Showing 84001 words to 87000 words out of 124287 words

Chapter 29 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16689

rashin ji na, sai da kunnuwa suka amsa sautin tsakin! kaina kawai na sunkuyar, ita kuma ta tashi ta fita daga dakin tare da bugo 'kofar da k'arfin gaske.

Tun da na sunkuyar da kaina bai d'ago ba, domin na ji ciwon kallon banzan da tayi min tare da tsakin da ta ja min.

Sautin maganarsa na ji, na d'ago kaina ina kallonsa, ya sake maimaita maganarsa wacce yake da tabbacin cewa; ban ji ba, wannan karon da sauti mai 'karfi yayi maganar.

"Kiyi hakuri." Ya fad'a tare da kamo hannuna yana 'kokarin tashi zaune. sai kawai na tsinci kaina da taimaka masa ya tashi na jingina masa fillo a bayansa kafin na koma na zauna. A nutse na ce."Ai ku za a bawa hakuri."

Ya ce." Saboda me?" murmushin takaici nayi kafin na ce" Na ga gabad'aya kun d'auki lefi kun d'ora min, domin na shigo na ga Hajiya tana kuka tana sheda min cewa; damuwata ce ta haddasa ciwonka ya tashi, bayan haka kuma, a gabanka Shukura ta ja min tsaki tana min kallon banza! idan da matsala kawai ka rabu da ni, domin ni bana so shiga cikin zargi, bayan da bakinka kafad'i ga wacce ta haddasa maka ciwon tun fil-azal, amma ana neman d'ora min jakar tsaba."


"Kiyi hakuri." Wannan kalmar ya furta kafin ya rintse idonsa, alamun sun nuna baya bu'katar doguwar magana.


Na ce" Ya jikin naka?" da sauk'i ya fad'a ba tare da ya bud'e idonsa ba.

Shiru d'akin yayi na 'yan mintina kafin na ce" Yanzu me kake bu'kata?"

Bud'e idonsa yayi yana bi na da kallon mamaki!

Fuskata na saki amma ban ce komai ba.

Ya girgiza kansa tare da fad'in" Ba abinda nake bukata a gare ki, sai alfarmar ki zauna tare da ni, ki kuma cire shakku a kaina, bayan haka kuma ki ri'ke ni amana."

Jim nayi na minti biyu kafin na ce" Shikkenan zanyi 'kokarin ganin nayi hakan muddin zan fita daga zargi don bana so wani abu ya same ka mutane su ce ni ce sanadi.

Murmushi yayi, yana min wani irin kallo kafin ya ce'' Babu wanda zai zarge ki don kin taka sawun 'barawo, kin 'karasa gawar da ba taki ba, dama can bani da cikakkiyar lafiya, ko da Hajiya tayi wannan maganar, ba da wata manufa ba, tayi ne domin ki gyara kuskuranki, ma'ana ki zama mai kula da mijinki domin ki samu rabauta ranar gobe 'kiyama."

Sunkuyar da kaina nayi tare da wasa da yatsun hannuna, ya tashi a hankali ya nufi band'aki cikin 'kwarin jiki, sai kawai na tsinci kaina da bin sa da kallo da tausayinsa 'kadan a cikin raina.



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*








*MAJANUNI*
_THE UNKNOWN RICH MAN_
92&93
Ba zai iya tantance wane irin hali yake ciki ba sakamakon tarayyarsa da yarinyar. ita ce mace ta uku da wata mu'amula ta shiga tsakaninsu. amma ya bata lamba ta d'aya a cikin jerin matan da ya yi mu'amula irinta ta auratayya. babu shakka Ubangiji baya tarawa bawa damuwa! domin ko da ya halliceta cikin jerin masu rangwamin gata sai kuma ya wadata ta da ni'ima tare da sauran abubuwan da ba kowace mace ke da irin shi ba, shi dai ya tabbatar da cewa; yarinyar ta zarce duk matan da yayi tarayya da su don ya samu gamsuwa da ita sosai, babu wani abu da yayi saura a mararsa, sakayau! ya ke jinsa tare da wani irin nishad'i da bai ta'ba shigarsa ba, lallai dole ya godewa Allah bisa ni'imar da yayi masa gurin azurta shi da 'yar baiwa wacce take da tarin nagartattun abubuwa masu alfanu a gare shi.
Da wannan tunane-tunanen bacci mai nauyi ya d'auke shi ya matse ta tsam-tsam! a jikinsa.


Da gari ya waye kuwa duk hidimar da ya kamata na yi da kaina shi ya yi min, yanda yake nuna kulawarsa a kaina hakan ya faranta min raina mutuka! sosai nayi farin ciki da ya samu budurci na domin kuwa shine abin alfaharin kowace 'ya mace, da kansa ya kai ni band'aki tare da had'a min ruwan wanka yana tattare hannun riga ya ce" Ko nayi miki wankan ne?"

Kai na girgiza! alamar A'a na tsuguna sai kace wata sabuwar maijego gabana ciwo kawai yake min, ba tare da na kalle shi ba na ce" Ka d'an had'a min wani ruwan amma kada yayi zafi sosai.

Da sauri ya had'a min ya taimaka min na shiga ruwan na zauna, rintse idona nayi sosai lokacin da zafin ruwan ke ratsa jikina, zugi da zafi suka sanya hawaye zubo min.

Duk sai ya tashi hankalinsa yana ta bani hakuri, juye-juye kawai naka a ruwan kamar na fito, wata zuciyar ta hana ni, nasan cewa ruwan zafin shine zai dakusar da ciwon dake gurin.

Hannunsa ya tsumbula cikin ruwan yana so ya ta'ba gurin "Ko dai na sa likita ta zo ta duba ki?" yana maganar yana so yasa hannanusa a gurin, ina kaucewa, na ce" A'a zai daina ciwon insha Allah.

Ya ce." Ina so na gani ne domin hankalina ya kwanta.

Kallonsa nayi naga da gaske yake maganarsa, na ce"A'a ba sai ka gani ba.

Cikin wata irin murya mai taushi ya ce." Saboda me? bayan na zama wani jigo a rayuwarki, kin zama ni, na zama ke, meye abin jin kunya.

Shiru nayi, domin bana tsammanin zan nuna masa.

Ya fara 'kokarin tayar dani tsaye wai dole sai ya gani, kuka nasa tare da ri'ke bahon ruwan ina ture hannunsa da fad'in" Ka fita ni dai."

Fita yayi ya bar ni a band'akin ba don ransa ya so ba.

Na jima cikin ruwan d'umin. sannan nayi wankan tsarki! na fito na d'aure da towel mai girma a jikina.

Ko da na fito baya cikin d'akin, amma ga kaya na nan, ya ajiye min a kan gado.

Na shirya cikin atamafa java mai ruwan ganye kuma dinki yayi min cif! a jikina, mai kawai na shafa tare da fesa d'aya daga cikin turarunkansa dake jibge a kan madubi, na gabatar da sallar asubah da ta wuce ni, kafin na rarrafa na hau gado na kwanta bacci ne fal a cikin idona, ga wani irin ciwo da jikina keyi min, abu dai goma da ashirin! sun dabaibaye ni, jiya dai na yabawa aya za'kinta, har bana so na tuna gumurzun da mu kayi saboda tsigar jikina ce take tashi, amma na godewa Allah da ni'imar da yayi min, duk isar mace mutuncinta ta kai budurcinta gidan mijinta, na yi farin ciki da ya same ni cikakkiyar mace, kuma yanda na fahimta ya samu gamsuwa da ni ko ga irin addu'ar da yake min tare da d'aukar min al'kawari iri-iri, cikin zuciyata nake adduar Allah yasa hakan yake a zuciyarsa, don gaskiya bana k'aunar kishiya duk da na san umarni ne na Ubangiji amma ni kam na fi buk'atar na zauna ni kad'ai da mijina.


Tare suka shigo d'akin da Hajiya, sai nayi saurin rufe idona, kunya nake ji kada ta fahimci wani abu ya faru. ashe zuwa yayi ya fad'a mata abinda ya ke da akwa. shine ta shigo ta duba ni.

Kamar na fashe da kuka saboda takaici! ban iya cewa komai saboda nauyi da jin kunya baccin 'karya na tsira, ina jin suna ta maganganu nayi luf! sai da ta fita daga dakin sannan na bud'e idona na kalle shi. yana zaune kusa da k'afafuna yana waya!

Cikin dubara na tashi zaune na d'an jingina da fuskar gado! ganin na tashi yasa ya katse wayar da ya kalle ni, cikin kulawa ya ce." Sannu kin ga yanzu Hajiya ta fita ta shigo duba ki."

Zum'bara baki nayi tare da fad'in" Me yasa ka fad'a mata wani abu ya faru a tsakaninmu?"

"Me yasa ba zan fad'a mata ba? bayan ta damu da nayi aure na haihu, sannan kuma yanda ki ke kuka da gurin shi ya bani tsoro na je na sanar da ita ko da wani taimakon da za tayi mana." Yafad'a idonsa a tsaye a kaina.

Na ce" Gurin fa zai dusashe in sha Allahu.

To "Allah ya yarda, amma na yi waya da likitana duk nayi masa bayani abinda ke da akwai, ya bani tabbacin cewa; idan ana bu'katar gurin ya zama normal sai an 'kara wani abun, shine na ce ko zaki bari nayi wani yanzu ko da sau d'aya ne.


"Bangane ba." Na fad'a gabana na duk uku-uku! don gabad'aya hankalina ya tashi jin abinda ya ke fad'a.

Sai ya fashe da dariya yana kallona. Ganin haka yasa na juya masa baya domin na fahimci tsokanata yake.


Da sauran dariyar a tare da shi ya ri'ke hannuna da fad'in" Da wasa nake miki my love ba zan miki komai ba sai gurin ya warke in sha Allahu."

Ba tare da na juyo ba na ce" Ka tabbata?"

Shiru yayi be bani amsa ba.

Shukura ta shigo da'kin da sallama a bakinta. shi ne ya amsa, ni kam kunya tasa na rufe idona, ina 'kokarin 'kwace hannuna dake cikin nasa, ya ri'ke da kyau!

'Bangaran Shukura kuwa ganin ta, kwance lakadan a gadon mahaifinta, sai wani bakin ciki ya turnu'ke ta, ga shi kuma a zaune ya kusa da ita hannunsa cikin nata, kamar ta kurma ihu! saboda takaici.

A sanyaye ta ajiye kwandon abincin dake hannunta, ta ce"Daddy ina kwana?"

Ya amsa cikin kulawa yana nazarin fuskarta domin ya hango damuwa a tare da ita.

Sai da ta daure zuciyarta sannan ta ce" Antina ina kwana."

Ba tare dana kalle ta ba na amsa da "Lafiya lau." daga haka ban ce komai ba, amma cike nake da mamaki ya akayi yarinyar ta sauko har take gaishe ni.

Ta ce"Daddy Hajiya ta ce na kawo muku abin karin kummalo idan anti ba za ta iya saukowa 'kasa ba"

Hankalinsa gabad'aya yana kaina ya bata amsa da cewar" To babu laifi hakan."

Hanyar fita ta nufa jikinta duk a sanyaye. sai kuma ta kasa daurewa ta tsaya tana kallonsa kafin ta ce"Daddy ya maganar da mu kayi da kai kwana biyu da ya wuce?"

Ya ce." Wace magana kuma?" domin shi ya manta ma sunyi wata magana.

Ta ce" Akan dawowar Mommyna d'akinta da kuma al'kawarin da kayi min."

Tsawa! ya buga mata tare da nuna mata hanyar fita. " Wuce ki bani guri shashashar banza."

Da saurin gaske ta bud'e k'ofar ta fita tana sgare hawaye.

Na kalleshi sai na ga duk babu walwala a tare dashi.

Na ce" Ya za ayi ka kore ta har kana yi mata tsawa! kada fa ka janyo min 'bakin jini, Shukura 'yar ka ce bai kamata kayi haka ba."

Babu fara'a a tattare dashi ya ce." Ke a ganinki abinda tayi ya da ce?"

Ido na tsira masa da fad'in." Magana kayi da ita har kayi mata al'kawari lefi ne don ta sake tuntu'barka da maganar.

Ya ce." A'a ni ban yi mata al'kawarin dawo da mamanta ba, ta dame ni da maganar sai na ce mata zan duba na gani."

Dama abinda nake so na ji kenan daga bakinsa.

Sai kawai nayi shiru raina gabad'aya ya 'baci! ban san me yasa ba haka kawai nake jin kishin matan da yayi tarayya dasu duk da cewa a yanzu basa tare, amma haushinsu nake ji sosai!


Shiru d'akin yayi na 'yan mintina, kafin ya kalle da cewa" Ki tashi ki ci abinci ga farfesu Hajiya tayi miki." Yana 'kokarin bud'e fulas din yake magana.

Motsi ban yi ba ballanatana yasa ran zan sauko na ci wani abu.

Ya gaji da maganarsa ya had'a shayi da kansa ya karya ya sha, kafin ya zuba farfesun ya dangwala da biredi.


Cikin bacci da ya fara fizgata na ji shi yana laluben hannuna dake cikin bargo, ya saka min wasu takardu.

"Tashi zaune za muyi magana."
Yafad'a babu wasa a muryarsa.

Sai da na mula tukkuna na tashi zaune. har yanzu na kasa sakin fuskata, duk na damu jin maganar dawo da uwar gidansa.

Cikin nazari ya ce " Duk kin sauya fuska saboda wani dalili mara tushe! kada fa ki damu, na riga na shafe babin Fatima a rayuwata, domin da zan dawo da ita to da tun kafin na aure ki na dawo da ita, don haka ki samu nutsuwa.

Daurewa nayi na ce'' Waye ya fad'a maka na damu? kaina ne fa yake min ciwo ba wani abu ba.

Murmushi kawai yayi tare da fad'in ''Ai na gane ana 'kaunata yanzu tunda na ga kishi 'karara a cikin idonki."

Shashantar da maganar nayi ta hanyar fad'in" Wannan takardun fa?"

Ya ce" Naki ne."

Na tsira masa ido domin yayi min 'karin bayani.

Ya fuskance ni sosai kafin ya ce." Kasancewar na samu abu mai muhimmanci a gurinki yasa nayi miki wannan kyautar. takardu biyu ne a hannunki, akwai na gidan mai da kuma na rumfar kasuwa dake kwari, yanzu haka ana cigaba da hada-hada na kasuwanci a kowane sassa, abinda aka samu duk ya zama mallakinki, ina miki fatan alheri.

Na kalle shi da mamaki mai yawa a tare dani, na ce"Saboda kawai ka samu budurci a tare dani zaka bani gidan mai sukutum! nayi me da shi to?"

Sai ya 'bata fuska da fad'in" Ba wai ba ne a gurina, kuma budurcinki ya cancanta da komai. domin zan iya tattare duk abinda na mallaka a duniya na baki saboda farin cikin da ki ka sanya ni a ciki, saboda haka ki dauki al'amarin da muhimanci, ki kuma sa a ranki cewa; kin bani abu mai daraja wanda bani da abinda zan biya ki dashi.

Gabad'aya jikina yayi sanyi da kalamsa. kawai na ri'ke takardun tare da zuba masa ido, ni dai ban ga abinda zanyi da gidan mai ba, ina lefin rumfar kasuwar.

Kira ne ya shigo wayarsa ya d'auka! nan na ji yana fad'in" In sha Allahu gobe zan shigo kano d'in sai a san yanda za a yi.

Na ce" Don Allah mu tafi tare."

Girgiza kansa yayi da fad'in" Za ki je amma ba yanzu ba sai kinyi nauyi.

Sai na rasa inda maganarsa ta nufa, sai nayi nauyi kamar yaya?

Ya katse tunani na ta hanyar fad'in." Kina bu'katar zama a wannan sashen ko za ki koma naki domin na riga na gama shirya miki komai."

Girgiza kai nayi da cewa" A'a gwara nan d'in."

Ajiyar zuciya ya sauke da tare da cewa "Shikkenan abinda ki ka za'ba shine za'bi na."


*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*

*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*



_*MAJANUNI*_
94&95
Yini cur! mu kayi a d'aki sallah ce kawai take fitar dashi, amma na samu kula sosai da garinsa, sai dai na kasance cikin fargaba da damuwa! domin damuna ya dinga yi ta'ba nan, ta'ba can, duk jikina ciwo yake min mussaman kirjina zafi yake min sosai irin na rashin sabo, ban san me yasa ba, gabad'aya hankalinsa ya fi karkata a gurin, haka ya yini yana lugudar min jiki, ni sam bana wani jin dadi saboda tsoro, shi kuwa jikinsa har karkawa yake, duk yanda ya so na yarda yayi irin na jiya na'ki yarda da shi, domin ba zan amince ya dawo min da ciwo sabo ba, wannan dalilin ne yasa ya damu kirjina kamar zai raba ni da su, sai zafi suke mussaman nipples d'in.

Bayan fitarsa sallar magariba, na daddafa na shiga bandaki nayi wanka tare da shiga ruwan d'umi, na d'auro alwala na fito, akwatin kayana na bud'e na dauko doguwar riga milk mai adon duwatsu da hula, sosai rigar tayi min kyau! kuma da ka gani tana da tsada, na sa a jikina a take ta zauna ta kuma fitar min da surori, kamar na cire na sanja domin ina gudun abinda duk zai gani a tare dani da zai ya tayar masa da hankali. haka dai na hakura na zauna da rigar a jikina, bayan na gabatar da sallar isha'i yunwa ta addabi cikina gashi an sauka da tarkacen kwanukan abincin rana, babu komai a dakin.

Firjin dake gefan gado na bud'e nan naga lemuka kala-kala da fresh milk da yogurt sunyi sanyi sosai. na dauko fresh milk din guda daya na mayar da firjin na rufe.

Ina kokarin bud'e robar madarar ya shigo d'akin. da sallama a bakinsa. na amsa hankalina na kan madarar dake hannuna. Gefe na ya zauna tare da zagaye

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login