Showing 90001 words to 93000 words out of 124287 words

Chapter 31 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16698

ya dawo daidai! wannan shine abinda ya faru. Hujaj yana zaune yana kallonsa har ya gama sanjawa kansa hallita ya dauki yagaggiyar rigar da yake amfani da ita a lokacin yasa a jikinsa, lokaci guda ya rikid'e ya zama Baban-baba.

Ya nemi guri ya zauna suna fuskantar juna ya ce."Nayi hakan ne saboda manufofi da yawa, alhamdulillhi na ci nasara domin na samu biyan b'ukata na had'uwa da macen da ta dace da rayuwata, a can baya nasha wuya sosai a hannun mata amma yanzu dole na godewa Allah na kuma gode maka da ka kasance mahaifi ga wannan yarinyar, na kuma yi alkawarin ri'ke ta da kyau dalili nasha wahala kafin na sameta, wannan shine dalilin da yasa na ce kazo domin na sanar da kai abinda baka sani ba. Asalin Sunana Abubakar Saddiku wanda jama'a da yawa suke kirana da 'Dangaske, ni mutumin jahar katsina ne cikin karamar hukumar Jibia kamar yanda nayi maka bayani a farko lokacin da nazo neman auran 'yarka da sunan Baban-Baba. sannan kuma ina so na tabbatar maka da cewa; Shahida tana nan cikin koshin lafiya ta kuma bani sa'kon gaisuwa a gare ka."
*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*


*MAJANUNI!*
(THE UNKNOWN RICH MAN)

98&99
Hujaj dai kasa daurewa yayi cikin rawar murya ya ce." Wallahi Yallabai na rasa wace irin godiya zanyi a gare ka. gabadaya kaina ya d'aure! ashe har na kai matsayin da zaka iya had'a jininka da nawa? Alhaji yanzu ace ka tsallake duk matan dake wannan duniyar ka zo ka auri yarinyar nan da bata cikakkiyar lafiya wallahi ni duk a tunanina wanda zai aureta irinta ne ko kuma dai mai ramgwamin gata saboda wai lalurarta ashe ba haka bane yarinyar tana tare da baiwar da ba kowa yake da irinta ba."

Cikin rashin jin dad'in lafazinsa ya ce."Amma ban ji dad'in jin wannan kalaman daga bakinka ba, ni waye dana wuce na auri yarinyar, na fad'a maka cancanta na duba har naji sha'awar auranta, kyawun sura ko tsantsar kyau na fuska bashi nake da bukata ba, kwanciyar hankali nake bukata, babu ruwana wai don yarinyar na da matsalar kunne! wannan sam bai dameni ba, kuma sonta nake da gasken gaske, duk duniya babu wata mace da take gabana kamar ita , saboda haka ina so kasa a ranka cewa; ni Shahida tayi wa alfarma tunda ta aure ni a matsayin mahaukaci! talaka! ta toshe kunnanta tace taji ta gani saboda k'aunar da take min babu halin da bata shiga ba, don haka wallahi ina kara jadadda maka cewa; Alfarma tayi mini, ba ni nayi mata ba, kuma tafi k'arfn komai a gurina."

Hujaj jikinsa yayi sanyi jin kalaminsa, sai bakinsa ya mutu, cikin zuciyarsa yake kad'aita Allah! lallai idan Ubangiji yana saukar da ikonsa dole kowa ya zuba ido, shi a haukansa saboda yarinyar kurma ce! to ba zata auri cikakken namiji ba dole shima zai kasance muskini sai gashi Allah ya d'aukaka darajarta ya aura mata miji mafi k'ololowa.

Shiru ofis din ya d'auka na 'yan mintina kowa da tunanin da yake.

Shi ya katse shirun ta hanyar fadin." Sannan ina neman wata alfarma a gurinka.


Da sauri ya ce."Ranka shi dade wace alfarma ce wannan?"

Yayi shiru yana nazarin maganar dake ransa, da akwai nauyi amma ya zama dole ya nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa tunda yana matsayin surikinsa ba zai so a ce mahaifin matarsa na aikata shirme ba.


Ya ce."Ina da labarin irin abubuwan da kake a gari na rashin kyautawa da zubda mutunci. ina rokonk'a da Allah da Annabi ka daina, saboda abinda ka iya zuwa ya dawo a nan gaba."


Jamilu kunya ta rufeshi ya sunkuyar da kansa yana wuri-wuri! tare da 'kokarin kare kansa.

Sai ya katse shi da cewa; Wannan duk ba hujja bace, Ubangiji da kansa ya ce" Ka tashi ka nema ni kuma sai na taimaka maka, ba zai yuwu garin son zuciya ka jefa kanka cikin sabon Allah ba, cah-cah! sam ba sana'a bace, akwai wulakanci da tozarci a ciki, sannan kuma dole ranar lahira Ubangiji ya tuhumeka, saboda haka ina neman wannan alfarmar a gurinka ka ajiye wannan harkar ka fuskanci alkibula mai kyau, ni kuma nayi maka alkawarin taimaka maka."


Cikin mashahuriyar kunya da nadama ya sunkuyar da kansa 'kasa a sanyaye ya ce." In sha Allahu na bari har abada Alhaji na daina da ikon Allah.

Cike da jin dadi ya ce."Na gode sosai da wannan alfarmar da kayi min.


Yana murmushi irin na ya'ke ya ce."Yallabai kafi karfin komai a gurina saboda haka babu godiya a tsakaninmu.

"Hakane" ya fad'a tare da tashi ya nufi wata dirowa kudi ya d'auko d'auri biyu dubu dari biyu ya isa har kusa dashi ya mika masa tare da cewa" Ga wannan ayi cefane, kafin na kammala shirye-shiryen da nake a kanka, sannan kuma ina so zaka bar wannan gidan da kake ciki a zaune akwai wani gidana dake rijiyar zaki zaka koma can da zama domin tuntuni an kammala komai ko gobe kake da ra'ayi zaka iya tarewa a gidan, tunda akwai komai na bukata.


Da sauri ya ce."Haba Alhaji ai babu wata jayayya a tsakaninmu, kayi min kyauta irin wannan nace sai nayi tunani wannan bai taso ba gobe in sha Allahu zan tare a sabon gidana, ina kara jadadda godiyata a gare ka, rabbi ya rufa maka asiri duniya da lahira ya jikan magabatanka."

Cikin jin dadin adduarsa ya amsa "Allahumma ameen na gode sosai Babana Allah ya 'kara girma "

Jamilu farin ciki ya cika masa zuciya, hakika yana alfahari da mutumin, kuma yana jin dadi a duk lokacin da zai kira shi da uba a gare shi, wannan kad'ai ya isa ya godewa Allah.


Mukkulin gidan ya bashi tare da fadin" In sha Allahu gobe kafin na tafi Sule zai kai ka gidan. Allah ya sanya alheri yasa an shiga asa'a." Ya 'kare maganar da yi masa fatan alheri.

Hujaj ya dinga amsawa yana washe baki! ga damin kudi na dubu dari biyu, ga kuma sabon gida! lallai haihuwa tayi masa rana.

Godiya ya dinga zabgawa har sai da ya dakatar da shi, ya nuna masa cewa; babu godiya a tsakaninsu, sannan ya hakura yayi shiru amma kana kallonsa zaka fahimci cewa; yana cikin farin ciki.


Kafin su yi sallama sai da ya sake neman wata alfarmar a gurinsa saboda ya lura cewa; kamar yana zumud'in zuwa ya kwazawa duniya halin da ake ciki, ya ce masa yayi shiru da bakinsa a hankali koma meye duniya zata sani.

Wannan ya sanyayyar masa da jiki! domin da sauri kawai yake ya fita ya je ya shedawa abokansa abinda yake faruwa domin ya nuna musu cewa; bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane. sai kuma aka katse masa hanzari, a sanyaye ya ce."Yallabai ai komai yana 'bukatar sirri in sha Allahu nayi alk'awarin babu wanda zan fad'awa halin da ake ciki, sai dai kowa ya gani a aikace."

Ya ce" To na gode sosai Babana, wayarsa ya d'auka ya kira Sule ya bashi umarnin ya d'aukeshi ya mayar dashi gida.

Jamilu ya tashi da kwarin gwiwa da karsashi! Aljihunsa cike da kud'i! su kayi sallama cikin mutunci da mutunta juna.


Yayi niyyar komawa gida a ranar, amma hakan bai samu ba saboda cinye lokacin da yayi gurin tattaunawa da mahaifin matar tasa, bayan haka kuma yana so ya je gurin Baba Asabe domin itama yayi mata cikakken bayani don fita daga cikin duhu! ya kamata ace kowa ya san waye shi a cikin dangin matar tasa.

Shukura ya kira a waya ya bata umarnin cewa; ta shedawa Shahida ba zai samu dawowa yau ba sai gobe."

Ta ce" To shikkenan Daddy zan fada mata in sha Allahu." kashe wayarta tayi ranta a 'bace! cike da kishi da jin haushi ta kalli Mamanta ta ce." Daddy ne fa ya kira yana cewa; na je na fad'awa kurma ba zai dawo yau ba sai gobe, sai kace ita kad'ai ya ajiye a gidan, ai mu ma muna da hakki a kansa.

Hajiya ta ce" To menene don yace ki fad'a mata matarsa ce fa, sannan kuma bata saba da wannan tafiye-tafiyen ba, mu kam! ai mun saba don haka ni banga abin damuwa b.....Hajiya Fatima ta katseta. rai a 'bace ta ce"Hajiya na lura fa bakya son abinda zai 'batawa yarinyar nan rai! duk maganar da za ayi a kanta sai ki kare! kada fa ki manta mune naki ita kuma kawota akayi daga baya kuma idan ta samu dama wallahi ba zata tuna dake ba, gwara ma kiyi karatun ta nutsu kuma kisa baki ya mayar dani dakina"

Ta ce" Ba zan yi masa dole ba wallahi! yarinya kuma ba za a had'a baki dani a zalince ta ba, me yasa ki kayi wasa da damarki a can baya wane irin rashin mutunci ne ba kiyi masa ba, yanzu ai na fahimci dalilin da yasa ki ke so ki koma d'akinki saboda kinga yayi arziki shiyasa ki ke binbini! to ni ba zan tilasta shi ba domin mai d'aki shi ya san inda yake masa yoyo."


Hajiya Fatima ta fashe da kukan takaici! "Yanzu Hajiya har wata banza ta fi ni a gurinki? kece fa ki ka haifi ubana amma 'kiri-'kiri ki ke nuna min 'kiyayya! meye a ciki don kin bashi umarni ya mayar dani, ai d'an adam ajizi ne, kuma kowa yana lefi, nayi nadama na bashi hakuri ko don darajar zuriar dake tsakaninmu ai ya kyautu ya tausaya min."


Hajiya ta ta'be baki da cewa" Yanzu ki ka san da haka, kina maganar zuria sau nawa kina zubar masa da ciki? itama Shukuran Ubangiji ne yasa zata zo duniya shiyasa ya nuna miki ishara! saboda haka yanzu ni na dawo daga rakiyarki Fatima ki nemi miji kawai kiyi aure don ni ba zan sa Alhaji Habu ya dawo dake ba alhalin baya ra'ayi."

Hajiya Fatima bakin ciki kamar ya kasheta ya zama dole ta shirya zuwa jibia domin ta samu Baba Audu da maganar tana ganin idan ta biyo ta kansa bu'katarta zata biya.

Ni dai na sauko na gansu jigum-jigum! muka had'a ido da ita sai kawai naga ta galla min harara! idonta yayi fululu! da alama kuka tayi, abin ma sai ya bani dariya amma banyi ba, nayi saurin dauke kaina daga kanta. Hajiya ta kalle ni da kulawa take tambayata Na ce" Zan shiga kicin ne domin samun abinda zan ci yunwa nake ji."

Fad'in Wannan maganar nayi sai naga Shukura tana motsi da bakinta tana min wani irin kallon banza! na san dani take, amma ban tanka mata ba kawai nayi hanyar kicin din, Hajiya ta ce." Da kin bari ma yanzu Marka zata fito ta shirya mana gurin cin abinci domin tana ciki tana aiki."

Sai na tsinkayi maganarta tana cewa" Jakar mata kawai dama ai irinsu ci gare su mussaman an samu shinkafa 'yar gwamnati da jar miya ai sai abinda muka gani."

Tayi maganar ne da sauti mai k'arfi don na ji, kuma sa'konta ya iske ni domin duk na karanci inda ta nufa, wato neman masifa take dani daga zuwanta.

Hajiya ta bude baki kenan za tayi magana na ce"Hajiya rabu da ita don Allah! domin duk na fahimci abinda take nufi da ni, to ni dai ba karya bace ballananta nayi ta haushi! sai an kula kashi yake d'oyi!


Aikuwa! da fad'in wannan maganata tawa sai suka fusata! Shukura kaina tayo tana d'ura min ashar da fad'in" Sai dai idan ni ce karya amma ba Mommynta."

Na kalle ta da cewa" Kin ga da wacce zanyi domin ita ce daidai da ni, ke baki isa nayi hayaniya dake ba sai da wannan." Na fad'a ina nuna uwarta dake zaune tana mamakina! domin bakinta mutuwa yayi, yanda na fuskanta tana mamakin yanda akai nake mayar mata da martani.

Darajar Hajiya kawai tasa na saurara musu na haye sama zuciyata sai tafasa take, dole ne idan ya dawo ya yi wa tufkar hanci domin ba zan lamunci cin mutunci ba.




*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
100&101
Jama'a da yawa sun yi mamakin ganin daya daga cikin motacin 'Dangaske na kutsa kai cikin layin dake tattare da kwazazzabai tare da kwatoci da tsibiri-tsibirin bola dake jibge a bakin kwatar. manya da yara suka dinga bin motar da kallon mamaki da tunanin dalilin da yasa motar shigowa layin,

To duk da cewa; ya shirya shiga unguwar da daddare hakan bai hana mutane fahimtarsa ba. abinda baya b'ukata kenan k'allo da surutun jama'a, hakan ne ya faru domin dai yara da manya cika su kayi suna bin motar da kallo har Sule ya damu guri ya tsaya daf da kofar gidan Baba Asabe. Aikuwa kafi ki ce kwabo wani yaro ya shiga gidan da gudu yana fad'in"Baba motar 'yan sanda ta tsaya kofar gidanki." Domin shi duk a tunaninsa motar 'yan sanda ce ganinta zungureriya baka wuluk! domin tintac ce ba a ganin wanda yake cikin sai dai na ciki ya ga na waje. abinda yasa jama'a suka fahimce shi saboda sunansa dake bayan motar 'Dangaske14 duk motacinsa na sufiri (zirga-zirga) sunan dake jiki kenan, shiyasa duk inda ya shiga baya 'buya jama'a sai sun sheda shi.


Baba dake lissafin kudi ta kalli yaron da faduwar gaba ta ce."Laminu 'yan sanda kuma? wane dalili ne ya kawo su gurina?"

Ya ce."Wallahi nima ban sani ba." yana fadin haka ya ruga a guje ya fita daga gidan



Gaza samun nutsuwa tayi ta suri mayafi ta d'ora a kanta don fargaba ta hana ta tsaya ta yafa mayafin a jikinta, da sauri ta kama hanyar fita tana salati, Saliha itama ta fito daga cikin d:aki gabanta sai dukan uku-uku! yake amma tsoro ya hana ta fi bayan kakar.

Hayaniyar jama'a ta cika gurin, yana so ya fito daga motar abin ya gagara domin dai yara da manya ne su kayi dafifi! a jikin motar, sai kace wani d'an siyasa! jama'a sai kambaba darajarsa suke tare da yi masa fatan alheri akan abubuwan da yake na alheri, sam bai ta'ba tsammanin cewa; zai samu wannan karamcin daga gurin jama'a ba.

Sule da Escorts d'insa suka dinga fama da mutane, cewa; suyi hakuri su bashi hanya ya fito domin gabatar da uzurinsa. Baba Asabe ta kutsa gurin tana tambayar abinda yake faruwa.Sule yake mata bayanin wanda yake cikin motar kuma gurinta yazo.

Kallon mamaki take masa bakinta yayi nauyi ta rasa abinda za ta fad'a, shin me ya kawo wannan Attajirin gurinta? Allah yasa dai ba wani sharrin aka 'kulla mata ba, domin dai tunda Shahida tayi mata gargadi ta daina sakin baki tana aibata shi a gaban jama'a.

A sanyaye ta koma cikin gidan tana shedawa Saliha abinda yake faruwa, Ita kuma shashashar sai ta raya a ranta cewa; ko ita yake so, tana farin ciki ta ce" Watakila ko ni ya gani yake so.

Baba tayi mata wani irin kallo kafin ta ce" A gidan uwar wa zai gan ki har ya ce yana sonki, bana son rashin hankali da shashanci! maza ki kira min babanki a waya! domin dai gabad'aya na tsorata da al'amarin wallahi."

Saliha da sauri ta shiga d'aki hannu na rawa ta kira Kawu a waya ta sheda masa cewa; Maza ya zo Babarsa tana nemansa.

Ta fito ta samu Baban a tsaye tana tunani ta ce" Na kira shi ya ce yana kan hanya.

Baba talfe ha'ba da hannunta jikinta yayi masifar sanyi duk ta tsure! sai tunane-tunane take. ita kuwa Saliha sai murna take cikin zuciyarta tana addua Allah yasa saboda ita mutumin ya zo gidan.


Yana zaune a cikin motar yana ganin yanda yaran nasa suke fama da jama'a, amma ko gezau! sun ja tunga sun'ki barin gurin, kamar ma jama'a k'aruwa suke a gurin, domin duk wanda ya zo wuce wa ya ji wanda yake cikin motar sai ya tsaya domin dai (Bangon sukari) ne a gurin kowa ya jingina dashi sai ya lasa.


A hankali ya sauke gilashin motar ya fito da kud'i masu yawan gaske ya bawa Sule da saurin gaske ya zuge gilashin yana murmushi ganin yanda hayaniya ta 'kara tashi a gurin sakamakon hango shi da sukayi.

Kud'i kenan masu raba gardama! kamar dama abinda suke jira kenan, sai suka yuya yuuuu! suka bi bayan Sule dake rike da damin kudin a hannunsa.


Wannan ya bashi damar bude motar wuf! ya shiga soron gidan, yana godewa Allah a zucci da fili na yanda ya azurta shi da dukiyar da yake taimako da ita "Allah ya kara rufa mana asiri." Ya fadi wannan kalma a fili.


Gyaran murya yayi kafin yayi sallama cikin gidan.

Baba ta amsa cikin sanyin jiki ta shimfida tabarma

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login