Showing 99001 words to 102000 words out of 124287 words
umarnin mai-gidan, abun mamaki! Hajiya Fatima da Shukura suna zaune a falon su kad'ai, Hakimar ta she'ka ado wanda ya ba ni mamaki! sai ka rantse da Allah cewa ita ce matar gidan, abinda ya sake d'aure min kai shine yanda gabad'aya hankalinsu yake kaina a lokacin da nake kokarin saukowa, sai muka shiga kallon-kallo a tsakaninmu, wani bahagon kallo suke min, yayin da ni kuma nake masu kallon mamaki! yanda na fahimta gabad'aya babu alheri a zuciyoyinsu. shiyasa na gyara fuskata, ban kuma yarda na bi ta kansu ba ballanatana wata magana ta had'amu kai tsaye kicin na nufa, a jikina kuma na ji cewar ba su janye idonsu daka kaina ba.
Wainar shinkafa da miyar tantakwashi! tare da kunun gyada Marka tayi na karin kummalo. lokacin dana shiga kicin din ta kammalla komai sai k'amshi ne yake tashi. Marka tana da tsabta da kula, kuma ta iya sarrafa abinci nau'i-nau'i! ba yanda za a yi ka shiga kicin din ka ga 'kazanta daga zarar ta kammala girke-girke take gyarawa ta goge ko'ina tasa turaran wuta, idan kuwa tayi abinci kamar kunne zai tsinkr?e saboda dad'i! shi kansa mai-gidan yana yaba k'okarinta! kuma baya shakkar cin abincinta, sa'i da lokaci kuma yana yi mata alheri sosai, domin har aikin hajji taje ta dalilinsa.
Cikin mutunta juna muka gaisa da juna. A nan ta samu damar yi min nasiha akan abunda yake faruwa, ta kuma bani shawarwari masu kyau! mutukar na daure zuciyata nayi amfani da shawarwarinta zan ci riba, sai dai hakurin shi yake da wuya.
Godiya nayi sosai! kafin na had'a duk abinda nake bu'kata na d'auki kwandon abincin na fita.
Wuce ta nayi tana waya amma babu Shukura a gurin ita kad'ai ce a zaune.
Cikin zuciyata na ce"Allah shine zai yi min maganinku.
Ina shiga d'akin ita kuma tana k'okarin fitowa! kallonta nayi, sai tayi saurin cewa;Anti ina kwana?" na amsa da nazarin abinda ya shigo da ita dakin, da sauri ta bude kofa ta fita, na sauke ajiyar zuciya tare da nufar gurin da yake zaune.
Na ajiye kwandon abincin dake hannuna a gabansa, na zauna tare da tsira masa ido. har yanzu fuskarsa tana nan a yanda take kadaran-kadahan! sai kawai na tsinci kaina da tambayarsa dalilin shigowar 'yar tasa d'akin.
Hankalinsa na kan wayar dake hannunsa ya ce." Wai mamanta ke kira na."
Wani irin kallo nayi masa mai kama da harara!
Ya ajiye wayar yana 'yar dariya da satar kallona. kawai sai idona ya ciko da ruwan hawaye! wato ya mayar dani abin dariya kenan.
Murya na rawa na ce"Gaskiya ba zan lamunta ba, kada yarinyar nan ta sake shigo mana d'aki domin hakan bai dace ba, sannan kuma ba tarbiya ba ce"
Ya ce"Zan yi mata magana in sha Allah."
Tashi nayi na bashi guri na je na kwanta duk yanda na so daurewa na kasa, hawaye suka shiga zuba a kumatuna.
Ni ban san yanda zan yi da wannan masifar ba, gabadaya matar ta hana ni kwanciyar hankali. masifar kishinta nake a raina.
A nasa 'bangaran kuwa dad'i yake ji ganin yanda take nuna kishinsa, hakan na 'kara masa sonta a cikin ransa, shi duk abinda take kawai kallonta yake idan ba wani kad'aru na Ubangiji ba babu yanda za a yi ya sake zaman aure da Fatima.
Abinci ya ci sosai! ya gama ya wanko bakinsa duk ina kallonsa.
Ganin yana nufo gurina yasa nayi saurin juya masa baya. ya hayo gadon yana d'ora hannunsa a jikina. na tashi zaune ido jawur na ce" Ka je kiran da take maka mana."
Girgiza kansa ya yi ya ce."Ba zan je ba domin shirme za ta zo min da shi a halin yanzu ke kad'ai nake da muradi."
Shiru nayi masa, ya kalle ni da cewa" Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki kinji ko, in sha Allahu komai zai daidaita, kuma zan yi miki hallaci fiye da yanda ki kayi min a baya.
Zuciyata ta tsinke! hawaye suka zubo! na ce"Sanin zuciyar mutum sai Allah! amma a jikina nake jin kamar akwai abinda zai faru mara dad'i, domin naga Fatima ta bud'e wuta! a kanka, ga kuma 'yarta tana taimaka mata da campaign. "
'Yar dariya yai ya ce." Da zan cigaba da zama da Fatima da sai dai ki zo ki sameta a matsayin matata, haukan banza take kuma zan kawo k:arshen matsalar in sha Allahu."
Ajiyar zuciya na sauke ina d'an jin sassauci a raina.
Hannu yasa ya goge hawayen da ya rage a fuskata. ido ya lumshe yana min wani irin kallo. Ya ce." Zaki biya ni bashin dana ke bin ki ko?"
A shagwabe na ce"Bani fa da lafiya ina ganin ma kamar na samu ciki."
A take fuskarsa ta sauya da wani irin annuri! ya rungumeni tsam-tsam! a jikinsa, sai godiya ga Allah yake, gabadaya sai jikina ya mutu! na dinga nadamar 'karyar da nayi masa lafiyata lau. kuma bana jin wani sauyi a jikina irin na masu ciki.
Cikin kunnansa na ce"Da wasa nake maka fa." Sake matseni ya yi kafin ya ce." Hakan zai tabbata in sha Allahu rabbi, yau zan bada himma! sai nayi cikin 'yan biyu a wannan rana."
Murmushi nayi tare d'ora hannuna kansa a hankali nake shafa gashin kansa had'e da wuyansa, na tsinci kaina da sumbatar gefan fuskarsa cikin tsantsar tausayi da k'auna na ce"Allahu ya amshi adduarka mijina."
Ya amsa da "ameen ya Allah." lokacin ya fara rikicewa sakamakon abubuwan da nake masa, wanda ni kaina nake mamakin hakan, sosai na tarairayeshi a ranar, ya mayar da kansa 'karamin yaro, ya dinga biye min ina zuba sangarta da shagwaba iri-iri! da wani irin salo ya tafiyar da ni, wanda muka jima a cikin yanayin cikin jin dadin juna, na kasance cikin farin ciki, domin ban ta'ba jin dadin al'amarin ba sai a ranar, salon ya tafi da ni mutuka! dan har sai da na fi shi za'kal'kalewa! hakan kuwa ya faranta masa rai! ya dinga sanya min albarka har iyayena sai da suka samu nasu rabon.
Bayan komai ya kammala sai kuma kunyarsa duk ta dabaibaye ni, na gaza kallonsa, shi kuwa babu abinda ya dame shi sai tsokanta yake da cewa; muddin zan dinga bashi irin wannan kulawar to ya rufe 'kofa! kuma sai yanda nayi da shi. murmushin kunya kawai nake amma a zuciyata wani irin farin ciki nake ji, ganin yanda na faranta masa, lallai kuwa zan zage damtse domin gaskiya bana kaunar kishiya, shiyasa na tashi hankalina akan tsohowar matarsa dake nema ta zama min ciwon ido.
A gurguje nayi wanka na fito yunwa na sasakar cikina, dama ban ci abinci ba, al'amarin ya wanzu! shiyasa har jiri-jiri nake. ko da na fito daga bandakin, baya nan, a zuciyata na raya cewa; ko ya tafi amsa kiran da akayi masa, ina shirya jikina ina wannan tunani, yayin da wani sashi na zuciyata ke nuna min ba hakan bane.
"Fatima." Ya ambaci sunanta idonsa a tsaye a kanta.
Ta amsa tana kallonsa tare da marairaice fuskarta!
Ya ce" Wai tun yaushe muke maimaita magana guda a tsakaninmu?"
"Bangane ba?" ta fada gabanta na fad'uwa!
"Ki nemi miji kiyi aure! wannan kalmar har na gaji da fad'a miki ita, idan domin ni Abubakar ki ke zaune a haka ba zan ta'ba mayar dake ba." Ya cire shakku da jin nauyi ya fada mata gaskiyar abinda ke zuciyarsa.
Sai ta rushe da kuka! da fadin" Me yasa? yanzu ashe ba zaka tausaya min ba, wallahi nayi nadama! a yanzu babu wani namiji da yake burgeni sai kai."
Ya ce." Bayan na zama wani abu a duniya ko?"
Shiru tayi tana kallonsa hawaye na zuba.
Ya girgiza kansa yana tuna kuttun! takaicin daya k'unsa! a can baya. ya ce" Abu biyu nake dubawa nake sassauta miki Shukura da zumuncin Allah. idan ba haka ba, da tuni na san yanda nayi dake wallahi, kin zame mini masifa a rayuwata, kin hana ni nutsuwa, nayi aure domin na samu kwanciyar hankali kin zo kin zaune min a gida kina neman fitina da matata, wannan shine maganata ta k'arshe dake, ki fitar da miji kiyi aure ko kuma ki fice min daga gidana, kada ki sake tafiya yawo ki ce zaki sauka a nan, sai na ci mutuncinki."
Kuka! take sosai tana kallonsa, shi kuma ya sha kunu! kamar bai ta'ba dariya ba ta ce" Abinda ta kitsa maka kenan? tun safe kana daki manne da ita tana shirya maka mugun abu har kake i'kirarin tozarta ni da cin mutuncin barin gida, ai idan Sadiya ce ba za ka yi mata wannan cin mutuncinba tunda ciki daya kuka fito, shikkenan babu komai rayuwa ce."
Tana mashahurin kuka take maganar.
Ya ce." Ke kin fi kowa sanin halina, babu wata mace da ita isa ta juya ni ko ta tsara min magana na hau kai na zauna, dama can kawaici nake miki, amma naga kina nema ki wuce gona da iri! don haka na fad'a miki ni ba zan mayar dake ba, ki fitar da miji kiyi aure, idan kuma ba hakaba ki tattara kayanki ki fice min daga gida.
Hannu ta d'ora a kanta ta kurma ihu! tana kiran sunan babanta wato Baba Auta. ni da nake sama sai dana ji ihun! ballantana su Hajiya dake daki, Sadiya na shirye-shiryen tafiya
Gabad'aya muka had'e a falon muka riski abinda yake faruwa.
Tana kuka ta je ta rungume Hajiya tana sheda mata irin hukunci daya yanke, Hajiya a sanyaye ta ce" Alhaji Habu kana cikin nutsuwarka kuwa? Fatima fa 'yar uwarka ce kada giyar kudi tasa ka ci mutuncin zumunci!
Ya ce." Hajiya na gaji da abubuwan da suke faruwa a gidan nan, ke da kanki kin san yarinyar nan itace matsalata, to mai zai sanya ta zo ta hana ni nutsuwa da matata? darajarki da zumuncin dake tsakaninmu yasa har na amince take zaune a gidana, amma bayan haka banga dalilin da zai sanya tazo tana tayar min da hankali ba, ga yarinyar nan Shahida kullum cikin kuka take da 'bacin rai iri-iri, saboda haka hukunci na riga na yanke ta fita min a gida mutukar ba zata fito da miji tayi aure ba."
Kafin Hajiya tayi wata magana Shukura ta yanke jiki ta fadi a gurin, hankali kowa ya tashi, yarinyar wani irin abu take kamar mai farfad'iya! ko wacce manyan aljanu suka buge! gidan ya hargitse da koke-koke! ni kaina kukan nake ina nadamar tunzura zuciyarsa da nayi gurin yanke wannan hukunci!
Da 'kyar da tasirin addua Shukura ta dawo daidai! amma sai kuka take tana rokon mahaifin nata, ba tare da ya yi wata magana ba, ya haye sama ya bar mu cikin alhini da tashin hankali.
Fatima a ranar ta tattara kayanta ta wuce Jibia cikin halin damuwa tare da nemo hanyar warware matsalarta, tafiyar uwar ya 'kara tayar da hankalin 'yar a ranar dai sai da ta fad'i sau uku! har sai da uban ya kira wani malami ya raba dare a kanta yana addua sannan aka samu sassauci!
Babu wanda ya rintsa a tsakaninmu, domin nima kuka nasa masa na ce hukuncin da ya yanke ya yi tsauri da yawa! kada jama'a su zarge ni, tunda ina jin lokacin da Hajiya ke fad'in" Shekara da shakaru! Shukura bata ta'ba abu makamancin wannan ba, lafiyarta lau kuma bata da iskokai!
Washe gari! Sadiya ta had'a kan yaranta suka tafi cikin kuka da damuwa domin ita kanta ba ta ji dadin faruwar al'amarin ba, saboda ganin yanda Hajiya ta sauya gabad'aya tunda abun ya faru take kuka! al'amarin dai yana nema ya zama tashin hankali da rabuwar kai.
Ashe tashin hankali na gaba, domin mai-gidan ne ya kwanta magashiyan ciwo ya ta shi, muka sake shiga damuwa matsananciya! kuka! nake ina nadama domin gani nake kamar ni na haddasa rikicin! yayin da a 'bangaransa yake jaddada min cewa; kada na dami kaina, dama can da wannan kudirin a cikin ransa.
Da taimakon Allah dana likitansa jikinsa ya warware! amma sai da ya yi sati biyu bai fita ba a cikin halin jiyyar Baba Audu ya kira shi a waya wai yana nemansa, wannan dalilin yasa bai tunkari garin ba sai da warware sosai! sannan ya shirya zuwa, nima ya ce na shirya domin gabadaya zamu tafi har da Hajiya, wacce gabad'aya ta sauya min, ta daina sakar min fuska, sai dai duk lokacin dana gaisheta zata amsa amma babu kulawa kamar yanda ta saba.
*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*
116&117
Jikina gabad'aya ya yi sanyi sakamakon faruwar al'amarin, yanda Hajiya ta d'auke min wuta shine ya fi damuna, dalilin da yasa nake tsoron zuwa garin nasu domin ban san abinda zai faru ba, abinda na fahimta shine Hajiya tana ganin kamar da sanya hannuna gurin hukuncin da mai-gidan ya yanke. shiyasa nake shakkar shiga cikinsu don ban san irin kallon da za su yi min ba.
Jiki babu k'wari nayi wanka na fito na same shi har ya kammala shiryawa yana sanye da manya kaya dakakkiyar shadda (wagambari) da aikin irin na sarauta a jikin babbar rigar, kasancewar shaddar sky blue ce sai ya yi amfani da farar dara ya nad'a farin rawani a kansa, kamar dai koda yaushe ya sakaye idanuwasa da farin gilashi. gefen gado ya zauna yana sanya safa a k'afarsa gefe takalminsa sahu ciki ne a ajiye.
Babu kuzari nake shiryawa lokacin na ji yana waya da alama babban abokinsa ne don na ji lokacin da ya ambaci sunansa Alhaji Faruk!
Ina k'o'karin daura dankwali a kaina ya ce." Ki maza ki sauko ku gaisa da abokina yana 'kasa, saukarsa kenan ya shigo domin duba ni, gashi kuma mun shirya barin garin.
A sanyaye na amsa da "To." daga haka bai yi wata magana ba ya fita daga dakin.
Mayafi na d'auko wanda ya dace da less din dake jikina, Sannan na fito da set din takalmi da jaka masu kyau! wanda suka dace da shigar da nayi.
Duk da ban yi wata kwalliya a fuskata ba, nayi kyau sosai! ni kaina na sheda hakan, komai na jikina na mussaman ne, mussaman gold din dake wuya da hannuwana.
Ban fesa turare ba saboda na san hakan haramun ne a matsayina na matar aure sai dai idan ina tare da mijina
A nutse na sauka k'asan na same su gabad'aya har da Hajiya suna gaisawa.
Wani irin kallo Hajiyan tayi min kafin ta amsa gaisuwata, ban ji dad'in hakan ba, shima na lura bai ji dadin abinda tayi min ba.
Gudun kada ba'kon dake zaune a gurin ya fuskanci wani abu yasa na saki fuskata sosai! na gaishe shi da yanayin da Allah ya hallice ni, shi ma wani irin kallo naga yana yi min, sai na sunkuyar da kaina ina jin wani irin rashin dad'i, a duk lokacin da zanyi magana da yawa mutane sai su dinga yi min wani irin kallo wanda bana jin dadin hakan, shiyasa sau tari idan na shiga cikin mutane nake shiru da bakinta idan ba da wani dalili mai k'arfi ba bana magana har na bar gurin, to a halin yanzu mijina ne kawai yake fahimtata kuma baya kyarata! baya nuna gazawarsa akan komai nawa, shine yake magana da ni kai tsaye kamar yana magana da mai lafiya irinsa, ya riga ya gama gane yarena, wanda a cikin kurame ni ina daya daga cikin masu saukin fahimta.
Yana murmushi ya ce."Amarya tuntuni nake son zuwa mu gaisa Allah bai nufa ba sai yau! kwana biyu bana zama shiyasa, sai kuma na samu labarin rashin lafiyar abokina wannan dalilin yasa ina sauka a garin na shigo domin na dubashi sai gashi kuma kun shirya barin gari zaku je jibia ko?" Bakinsa na bi nan na gane abinda yake nufi tunda bai yi maganar da karfi yanda zan ji ba.
Na ce"Eh wallahi. Ai ya ji sauki da taimakon Allah da na likitansa, amma duk da haka mun gode sosai da ziyara."
Ya ce."Babu komai ai an zama d'aya Allah ya sanya alheri." na amsa da "Ameen" Ina wasa da yatsun hannuna.
Kud'i masu yawa ya ajiye min a gabana, da cewa; Ga wannan babu yawa ko."
Na ce" Kai da kazo dubiya kuma har da wahala."
Dariya yayi, ya kalli abokin nasa dake tsaye ya zuba hannuwansa cikin aljuhu, kallo daya za kayi masa ka fahimci cewa yana da damuwa!
Ya ajiyewa Hajiya kudi masu yawa irin wanda ya bani, sallama ya yi mana suka fita tare da abokin nasa suna tattaunawa.
Ya ce" Abokina amma abun ya bani mamaki fa."
Murmushi yayi da cewa" Dole ne amma hakan shine alheri a tare da ni.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce." Sosai yarinyar ta bani tausayi wallahi. Babu yanda Allah baya zartar da ikonsa. amma Allah yasa hakan shine alheri da samun kwanciyar hankalinka."
Ya amsa da "Ameen ya rabbi amma ina da damuwar Fatima har yanzu."
Kallonsa yayi da bukatar k'arin bayani.
Nan ya warware
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download