara saukar da ishara akan Hujaj! kasuwancinsa ya tsaya duk abinda ya ta'ba sai ya lalace ta kai ta kawo idan ya fita kasuwa haka zai wuni babu wanda zai zo gurinsa da niyyar sayan kayansa, Idan zai tafi gida sai ya ci bashi domin kuwa idan yaje gida babu kudi a jikinsa zasu kwana suna tafka rigima da Talatu.
Wani abokinsa ya jashi gurin wani malami domin yayi masa duba acikin al'amuransa yaga abunda yake kai kawo.
Kai tsaye malamin yace."Matarsa da ya rabu da ita itace mahad'in arzikinsa saboda haka idan yana so arzikinsa ya dawo tilas yaje ya dawo da ita gidansa.
Jin wannan magana sai hankalinsa ya tashi ya dinga share zufa yana tunanin yanda za'ayi ya cigaba da zaman aure da Mariya bayan yayi mata saki uku.
A hanyarsu ta dawowa gida Alhaji Shu'aibu ya kalleshi da fadin." Ya hujaj! naga duk ka tashi hankalinka wannan al'amarin fa duk mai sauki ne."
Ya kalleshi cikin damuwa yace."Alhaji Sha'aibu ya kake kiran wannan al'amari me sauki saki uku fa nayi mata ta yaya zan aureta dole sai ta auri wani sannan zata hallata a gareni."
Alhaji Sha'aibu yayi murmushi da fadin." Yanzu dai mu bari ta haihu akwai shawarar da zan baka."
Yace." Alhaji zama cikin kuncin talaucin nan ya isheni wallahi."
Yace."To ya za kayi kaine kayi ganganci ai irin wannan ba'a yanke hukunci kai tsaye sai mahukunta sun duba maka abunda ya dace da rayuwarka gashinan ka saketa ba tare da ka san itace abokiyar arzikinka ba."
Hujaj! ya girgiza kai da fadin." Wallahi sharrin zuciya ne amma nan gaba dole na kiyaye a yanzu dai burina ta dawo hannuna ko arzikina ya dawo."
Yace."Ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauki insha Allah.
*****
Alhaji Sha'aibu shi ya cigaba da kwantar masa da hankali, amma duk da haka kullum cikin lissafin wattanin cikin yake sai da ta haihu sannan hankalinsa ya kwanta.
Alhaji Sha'aibu shi ya bashi bashin kudi wanda yayi wa 'yar da aka haifa siyayya, sannan kuma shine ya jagorance shi zuwan gidan, kunyar duniya ta isheshi sai sunkuyar da kai yake, Alhaji Sha'aibun ne mai k'ok'arin magana
Baba ta kalleshi da fadin." Da dai banyi niyyar yi maka magana ba amma ta kama dole sai nayi inaso ka bude idonka sosai ka kalli wannan 'yar dake hannunka."
Yayi ta maza ya daga kai ya kalleta da fadin." Ai tunda na kalli yarinyar nan na tabbatar da cewa ni ne ubanta saboda haka don Allah Baba ayi hakuri kada ayi tone-tone duk abubuwan da suka faru a baya tsautsayi ne amma na san ban kyauta ba.
Ta girgiza kai da fadin." To naji maganarka wane suna kake ganin za'a sanyawa yarinyar ."? Da murmushi a fuskarsa yace."Sunan mahaifiyata nake da niyyar sanya mata Maryama kenan."
Tace."Shikkenan Allah ya raya ta yasa cikon addinin musulunci ce." gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah."
Da zasu tafi ya ajiye mata dubu biyar da fadin duk hidimar da ta tashi tayi da kudin kafin ranar suna."
Ba tace komai ba har suka fita daga gidan, Ta girgiza kai da fadin." Kullum yana fama da malin-malin(babbar riga) sai kace limami amma shaid'ancisa yafi karfinsa.
Itama Mariya dake uwar dakin maganar da take kenan, idan yana magana kamar mutumin kirki amma mugun halinsa yafi dubu! gabad'aya yanzu bata kaunar ta bude ido ta ganshi ta tsaneshi don dai kawai kaddarar aure ta ratsa a tsakaninta dashi babu yanda za tayi tunda ya kasance uban 'yarta dole tayi hakuri ta manta da abubuwan da suka faru a baya.
Ashe rigima ce take jiransa a can gidansa.
Ya shiga gidan cikin nishadi da walwala domin kuwa gani yake kamar Mariya ta dawo gidansa ta gama tunda Alhaji Sha'aibu ya fada masa shawarar da ya yanke kan cewa shi din ya amince zai yi *(Auran kisan wuta)* da ita zai saketa idan tayi wata daya ko biyu a gidansa, To tunda ya fada masa wannan magana yake farin ciki tabbas ya san Alhaji Sha'aibu ba zai cutar dashi ba.
A tsaye ya sameta a tsakiyar tsakar gidan sai kace wacce aka dasa! tsoro ta bashi da sauri ya kira sunan Allah kafin ya fuskanci itace yaja mummunan tsaki da fadin." Talatu ke wace irin jahila ce zaki tsaya tsakiyar tsakar gida sai kace aljana ko wani siddabarun kike min a gida."?
Ta fusata! dama a wuya take ta hayayya'ko! masa tana kumfar baki tace." Rufe min baki algungumi! munafiki duk halin da kake ciki na sani tsohuwar matarka daka saki ta haihu har kana siyayya kana kai wa jaririyar data haifa bayan da bakinka ka furta cewa ba kaine ubanta ba."
Ya daga mata hannu da fadin." Kinga saurara min! idan kuma kin 'kiya zanyi maganinki ni ba shashashan namiji bane da zaki titsiye da maganganun banza ni ne nan Uban yarinyar da Mariya ta haifa kuma a yau nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyata Maryama saboda haka ki hadiyi zuciya ki mutu."
Ihu! ta kurma! taje ta cikwikwiye masa riga tana zaginsa da fadin." Ya cuceta wallahi ba zata yarda ba sai ya sake ta.
Ya fizgeta daga jikinsa ya yar! a gurin yana fadin." Dama ai ke din baki dace dani ba saboda tunda na aureki komai nawa ya lalace
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download