Showing 123001 words to 124287 words out of 124287 words
tausayi wallahi domin abin nan dai ba zai samu ba, saboda ba ni da tsarki.'
Lokaci guda yanayinsa ya sauya, ya ce." Ban yarda ba wallahi sai na duba." Ya fada yana kokarin kamo ni. na goce tare da kokarin guduwa! ri'ke ni ya yi da kyau! ya kwantar da ni kan gadon da cewa; idan na duba na ga 'karya ki ke to mai k'watarki a hannunsa sai Allah."
Kukan shagwaba na fara ina tureshi tare da san bugun 'kirjinsa. a kasalance ya kalleni! yana lumshe idonsa, turje-turjen da nake na lura kamar yana kara masa kuzari! da za'kuwa!
Aikam na samu abinda na ke so, domin dai ni babban burina naga yana yi mini rawar jiki, ina jin d'adin hakan.
Ya dinga bin fuskata da zafafan kesses masu hargitsa lissafi, yana yi yana shanye hawayen da ke fita na iya shege! jikinsa sai kyarma yake, ya fara yi mini wasu abubuwa wanda na gaza jurewa! da yake nima a bu'kace nake! ban san lokacin dana matseshi a jikina ba, tare da bashi taimako. ban san wanda ya bi buk'atuwa ba a tsakaninmu, ban ta'ba kuka ba a ranar sai da nayi saboda irin abubuwan da yake mini wad'and'a suka susutar da ni, na dinga buga sambatu! gashi na ri'ke wuta ya zama ni nake sarrafa komai.
Tabbas a ranar munyi abubuwa masu wuyar mantuwa da tsayawa a rai! kuma babu shakka Allah ya yi ikonsa ya rantsar da rabo a tsakaninmu.
Haihuwa nake duk shekara, yayin da arzikin mijina ya cigaba da yalwata, na samu nutsuwa da shi, ya samu nutsuwa da ni, bani da matsalar komai domin mijina ya tsaya mini yana kula da ni da yara na biyar maza uku mata biyu, sai cikin da nake d'auke dashi a yanzu haihuwa ko yau ko gobe.
Ina rokon Allah ya sauke ni lafiya tare da masu lalura irin tawa.
'KARSHE
*ALHAMDULILLAHI.*
Abinda na rubuta daidai Allah ya ba mu ladan tare, kuskuran kuma ina rokon Ubangiji Allah ya yafe mini.
*BINTA UMAR ABBALE*
Ina mika godiya ta ga ilahirin masoyana mussaman manyan matan da ba su ganin kyashin cigabana, gaskiya na jinjina muku sosai gurin ganin yanda kuka dinga rige-rigen sayan complete din littafin nan tun kafin na fita dashi. na yab da Amanarku da kuma kaunar da kuke mini. Ubangiji Allah ya yawaita mana irinku??????
VIP Tare da NORMAL da kuma Comments Section ina godiya kwarai da gaske! sai mun hadu a sabon littafina.
_*TSAKURE DAGA: ALKALAMIN BINTA*_
_NANA KHADIJA Rikitacciyar soyayya zazzafa mai abin tausayi tsakanin 'yan uwan juna biyu da suka kasance ma'aurata, sai dai sun kasa samun nutsuwa sakamakon kutsuwar wani al'amari da ya shafi zamantakewar auran nasu. babu shakka sihiri gaskiya ne kuma yana taka muhimmiyar rawa gurin raba tsakanin ma'aurata._
YARO DA KUDI
_Bahagon mutum ne mara jin magana wanda ya tasa duniya a gaba. bashi da aiki sai neman mata da zuwa club! babu abinda ya karya alkadarinsa sai soyayyar 'yar maigadin gidansu, yarinyar da kullum ya ke kiranta da aljana ita ce ta saita shi masa hanya madaidaiciya_
GIMBIYA BALARABA
_Ba ta gaji sarauta ba amma tana da k'asaita irinta ta sarakai! mace ce kamila da ta ri'ke maraicinta, sosai ta sha gwagwarmayar rayuwa, 'karshe hakuri ya yi mata rana lokacin ta dace da auran Almansur Sarki k'asaitacen sarkin dake mulki bisa adalci._
BABBAN YARO
_Matashin Attajirin da al'umma suke amfanuwa da dukiyarsa. sai dai dan adam tara yake bai cika goma ba, lokacin da yake kan sharafin neman mata domin jin dadin duniya, sai yarinyar ta shiga cikin rayuwarsa Asma'u ta taka muhimmiyar rawa ga rayuwar Amjad, amma kuma kafin burinsu ya cika na mallakar juna sai da suka koka! mutuka! sun sadaukar da soyayyarsu domin ceton rai!_
MASHAHURI
_Mashahurin mawaki ne da duniya ta san da zamansa! baya jin magana kuma baya jin nasiha! ya shahara! sosai a fanni wa'ka! amma lokaci guda Ubangiji ya jarabce shi da soyayyar 'yar abokin gabarsa, mutumin da kullum ke masa nasiha akan ya kula da duniya! Hanifa ta fad'a tarkon Khalid bayan muguwar gabar dake tsakaninsa da mahaifinta Ya shaik malami ne wanda kowa ya san shi a cikin gurin mabiyin sunnah ne! 'Yarsa d'aya ta bijire masa ta biyewa son zuciyarta, amma ta d'and'anawa aya za'kinta bayan cikar burinta_
TSANTSAR BUTULCI
_Nagarta da Dattako irin na mutanan da ya sanya Alhaji Madu ri'ke d'an abokinsa tamkar shine ya haifeshi, sai dai Khamis ya zama butulu bayan alherin da Alhaji Madu ya yi masa, sai ya mayar masa da sharri! lokacin daya haddasa tashin hankali a gidan ranar daurin auran abokinsa Habib, ya d'auke amaryar ya gudu da ita. a cewarsa shi ya fi dacewa da ya aureta. Babu shakka ramin 'karya 'kurarre ne!_
_SADAUKI OMAR_
_'Dan Sarki ne shi amma sai ya kasance ya rayu a masarautar gidansu a matsayin bawa! hakan ya janyo Gimbiya Aysha 'yan kanin mahaifinsa keyi masa tujara da fitsara, da yake miskili ne kuma ba ya daukar raini sai da ya karya alkadarinta yayin da mugun sonsa yayi mata dabaibaiyi! bayan kuma ta gama kaskantar dashi tare da fad'in sai ta wulakantashi. a karshe dai shi ya yi nasarar auranta ya kuma yi silar fitar ta daga gidan sarauta su nufi wani bigire mai muni inda suka dinga gabatar da wata irin rayuwa! sai dai kuma kad'aicewarsu a guri daya ya janyo zazzafar soyyaya tare da gudanar da wasu al'amura da su kansu basu yi tsammani faruwar hakan ba_
_NI DA YAYA SADAM_
_Miskilin Soja ne amma fa ya iya soyayya! da kula da abinda yake so. Sayyada ta yi nasarar janyo hankalinsa gare ta bayan fadi tashin da ta yi kafin hakan ta faru. sai dai a lokacin da suke tsaka da gudanar da amarcinsu wani mummunan a'lamari ya faru. wanda ya janyo rabuwarsu duka suka shiga cikin mawuyacin hali bayan azababbiyar soyayyar da take dawainiya dasu_
_'YAR BANGAR SIYASA_
_Amadu Musa wanda jama'a ke kiransa da (Ba iya ka) Attajirin mai kudi ne da al'umma ke cin abinci a karkashinsa, wannan dalilin ne ma ya sanya talakawan garin tsayar dashi a matsayin dan takarar governor domin suna ganin idan ya samu nasara zai kawo cigaba a jahar tasu. sai dai kuma 'yan adawa suna gefe masu shirya masa bita da kulli. cikinsu har da WASILA 'YAR GASKE! yarinyar da ta yi k'aurin suna! ba kuma ta shakkar kowa harkar siyasar ta shigo gadan-gadan! ita ce ta dinga cin dunduniyarsa tana shirya masa manakisa, abokan hammayarsa na yi mata wanka da kudi da manyan motoci! sosai ya zurfafa tunani akan nemo hanyar da zai tagayyara ta ya sanya rayuwarta cikin k'unci tare da wadanda suke bata masa suna a gari. kai tsaye kawai sai ya nufi mahaifarta aka d'aura masa aure da ita, wannan ya kawo k'arshen makircinta sai dai fa duk da haka bata saduda ba, tana gidan nasa tana binsa ta bita da kulli tare da abokan gabarsa, har sai da bukatarsu ta biyu, sai dai abubuwan da suka biyo baya masu muni sun sanya ta zubar da hawaye tare da nadamar abinda ta aikata. Allah Annabi ta dinga binsa tana roko ya mayar da ita dakinta amma ya shafawa idonsa toka! akwai wani babban al'amari da ya faru wanda ya sanya dole ya sauko ya saurareta domin neman mafitarsu gabad'aya_
*TASKAR BINTA UMAR*
*NANA KADIJA*
*YARO DA KUDI*
*BABBAN YARO*
*GIMBIYA BALARABA*
*MASHAHURI*
*TSANTSAR BUTULCI*
*LADIDI KWADAGA*
*NIDA YAYA SADAM*
*RUWAN DARE*
*SADAUKI OMAR*
*'YAR BANGAR SIYASA*
*MADADI*
*DA WATA A KASA*
*'KWARYA TABI KWARYA*
*GA IRINTA NAN*
*MATSALAR MU A YAU*
*GOJE*
*MAJANUNI*
_In sha Allah za ku samu duka littafai na complete cikin farashi mai rahusa, akwai discount ga wadanda suka saya da yawa. Amma ban da kiran waya ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262 or 08089965176_
29, August 2025
Mohamed Amina Nyam
Pls I want to download