Showing 24001 words to 27000 words out of 124287 words
da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai.
Shi da abokansa suka rasa bakin godiya.
To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu.
****
Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take.
Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci.
Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji."
Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata.
Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma.
Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai."
Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri.
Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci.
Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba.
Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba.
Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta.
Bakinta na rawa ta kirayi sunansa.
Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake k'asan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu.
Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki.
Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.''
Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take.
Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda take da 'kyankyami
Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau.
Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta sayi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba.
daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, ta ce." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar.
Ta fara k'ok'arin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi ka ci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a."
Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba.
Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka ta ce." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.''
Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne.
Hannu yasa ya 'karbi wainar a takaice ya ce." Na gode."
A hankali ya yi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata.
Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo."
Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta.
Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu.
Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko?"
Ta ce." Eh saura naki a kadai gashi can a jug."
Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.'
Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya."
Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi."
Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita.
Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa ba sai wannan mahaukacin.'
Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar."
Tana 'yar dariya ta ce." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa."
Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri.
"Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci."
Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bud'e kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai k'amshi yake.
Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba.
Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba.
A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?"
Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.?
Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo."
Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka."
Shuru yayi bai ce komai ba.
Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu."
Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin.
Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya.
'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata!
Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka!
Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.?
Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta.
****
"Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj.
Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa."
Ta ce." To za'a fada masa.
Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya.
Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar.
*BINTU*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*25&26*
Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.
Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo.
Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."
Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."
"Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne?"
Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje."
Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni.
Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka."
Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa.
Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji."
Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri."
Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai.
Jallabiya yasa ya fita.
Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne.
Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo."
Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba."
Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka."
Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin."
Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa.
'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba.
Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka."
Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah."
Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul sai uban 'kyalli yake.
Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa.
****
Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya.
Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa.
A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara."
"Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci."
Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane."
Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi."
Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina."
Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake."
Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba.
Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin."
Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta.
Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado.
Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu.
Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba.
Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa.
Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar.
****
Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye.
Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa.
Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa.
*Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce??*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*27&28*
Ha'ki'ka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwad'ayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sa ni, Hujaj cikin rashin k'ima da rashin arziki ya nufi gidansa da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an k'wamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin 'kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne su ka yi arangama da mak'ocinsa mai suna Malam Habu yana nannad'e tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, ya yi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai.
Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da ma'kocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download