Showing 30001 words to 33000 words out of 124287 words
da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so."
Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake.
A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana!
Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa."
Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan."
Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa.
A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci!
Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata.
Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani!
Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido.
Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta.
Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin.
Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin.
''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta.
Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."?
Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka."
Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."?
Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci.
Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."?
Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa."
Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza!
Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin."
Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi."
Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin.
Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya.
Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*31&32*
"Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar.
Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita.
"Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa!
Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan!
Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali.
Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse?
Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata k'arfin iko na a kan 'ya ta."
Ta ce." Me take nufi to?
Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana."
Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke."
Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa.
Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa.
Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya."
Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!"
Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki."
Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan."
Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta."
Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi."
Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.''
Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa.
Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata.
Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici!
Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba."
Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu."
Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba.
Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan.
Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa.
Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba.
Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!
Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta."
Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu.
Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.''
Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?"
Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku!
"Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun.
'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?"
Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.?
Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci."
Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau."
Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa.
Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu.
Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke......
*****
"Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa.
Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.?"
Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a."
Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa.
Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune.
"Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba."
Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa."
Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe.
Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa.
Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake.
*Binta tana mik'a sak'on gaisuwa ga ilahirin masoyanta??????*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
*33&34*
*KANO*
Unguwar giginyu.
Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take.
Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai!
Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje.
Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko?
A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah."
Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida."
Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar.
Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba.
Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara."
Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka!
Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar dalili ita kad'ai ce babu wasu. shiyasa take lallabata. ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa
Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba.
Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa.
Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu."
Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu."
Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana."
Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare su ka yi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma."
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita."
Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin.
Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download