Showing 3001 words to 6000 words out of 124287 words

Chapter 2 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16665

k'arkashin motar ta fara dube-dube duk da tasan kudin basa gurin.

Kallonsa tayi da fad'in." 'Yan sanda zan dauko maka yanzu ai gamu ga police station haukanka na 'karya ne" Cikin sauri ta bar gurin.

Yana tsaye ya rungume kirjinsa da hannuwansa idanuwansa a kanta a lokacin da take karkashin tsohowar motar tana dube-dube.

Jikinta ya jik'e da gumi ta fito daga 'kasan motar da 'karfi tace."Baba banga 'kudin b........Had'a ido sukayi yana kallonta jiki a sanyaye tace."Babu kudin a gurin." Kai ya gyad'a mata. sai ta matsa ta bashi guri ganin yana kokarin ture ta, ya shiga ya zauna tare da rungume gwiwarsa still idanuwansa na tsaye a kanta.

Baba Asabe Cike da kwarin gwiwa ta isa station din duk ta zayyane musu abinda yake faruwa.
Koda sukaji abinda take tafe dashi sai suka shashantar da maganar saboda sun riga sun san sharia da mahaukaci sai wanda ya shirya bayan haka kuma duk tsayin watannin da mahaukacin yayi a unguwar ba'a ta'ba kawo musu shi da sunan ya aikata mummunan aiki ba. saboda haka sai suka sallameta tare da kafa mata hujja da cewa ko don gaba ta daina cewa za ta yi sharia da mahaukaci domin kuwa al'kalami ya sauka daga kan duk wani mai matsalar k'wakwalwa.

Jiki a sanyaye ta fito daga station din ranta duk a bace! tana tafe tana zancan zucci da irin hukuncin da za tayi wa yarinyar.


Ita kuwa Shahida tana nan tsaye a gurin gabanta sai faduwa yake ta san halin Baba Asabe akan kudi babu shakka yau sai buzunta.

A jikinta take jin yana kallonta amma tsabar fargaba ta kasa juyawa ta kalleshi ta fahimci a cikin haukan nasa harda kallo a ciki to idan ba haka ba menene abin kallo a tare da ita.


Ya jima yana kallonta kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya hannunshi yasa ya ja gefan hijab dinta.

Cikin wani irin yanayi ta juya suka hada ido. muryarsa ya daga sosai da fadin." Wacece ita?"

Zuciyarta ta karye hawayen da take ta tattalinsu suka su'bce. A raunane tace."Kakata ce."

"Ina iyayenki?" ya fad'a still idonsa na kanta, kai ta sunkuyar jin tana shirin fashewa da kuka, ya sake maimaita maganarsa.

Murya na rawa ta ce." Mahaifiyata ta mutu Babana kuma yana can unguwar Ja'in da matarsa da sauran 'yan uwana."

Zama ya yi ba tare da ya sake magana ba. A sace ta d'an Kalleshi da gefen idonta, al'amarinshi akwai abun mamaki a ciki maganarsa cikin nutsuwa babu alamun ta'bin hankali a ciki ko dai akwai wani abu da yake 'boyewa ne? gashi ba yaro bane da shekarunsa yanda take ganinsa ma kamar zai yi shekarun mahaifinta, Kallonsa ta sake yi taga ya rungume gwiwarsa da hannuwa biyu yana girgiza kansa can kuma sai taga yana 'yar dariya.
Cikin faduwar gaba Ta ce." Baban-Baba kana jin yunwa ko?"
Ba tare da ya kalleta ba ya daga kanshi.
Ta ce." Yanzu a ina zaka samu abinci?"
Ya kalleta na second biyu kafin ya kauda kansa.

Wata maganar take shirin yi masa ta hango Baba Asabe ta tsallaka titi, ya kalleta cikin tsawa yace."Ki tafi ki bani guri." da sauri taja gefe tana kallonsa, ya dauki iccen dake gabansa yana nuna ta dashi.
"Na ce dake ki tafi ki bani guri ko ba kya ji ne?

Saurin barin gurin tayi tana waiwayensa.

Sai girgiza kansa yake tare da wasa da iccen dake hannunsa, Hawayen tausayinsa ta goge tana tunanin a inda zai samu abinci ya ci watakila kan bola zai je ya yi tone-tone ya samu lalataccen abinci ya ci tunda mafi akasari da haka mahaukata 'yan uwansa suke kawar da yunwar da ta damesu.

A soran gidan ta samu ghana masgo kayanta kaf a ciki. Ta dinga jin masifarta daga gidan Saliha na taya ta.

Jiki a sanyaye ta shiga da sallama a bakinta, ta kalleta da fadin." Na gama zama dake ki tafi duk inda za kije mara mutunci."


"Baba kiyi hakuri tsautsayine kin san dai tunda kike aike na banta'ba zubar miki da kudi ba wannan ma kaddara ce."

Tace." Ban san kaddara ba na fada miki na gama zama dake ki tafi can gidan Ubanki duk abinda za su yi miki dama tausayi yasa nake rike dake to tunda kin zama munafuka zama na dake ya 'kare Kije duk abinda Talatu za tayi miki ba zai dameni ba.

Ta durkushe a gurin tana kuka da rokonta tayi hakuri tayi kunnan uwar shegu da ita kicin ta shige ta barta a gurin, ta kalli Saliha da fadin." Ki sanya baki tayi hakuri kinji." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da abinda take,

A fusace! ta fito daga kicin din ta nufi dakin sai gata ta fito da bulala a hannunta ta riga ta san idan tazo babu abinda zai hana ta doke ta. dan haka da gudu ta ruga a guje ta fita daga gidan tana jin lokacin da ta sanya sakata ta koma ciki tana surutai.
Babu yanda ta iya haka ta kama hanya domin tafiya gidan mahaifinta dake can Ja'in Tafiyar 'kafa za ta yi tunda babu kud'i a hannunta gashi akwai tazara mai tsayi tsakanin Gadar salga da Ja'in.
Koda ta fito bakin titin hankalinta na gurin zamansa, babu shi a gurin sai tarin tarkacensa , sai ta tsinci kainta da kasa tafiya har sai da ya dawo da ledar biredi a hannunsa taga ya shige karkashin motar ya zauna.
Ajiyar zuciya ta sauke cikin zuciyata Tace."Watakila wani ne ya tausaya masa ya siya masa biredin.

Sai da taje Sabon titi na gidan 'kankara a kasa kafin ta samu wani d'an kirki ya taimaka mata ya rage mata hanya.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
____

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
Kuyi join domin samun damar karanta littafi na d'aya.



_Gaisuwa ta karamci zuwa ga iyaye na biyu._??
*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
Tare da
*USAINA ABDUL-MALIK KAITA (HAJIYA BABBA)*



*5&6*
Ta zo shiga gidan kenan ta yi karo da 'karamar k'anwarsu Walida tana d'auke da markad'an awara a kanta. kallon juna su ka yi sai kawai yarinyar taja tsaki ta wuce ba tare da tayi mata magana ba.

Idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan wulakanci da 'kas'kancin da 'yan uwanta suke mata duk da cewa itace babba a cikinsu amma mutum d'aya ce take ganin girmanta.

Gabanta na fad'uwa tayi sallama cikin gidan.
Talatu tana kicin ta baza kwanuka tana rabon abinci yayin da Hadiza babbar 'yarta ke yanka musu salak da tumatur. ita kuma Jamila tana shanya kayan makarantarta akan igiya.
Itace ta amsa sallamar fuska a sake tace."Auntymu kece ki ke tafe da wannan ranar.?"

Hadiza ta kalleta a watse ta mayar da kanta kasa tana cigaba da gyara salak din dake gabanta.

Jamila tace."Talatu ga fa Aunty Shahida tazo." Ba tare da ta juyo ba tace."To Ubanta zan yi mata kome?"

Jamila ta girgiza kanta ba tace komai ba taja hannunta suka shiga daki tana 'kokarin kawar da 'bacin ran dake damunta, ta tsani halin ko in kulan da mahaifiyarsu take mata a ganinta Shahida abar tausayi ce duba da maraicin da take ciki bayan haka kuma akwai nakasu na rashin ji a tattare da ita, babban damuwa yanda mahaifinsu yayi shakulatun 'bangaro da lamarinta da kuma lalurarta a matsayinsa na mahaifinta baya taimaka mata da komai gabad'aya ya sakarwa kakarta wacce ta haifi uwarta ragamar rayuwarta, bai san ci da sha da sutturarta ba, Uwa uba karatunta duk be san wannan ba, ta wannan fanni dole a jinjinawa Baba Asabe domin ita d'in maca ce mai kamar maza duk da nauyin ba akanta yake ba amma ta d'auka tana iyakacin 'bakin 'ko:karinta akan yarinyar.

Tsaf Talatu ta gama rabon abinci amma babu rabon Shahida a ciki duk da cewar lokacin da ta zo gidan bata gama rabon abincin ba idan da ta yi niyyar sanya mata kwano zata san yanda tayi ta fitar mata da rabonta amma k'emagadas! tayi mirsisi ta rabe abincin kaf ta kira kowa ya d'auki nasa.

Jamila a sanyaye ta nufi dakin da nata kason a hannunta.
Kamar ta san niyyarta sai ta kira sunanta, taja ta tsaya tana kallonta, fuska a tsuke tace." Ki ka shiga da abincin nan ku ka ci tare sai na tsine miki albarka."
Dama sarar ta kenan daga zarar 'ya'yanta sunyi mata laifi sai tace zata tsine musu.

A marairaice tace."To yanzu ita Shahidan haka zata zauna Talatu kada fa ki manta itama tana da hakki a gidan nan tunda duk ubanmu d'aya."

Ta ciko hannu da shinkafa 'yar manja wacce taji salak da yaji ta watsa a bakinta tana taunawa ta ce." Kafin ki san haka na rigaki sani ban yi niyyar bata abincin ba shiyasa nayi rabo babu ita idan kuma ki kayi wasa wannan na hannun naki zan k'wace na bawa almajirai kema kiyi asara."

Hadiza ta kalleta da fadin." Banza mara kishin uwarta shin har kin manta labarin da Talatu ta ba mu a lokacin da suka zauna tare da mahaifiyarta yanda ta azabtar da ita amma shine saboda rashin kamun kai kike tausayin abinda ta tafi ta bari ai wallahi ni da wannan kurmar yarinyar har abadah."

Jamila ta girgiza kanta da fadin." Ke Hadiza jahilci ne yake damunki wallahi ni ina ruwana da irin zaman da su ka yi kawai 'yar uwata na sani saboda duk rintsi ba'a sanjawa towo suna Shahida 'yar uwarmu ce dole ko mun 'ki ko mun so."

Hadiza ta fusata! ta hau d'ura mata ashar wai ta kira ta da jahila. 'Kokarin tashi take taje inda take tsaye ta doke ta uwar ta hana ta.

Sallama ya yi cikin gidan yana sanye da manya kaya sabuwar shadda mai uban surfani, kansa sanye da hula zanna bukar idan ka ganshi sai ka dau'ka wani hamsha'kin mai kud'i ne nan kuwa tsabar 'karya ce da fafar tsiya Jamilu kenan wanda abokansa suke kiransa da Ya hajuj! tsabar 'karya da nuna shi wani ne. ya sanya sunanshi ya 'bata a ko'ina ake kiransa da Hujaj!

Ya kallesu da fuskar shannu "Menene na ganku a tsaye ke Jamila ya akayi?"

Da sauri tace." Baba ka ga Aunty Shahida ce tazo shine Talatu ta raba abinci babu ita wai don na d'auki nawa zamu ci tare shine fa suka had'u suke zagina.

Ya gyara zaman babbar rigarshi da fadin." Ina Shahidan take? Tace."Tana daki a zaune.'' Tsaki yaja da fadin." Shige ki je kuci abincin tare." da sauri ta shige dakin.

Talatu ta kalleshi da fadin.'' Yau kuma? ba tare da yace mata komai ba ya bude dakinsa ya shiga ya turo k'ofa.

Kasan kafet ya zauna ya cire babbar rigar jikinsa, hannu yasa cikin aljihu ya shiga fito da kudi daure da kyaure bandir biyar ne ya zube a gabansa yana wani irin murmushi babu shakka yau kura tayi nama ya tashi da Sa'a ko da yake dama sana'ar tasu ta gaji haka yau kai gobe wanin ka da yake shi akwai nasibi duk ranar da suka buga wasa baya fad'uwa, wasan yau yafi na kullum domin ya samu kudi masu yawa, burinsa a yanzu bai wuce siyan babur ba, zai sayi vespa d'an 'kasa irin wanda manya alhazawa suke hawa a duk lokacin da ba suyi ra'ayin hawa mota ba.

Tura kofar dakin tayi sai yayi saurin boye kudin a bayansa.

Tayi sallama tare da tsayawa 'kerere a gabanshi, yace."Kefa dadina dake rashin ladabi meye haka kin shigo ba tare dana nemeki ba kin tsaya min 'kerere a ka."

Ta gyara daurin zaninta da fadin." Ka san kwanan zance ai bana so muyi hayaniya da kai a gaban yara saboda haka ka bani kudin dana ranta maka."

Yaja tsaki da fadin." Wai shin har nawa ne kudin naki?"

"Dubu biyu da dari hudu ne kada ka manta yau kwananka uku baka ba da ko kwabo ba tun daga safe har dare ni nake d'awaniya da gida to tunda Allah yasa yau ne cikar alkawarin da kayi min ba zan fita ba sai ki biya ni kud'ina."

Kashingid'a yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa. Tace."Jamilu meye haka zaka dinga yi min murmushi kada fa kayi min wata magana don wallahi baza mu wanye lafiya ba."

Ya sosa gemunsa da fadin." Ki je yanzu zan fito zan baki kud'inki ina jin shikkenan ko?"

Kai ta girgiza da fadin." Ba fa zan fita ba sai da kud'ina a hannu.

Ya mike zaune da fadin." Idan kika matsanta min wallahi zan ha naki ni nace kije zan baki idan na fito sanin kanki ne bana san takurawa."

Ta yi jim tana kallonsa kafin ta gyada kai da fadin." Na kawo maka abincinka ne.?

Sai da ya mula tukkuna ya ce."Aa ki bawa Jamila da Shahida suka 'kara ni na koshi."

Ba tare da tace komai ba ta juya ta fita, koda ta fito daga dakin a maimakon tayi abinda yace kai tsaye kicin din ta nufa ta dauko abincin nasa tasa a gabanta ta dinga ci sai kace jaka, Walida dake sud'e hannu tace."Talatu d'an k'ara min wallahi ban koshi ba."

Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kai loma bakinta, yarinyar dake mara kunya ce ta yatsine fuska da fadin." Talatu ki dai ci a hankali kada ki 'kware wannan loma haka."

Bud'e baki tayi za tayi magana aikuwa ta shaki shinkafa ta hanci tari ya sar'ke ta ta dinga yi hawaye na zuba, yarinyar ta tashi ta bar gurin ba tare data debo mata ruwa ba.


Shahida da Jamila haka sukaci abincin ba tare da sun 'koshi ba, suka fito domin wanke hannu nan suka ga Talatu tayi wurjajan ido yayi jawur har yanzu da sauran tarin amma saboda zulama bata daina cin abincin ba.

Shahida ta banka mata harara ta wuce dama duk sanda tazo gidan abinda ke shiga tsakaninsu kenan harar juna, sai taso take gaishe da ita, Hadiza ta fito daga d'aki Talatu tace."Kinga 'yar iskar yarinyar nan saboda ban zuba mata abinci ba take hararata.

Hadiza tace."Take harararki kamar sa'arki." Tace."Au! keda baki ta'ba gani ba? ai a duk san da zata zo gidan nan hararace take shiga tsakaninmu."

Bagazan! bagazan ta nufi inda take ta juyo da ita suka fuskanci juna, murya ta d'aga da fadin." Don Uwarki mahaifiyarmu sa'arki ce?"

Jamila tace."Hadiza neman fitina bashi da amfani me kuma tayi miki?

Ta juya tana yi mata bayani yayin da ita kuma Shahida ta juya inda Talatu ke zaune ta dinga watsa mata muguwar harara tunda ta lura da abinda bata so to ta daura d'amarar 'bata mata rai.

Talatu ta rike ha'ba da fad'in.'' Ni kike harara don Ubanki! ta dauke kanta tana jan tsaki tare da niyyar barin gurin.

Hadiza ta fizgo kafad'arta tana nema ta kai mata duka, sai ta rike mata hannu cikin yanayin maganarta tace."Hadiza ki kiyaye ni wallahi ni nafi karfin ki dake ni."

Ta fizge hannunta tana d'ura mata ashar!! Ya fito d'aga daki da yanayin bacci a tare dashi ya ce." Baku da hankali ne? sukayi shuru ya kalli Shahida da fadin." Me yasa duk lokacin da ki kazo gidan nan sai anyi rigima dake?

Ido ta zuba masa, yaja tsaki da fadin." Ana magana kin tsare mutune da ido kizo ki tafi inda ki kafi wayo."

Da yake da 'karfi yake maganar duk taji komai sai tace." Ai na dawo gidan ubana da zama."

Talatu ta zabura! ta mike tsaye da fadin." A'ina.? Babu tsoro tace." A nan."

Jikinsa ya mutu ya ce."Kinyi mata laifi ko?Fashewa tayi da kuka ta durkushe a gurin!.

Talatu cikin masifa ta ce."Wallahi ko kukan jini za kiyi baki da gurin kwanciya a gidan nan aikin banza kawai."

Ya kalleta da fadin." Kin san dai 'yata ce ko?"

A fusace! Tace."Na sani amma wallahi ba zan zauna da ita ba."

Ya girgiza kai da fadin.'' Duk lokacin da nayi ra'ayi 'yata zata dawo hannuna da zama."

Tana numfarfashi! tace."Ni kuma a ranar zan tattara kayana na bar maka gidanka domin kuwa ba zanyi kishi da uwarta nazo nayi da ita ba.

Murya ya d'aga gurin kiran sunanta, ta d'ago kai tana kallonsa fuskarta gaje-gaje da hawaye,

Ya ce."Tashi muje ki fad'a min laifin da ki kayi mata."

Ta mike tana share hawaye tabi bayansa zuwa dakinsa, kallon banza Talatu ta bisu dashi tayi k'wafa tana girgiza kanta.

Duk abinda ya faru ta sheda masa tana kuka, ya ce."Kiyi hakuri kinyi sara a bakin ga'ba matsalar Baba Asabe kudi za'a biyata kud'inta"
Cikin izzah! da nuna isa yayi maganar kamar wanda yake da burin biyanta kud'in dawainiyar da tayi masa daga farko har 'karshe.

Yasa babbar rigarsa da fadin." Tashi mu tafi." Ta mike da sauri ta fito, shima ya fito yana kokarin kulle kofa tazo ta ta rike k'ugu tare da jan tunga a gabansa.

Hannu yasa cikin aljihu ya zaro sabbin 'yan dubu-dubu uku ya watsa mata.

Ta tsuguna tana tsincewa da fad'in." A banza dai duk abinda za kayi ni na rufa maka asiri."

Ya gyara zaman hularsa ya kama hanyar fita ba tare da ya tanka mata ba.

Ta kalli Jamila dake kan rijiya a zaune ta ce." 'Yar uwata na tafi na gode da zumunci."

Jamila tana murmushi tace."To Aunty Shahida ki gaishe da Baba Asabe da kyau."

Tace." Za taji da kyau." Hadiza tace."Banzaye kawai wannan munafurcin naku babu inda zashi." babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Shahida tabi bayan mahaifinsu ita kuma Jamila ta shige daki tana jiyo irin zagin da sukewa Shahida tamkar maguzawa!

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO...
_____

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
Kuyi join domin samun damar karanta littafi na daya.


*Marubuta*
_Nimcy luv (Sarauta)_
_Hassana Bamalli_ _(OmApanan)_
_Sa'adatuBintuAbdullahi_
Ina godiya 'kwarai??



Kyautar feji zuwa ga:
_*Ummul-Khairi Shaik*_ _*Muhammad (Kairatu)*_
Binta tana godiya da k'auna tare da k'warin gwiwa??



*7&8*
Jamilu Ya hujaj! mutum ne mai fara'a da wasa da dariya shiyasa yake da jama'a yara da manya duk inda ya gifta za ka ji ana fadin "Ya Hujaj! Shi kuma

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login