Showing 60001 words to 63000 words out of 124287 words
ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta.
Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje!
Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta.
Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba.
A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba.
Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta.
Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu.
Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar.
Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani.
Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta.
Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take.
****
"Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba.
Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan."
Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki."
Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta."
Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida.
Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba.
Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri.
Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen"
*****
_"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_
Wannan shine abinda Saliha ta rubuta.
Tana hawaye take tura amsa kamar haka.
_"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_
Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba.
Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa.
Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali.
Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta.
Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah.
Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.''
Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari."
Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da har zai farauce ki, to shikkenan misali a ce maganarki gaskiya ce, ni na amince ki bashi kanki a madadina domin bani da wata cikakkiyar lafiyar da zan kwanta dake, na fad'a miki wannan mutumin ya fi karfin komai a guri na, saboda haka na amince a duk lokacin da ya buk'aci
wani abu a gurinki ciki kuwa harda kwanciya dake, to kada kiyi masa jayayya domin yin hakan na barazana da auranki, ki amince masa kai tsaye kuma ki sakar masa jiki sa'anan kiyi k'o'karin faranta masa, ki ji a ranki kamar kina tare dani, wannan shine abinda za kiyi ki faranta min rai.
*WASA FARIN GIRKI!??*
Ko ya zata kasance? ina fatan za ku biyo ni domin karanta cikakken labarin, don wannan sominta'bi ne, kada ku manta akwai labari a 'kasa jingim! don haka masoya kada ayi 'kasa a gwiwa gurin biyan kudi domin jin yanda za ta kasance. Ni ce taku a koda yaushe
*BINTA UMAR ABBALE*
MARUBIYAR
*1-NANA KADIJA*
*2-YARO DA KUDI*
*3-GIMBIYA BALARABA*
*4-BABBAN YARO*
*5-MASHAHURI*
*6-LADIDI KWADAGA*
*7-RUWAN DARE*
*8-SADAUKI OMAR*
*9-NIDA YAYA SADAM*
*10-YAR BANGAR SIYASA*
*11-DA WATA A KASA*
*12-MADADI*
*13-KWARYA TABI KWARYA*
*14- GA IRINTA NAN*
*15-MATSALARMU A YAU*
*16-GOJE*
*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*
65&66
Lamarin dai babu dad'i domin wani lokacin idan tsanani yayi yawa sai mutum ya gwammace mutuwarsa akan rayuwar da yake, sai dai kuma hausawa suka ce idan aski yazo gaban goshi to ya fi zafi! hakane kowane bawa akwai irin tasa kaddarar wanda babu wanda ya isa ya goge ta, to ita kam tana tunanin wannan ce kaddararta wanda ta tazo da kafafunta ta sameta har inda take, babu shakka wannan mutumin ya zame mata jaraba da kuma kaddara, ba kowa ne sila ba sai Mijinta wato wanda ta kwallafa rai a kansa take ganin shi din mai kaunarta ne, ashe kallon kitse takewa rogo, mutum ne shi azzalimi mayaudari, ta amince masa ya cutar da ita.
Har ta gaji da zubar da hawaye, watakila rashin kukan ne ya janyo mata toshewar mak'ogwaro domin wani k'atoton abu ne ya zo ya tsaya mata a wuya! sai kuma damuwa da fargabar da tayi mata katutu!
Da 'kyar ta iya tsakurar abinci cokali biyar kacal ta ci gabad'aya cikinta ya cushe! tasha ruwa ta kwanta lamo a tsakanin kujeru! wannan duhun ma babbar masifa ce, domin tuntuni batiran fitilar suka mutu! sunyi ruwa basa bada haske, gashi kwana biyu bata ga Sule ba ballantana ta fad'a masa.
Sosai kanta yake mata ciwo domin ba wani cikakken bacci take samu ba saboda tunani yayi mata yawa shiyasa bacci ya kauracewa idonta sai dai ta yi shi a tsin-tsinke.
Lumshe idonta tayi tare da kiran sunan Allah da ya kawo mata d'auki! a rayuwarta.
Motsi ta ji a kanta bayan masifaffen kamshin turaransa da ya bakunci hancinta, sai tayi gaggwar bud'e ido ta tashi a razane! shine ya shigo, to ta wace hanya? bayan duk ta rurrufe k'ofofi!
Innalillahi-wa'ina ilahi raji'un! abinda ta fada kenan kafin ta ja jikinta ta matsa can gefe tare da takurewa a jikin kujera.
Gurin yayi shuru bayan zamansa da minti biyar ya bud'e muryarsa sosai kafin ya ce." A ina maganarmu ta kwana ina fata baki mance cewa yau ne cikar kwanakin dana baki ba.
Shuru tayi tana kallonsa amma ba sosai ba, saboda babu hasken a dakin sai na wayarsa da ya kunna.
Ya ce"Shurun da ki kayi ya tabbatar min da cewa kin amince kenan?"
Uffan ba tace masa ba, wata mummunar shawara ta yanke a zuciyarta. kawai sai ta tashi ta nufi kicin cikin zafin nama!
Ya bi ta da kallo tare da tunane-tunane a ransa.
Hannu bibbiyu ta ri'ko zabgegiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta cikin set ta zo ta tsaya a kansa tana wani irin huci! kamar kububuwa!
Gabansa ya fad'i! amma bai nuna a zahiri ba sai ma gyara zamansa da yayi ya kalle ta a lokacin da jikinta ke wani irin rawa ga wu'kar a rik'e a hannunta sai kyalli take! Ya ce."Me ki ke shirin aikatawa?" Kai tsaye ta ce." Kashe ka zanyi, na kashe mugun iri." sai maganar ta bashi dariya, da murmushi a tare dashi ya nuna kirjinsa da fadin." Ni zaki kashe?" Ta ce." K'warai kuwa, meye amfaninka a wannan duniyar ai baka da amfani wallahi"
Yayi dariya tare da cewa" To na ji yanzu ya ki ke so ayi?"
''Ka fice daga rayuwata mutukar kana so ka cigaba da numfashi a doran duniya. Tafada tana gyara ri'kon wukar da hannunta
"Ba zan iya ba domin na fada miki cewa zuciyata da gangar jikina ne suke bukatarki"
"Ashe kuwa za kayi asarar rayuwarka" Ta fad'a tana wani irin nishi! ba kuma tare da yayi tsammani ba ta kai masa wani irin sara! yayi saurin kaucewa wuk'ar ta sauka a hannun kujera tsabar yanda wukar ta huda kujerar sai da soson ta fito!
Jikinta na rawa! ta ce"Sai dai a kashe ni amma nayi alkawarin raba ka da rayuwarka mutukar ka keta min alfarma.
Ya shiga rud'ani sosai! yarinyar da gaske take, kuma ya yaba da k'okarinta kwarai da gaske, sai dai makamin dake hannunta yana nufin abubuwa da yawa, wani tunani yayi kafin ya ce." Ajiye wannan makamin na hannunki mu yi magana."
'Kin ajiyewa tayi ta kalle shi sosai da fad'in." Ashe kana tsoron mutuwa"
"Bana tsoron mutuwa sai dai ina fargabar a ce kece sanadiya domin zaki kare rayuwarki a wahalace!
Ta ce" Bana nadamar hakan, ni dai burina rage mugun iri, irinka wanda baya tsoron Allah."
Kansa ya girgiza tare da auna maganganunta.
''To yanzu idan nace na janye aniyata a kan ki zaki yarda?"
"Wallahi ba zan yarda ba domin ban ga alama ba"
Yayi yun'kurin tashi! ta sake kai masa wani saran a karo na biyu nan ma Allah ya kiyaye bata same shi ba.
Wannan karon ya tsorata sosai! ya kuma fahimci da gaske take tana iya kashe shi, domin tseratar da rayuwarta. A halin yanzu ta sa shi a tsaka mai wuya domin daga yayi motsi zata zabura! ta nemi illata shi da wukar hannunta.
"Na janye kud'iri na a kanki idan na rantse da Allah zaki yarda?" Yafada da alamar roko da tsoro a tare dashi.
Ganin haka yasa ta ce." Ka rantse da zatin Allah da buwayarsa"
Ya ce."Ni Alhaji Saddiku na rantse da girman Allah ba zan aikata abinda nayi niyya ba, na tuba ga Allah na tuba gare ki"
Ta matsa gefe tana numfarfashi tare da sauke wu'kar 'kasa.
Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi tsaye tare da zuba hannunwansa a cikin aljihu!
Cikin nutsuwa ya nufi gurin da take tsaye! gabanta ya fad'i! ganin ya nufo ta sai tayi yun'kurin sake d'aukar wukar yayi sauri ya riga ta har sai da ta yanke musu hannu ita dashi, amma ba sosai ba, saboda halin da suke ciki yasa babu wanda ya damu.
Fuskarta yake kallo jikinta na ta wani irin rawa! ya kama hannunta suka zauna a kujera! matsawa tayi can gefe tare da nuna masa hanyar fita da hannunta,
Ya gane abinda take nufi sai ya girgiza kansa alamar "A'a"
Da muryar Baban-baba ya ce"Ba zan fita anan ba domin ke mallakina ce kuma matar rufin asiri uwar 'ya'ya na anan gaba.
Da mummunan tashin hankali take kallonsa a lokacin da yake maganar gabad'aya rasa miyau tayi a bakinta. "Baban baba kuma? shine kuwa domin muryarsa ce ke mata amsa kuwwa a kunne!
"Ni ne Alhaji Saddiku Dan gaske, kuma ni ne Baban-baba mahaukacin nan na bakin kasuwa mai kwanciya a k'ar'kashin mota."
Shikkenan ta faru ta 'kare! innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wai shin me yake shirin faruwa ne da rayuwarta!
Hannayenta ya ri'ke tsabar tashin hankali ta kasa k'wacewa sai wasu irin tunane-tunane take wanda suke nema su haukatar da ita.
Ya ce."Na san dole kiyi mamakin haka amma ina neman afuwa a gare ki matata! duk wannan abubuwan da suka faru tsakanina dake ina da manufa kuma ina so ki bani hankali da nutsuwarki"
Hannu ta d'aga masa tana so tayi magana amma ta kasa! sai kawai ta fashe da wani irin kuka! jikinta in banda rawa babu abinda yake.
Rungumeta yayi a jikinsa yana rarrashinta tare da shafa bayanta, bata hana shi ba, domin a wannan lokacin rarrashin take bukuta, tayi lamo a jikinta shi kuma yana ta aikin jijjigata kamar wata jaririya!
A hankali ta cire jikinta tana kallonsa shima din ita yake kallo tausayinta duk ya cika masa zuciya ya rasa wane kalar rarrashi zai mata, domin ya san dole hakan zata faru idan ya fito mata da gaskiyar lamari.
Kokarin tashi ta fara sai yayi gaggawar ri'ke mata hannu da fadin" Ina zaki je?"
Shuru tayi masa tana dauke kanta.
Ya janyota ta zauna a cinyarsa! ya ri'ke ta sosai suna kallon juna! ya ce." Ki kwantar da hankalinki fa wannan duk ba abin damuwa bane! wallahi nayi hakan ne domin wata manufa tawa, za kuma ki fahimce ni idan na baki labarin abinda ya faru da rayuwata a shekarun baya, saboda haka ki cire shakku ko mamaki a ranki, Ni ne Alhaji Saddiku d'an gaske! kuma ni ne Baban-baba."
"Me yasa kayi min haka?" tayi magana a karo na farko da faruwar al'amarin.
Ya ce." Ina da hujjoji da yawa, amma ina so ki bani aron hankali da nutsuwarki domin na sheda miki abubuwan da suka faru a shekarun da suka wuce.
Ido kawai ta zuba masa tana kallonsa, shi kuma sai ya sake matseta jikinsa, ta kwantar da kanta a kafad'arsa tayi sanyi sosai domin al'amarin ya tsorata!
Muryarsa ya bud'e sosai yanda za ta ji ya ce."
*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
_*Hajiya Umma Hamdala ina godiya da shawarwari tare da k'warin gwiwa??????*_
69&70
Jin saukar ajiyar zuciyarta, yasa ya d'an shafa gashinta, a hankali yasa bakinsa daidai kunnanta ya hura iska kad'an, kafin ya ce." Kinyi shuru, na cigaba da baki labarin ko?" kanta ta d'aga tare da sake gyara kwanciya a kirjinsa, gabad'aya jikinta ya mutu sakamakon labarin rayuwarsa da yake bata ashe da sauran rina a kaba, domin kukan da take shafar mai ne akan wanda za tayi anan gaba.
Ya sauke nannauyar! ajiyar zuciya kafin ya ce.
"Mahaifina ya samu jama'a sosai wad'anda suka sallaci gawarsa da wad'anda suka bada sheda arziki a kansa! sai dai kuma tun bayan da aka kai shi gidansa na gaskiya kowa ya watse babu wanda ya zauna, suma 'yan uwanshi zaman da su kayi na 'yan mintina ne, suka kama gabansu, al'amarin ya bani mamaki sosai, a nan na gane cewa babu wanda yake saurin kaskanta a duniya sai talaka, wato mutane sun san ko da sun zauna zaman makoki babu abinda za a fito musu dashi daga gidan mamacin, shiyasa suka watse! sai nake tunanin yanda jama'a ke tururrubi gurin zaman makokin wanda yake da farcen susa, wani ma don ya ci abinci ya ke zuwa ya zauna, ko da bashi da alaka da mai mutuwar, wannan kuwa talaka ne wanda bai ajiye ba, kuma bai bawa kowa ajiya ba, amma dai ko da kowa bai zauna ba, 'yan uwansa sa zauna domin kar'bar gaisuwa, duk da cewa zaman ba dole bane a shari'ar musulunci, amma ai an mayar dashi al'ada, a lokacin zan ji dad'i mutukar da wani a kusa dani, sai ya kasance ni kad'ai nake kar'bar gaisuwa domin babu wanda yake zaune gefe da gefe na, sai dai ina farin ciki sosai idan na tuna cewa mahaifina yayi mutuwar shahada, ya kuma shiga ranar juma'a, bayan kyakykyawar sheda ta mutane.
Ranar sadakar uku ni da k'anwata Sadiya muka yi masa saukar al'kurani maigirma, bayan haka kuwa babu wani abu da 'yan uwasa suka yi masa na sadaka, a tsaitsaye suka tafi mussaman Baba Auta don shi ko zama beyi ba yace yana da uzuri, gwara Baba Audu ya d'an zauna na 'yan mintina kafin ya tashi ya tafi.
Hakan bai dameni ba, domin ni babban buri na da fata na, ace mahaifina ya dace da rahamar ubangiji.
Sosai na tashi hai'kan! da neman kud'i, duk abinda za'ayi da jiki k'arfi ina zuwa na yi mutukar zan samu abinda
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download