Showing 102001 words to 105000 words out of 124287 words

Chapter 35 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16702

masa dukkanin abinda yake faruwa da kuma dalilin zuwansa jibia.

A matsayinsa na abokinsa da suke taimakon junansu ta kowane fanni, sai ya bashi shawarwari masu kyau! ya kuma ce dashi ya daina sanya damuwar komai a ransa yin hakan zai janyo masa samun matsala tunda dama lafiya bata wadace shi ba. Cikin karamci da girmama juna su kayi sallama. Alhaji Faruk ya shiga mota direbansa yaja suka fita daga gidan.
Cikin nutsuwa ya juya ya koma gidan, da tunanin abubuwa da yawa a cikin ransa.


KANO
Hujaj dai ya ga ranar haihuwa, domin gabad'aya rayuwarsa ta sauya ta dalilin yarinyar da ya hofintar a can baya yake ganin kamar wahala ce a gare shi, sai gashi itace sanadin samun rufin asirinsa, domin a yanzu mijinta shi ya rufa masa asiri ya bashi muhalli tare da bude masa babban shagon sayar da takalma a kasuwar kwari! sannan ya bashi kudi masu yawa ya biya mutanan dake binsa bashi, a yanzu bashi da wata matsala sai ta Talatu domin ta riga ta zame masa matar jaraba! amma ba zai rabu da ita ba zata cigaba da zaman 'ya'yanta. gefe guda kuma shirye-shiryen auransa ya kammala saura sati biyu a d'aura aure! hankalinsa kwance yake gudanar da harkokinsa, sai dai wasu daga cikin abokansa sun takura masa maula mussaman wanda suka she'ka suka ga ba k'waya, da yawa daga cikinsu sun tsiyace!
sun fatarce! dalilin abinda suke aikatawa na sabon Allah. wadanda Allah yaso daga cikinsu sun shiryu, shiyasa suke lallabowa gurin abokin nasu domin ganin yanda Allah ya rufa masa asiri! Sunyi-sunyi da shi, ya yi musu jagora gurin surukin nasa, amma ya'ki a cewarsa ba za su je su zubar masa da mutunci ba, bayan duk kanwar ja ce, su kuwa sun riga sun san cewa Alhaji Habu (Dangaske) Bangon sukari ne kowa ya jingina sai ya lasa.

To dama ai duk wanda ya ketare umarnin ubangiji yana 'kare rayuwarsa ne a tsiyace! shiyasa duk rintsi bawa yayi k'o'karin ganin ya ci halilinsa.



Kasancewar akwai abun. ginin gidan Baba Asabe bai ja dogon lokaci ba, bayan tafiyarsa da kwanaki biyu ma'aikata suka rushe gidan, aka fitar da tsari mai kyau. cikin kwana goma gida ya kammala, ya fita zakkah a cikin unguwar! zuwa yanzu jama'a da yawa sun samu labarin abinda yake faruwa. da yawa 'yan uwa suna alfahari da kasantuwar mutumin a cikin zuriarsu, hakan abin farin ciki ne, a ce babban mutum irin wannan ka had'a nasaba dashi, shi kansa Kawu Musa rayuwarsa ta sauya data iyalinsa, itama Baba Asabe sai dai ta wanke goma ta tsoma biyar, bata cas bare as! dalili surikin nata ya wadata ta da duk abubuwan bukata kamar yanda yayi alkwari. sai suka kasance cikin farin ciki idan ka cire Saliha data kwarzabi kanta kullum cikin kuka da damuwa! Har Baba Asabe ta ranfo abinda ke damunta wato hassada takewa 'yar uwata bisa alherin da ya same ta, al'amarin ya bata mamaki mutu'ka! ta zaunar da ita domin tayi mata nasiha sai ta rushe da kuka! a guje! taje ta rungume! rijiya wai gwara ta fad'a ciki ta mutu!

Hankalin Baba Asabe ya tashi ta kira ubanta ta sheda masa duk abinda ke faruwa!

Kawu Musa ya fusata! ya zazzabga mata mari! a fuska ya rufe ta da fad'a da cewa; tayi hattara da rayuwa, kuma ta ajiye a ranta cewa; hassada babu inda zata kaita sai tashar nadama, kuma idan Ubangiji yace ?? ?? ?? akan bawansa babu wanda ya isa ya ce dan me."
Ta tashi ta shiga d'aki tana rusa! kuka tare da nadamar rayuwa, wato dai ta tabbata cewa; Shahida tayi mata nisa kenan, itama dole tayi mubaya, tunda iko ne na Ubangiji ya sauka kamar yanda mahaifinta ya tabbatar mata, sai ta kwanta kan gado tayi lamo! tana hasaso fuskar Shahidan, tana can cikin daula da kwanciyar hankali, ganinta sai an cike form watakila ma duk gurin da zata je akwai masu tsaronta.
Abinda Saliha bata sani ba shine Ubangiji yana iya jarrabawar bawansa ta hanyoyi da dama, da yawa jama'a suna ganin Allah yayi wa yarinyar gyadar dogo gurin auran attajirin mutum irin Dangaske! tabbas akwai jin dadi da dukiya wacce bata da iyaka! sai dai har yanzu bata samu irin nutsuwa da kwanciyar hankalin da take bukata ba, duba da cewa; tunda akayi auran take cin karo da matsala daban-daban, kuma har yanzu a cikinta take, wannan shine cikar mumini a gurin Ubangji, kuma duk wanda Allah yake jarabtarsa sa'i da lokaci yasa a ransa cewa shi d'an gatane, wanda aka bari sa-sakai yake sabgoginsa ba tare da ibtila'i ba, babu shakka shine abin tausayi.

Talatu ita ma dai ta kasa tawakkali! duk ta zauce! tasa masifa a cikin ranta kullum tana tafe! a hanya kuma duk inda ta ga shanyar mutane sai ta kwashe ta tura a buhu ta je ta sayar, abinda Allah ya jarrabeta kenan. Hujaj duk yana da labarin abinda take aikatawa a gari, ga Hadiza ta famtsama har yanzu ba a san ina take ba, idan Talatu ta fita tun safe sai dare take dawowa gida. kuma babu yunwa bare kishirwa a gidan, tunda ya samu abinyi yana basu abinci su ci su k'oshi! amma ta gaza hakuri babban burinta ta samu nasarar hana shi aure sannan kuma ta haukata yarinyar da tayi mata fintinkau!


Sutturun mutane cike da buhu! ta d'auka ta kai gurin dilallai ta sayar ta hada kud'in ta nufi gurin malamin dake mata aiki.

Ta bashi kudin kamar yanda ya bukata. ya d'auki kayan asirin ya bata cikin wata k'warya da aka rufe da jan yadi! yayi mata bayani duk yanda zata aiwatar da aikin, cikin mota k'waryar asirin ke ciki ta fad'i! a take wasu tsintse sukayi firr! suka fito, lokacin ta kurma! uban ihu! direban ya tsayar da motar yana tambayar ba'asi! cikin fitar yayyaci! ta bude kofar motar ta fita tana ihu! tare da kokarin kamo tsuntsaye dake shawagi a kanta, sai ta cire dankwalinta tayi d'amara! dashi kawai ta dauki hanya yayin da tsuntsayen ke mata wani irin kuka a tsakiyar kanta. sune suka saita mata hanya ta dinga tafiya tana wasu irin surutai!

Direban kuwa yana addua ya watsa sauran kayan shirkan, yaja motarsa ya bar gurin yana neman tsari da sake d'aukar fasinja irinta.


****
Duk da kasancewar wannan shine karo na farko shiga jirgi a gareni ban nuna k:auyanci ba, na dai ji tsoro a cikin raina amma na daure ban nuna ba, kusa da shi na zauna Hajiya da Shukura suna tare.
Hira suke a tsakaninsu wanda duk na tsargu sai nake ganin kamar da ni suke duba da yanayin fuskokinsu babu walwala.

Shi kansa tunda muka shiga jirgin be ce komai ba, kuma har yanzu da damuwa a tare da shi, kuma ya lura da duk abinda su Hajiyan suke min, hakan ma ya 'kara masa 'bacin rai! kawai sai ya mayar da hankalinsa gurin jan madaidaicin carbin dake hannunsa.
Ganin haka yasa nima na kama kaina amma cikin zuciyata na tsananta da addua.

A haka muka sauka garin.
Direbansa ne yazo ya d'auke mu bayan mun sauka a filin jirgin kai tsaye gidansa dake garin muka nufa domin shine umarnin da ya bayar.



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*

118&119
Babban gida ne mai d'auke da 'bangare hud'u! ma'ana zaman mace hud'u! ginin gidan irin na zamani ne, kuma ya k'ayatu! da ababen more rayuwa, masu gadi da masu aiki cike da gidan kai kace a nan mai-gidan yake zaune dindindin!

To jin cewa ya shigo garin yasa jama'a suka fara turereniya, kafin kice kwabo harabar gidan ta cika da mutane mata da maza.
Akwai bu'katar ya samu hutu, idan san samu ne ma ya kwanta yayi bacci domin abinda na lura yana damunsa kenan bacci da gajiya da kuma damuwa! ga jama'a sunyi dafifi sun ja dogon layi suna jiransa a waje.

Sama ya hau domin ya watsa ruwa a jikinsa ko ya warware. ganin haka yasa na bi bayansa domin ba zan iya zaunawa a tsakanin Hajiya da Shukura ba duba da irin kallon zargin da suke min.

A sanyaye na bud'e dakin na shiga k'amshin sanyayan turaransa ya ba'kunci hancina, d'akin ya tsaru sosai! komai na mussaman ne a dakin, na samu gefen katafaran gadonsa na zauna ina kallon wani hotonsa dake kafe a bangon dakin, lokacin yana samartaka yayi kyau sosai!
D'aya bangon kuma hotonsa ne a yanzu wanda yake cikin manya kaya farar shadda babbar riga da 'yar ciki da d'inkin sarakai! kamar koda yaushe da nad'in farin rawani a saman hular dake kansa, idonsa sakaye da farin gilashi. sosai na shaga gurin kallon hoton har ya fito daga band'akin ban sani ba, gilmawarsa na gani d'aure da babban towel a jikinsa da wani k'arami a hannunsa yana goge kansa .

Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi, shima ni yake kallo har ya zo ya zauna kusa dani da vasilin a hannunsa.

Sai kawai na tsinci kaina da yi masa sannu.

Ya yi murmushi da cewa; Ke za ayi wa sannu."

"Saboda me?" na fada ina kokarin kar'bar vasiiln din dake hannunsa.

Shiru ya yi bai bani amsa ba. kawai sai na fara shafa masa man a bayansa da hannayensa.

Ya lumshe a ido tare da sauke ajiyar zuciya. cikin nutsuwa nake shafa masa man a sassan jikina ba tare da na kawo komai a raina ba na ce" Jiki ya yi sauki alhamdulillhi, ya kamata ka kwanta ka huta sai dai hakan ba zai samu ba duba da irin tarin jama'ar dake jiranka a waje, gashi kuma ka ce yau zamu koma gida.

Duk maganar da nake bai ce min komai ba sai aukin kallona da yake.

Lokacin gabana ya fad'i ganin yanda yanayinsa ya sauya, da sauri na cire hannuna daga kirjinsa tsoro nake kada ya ce zai min wani abu, dama tunda ya kwanta jinyya tsayin kwanaki takwas kenan babu wata mu'amula da ta shiga tsakaninmu.

Aikam kafin ma nayi wani yun'kuri ya kamo ni zai kwantar a gadon.

Ture shi nayi na matse a tsorace tare da gyara wuyan rigata.

Ya kalleni a galabaice ya ce." Meye haka kuma?"

Kai na sunkuyar k'asa na ce." Kayi sauri ka kintsa jikinka jama'a suna jiranka a waje.

Ya ce." Bayan kin tayar min da hankalina, ba zan sauka ba sai nayi wani abu."

Na ce."Ni kam babu ruwana me nayi maka?"

Ya nuna kirjinsa da fadin." Nan kika sosa min."

Kunya ta rufe ni ganin yana nuna min nipple dinshi, wai nufinsa lokacin da nake shafa masa mai na sosa masa gurin.

Ya sake kamo ni a karo na biyu yana kici-kicin cire min riga. kuka nasa da cewa; daga zuwa sai wani abu don Allah ka bari ka fuskanci abinda ya kawo ka garin".

Kai ya girgiza da cewa; Idan ban manta ba yau kwanaki takwas kenan rabona dake! kokari kawai nake, amma bana tsammani zan iya hakuri a yanzu kiyi hakuri ki sakar min jikinki, kuma ki taimaka min tunda babu kwari a jikina har yanzu.

Na ce" To ka bari mana sai ka warware gabad'aya, nima jikina babu kuzari! ba zan iya komai ba."

Shiru yayi na minti biyu kafin ya ce" Duk da haka dai idan kina so nayi sauri na kammala, sai kinyi wani abu akai, tunda kin fi kowa sanin yanda nake."

Bude baki nayi zan yi magana yasa hannu ya rufe min baki tare da lumshe idonsa da duk suka sauya kala!

Hakanan nayi ha'kuri! al'amarin ya kasance! wai mutumin da yake fadin bashi da 'kwari! amma sai da ya shud'e mintina arba'in yana abu daya kuma kamar koda yaushe sai da yayi sau biyu tukkuna ya sauka!

A galabaice na tashi zaune ina gyara jikina, shimfidar gadon duk ta lalace! sai dana gyara tukkuna yana fitowa daga bandakin na shiga domin tsarkake jikina.


Bashi da matsalar suttura a ko'ina, wardrobe dinsa dake dakin cike take da kaya nau'i daban-daban, ya zabi wanda yake so ya shirya ya sauka kasan, lokacin har iyayen nasa sun hallara suna zaune a falon gabadaya har da ita wacce ta assasa zaman wato Fatima.

A mutunce ya gaishe da 'yan uwan mahaifin nasa, ya nemi uzurin zuwa ya sallami jama'ar dake jiransa a waje, kafin ya zauna domin gabatar da abinda ya tara su.


Kimanin awanni biyu ya dauka da talakawansa ya yi musu alheri kamar yanda ya saba, sai dai matsalar har yanzu sun ki 'karewa dalili wasu na shiga wasu na fita, domin dai garin ya riga ya san da zuwansa.

Ba don ya gaza ba, ba kuma don babu kudin ba a'a saboda uzurin dake gabansa ya dakatar da jama'a da cewa; suyi hakuri sai wani lokacin idan Allah ya nufa. sannan ya sanya daya daga cikin ma'aikatan gidan ya yi list din sunayen wanda suka rage, ya yi musu alkawari cewa; duk ranar da ya sake zuwa garin da su zai fara.
Wannan ne ya kawo sanadin watsewar jama'ar da sukayi cikar kwari ciki da wajan gidan domin samun tallafi na abinci ko na kudi da makamantansu.


Sai da suka gabatar da sallar azuhur tukkuna suka zauna Baba Audu ya bud'e taro da addu'a kafin ya d'ora da fad'in abinda ya tara su.


Sai bayan da Baba Audu daya kammala maganarsa tukkuna ya kalli Sadiya dake zaune a kusa dashi ya ce." Hau sama ki kira min Shahida domin yana da kyau a zauna da ita."

Hajiya da sauri ta ce" Alhaji Habu anya yarinyar ba ita ke sauya maka tunani ba? nifa yanzu na daina tausaya mata, bayan haka kuma meye amfanin zamanta a cikinmu, ita da ba kunne ba, me zata fahimta? ai na dauka itace ta assasa tashin hankalin.''


Ranshi ya sosu! da irin zargin da Hajiyar keyi wa yarinyar, ya gyara fuska da cewa; Shahida bata da hannu cikin faruwar wannan al'amarin, saboda haka don Allah Hajiya ku kyautata zatonku a kanta, sannan kuma ni dai wannan yarinyar bata isa tasa ni ba, bare ta hana ni."

Kwafa! tayi da cewa" Mutum mugun icce ne wallahi, ni tausayinta nake da farko, amma ganin yanda lokaci guda ta birkita maka tunani yasa na fara zarginta, wani sa'in talaka abin tsoro ne."

Baba Audu ya ce." Hajiya kiyi shiru wannan maganganun duk basu taso ba, idan fa an bi ta barawo to abi ta mabi sawu! itama Fatima bata da gaskiya, mai zai sanya ta je tana neman fitina da matarsa"

Baba Auta ya kalleshi yana girgiza kai, wato ba tun yau ba, ya lura da cewa; D'an uwan nasa yafi goyuwa da bayan daya b'angaran duba da cewa akwai k'umbar susa! a duk lokacin da zama zai had'asu irin wannan kullum Saddiku ne mai gaskiya a gurinsa saboda yana da kud'i! yana ganin idan yaso zai iya umartar yaron ya mayar da Fatima dakinta amma yayi shiru saboda ba 'yarsa ba ce, ya san irin zaman da zai yi da shi.


Ina kwance ina sa'kawa da kwancewa! Sadiya ta shigo na tashi zaune ina kallonta da tambayar yaushe ta zo?

A sanyaye ta ce" Ban jima da zuwa ba, ki zo kasa ana nemanki."

Gabana ya fad'i na ce" Ni kuma? Sadiya meye amfanin zuwana? ko nayi muku wani lefin ne?"


Ta girgiza kanta da cewa" Ya kamata ki zo dai ki gaisa da iyayanmu suka ganki sannan kuma ki wanke zargin da suke miki, Hajiya ma yau ta furta da bakinta cewa; da sanya hannunki al'amarin ya faru."

Hawaye suka cika idona na ce"Sadiya wallahi dana san abinda zai faru kenan da nayi shiru da bakina, domin na tsani abinda za a ce ni ce sanadi, kuma bana so zumunci ya lalace! sanadiyata.
Amma wallahi ni ban sanya shi yin abinda ya yi ba."


Ta ce." Kina da hujja mai karfi ba, ni kaina banga amfanin zamanta a gidan ba, tunda babu aure a tsakaninsu, kuma komai yana iya faruwa! baki da laifi domin kin nuna rashin amincewarki akan hakan, matsalar dai shi da ya yanke hukunci cikin fushi, shine dalilin da yasa Hajiya take zargin da sanya hannunki tunda bai ta'ba irin wannan furjewar ba.


Jiki a sanyaye na ce" Ai shikkenan. ni fa idan abin zai zama rikici wallahi na hakura ya mayar da ita mutukar zamu zauna lafiya."


Ta ce." Lallai Antina baki da wayo! kuma har yanzu baki san wacece Fatima ba, ko da yake zama bai had'aku ba shiyasa ki ke tunanin zaku zauna lafiya, wallahi bana sha'awar ta dawo gidan d'an uwana domin gabadaya sai kun rasa kwanciyar hankali. saboda haka duk rintsi kada kiyi wannan furucin.

Shiru kawai nayi ina kallonta da tunanin abubuwa da yawa a raina.


Tare muka sauka kasan, suka zuba mana ido har muka samu gurin zama. cikin girmamawa na gaishe su, suka amsa babu yabo babu fallasa, cikinsu babu wanda ya nuna min wani abu a fuskarsa, sai dai sanin zuciyar mutum sai Allah.


Shiru na minti uku bayan zuwanmu gurin, Ya ce." Baba Audu duk na ji bayaninka, kuma ina so ku ajiye a ranku cewa! ni Abubakar abin ikon ku ne, komai na zama a duniya ban isa na sauyawa towo suna ba, ku ne iyayena kuma ina alfahari da hakan, koda yaushe kuna da damar yanke hukunci a kaina a matsayinku na 'kashin bayan samar da ni, sosai nake jin ku a raina dalili bani da wasu bayanku, amma ina so ku san da cewa; shi aure na mutum biyu ne, kuma ana yin sa ne domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali, idan baku manta ba a can baya dole ku kayi min na auri Fatima ba don raina yana sonta ba, hakan yasa na sha wuya a hannunta, bayan ina iyakar bakin kokarina

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login