Showing 45001 words to 48000 words out of 124287 words

Chapter 16 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16679

ne mara mafad'i."

Jamila ta ce."Haba Talatu abinda ki ke fa bai dace ba, kefe uwa ce idan ba zaki fadi alheri ba to kiyi shuru."

"Rufe min baki ba'kar munafuka algunguma." ta katse ta a zafafe!

Jamila ta mik'e ranta duk a 'bace ta kama hannunta suka fita tsakar gidan.

"Don Allah Aunty Shahida kiyi hakuri da abinda Talatu take miki wallahi ba na jin dad'i."


A jiyar zuciya ta sauke ta ce."Jamila Mahaifiyarku ba ta k'aunata ban san abinda nayi mata ba. amma ki sani wallahi ta na cin albarkacin ki, da ba don haka ba da tuni na dauki mataki a kanta."

Ta ce.'' Ki cigaba da hakuri watarana sai labari yanzu ina mutumin da ku ka zo tare?"

Ta ce." Yana can waje a tsaye kuma wallahi da gaske ya ke aure na zai yi."

Ta ce.''Amma na ji dadi wallahi. mu je na gaishe shi kafin Baban ya dawo"

Tare su ka fita suka same shi a tsaye a jikin bango (garu) yana danna 'karamar waya nokia da aka d'aure ta da kyaure.

Jamila wani irin kallo take masa a tsorace! kwata-kwata mutumin bai kwanta mata a rai ba, ganinsa wani iri babu sutturar arziki gashi tsoho gemunsa da tsalli-tsallin furfura!

"Ina wuni." Ta fada tana dan sunkuyar da kanta.

Ya amsa fuskarsa a sake yana dan tsokanarta.

Tana 'yar dariya ta ce." Ga aunty na nan; don Allah ka rike mana amanarta! kaga tana da lalura ta rashin ji a kula mana da ita.

Murmushi yayi ya ce." Kada ki damu 'kanwata zan ri'ke amana insha Allahu; yanzu ina so ne nayi magana da babanku domin da gaske na ke."

Tana k'okarin magana Hujaj ya k'araso gurin! kallonsa yayi sama da 'kasa da fadin." Malam menene? ka tsaya min a kofar gida tare da yara na."

Ya d'an rusuna da fadin." Barka da dare Baba." A takaice ya amsa da "Barka dai"

Gurin yayi shuru dukkaninsu jikinsu yayi sanyi!

Ya kalli Shahidan da fad'in."Waye wannan ki ka kawo min?"

Ta ce." Shine wanda nake so na aura, mun daidaita junanmu shine ya ce yana da kyau ya zo ya gaishe ka, kuma akwai alherin da yake tafe dashi."

Bud'ar bakinsa sai ya ce." Ni da kai na nace ki fito da mijin aure, amma kin san dai a yanzu ba ni da kud'in da zanyi miki wata hidima ko? don haka maganar aure a tattara a ajiye a gefe guda. idan kuma zai aure ki babu kayan daki falillahil-hamdu."

Ya ce."Babu komai Baba Shahida nakeso ita kanta ba wani k'yale-k'yale ba, buri na kawai ka bani ita.

Wani irin kallo yake masa yana raya abubuwa da yawa a ransa! wannan mutumin da yake gabansa da ka gani talaka ne duba da yanayinsa, amma kuma ya yaba da nagartarsa kuma ba 'karamin yaro bane, Shahida 'yarsa ce mai rangwamin ga ta, shiyasa bai wani ci buri a kanta ba, amma zai so nagari ya aure ta ko dan ya kula da ita saboda lalurarta.

Ya ce." Na baka yarinyar nan amana. sai abu na gaba wane alheri ne yake yafe da kai bayan wannan."

Fuskarsa cike da annuri ya ce."Alhamdulillhi na gode sosai insha Allah zan kula da amanarka. bayan haka kuma Shahida ta shaida min irin halin da ka ke ciki na rayuwa, zanyi iyakar bakin kokari na akan lamarin.

Ya ce." Wane irin taimako za kayi min? da ka ganinka dai talaka ne, wanda baka ajiye ba, baka bawa wani ajiya ba, shin ko akwai wata hanyar da ka ke samun kudi a b'oye kake yawo a tsiyace! kana da hanyar miliyan biyu da rabi ne?"

Ya girgiza kai cikin rashin jin dadin maganganunsa ya ce." Eh insha Allahu, ina da alfarma a gurin maigidana, mutum ne shi mai tausayi da taimako insha Allahu zai duba uzuri na."

Nan da nan fuskarsa ta washe ya ce." mutukar kuwa hakan ya tabbata baka da matar aure sai wannan yarinya na baka ita halak malak."


Bai yi mamakin jin haka daga gare shi ba, ya ce."Shikkenan Baba na gode sosai, yanzu abinda za ayi shine ka bani number wayar mutumin da yake bin ka bashin kud'in koda maigidana zai bukaci magana dashi idan na koma can abujan."

Ya ce." Don ta lamabar waya ai babu matsala sai na baka yanzu.

Ya shiga fad'a masa lambar shi kuma yana d'auka a 'kwara'babbiyar wayar dake hannunsa da aka d'aure ta da kyaure.

Sai bayan ya gama fada masa lambar wayar ne ya kalle shi da fadin." Da gani kai ba yaro bane ga alamun shekaru nan a tare da kai. shin kana da aure ko kuma yarinyar nan ita ce matarka ta farko?"

Ya ce." Nayi aure shekarun baya har 'yata ta girma ta zama budurwa amma tana can garinmu."

Ya ce." Ina kenan?"

"Katsina a cikin karamar hukumar jibia, nan ne mahaifata.

Ya ce." Ma sha Allah. kayi kokarin ganin ka fitar dani a wannan masifar ni kuma nayi maka alkawari sati guda yayi yawa gurin daurin auranka da yarinyar nan.

Ya ce." Insha Allahu zanyi kokari."

Gidan ya shige zuciyarsa fes! yau haihuwa za tayi masa rana.

A tsakar gida ya same ta a tsaye. kamar wacce take jiran shigowarsa babu sannu da zuwa ta ce." Maganar da Jamila ta zo fad'a min gaskiya ne?"

A lalace ya kalle ta kafin ya ce." 'kwarai kuwa yau haihuwa za tayi min rana dake da yaranki kun zama yuyuyu! sakarkaru kawai."

Yana 'kare maganarsa ya bude dakinsa ya shiga ya bar ta a tsaye a gurin cike da d'umbun mamaki!


A hanyar su ta komawa gida take tambayarsa ashe ya ta'ba aure har da haihuwa, ya tabbatar mata da gaskiyar magana ya ce." Amma yarinyar ta na can garinsu kamar yanda ya shedawa mahaifinta.

Cike da 'kauna da begen juna su kayi sallama da juna tare da alkawarin cewa gobe da wuri zai zo ya gaisa da Baba Asabe kafin ya tafi.

Lokacin da ta shiga gidan, muryoyinsu ta ji a can cikin daki harda Kawu Musa. gabanta ya fad'i! jin kawu Musa a gidan ba alheri ba ne.

Saliha ta fito tsakar gidan ta sameta a tsaye ta kasa shiga dakin.

Ta dan d'aga muryarta da fadin." Matar mahaukaci kin dawo kenan?"

Kallonta kawai tayi amma ba tace mata komai ba, ba don ba taji haushin kalaminta ba.

Suka fito daga dakin a tare, Baba Asabe na sake jadadda masa matakin da zata dauka akan al'amarin, ya yin da shi kuma yake nuna mata cewar tabi a hankali domin ba ta da k'arfi akan yarinyar kamar ubanta.

Ya kalle ta suka had'a ido! sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa.

Ya d'an bud'e muryarsa da fad'in." Shahida wannan rayuwar ki ka za'bawa kanki ko?"

Shuru tayi hawaye na 'kok'arin kufce mata.

Ya cigaba da cewa." Shin me ki ka hango a tare da wannan mutumin wanda shi ba mai hankali ba kuma ba mahaukaci ba, a matsayin ki na mara lafiya zaki za'bi wannan rayuwar da mara galihu. wanda ba a san asalinsa ba."

Baba Asabe ta d'ora da fadin" Yo idan ba rashin hankali ba ina ke ina auran mahaukaci mutumin da ba a san daga ina ya ke b......gurin ta bari tana wani irin kuka! duk suka bita da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu.

*An fara biyan kudin littafin masoya*
*Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce #500 Vip 1k 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE??*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
[ 47&48
To a daran ranar Talatu dai da kyar ta iya rintsawa, domin ta jima tana tunani akan al'amarin, ka da fa tana zaune baki a sake yarinyar da ta tsana! tayi mata zarra! tunda gashi tun kafin aje ko'ina Hujaj ya fara yi mata habaici ita da 'ya'yanta, dole ta je ta bincika domin sanin ainihin mutumin da ya ke neman auran yarinyar.


Shahida da 'kunci! da 'bacin rai ta tashi. tsakanin Baba da Saliha jira take wani ya ce mata kule tace cas! domin gabad'ayansu a ciki take dasu, saboda suna kiran masoyinta da mahaukaci.

Ta shiga d'akin ta same ta a kudindine a cikin bargo amma ba bacci take ba. kawai ta tsirawa rufin dakin ido!

Ta d'an bud'e muryarta ta ce." Shahida ki tashi ki karya kummalo mana kina kwance kina tunane tunane mara amfani ko?"


Ta mike zaune tana kallonta ta ce." Baba ina neman alfarma a gurinki."

Kallonta tayi tana ayyana wani abu, labarin gizo dai baya wuce na koki, amma sai ta ce." To Allah ya sa zan iya.

Ta ce." Don girman Allah da darajarsa ki kar'bi wannan al'amari da zuciya d'aya! wallahi nayi imani da Allah cewa alheri ni, nayi istahara akan al'amarin, Baban Baba ba zai cutar dani ba, mutumin kirki ne kuma ba mahaukaci bane kamar yanda ku ke zato, yau ce kawai ta mayar dashi haka, amma tunda ya samu ubangida ya koma mutum kamar kowa, arziki da rashi duk daga Allah suke, kiyi min addua kawai Allah ya sa hakan alheri ne.

Gabadaya ta gama kashe mata jiki da kalamanta, a yanda ta shirya ta kuma kudire a ranta cewa sai bayan ranta wannan al'amari zai tabbata, amma wannan maganganun da tayi gabadaya gwiwarta tayi sanyi, babu shakka akwai wani abu da Allah ya rufe, kuma sha'anin aure irin wannan ba'a tsawwala wa domin idan ka tsananta sai ayi babu kai.

Ta ce." Shikkenan Shahida na rabu dake da abinda ki ke so Allah ya sa hakan alheri ne dake damu baki daya.

Cike da tsantsar farin ciki ta ce." Na gode sosai Baba insha Allahu za muyi farin ciki gabadayan mu, amma ki shirya an jima kadan yana tafe zai zo ku gaisa kafin ya tafi Abuja gurin sana'arsa.

Ta na kokarin fita daga dakin ta ce." Shikkenan Allah ya kawo shi lafiya.


Zama tayi kan kujera 'yar tsuguno jikinta duk a mace!

Saliha ta ce." Baba Lafiya dai?"

A sanyaye ta ce." Lafiya lou Saliha al'amarin Shahida da wannan mutumin ne yake ban tsoro.

Ta ce." Tuntuni na ce miki ki daina damuwa amma kina kokarin janyowa kanki matsala! duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka."

Ta ce." Na yi fatan alheri ai Allah ya ba su zaman lafiya."

Shuru tayi ba ta amsa da ameen ba, kawai ta cigaba da feraye kabewar dake gabanta.


**
To kamar yanda Talatu ta kudire a ranta cewa za ta je tayi tambaya a kan lamarin, da asubah zakara ya bata sa'a ta fita can wani 'karamin k'auye ta nufa gurin wani malami, wanda ya duba mata al'amarin ya kuma tabbatar mata da cewa shi bai ga komai ba face alheri domin kuwa babu da na sani ko bak'in ciki a cikin al'amarin, sai farin ciki.

Jikinta a sa'bule ta dawo gida da tunanin yanda za tayi ta wargatsa auran.


***
Cikin nutsuwa ta fito ta same shi a tsaye a soran gidan, sosai tayi farin cikin ganinsa tsaf dashi cikin shadda bulu mai duhu tazarce har k'asa da hula da takalmi ya dora rigar sanyi a sama saboda yanayin garin sanyi ya fara busawa, ta tsuguna har kasa tana gaishe shi, ya amsa a nutse yana mata wani irin kallo wanda ya sa ta jin kunyarsa ta kasa tashi tsaye.

Ya ce." Kin yi min kyau fiye da tunaninki.

Murmushi tayi ta ce." Ni ma haka idan na gan ka cikin suttura cike da kamala sai na yi ta mamaki kamar ba kai ba, wanda da yawa mutane suke maka kallon mahaukaci! lallai babu shakka wannan ubangida naka dole a jinjina masa domin ya taka muhimiyyar rawa a rayuwarka, ya sanya ni cikin farin ciki mara mislatuwa domin ni yayi wa tagomashi yayi wa bajinta ba zan gushe ba face na cigaba dayi masa addu'a har karshen rayuwata."

Ya dinga jin wani irin farin ciki na kwarara a zuciyarsa, ya ce." Za ki gaisa da maigidana insha Allahu sai kiyi masa godiyar alherin da yayi miki, duk da cewa yana da labarinki amma lokaci kad'an ya rage ku gaisa da juna da ikon Allah."

Ta mi'ke tsaye tana gyara mayafinta da ya sauka a kafadarta ta ce." Ina fatan zuwan wannan rana.

Kawu Musa ne ya shigo da shirin zuwa kasuwa a tare dashi.

Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta.

Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani."

Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu."

Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin farin ciki.


Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar.

Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa.

Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa.

Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta.

Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu.

Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan.

Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni".



Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin."

Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen."

Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya"

Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri.


'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba.

****
"Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa.

Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj."

Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne.

Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu."

Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?"

Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura."

Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?"

Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon.

Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu."

Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai.

Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi!

Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane.

Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa.

Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe.

_"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_


Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki.


" Na san da hakan, domin kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera!

Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba."

Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke."
Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert.

Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta.

Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa.

Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba."
Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login