Showing 36001 words to 39000 words out of 124287 words
yake."?
Cike da rashin fahimta ya ce." Waye?
Murya a sama ta ce." Baban-Baba."
Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa."
A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata.
A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji."
Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan."
Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba."
Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko?"
Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin.
Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka.
Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida."
Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka.
Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba.
*Jama'a tafiya tana kara nisa kada dai ku manta cewa wannan littafin na kudi ne adalci guda da nayi muku tsawaita free peges har book1 ina fatan za ku yi kokarin sayan littafi na biyu, domin karanta cikakken labarin.*
Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce...#500 Vip 1k 0542382124..Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ki dauko hoton katin mtn ki tura mini ta WhatsApp, mutanan nijar kuma za ku turo da dala dari Vip jakka daya, katin airtel za ku tura min da shi ta wannan number
07084653262
Allah ya ba mu sa'a da rabo mai amfani.
_Akwai ingantaccan maganin???? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci????_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joining domin samun damar karanta littafi na daya*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
Pege
37&38
'Kamshi turaran ta ne ya tabbatar masa zuwan ta gurin.
Cikin nutsuwa ya d'ago kansa daga barin karanta jaridar da ke hannunsa.
'Bata fuskarsa ya yi yana yi mata wani irin kallo na tuhuma.
Lallausan murmushi ta yi masa ba tare da tace komai ba ta fara kokarin zama a kujerar dake fuskantar sa.
Cikin tsawa! ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi. "Ka da ki sake ki zauna anan gurin.'' Ya fada yana zare mata gabad'aya idanuwansa yanda ya tsani mutuwarsa haka ya tsane ta Fatima tayi masa illah a rayuwarsa.
Da hannu ya nuna mata hanya da fadin." Fita ki bani gurin tun kafin ranki ya 'baci."
Ta girgiza kai still da murmushin a fuskarta ta ce." Ai ko babu komai ka tsaya ka saurare ni domin kaji da abinda nake tafe, idan ban ci albarkacin Shukura ba sai na ci arzikin zumuncin dake tsakaninmu domin dai ni ba zan yi gaba da kai ba."
Tsaki ya ja ya koma ya zauna tare da cigaba da karanta jaridar dake hannunsa.
Gurin yayi shiru na minti biyar kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta kalle shi wani irin bala'in son sa na ratsa dukkan sassanan jikinta, ita ce tayi wauta a wancan lokacin, gashi yanzu ya yi mata nisa tayi-tayi ta shawo kansa ta kasa, saboda babu wacce ya tsana sama da ita.''
"Maganar Shukura nake tafe da ita." Ta yi maganar idonta a kansa.
Shuru bai d'ago kansa ba ballananta ya bata amsa. sai ta d'ora da fadin." Aiki na samo mata a babban kotun birnin tarraya ina fata ba zaka watsa min 'kasa a ido ba."
Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.''
"Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita.
Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba."
Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko?
"Yes na sa ni da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah."
Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta."
Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace!
Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin.
Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya.
*******
Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya!
Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba."
Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na."
Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki?"
Jin abinda Baban ta ce yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa."
Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar ta yi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka!
Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko za ki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne."
Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa."
Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi."
Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa."
Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai.
Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban."
Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."
*******
"Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa.
Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin dai Hujaj! gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa.
Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata!
Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa ya yi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa!
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
WANDA BAI JI BARI BA...!
39&40
To ko da ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo domin ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. sai wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance!
Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama gidan a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da yake sanya rai a kansu duba da cewa malaminsa ya tabbatar masa da samuwar su.
Alhaji Sammani ya nu na rashin amincewar sa akan hakan. A cewarsa ya za ayi yai masa wasa da dukiya duba da cewa shi a dunkule ya bashi, amma zai tsinka masa kud'i a cikin miliyan biyu da rabi an bashi miliyan d'aya mai zai yi da ita a wannan lokacin da yake bukatar kud'in masu kauri da zai yi order amma za a zo masa da wasa! ba tare da 'bata lokaci ya nufi police station. domin shigar da 'kara mutukar akan kudi ne baya saurarawa kowa ciki kuwa har da 'yan uwansa.
"Alhaji Sammani ban yi tunanin za kayi min haka ba wallahi, yanzu ni ka kawo police station? na d'auka ai kai mai rufa min asiri ne a kowane hali. Alhaji Sammani me akayi akai miliyan biyu da rabi da har zaka tozarta ni."
Murmushi ya yi ya ce" Alhaji Jamilu ni kaina ban so hakan ba amma duk kaine ka janyo duba da ganin yanda kake min yawo da hankali alhalin na sheda maka cewa ga bukatar da zanyi da kudin nan. shin wai ko so ka ke ka talautani ne kamar yanda ka talauta kanka."
Murmushin takaici ya yi ya ce." Kana da damar da zaka fad'i duk abinda kake so, amma ka sani sai kayi nadamar abinda kayi min.''
Ya zakud'a kafad'arsa da nuna alamun bai damu ba ya ce." Kud'i na kawai nake bu'kata a yanzu gani a zaune ga kuma Yalla'bai shi zai zama shaida zan kar'bi miliyan d'aya ba don raina ya so hakan ba sai don samun maslaha a tsakaninmu, sabida haka ka fadi lokacin da zaka cikan kud'i na."
Shuru yayi gumi sai karyo masa yake.
D.P.O Ya ce." Alhaji Jamilu kai muke saurare."
Kansa ya d'ago ido jawur! ya ce." karshen watan nan insha Allah zan biya Alhaji Sammani Kud'insa."
D.P.O yayi rubutu cikin wata takarda ya bashi ya sanya hannu.
Ya kalle shi da fadin." Wannan shine 'karshen magana Alhaji Jamilu, iyakar adalci anyi maka kada lokaci ya cika ka zo da wata magana, hukuma ba zata saurare ka ba idan baka cika al'kawari ba to zamu d'auki mataki na gaba."
Ya ce." Babu damuwa Allah zai rufa asiri." Daga haka bai saurari jin wani abu daga gare su ba ya tashi fuuuuu! ya fita daga ofis din. Duk suka bi shi da kallon mamaki!
****
A shirye ya fito ya same ta zaune a falo tana kallo. kafin ma ya yi magana ta riga shi da fadin." Ranka ya dade ina son magana da kai." Tunda ya ji haka sai yayi murmushi ya nufe ta ya samu guri ya zauna tare da fuskantar ta. cikin zuciyarsa yake raya cewa maganar dai d'aya ce amma ba zai yi saurin yanke hukunci ba tukkuna.
Ta gyara zaman ta da fadin." Hajiya Fatima ta kawo k'arar ka akan Shukura wai ta samo mata aiki amma ka hana shine nake so na ji dalili."
'Bacin ransa ya danne ya ce." Hajiya ki cire kan ki a cikin wannan maganar don Allah. domin ba ni da wannan ra'ayin, babban buri na shine Shukura ta samu miji nayi mata aure amma ni ba zan yarda da wannan tsarin ba."
Ta ce." Sabode me? kenan karatun da tayi ya tashi a banza?" Ya ce." Bai tashi a banza ba mutukar za tayi amfani dashi ta hanyar da ta dace. nufi na anan shine ta tarbiyan tar da yaran ta sannan tayi biyayyar aure."
Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Hakane kai ma kana da hujja amma ai har yanzu ba ta samu tsayayye ba, mai zai hana ka bar ta domin ta ci gajiyar karatun da tayi."
Girgiza kansa ya yi, alamun bai amince ba. ya dan kalli agogon dake daure a hannunsa ya ce." Wannan maganar mu bar ta kawai Hajiya kawai ki cigaba dayi mata addua'a."
Ta ce." To shikkenan Allah ya za'ba mata miji nagari." Ya amsa da "ameen."
Kallonsa tayi lokacin da yake kokarin tashi ta ce." Yanzu kuma ina ka nufa? kwana biyu dai na ga ka zauna a gida ka huta sosai na ji dadin hakan."
Ya ce." Kano zan tafi amma iyakaci na kwana biyu zuwa uku zan dawo saboda akwai tafiyar da zanyi zuwa Spain insha Allah."
Ta ce." To Allah yayi jagora ya tsare ka a duk in da zaka shiga. Sai dai ba zan fasa yi maka maganar aure ba, Alhaji Habu mutukar ka naso ka cika cikakken mutum to dole kayi aure idan ba haka ba to jama'a ba za su daina zargin ka ba."
Murmushi ya yi ya ce." Na kusa aure Hajiya insha Allahu kiyi min addua."
Fuskarta cike da annuri ta ce." Alhamdulillahi haka nake so na ji to ubangiji Allah ya baka tagari.''
Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina."
********
Tsabar fargaba da tashin hankali ya haddasa masa matsanancin ciwon kai! wanda duk dauriyarsa sai da ya kwanta! hankalin Talatu ya tashi domin ko banza idan ya fita ya samo wani abu yana rage mata wata wahalar gidan! ta shiga nan, ta fita can. yawon cin bashi domin samun abinda za su ci da yara.
Ganin saura 'yan kwanaki wa'adin ya cika ya sanya ya yanke shawarar sanar da ita halin da ake ciki ko da taimakon da za tayi akan lamarin.
Tashin hankali kenan! maimakon ta tausaya masa halin da yake ciki sai ta shiga surfa masa rashin mutunci da tsiya iri-iri da tozarci! a cewarta shi ya sayi hakan da kud'insa saboda haka ita babu wani taimako da za tayi masa domin shi kadai yake cin kud'insa hakkinta da na yara baya saukewa! saboda haka matsalarsa ce! a halin da ake ciki 'ya'yansa ne kawai suke tausaya masa domin sune suke jinyarsa! Talatu ba ta bi ta kansa harkokin gabanta kawai take.
Jamila ce ta yanke shawarar zuwa ta fad'a mata halin da mahaifin nasu yake ciki na rashin lafiya, da kuma irin tashin hankalin da suke ciki.
Kasa hakuri tayi hawayen takaici suka k'wace mata! ko shakka ba tayi fargaba da tashin
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download