Showing 111001 words to 114000 words out of 124287 words
wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*
124&125
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya yau fari gobe b'aki, jin dad'in duniyar gashi nan, amma babu kwanciyar hankali, rashin nutsuwar kuma bai sanya na lalace ba abin mamaki! ma wata irin ki'ba na ke yi mussaman ta k'asa, kwankwasona ya bud'e sosai! haka ma k'irjina ya bun'kusa, ga wani irin kyau da na yi fatar jikina ta yi taushi da kyau! tamkar ta jarirai! wannan shi yake d'aga hankalin Hajiya da duk wanda zai ga yanda na zama babbar mace! tabbacin cewa; ina hutawa da jin dad'i, ko ga yanayin sutturun da nake tu'ammali da su, domin duk lokacin da ya yi tafiya 'kasashe! tsarabata ta mussaman ce, idan ya je india akwati guda yake kawo min ta kayan ado irin na su, fakistan da sar'k'oki da abun hannu har da sar'kar k'afa, a cewarsa yanda na zama yar duma-duma shigarsu za ta yi min kyau! ganin yana so sai na mayar da hankalina gurin yi masa ado iri daban-daban.
Zuwa na ganin gida na farko! 'karara na ga bacin a fuskarta Saliha, sai dai ta yi 'kokarin 'boyewa amma hakan bai yuwu ba, tunda dama can haka take nuna min sam bata k'aunar wani cigaba na.
Baba Asabe kuwa ta din ga ina asa ka ina a aje da ni, duk ta rasa yanda za ta yi, kula ta mussaman take ba ni, har abin ya so ya yi yawa, sai da na ga ji nayi mata magana tukkuna ta rage, to hakan ma ya 'bata ran Saliha, ni kuwa duk da na fahimci hakan daga gare ta ban fasa yi mata alheri ba, zannuwa masu kyau na yi mata kyauta da su tare da sar'koki irin wanda na cire.
Gidan Babana ma haka sun tar'be ni hannu biyu, wannan karon Baba ya yi sa'ar matar aure tun bayan rabuwarsa da mahafiyata, ko da yake shima ba halin kirki gare shi ba, yanzu ne dai ya kintsu!
Lokacin da naga Hadiza turus! da ciki wasu hawayen takaici ne suka ciko idona! wanda duk da na yi 'ko'karin dakatar dasu sai da suka zuba. na kalleta a lokacin duk hallitunta sun sauya, da alama daf take da haihuwa, lebanta ya yi jajawur! haka nan, jikinta duk ya kumbura! kawai na zauna ina kuka! ina kallonta
Itama sai ta fashe! da kuka ta rike min hannu tana kukan ta ce." Kin ga halin da Talatu ta je fa ni ko? watakila ma cikin nan shine ajalina."
Na yi saurin rufe bakinta da cewa; Hadiza k'addara ba ta wuce kan kowa ba, amma wani lokacin mutum na biye wa son zuciyarsa gurin aikata mummuman aiki, lokacin da na samu labarin abinda ya faru da ku hankalina ya ta shi, sai dai ba ni da yanda zanyi, bahaushe ya ce." Tun ran gini ran zane, ki yi hakuri ki kar'bi wannan jarabawar kuma idan kin haihu lafiya kada ki nemi wata hanya domin kashe abinda ki ka haifa, ki nemi gafarar Allah, in sha Allahu zai gafarta miki, abu na 'karshe da za ki yi shine; aure. domin shine cikar mutumcin duk wata 'ya mace!
Ta share hawaye da cewa; Yanzu wa ki ke tunanin zai aure ni da abinda na haifa, wallahi ni na fi bukatar na mutu! domin ba zan iya da abin kunya ba."
Rushewa ta yi da kuka tare da dafe kanta!
Jamila ta kalleni ina goge mata hawaye ta ce" Anti Shahida ki 'kyaleta don Allah kullum haka take tayar mana da hankali, ai dama duk wanda ya sayi rariya ya san zata zubar da ruwa, lokacin da take kan sharafi babu irin nasihar da ban yi mata ba, amma wani sa'in sai su had'a kai da Talatu suyi ta zagina to yau ga ranar da nake gudu ta zo, kin yo cikin shege, ita kuma Talatu garin yawon malamai 'kai'kayi ya koma kan mashe'kiya." Cike da 'kunar zuciya take maganar muryarta na rawa, da alama itama daf take da ta rushe da kuka!
Na ce"Jamila kada ki sake taso da abinda ya ri ga ya wuce, ina so gabad'ayamu, mu dauki wannan a matsayin 'kaddara wacce ta riga fata, sannan mu yi wa Hadiza adduar haihuwa lafiya, ita kuma Talatu Ubangiji Allah ya bata lafiya."
Ta amsa da ''Amen anti Shahida in sha Allahu ba zan sake ba.''
Duk muna zaune jigum!-jigum! domin halin da Hadiza take ciki na ciwon mara mai tsanani! tana kwance sai rike ciki take! tana kuka Anti Murja ta shigo dakin, na kalleta da cewa" Anya kuwa ba za mu je asibiti ba watakila haihuwa za ta yi fa."
Ta ce'' Ai Babanku ya hana ban san meye dalilinsa ba, amma a duk lokacin da ta shiga irin wannan halin akwai wata likita dake zuwa ta dubata to yanzu ma gidanta na nufa na duba ko ta dawo daga aiki.
Na ce" Yawwa Don Allah ki je wallahi hankalina ya ta shi."
Ba ta ce komai ba ta shiga d:aki domin d'auko mayafi.
Na ce" Jamila kira wayar Babanmu ki fada masa halin da ake ciki.
Ta ce" Fad'a zai yi wallahi, domin fa har yanzu bai sauko ba, da k'yar ma yake amsa gaisuwarta a cewarsa ta gama ci masa mutunci a duniya shiyasa ya 'kullace ta!
Girgiza kai na yi da cewa; Ban san abinda yake damunsa ba wallahi. ita fa rayuwar duniyar nan hakuri ake da ko wane yanayi, kuma fad'in Annabi ne cewa; duk abinda ka yi shi za a yi maka, lokacin da yake kan ganiyarsa meye be yi ba? babu irin kukan da ba mu yi ba, a yanzu sakamako ya ke ga ni."
Shiru ta yi na minti biyu kafin ta girgiza kai da cewa; Ai kullum cikin tsinewa Talatu ya ke, ita kanta Hadiza a cikin tsiniwarsa take, ya 'ki ya yafe mata, ni da Walida ne kawai muke mu'amular arziki da shi.
Na bud'e baki kenan zan yi magana su anti Murja suka shigo.
Da sauri likitan ta sanya safa a hannunta, muka fita daga dakin ta fara dubata domin itama ta yi tunanin haihuwar ce ganin yanda take murkususu! da kiran sunan Allah.
Tabbas Haihuwa ce amma cikin ikon Allah babyn yana zaune daram ma'ana bai juya ba.
Ta kira Anti Murja tana sheda mata halin da ake ciki cewa lallai a tafi asibiti akwai matsala don abin ya fi 'karfinta!
Waya ta na dauko na ce Jamila ta kira Sule ta sheda masa cewa ya zo yanzu-yanzu da mota dama kuma shine ya kawo ni garin.
Minti goma sha biyar a tsakani, sai ga shi ya zo, da kyar muka fita da Hadiza daga gidan, lokacin ta kai ma'kura gurin galabaita, kai tsaye babban asibiti muka nufa.
Na ce Jamila ta kira Babanmu anti Murja ta kar'bi wayar ta yi masa bayanin halin da ake ciki, sai ya fara fad'a da cewa; da izinin wa suka fita shi ya fi so Hadizan ta mutu! ya huta da abin kunya! sai da ta fada masa cewa; ai ni ce na zo garin na riski abinda yake faruwa kuma ni ce nace aje asibitin, sannan ya saurara da fad'an ya kashe wayarsa.
Babban likita ne ya dubata, kuma shi ya tabbatar mana da cewa; ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ana bukatar ayi mata aiki da wuri! dukkaninmu mun shiga damuwa matsananciya! nan ma na ce a kira shi a fad'a masa ya zo ya sanya hannu.
Dole ba don ransa ya so ba ya zo asibitin, ya kalleni da fadin" Shahida don dai kin shiga cikin al'amarin nan ne, amma wallahi na fi bukatar mutuwar Hadiza da rayuwarta, domin dai ta gama tozartani a duniya."
Na ce" Baba don Allah ka daina wannan maganar, jahili kad'ai shi zai yi jayayya da abinda Allah ya hukunta, kaddara ta riga fata babu yanda za mu yi da ikon Allah, ka yi hakuri ka ya fe wa Hadiza kuma kayi mata adduar sauka lafiya."
Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, ba tare da ya sake wata magana ba ya kar'bi takardar ya sanya hannu kamar yanda likitocin suka bu'kata, cikin gaggawa aka shirya Hadiza aka shiga da ita tiyata.
Cikin ikon Allah a kayi aiki lafiya aka fito da baby girl k'atuwar gaske! kyakykyawa! jawur sumar kanta 'baka sunkuf! babyn ta fi kama da 'ya'yan k'warori ko larabawa, sam ba ta yi kama da Hadiza ba, na jima ina tasbihi ga Ubangiji ganin yarinyar cikin koshin lafiya an shiryata cikin kayan sanyi sai tsotsar hannunta take, wasu hawaye masu zafi suka ciko idona, lokaci guda yarinyar ta shiga raina ina jin dama ni na haife ta, rungumeta nayi a kirjina ina jijjigata a lokacin da take tsanyara kuka! ga uwar a kwance bata farfad'o ba.
Babanmu kuwa tafiyarsa ya yi, tun bayan da ya sanya hannu, sai Jamila ce ta kira shi ta sheda masa abinda yake da akwai. hakan ma bai sanya ya dawo asibitin ba, ya kuma umarci anti Murja da cewa; lallai ta koma gida.
Ni da Jamila muka zauna asibitin, da yake na kudi ne ba mu samu matsalar komai ba, kuma duk abinda suke bu'kata na ha'kkinsu na tura musu, shiyasa suke ba mu kulawa ta mussaman. hankalina bai kwanta ba sai da Hadiza ta farfad:o na kira sunanta ta amsa tare da kiran sunana, nan na tabbatar da cewa; ta dawo hayyacinta.
Na ce" Kin samu baby girl ga ta nan kyakykyawa." na fad'a ina murmushi tare da nuna mata babyn dake kwance a wani gado tana bacci.
Dauke kanta ta yi ba ta kalli gurin ba, sai wasu hawaye da na ga suna gangarowa ta gefen idonta.
Na ce" Ka da ki sanya damuwa a ranki don Allah kin ga baki da koshin lafiya."
A hankali ta juyo ta kalleni ta yamutse fuskarta da 'kyar ta ce." Gabad'aya na tsani duniyar nan wallahi. yanzu wa zan nuna a matsayin uban yarinyar nan? ba zan tantance iya adadin mazan da nayi mu'amula da su ba."
Wani kuttun! bakin ciki ya tokare min a wuya. na ce" Dama illar kenan Hadiza. ba ki ji bahaushe yana fadin." Duk abinda namiji ya yi ado ne, ita fa 'ya mace rayuwarta ta'kaitacciya ce, kamar yanda ki ka fad'a! babu wanda zai kar'bi yarinyar nan da sunan shine ubanta ko da kuwa kammani sun nuna! kin ga sun bar ki da wahala. babban tashin hankali anan shine; yarinyar ta girma ta bukaci sanin ubanta anan damuwar take."
Hanci ta sha'ka! wasu hawayen na sake zuba ta ce" Ki d'auke ta na bar miki don zatin Allah ki yi min wannan alfarmar."
Kallonta na yi , tausayinta ya cika min zuciya na ce" Ba zan 'ki ba Hadiza na kar'ba kuma zan ri'ke ta tsakani da Allah kamar ni na haife ta, amma mu bari ta yi 'kwari, ina nufin sai bayan kin cire ta daga bakin nono, tunda kinga ni ban ta'ba haihuwa ba, ban san ya ake ba."
Ta ce." To shikkenan haka za a yi." Shiru ta yi tana yamutse fuska! na ce" Ko wani abu yana damunki?"
"Jiri da ciwon kai nake ji." Na ce"Sannu bari a kira likita ya duba ki."
Tare muka shigo d'akin da likita lokacin babyn na wutsil-wutsil da kuka. na je na dau'kota. ya kalle ni da cewa" Yarinyar nan na bukatar abinci! saboda haka ko ya ya ne, mamanta ta bata nono. idan ya so sai a d'ora ta akan madarar da ta dace."
Na ce."To shikkenan.'' Ya kama hanyar fita da cewa; nurse za ta shigo yanzu sai ta taimaka miki gurin shayar da babyn."
Cikin dubara muka jingina babyn jikin Uwarta nurse din ta fito da nonon tasa mata a baki, cikin ikon Allah ta janyo ruwa ta dinga sha kamar babu gobe, ita kuma Hadizan sai hawaye take tana kawar da kanta. ita kanta nurse din sai da abin ya bata mamaki! ta gama aikinta ta fita. ni kuma na kwantar da babyn a gadonta.
Na dawo na zauna da fadin." Hadiza ki daina wannan kukan dan Allah.
Da 'kyar ta ce" Yanzu na tabbatar da uban yarinyar nan."
Da sauri na ce" Waye shi? kuma a ina yake?"
Girgiza kai ta yi ta ce" Wani k'wara ne! ba mu jima da had'uwa ba, kuma ban san a wace 'kasa yake ba, lokacin dai da muka had'u ya sheda min cewa; gwamnatin ce ta d'aukesu wani aiki. shine na tare a gidansa. kuma yake mu'amula da ni kamar matarsa ta aure, amma ya kashe min kud'i sosai, kuma fa duk lokacin da za mu yi wata mu'amula sai ya ba ni 'kwaya ya kuma sanya condom gudun samun wata matsala, dama ba a yi wa Allah wayo."
Ta karasa maganar da fashewa da kuka!
Da sauri na ce" Ki yi shiru don Allah ai kin san abinda yake da akwai, kada ki dawo da aiki baya"
Hannu nasa na goge mata hawayen fuskarta
Ta ce." Ina Babanmu ya zo asibitin?"
Na ce" Eh ya zo ya duba ki har ya yi miki addua.'' Na fadi hakan ne domin ta samu kwanciyar hankali.
Murmushi kawai ta yi tana kallona, yanda na fahimta kamar bata gamsu da maganata ba .
Ta ce." Ki nema min gafara a gurinsa tare da Talatu da duk wanda na 'batawa a wannan duniyar."
A sanyaye na ce" Mai ya kawo wannan maganar kuma?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Na ce." In sha Allah za ki samu lafiya.
A hankali ta amsa da "ameen Allah ya sa haka.''
Sai da na ga ta samu bacci tukkuna na fito daga d'akin da take, na samu Jamila tana bacci. na tasheta tare da fadin" Lokacin sallar la'asar ya yi. na shiga band'aki na d'auro alwala na fito.
Tare mu ka ci abinci muna tattauna abinda ya shafe mu. lokacin na samu 'yar nutsuwa na samu sararin duba waya ta. nan na ga tarin messages d'insa. duk rabi na soyyaya ne tare da sake jaddada mini cewa; yana nan yana kewata amma na tsammaci dawowarsa cikin satin da za mu shiga, karshe ya bada sa'kon gaisuwarsa gurin iyaye da 'yan uwa.
Nan nima nake sheda masa halin da ake ciki. ya tausaya sosai! ya ce kuma na yi 'kokarin ganin nayi duk abinda ya da ce kafin na bar garin.
Godiya na yi tare da ba shi amsa wacce ta yi dai-dai da umarnin da ya yi min. na kuma yi 'kokarin tura masa kalaman soyayya irin wanda na saba a duk lokacin da baya gari.
*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
126&127
Kwanan da mu ka yi babu bacci yasa na 'bingire kan dadduma bacci mai nauyi ya d'auke ni, tabbas Annabi ya yi gaskia da ya yi hani da baccin la'asar domin akwai firgici da razani a ciki, idan ba a yi sa'a ba ma mutum na iya tashi da ciwo mai tsanani! abinda ya faru kenan, domin mummunan mafarki nayi wanda ya sanya na farka a razane! na tashi zaune jikina duk ya jike da gumi! babu kowa a dakin sai ni kadai, da alama Jamila ta jima da fita. shiru nayi ina nazarin mafarkin wanda ya danganci Hadiza! gabana ya dinga dukan uku-uku! ina kiran sunan Allah a zuciyata, tabbas mafarkin d'anyan nama ba a bu ne mai kyau ba, domin da yawa ana dangata shi da mutuwa ko wani 'bacin rai mai tsanani!
Mafarkin da na yi kenan, bayan wanda na ga Hadiza cikin da fararan kaya tana d'aga min hannu da murmushi a fuskata, ta ajiye min 'yarta a kan cinyata, kafin ma nayi wata magana na nema ta na rasa a gurin, sai 'yarta dake tsanyara ihu!
Jikina ya mutu gabad'aya na gaza ta'buka komai wasu irin tunane-tunane nake marasa kan gado. Jamila ta shigo dakin da sauri tana fadin" Anti Shahida likita na magana na shigo ya kai sau uku kina bacci shine ban tasheki ba."
Gabana na bugawa na ce" Amma dai lafiya ko?" hawaye ne suka zubo a fuskarta, ta ce" Jikin Hadiza ne ya rikice! tun d'azu take suma, yanzu dai naga likitoci uku sun shiga dakin.
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan adduar na yi kafin na yun'kura na tashi saboda tsabar fargaba da razani 'kafafuna duk sunyi sanyi kamar an bubbuga min ta'barya haka nake jan k'afa muka fita daga dakin.
Babu halin mu shiga d'akin da Hadizan take tunda likitoci suna ciki sai muka samu guri muka zauna tare da tsirawa dakin ido! Jamila dai hawaye kawai take sharewa! ni kuwa addua kawai nake a zuciyata akan kada Allah ya tabbatar min da mafarkina, wanda na san hauka kawai nake domin ba zan dakatar da abinda Ubangiji ya hukunta ba.
Har akayi sallar magariba ba su fito, a daddafe muka gabatar da sallar muka zauna jigum-jigum! da jiran tsammani!
'Daya daga cikinsu ya fito. kallon fuskarsa kad'ai ya sanya gabana fad'uwa! bahaushe ya ce." Labarin zuciya a tambayi fuska."
Tsaye na mike baki na rawa na ce" Likita ya jikin nata? wallahi lafiya lau na fita na barta a dakin tana bacci.
Kallona ya yi da fadin." Ina mahaifinku yake?"
Na ce" Ya zo ya tafi." na fadi hakan ne domin kada ya fahimci wani abu.
Katsaham! ya ce." Allah ya yi mata rasuwa yanzu sakamakon jijjiga bayan jinin da ya b'alle, mun yi duk iyakar bakin k'o'karinmu abinda muke so bai samu ba, Hadiza kwananta ya 'kare."
Hannu na d'ora aka da fadin"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! na zube kasan gurin wasu hawaye masu
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download