Showing 96001 words to 99000 words out of 124287 words
tsabar tashin hankalin dana gani girmansa a zahiri ya tashi tsaye! jikina jagab! da ruwa ina yoyo na fara kokarin fitowa daga kwamin wankan, sai yayi saurin shigowa ciki ya mayar dani na fad'i cikin ruwan! yayi fallatsi! har cikin idona! kuka mai k'arfi nasa! tare da rufe fuskata da tafukan hannayena cikin takaici na ce"Wai meye haka? don Allah ka suturta jikinka." be ce min komai ba ya zauna kusa dani kawai ya sani a jikinsa yana kokarin cire min tufafin da suka jik'e. Ban san lokacin dana bud'e idona ba da tsoro ! na kallonsa nan na hango tsantsar fitina cikin idonsa don gabad'aya sun sauya kala duk girmansu sun 'kankance! kuma jikinsa sai wani irin karkarwa yake kamar wanda zazzabi yayi masa mugun kamu.
Wata irin runguma ya yi min a cikin ruwan ya turmushe ni bayan ya samu nasarar cire min tufafin jikina, gabadaya ya gigice! ya fice daga hayyacinsa ya dinga bin ilaharin jikina da zafafan! kesses har sai da ya samu nasarar janye hankalina domin ya riga ya gama fahimta abinda na fi bukata shiyasa ya mayar da hankalinsa gurin, a cikin ruwan dai mai afkuwa ta afku! hankalinmu bai kwanta ba sai da muka samu gamsuwa sannan muka dawo nutsuwarmu.
Kunyarsa nake ji sosai! hakan yasa na kasa kallonsa a lokacin da yake wankan tsarki! cike da farin ciki da annashuwa! sai da ya fita daga bandakin sannan na samu sararin yin nawa wankan na fito na same shi zaune a gefan gado har ya shirya yana waya da abokinsa
A gurguje na kimtsa jikina na samu guri na zauna amma ban iya kallonsa ba saboda har yanzu na kasa manta abinda ya faru a tsakanimu.
Hannuna ya ri'ke sai na kalle shi naga yana 'yar dariya, duk sai na tsargu! nayi saurin sunkuyar da kaina.
Ya ce."Ina fatan wannan had'uwar tamu ta haifar da alheri a jikina nake jin cewa; nayi ajiya mai muhimmanci."
Cikin nazari nake kallonsa domin ban fahimci maganar tasa ba. ya zura hannunsa kasan rigata ya ce."Ina da burin samun zuria masu yawa dake."
Ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa yana cikin wani irin yanayi zahirinsa ya nuna abinda yake d'ankare a cikin zuciyarsa, tabbas haihuwa rahama ce, sosai na tausaya masa na ce"Allah Ubangiji ya bamu masu albarka."
Ya amsa da "ameen" ya kanne min ido da fadin"Ya ki ka ji had'uwarmu ta yau?"
Tsira masa ido nayi da nazarin maganarsa.
Yasa hannu kan bakina ya ce."Akwai dad'i a cikin ruwan ko? don naga ba ki yi kuka ba, sai ma taimako da ki ka bani."
Kunya ta rufe ni, ashe abinda yake nufi kenan? da farko ban fahimci maganarsa ba. Shiru nayi masa na kasa magana sai dai tsabar mamakinsa da yake kashe ni.
Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke! yana ta murza tafin hannuna dake cikin nasa, na kalle shi. nan naga yanda idonsa ya sauya! da sauri na cire hannuna na matsa daga kusa dashi, na fahimci idan na biye masa sai mu yini muna abu daya, ni har mamaki yake bani yanda yake da kuzari da muzakkaranci tamkar bai kwana biyu a duniya ba.
"Tashi mu sauka kasa mu samu abinda za mu ci."
Ya fad'a yana k'okarin tashi.
Na kalle shi yana gyara doguwar jallabiyar dake jikinsa. Sunkuyar da kaina nayi Na ce"A haka zaka sauka dubi jikinka fa?"
Ya ce."Ya za a yi to?" ya fad'a tare da yi min wani irin kallo yana lumshe idonsa . A nan na fahimci abinda yake nufi. wanda ni kuma nake ganin ba zan iya ba gaskiya.
Na girgiza kaina tare da sake kallonsa a karo na biyu har yanzu girmansa yana nan a bayyane da yake rigar dake jikinsa irin mai kwanciya a jiki ce na ce"Ka dai kira waya a kawo abincin ina ganin hakan ya fi akan ka sauka a haka." sai ya zauna kusa da ni. ya fito da wayarsa ya kira Shukura tare da bata umarni.
'Kokarin tashi nayi daga kusa da shi. saboda ina jin kunyar ta shigo ta same mu a manne da juna, amma sai ya hana ni tashi ya sake matsowa jiki na, a haka ta turo kofar dakin ta shigo dama a bude ya bar kofar lokacin da ya shigo. ni dai da 'kyar na iya amsa gaisuwarta don ban iya hada ido da ita ba saboda kunya sai bayan ta fita daga dakin sannan na iya d'ago kaina.
110&111
Bacci ne ya 'kauracewa idona sakamakon masifar dake damuna, yini nayi a kwance a gado marata sai ciwo take, gaskiya da wuya na 'kara shan wani abu da zai tayar min da hankali duba da cewa; wanda zai d'ebe min kewar baya kusa, kwana biyar da tafiyarsa na ji su Hajiya na fadin zai iya yin sati biyu ko fiye da haka bai dai dawo ba, a lokacin na shiga tunani da nazarin maganarta domin dai sati d'aya ya ce min zai yi, yau ina lissafi kwanansa biyar kenan da tafiya, shiyasa na mayar da hankali gurin gyara jikina dalili na riga nasan yanayinsa. amma kuma abin yana nema ya zame min d'an zani. ga kuma maganar da Hajiya tayi cewa; bai zama lallai ya dawo a lokacin da ya fad'a ba saboda ya saba yin hakan a wasu lokatan zai yi tafiya da zummar yin kwana biyu ko uku amma sai ya shud'e wasu kwanakin bai dawo ba.
Gabadaya nayi saranda na fara tausayawa kaina halin da zan shiga, domin jikina ya riga ya saba da jangwale-jangwale, sai dai ni da kaina na fahimci cewa; ba ni da juriya, domin da tafiya tai nisa nake gajiya, amma kuma da alama inda da sha'awa a kusa.
Waya ta na daura tare da tura masa text Yaushe zai dawo?" sai ya bani amsa da cewa; sai wani satin saboda wasu dalilai."
Ban ji dadin amsar da ya bani ba.
Na sake tura masa da wani sa'kon cewa;
_"Amma dai kai ka ce sati d'aya za kayi don Allah ka dawo nayi kewarka."_
Sai bayan na tura masa text din kuma nazo ina jin nauyi domin ina tsoron kada ya fassara ni.
Ina ta tsumayin amsarsa shiru. a sanyaye na ajiye wayar na sauka daga gadon, band'aki na shiga na sake watsawa jikina ruwa a karo na biyu tun bayan wayewar gari wai a tunani na ko zan samu sassaucin wani abun.
Na shirya jikina tsaf na sauka 'kasa ba tare dana yi kwalliyar fuska ba.
Babu kowa a falon, dama tun safe Sadiya ta sheda min cewa za su zaga gari ita da yara domin mai-gidan yana dawowa za su tafi tasan kuma idan ya dawo ba zai bar su fita ba. ganin babu Hajiya a falon na raya a raina cewa da ita akayi tafiyar. murmushi nayi cikin zuciyata dana tuna cewa; jiya da daddare naji tana kuka da k'afafunta suna ciwo, tabbas da mai-gidan yana nan ba zai bari ba.
Kai tsaye kicin na nufa! Baba Marka tana ta aikace-aikace! muka gaisa cikin mutunci da karamci. na ce"Wallahi awara nake sha'awa ko zaki aikata min, kinga bana jin dadin jikina, amma da ba haka ba da kaina zan yi." Za tayi magana kenan sai gata ta shigo kicin din jikinta sanye da riga da wando masu kama dana sanyi, amma kuma dasu gwara babu domin duk hallitun jikinta a waje suka, babu hula ko dankwali a kanta sai tarin kitson attachment da ta daure da ribbon kamar ba cikakkiyar musulma ba, domin dai ni da ta tsaya a kusa dani ma 'karni na ji tana yi wallahi, ba komai ne ya janyo hakan ba sai bleaching din da take.
Baba Marka ta gaisheta ta amsa kamar ba ta so.
Dama ni tuntuni mun daina magana, domin ko na gaisheta bata amsawa sai dai kallon banza.
Bakinta nake kallo a lokacin da take magana, nan na fahimci abinda take nufi.
"Marka zanyi 'baki saboda haka ki ajiye duk wani aiki da ki ke yi ki fara hidimar shirya musu abinci. kada ki 'bata min lokaci"
Yanda take wa matar magana a tsatstsaye! daga gadara! sai abin ya bani haushi, na kalle ta da cewa; Baba Marka akwai waken suya ko?" da sauri ta ce"Eh Hajiya." Na ce"To ki fara aikin dana sanya ki.''
Sai ta fusata! ta kalle ni da fad'in" Ba ki isa ba kuwa! dole sai ta kammala uzuri na kafin naki".
Na ce"Saboda me?"
"Saboda na isa!" Tafada kamar zata cinye ni.
Dariya ta ba ni, na murmusa kafin na ce"Nan gidan aurena ne, ni nake da umarnin komai koda mai-gidan yana nan, to ballananta kuma baya gari, komai yana hannuna, don haka ban ce kada kiyi abinda ki ke bukata ba, amma ki bari ta kammala uzurina tukkuna ."
"Ke shashasha! rufe min baki anan gurin." Tafad'a tana girgiza.
Na jingina jikin bango ina kallonta tana magana kamar ta tsokane min ido sai kumfar baki take
Na ce"Wai don Allah mai na tsare miki ne? kin d'auki karan tsana kin d'ora min kin san ke baki isa ki kashe min aure ba, amma na fahimci abinda ke damunki idan mijina ya dawo zan rarrashe shi ya mayar dake dakinki shikkenan hankali ki sai ya kwanta ko".
Hannu ta daga zata zabga min mari! na kauce! da sauri ina kallonta idonta yayi jajawur! sai rawar murya take da alama maganata ta 'bata mata rai.
Baba Marka sai hakuri take ba mu, na ce"Baba don Allah ki cigaba da aikinki ki kyaleta idan ta gaji zata bari."
" 'Yar iska muskiniya kawai ke har kin isa ayi abu don ke? to wallahi ki rubuta ki ajiye idan mijina ya dawo hannuna sai kin kwashi kashinki a hannunki da k'afafunki zaki gudu."
Na ce" Ahaf! ai sai da amincewata tsohon mijin naki zai mayar dake, ki lallabani kawai na je na rarrashe shi.''
Cikin dariya nayi maganar domin na sake 'kuntata mata rai!
Aikuwa sai ta rarumi! kofin gilashi zata kwad'a min, nayi gaggawar shigewa kicin d'in ina mamakin al'amarin.lallai wannan bata da hankali.
Hanci ta sha'ka kwalla cike da idonta ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Zaki gane kuranki ne 'yar shegiya 'yar gidan d'an cah-cah!
Na ji kamar ta zuba min tafashashshen ruwa a jikina! ta cigaba da zumdumawa ubana ashar tana ambatar sunansa! da kiransa d'an bariki! al'amarin ya d'aure min kai mutu'ka! nayi mamakin! yanda a kayi ta san sirrina irin haka, shin waye ya fad'a mata asalin mahaifina!
Ban zubar da hawayen ba sai bayan data fita tukkuna, na tsuguna kicin din na rushe da wani irin kukan b'akin ciki!
Baba Marka ta dinga bani hakuri tana bani shawara cewa; ko don gaba da na sake biye mata mu zubar da mutumci, ta ce kuma aikina zata fara sai ta kammala tukkuna ko meye sai ya biyo baya.
Babu 'kwari na fita daga kicin. falo na ganta a zaune tana waya sai kuka take kallo d'aya nayi mata nayi saurin d'auke kaina, sai dai na tsinci wasu maganganun da take kuma da alama da mai-gidan take waya.
Raina ya sake 'baci na hau saman da tunanin matakin da zan d'auka dole idan ya dawo ya zaba ko-ni-ko-ita don wallahi ba zata zauna min a gida ba a rasa gane tsakanina da ita wacece matar gidan.
Kwanciya nayi ina nazarin da tunani akan lamarin. abinda yake bani mamaki shine; cikin labarinsa wanda ya ba ni ya nuna min cewa babu wacce ya tsana sama da ita, kuma a zahiri yana nuna 'kiyayyarta 'karara! to a ya akayi cikin lokaci k'ank'ani! ta janye hankalinsa har yake sauraranta su yi doguwar magana a waya da kuma zahiri? ni wallahi kukan da take yi ma shine yake ba ni mamaki! girgiza kaina nayi da tunanin abinda zai faru idan ya dawo don wallahi ba zan lamunta ba don na ga abin nata babu arziki.
Jin cikina na k'ugi yasa na sauka 'kasan domin duba Baba Marka ko ta kammala.
Suna zaune falo tare da 'kawayenta suna shewa wasu manya mata ne biyu 'yan duniya irinta, gabansu babban tire ne cike da kayan marmari.
Ganin yanda suka tsira min ido ne yasa na soma neman tsari a zuciyata.
Cikin dauriya da jarumta na isa gurin da suke a nutse na ce"Sannunku da zuwa."
Sai naga sun kalli junansu zuwa can kuma suka fashe da dariya suna kallona, raina ya sosu! na san maganata sukewa dariya abinda na tsana a rayuwata kenan!.
" 'Kawata wannan abar fa?" wacce take kusa da ita ke yi mata wannan tambayar.
Ta kalle ni a wulakance kafin ta ce"Ita ce matar tasa."
Suka dinga dariya suna kallona kafin d'ayar ta ce"Allah shi kyautawa Alhaji watakila dai kyawun sura ya duba, amma in ba haka ba meye abin so a tattare da wannan abar, na farko ga ta 'baka mummuna! uwa uba bebiya, wallahi wani cewa zai yi bata da hankali idan ya ga yanda take magana ai sai mutum ya tsorata.''
Bakinta kawai nake kallo a lokacin da take maganar. bayan haka kuma kunnuwana duk sun ji abinda take fad'i a kaina. sosai nayi mamakin furucinta.
Ta ce" Wai nan sai da aka gigita! tunanin mutane sannan aka same ta, domin shi fa a ganinsa daban take da sauran mata! bari ma ku ji wani abu mahaifinta d'an bariki ne mugun dan iska ne duk ina da labarin komai."
Al'amarin da ya fusata ni! nayi tsalle! na dira gabansu! da hannusu na ce" Ku shiga hankalinku wallahi 'yan iska jahilan banza da wofi!" na juya kanta tana zaune tana min kallon mamaki! ina ga ba tayi tsammanin zan iya mayar da martani ba, ido jawur! na ce" Ke kuma wallahi idan ki ka kuskura ki ka sake fadin mummunar kalma a kan mahaifina sai na fasa miki baki! idan kuma kina shakka! ki kara cewa tak! a gurin nan kiga abinda zanyi miki."
Cike da mamaki! take kallona kafin ta ce" Ai ba 'karya akayi muku ba, ko zaki rantse da cewa; mahaifinki ba mutumin banz......bata 'karasa ba na kaiwa bakinta bugu! ban sameta ba dalilin saurin kaucewa da tayi!
Tsaye! ta mi'ke da dumbun mamaki! ni kuma jikina sai tsuma! yake na sake nuna ta da yatsa a karo na biyu na ce" Abu d'aya nake dubawa yasa nake saurara miki, amma zan cire rigar mutumci muddin zaki ci zarafin mahaifina wallahi sai na cire miki iskar dake kanki! ki ji da wai! 'Yar Kano ce ni, kuma haihuwar Jakara! zan iya jure komai amma ba zan lamunci ki ci mutumin mahaifina ba, kuma mijina sai dai gani daga nesa."
Naushi ta kawo min 'kawarta ta ri'ke ta tana bata hakuri! tana fincikewa wai lallai sai ta doke ni, sai zunduma min ashar! take tana yi min cin mutumci, cikin wannan halin su Hajiya suka shigo.
Hajiya ta fashe! da kuka da fad'in "Me zan gani ni Saude! dama wallahi tun a mota gabana yake fad'uwa! wai shin Fatima me yake damunki ne?"
Cikin kuka take maganar tana mamakin al'amarin.
Sadiya ta janye ni daga tsakanin kujerun tana tambayata ba'asi, duk na warware mata komai.
Ta ce"Gaskiya dole ayi wa tufkar hanci domin zamanta a gidan zai haifar miki da matsala, ai iyaye sun fi gaban wasa."
Ashe ta ji lokacin da Sadiyar take wannan maganar. sai ta koma kanta da zagi! da fad'in" Sai ta ga wanda zai fitar da ita daga gidan.
Itama Shukura ta goyi da bayan uwarta suka dinga yi wa Hajiya rashin kunya! wai sune bata k'auna! komai su kayi lefi ne.
Hajiya dai barin gurin tayi. Yayin da 'yan iskan 'kawayenta suka d'auki jakukkunansu suka tafi babu wata damuwa a tare dasu duk da fitinar da suka haddasa!
Duk sona da awarar da 'kyar! na iya cin uku! na gabatar da sallar magariba na kwanta kan dadduma ina tunane-tunane.
Sadiya ta shigo dakin da sallama a bakinta
Zaune na tashi ina kallonta har ta zauna a kusa da ni.
"Hakuri na zo na baki Antina." ta fada tare da rike hannuna.
Na ce"Wane irin hakuri kuma 'kanwata?"
Ta ce"Kan abubuwan da Hajiya Fatima keyi min don Allah kiyi hakuri kuma kada kisa damuwar komai a ranki, akwai dalilin da yasa take hakan, ni kuma na san duk abinda za ta yi yayana ba zai sake zaman aure da ita ba."
Na ce"Meye hujjarki na fad'in hakan?"
"Saboda babu wacce ya tsana kamar ta."
Murmushin takaici nayi na ce" Da kenan! a yanzu dai ta janye hankalinsa akwai yuwuwar ya dawo da ita dakinta, tunda yana iya sauraranta a waya ko a zahiri, ni ganau! ce."
Ta ce"Kada ki manta 'yar uwarsa ce! kuma uwar 'yarsa, ina ganin wannan ala'kar ce ke sanya ya shiga huruminta, amma bana tsammanin zai cigaba da zaman aure da ita."
Dariya ta bani ganin yanda take kare shi, na ce"To shikkenan tunda kin ce haka, amma ni idan ya dawo zan zauna da shi, tilas ya fada min dalilin Fatima na zama a gidansa, idan kuwa babu k'wa'kwkwaran hujja! to zai za'ba ko-ni-ko- ita don mutane su bambance! wacece matar gidan a tsakaninmu.
Ta ce."Kema kina da hujjah antina, amma don Allah a sassautawa dattijo kinga shekaru sun fara hawa kansa, bayan haka ga zirga-zirga da hatsaniyar neman halal! a gurinki kawai zai samu sassauci! kada ki tsawwala masa da yawa.
'Yar dariya nayi na ce"Nayi miki al'kwarin ri'ke miki dan uwa bisa amana. ki taya ni addua."
Ta ce."In sha Allahu. zan taya ku adduar zaman lafiya tare da samun zuria masu albarka domin babban burin Yayana kenan."
Murmushi kawai nayi ina kallonta. cikin zuciyata na amsa da "Ameen" domin har ga Allah ina so na haihu domin tabbatuwar farin cikinsa tare da cikar burinsa.
114&115
Ina da bu'katar abinda zan ci." ya fad'a yana d'aukar babbar wayarsa dake ajiye a gefensa.
Tashi nayi na sauka k'asan da zummar cika
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download