Showing 63001 words to 66000 words out of 124287 words

Chapter 22 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16703

asiri na zai rufu, ni ne wanki da guga! gyaran takalma, aikin gini, dako cikin kasuwanni, gefe guda kuma ina yin gyaran babura da siyar da fetur a bakin titi, asiri na kuwa ya rufu, domin na d'aukewa mahaifiyata da k'anwata nauyin komai, don ba naso suyi kukan maraici! shiyasa nake fita nema ba dare ba rana.

Ganin haka yasa Hajiya dawowa gidan, a cewarta ai suma suna da hakki a kaina, duk neman da nake uwata nake wahaltawa, sai ta dawo gidan ta share d'aki ta zauna, tsirfar yau daban ta gobe daban, gashi ita kuma mamana bata da hayaniya! kuma bata son tashin hankali, shiyasa duk abinda Hajiyan tayi mata sai ta kawar da kanta, amma abin yana damunta mutu'ka, ni ma abin yana yi min ciwo, ranar da na samu zama a gidan, zan shiga har dakinta na zauna domin na nusar da ita cewa abinda take ba daidai bane, sai kawai ta fashe min da kuka ta lauya zancen da cewa; don naga 'kasa ta rufe idon mahaifina shiyasa nake nuna mata cewa mamana tafi ta girma a guri na, ganin haka yasa kawai na rabu da ita sai dai na daina sakar mata fuska, ko wasa take min bana saurararta nake shigewa na tafi harkokina, sai ta rarrafo ta fito tsakar gida ta zauna ta dinga habaici! wanda yake damun zuciyar mamana! bata kaunar tashin hankali da damuwa, haka za suyi ta kuka ita da Sadiya a daki abin na damun ransu.


Cikin ikon Allah da wannan buge-buge da nake na samu na sayi fili, sai dai tunda Hajiya ta ji labari, ta dame ni kan lallai sai na fito da matar aure tunda ina samun kudi, nayi kokarin nusar da ita cewa; kudin da nake samu na rufin asiri ne, zanyi aure amma ba yanzu ba.

Ta 'ki yarda da maganata, kawai ta kira Baba Auta ta fara sheda masa halin da ake ciki, 'kiri-'kiri na ga hassada a cikin idonsa, jin cewa na sayi fili har na soma gini, ya dinga fad'a mara dalili wai akan me duk abunda zanyi ba zan nemi shawararsa ba, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa.

Ya ce." Shikkenan Allah ya sanya alheri, maganar aure kuwa dole mu yi maka ka fito da mata, idan kuma baka da ita to na baka Fatima."

Gabana ya fadi! na kalle shi da mamaki a tare da ni na ce." Wace Fatima?"

Ya ce"Ta waje na mana ko kana ganin kafi karfin ka aureta ne?"

Na ce." Gaskiya bana ra'ayinta Baba auta babu maganar rufa-rufa a tsakaninmu, Fatima 'yarka ce amma kasan bata da kamun kai ko?"

Ya ce." Magana zaka fada min a gaban ido na?"

Na ce" Ba haka bane na jaddada maka abinda ka sani ne, ni d'in ba mace bane, ballanatana ayi min irin auran da bana ra'ayi, a kyale ni da kaina zan duba matar da ta cancata.

Sai kawai ta fashe! da kuka da fadin" Saddiku wannan sharrin na mahaifiyarka ne, domin ita take zama ta kitsa maka komai, amma ina laifin wanda yayi maka kyauta, Fatima dai 'yar uwarka ce duk lalacewarta ba zaka sanja ta ba.

Ya ce." Ki rabu dashi Hajiya tunda shi bashi da mutunci, a gaban idona yake cin fuskata, to shikkenan tunda kace baka sonta sai ka fito da wacce ka keso." yana gama maganarsa ya tashi fuuuu! ya fita.

Nima tashi nayi na bar gurin raina a 'bace! gaskiya ba zan lamunci wannan kama karyan ba. domin dai yarinyar kowa ya san halinta, sam bata da nutsuwa da tarbiya ga shegen kula maza da sauraran abubuwan da basu dace ba, a wannan zamanin kowane uba yana so ya za'bawa 'ya'yansa uwa ta gari, to akan me yana ganin kashi da rana ya taka, ba zai yuwu ba.


Ko da na shedawa mamana halin da ake ciki, sai ta ce tunda abun ya riga ya zama haka to nayi gaggawar fito da matar da nake so na aura, domin a ganinta hakan zai sanya su janye maganar Fatima.

Na shiga tsaka mai wuya a lokacin, domin kuwa tunda na girma na kai munzali na samartaka ban ta'ba kula wata budurwa ba, ba don bani da bukata ba, a'a asali ma ni mutum ne mai yawan sha'awa, shiyasa sa'i da lokaci nake azimi domin tseratar da kaina.

Ina son aure sosai, to amma ina cizawa! domin na riga na san aura a yanzu dole sai ka shirya, nauyi biyu ne zai hau kaina dana iyalina da na mahaifiyata da 'yar uwata.

Amma tilas tasa na yankewa kaina shawara domin gujewa auran Fatima wacce babu ita a cikin tsarin rayuwata


Na je na samu mahaifiyata da maganar Na'ima 'yar 'kaninta ce Baba Salihu, yarinyar tana da tarbiya sosai da kunya, wannan shine abinda ya ja ra'ayi na akanta har na ji ina sha'awar auranta.

Tayi shuru tana nazarin al'amarin kafin ta ce." *D'an gaske* da yake sunan da take kira na dashi kenan, sakamakon sunan mahaifinta ne, ta cigaba da cewa" ina gudun abinda zai biyo bayan al'amarin, domin bana son tashin hankali, kuma ban mance da wasiyyar mahaifinka ba, kan cewa lallai na kula da mahaifiyarsa ka da tayi kuka damu, muyi kokarin ganin mun rabu da ita lafiya, wannan dalilin yasa duk abinda Hajiya take min a gidan nan, bana d'aga kai na kalleta, domin zama na amana da mutunta juna nayi da mijina, duk da mahaifiyata bata yare, ya zama dole na girmama tasa, saboda haka ban hana ka nemi auran Na'ima ba, amma ka je ka shedawa 'yan uwan mahaifinka domin mu ji hukuncin da za su yanke.

Hajiya tayi tsalle ta dire tace bata amince ba, wato naje na had'a baki da uwata ta dauki 'yar kaninta ta bani, na guji 'yar uwata Fatima, to bada yawunsu ba, muddun nace dole sai na auri Na'ima sai dai na sanja iyaye, gabad'aya suka had'e bakinsu, Kawu Audu dashi Baba Auta din, babu wanda ya fahimce ni.

Mamana ta umarce ni cewa na janye maganar auran Na'ima na amince da auran Fatima domin samun kwanciyar hankali, amma zata tsananta da yi min addua insha Allahu ba zan lalace ba.

Jin haka yasa na amince ba don raina yaso ba, sai don samun zaman lafiyarmu bakid'aya. amma sam Fatima bata daga cikin tsarin matan da nake so na aura.


'Bangaran wacce ake dambawar don ita, ko da ta samu labarin abinda yake faruwa, sam bata nuna damuwa ba, domin ta jima da sona a cikin zuciyarta, duk da bata furta min ba, amma duk alamomi sun bayyana, idan zamu had'u a ko'ina ne sai tayi min magana irin ta rashin kamun kai, "Wallahi kana burgeni, ina son namiji dogo giant (ingarma) wanda na san ya cika cif, zai gamsar da ni a shimfida, ire-iren wannan maganganun banzan take min a duk sanda za mu had'u, sai nayi mata jan ido sannan! na nuna mata cewa; ni nafi k'arfinta, amma hakan baya hana ta sake zuwar min da maganganun banza makamanta wannan. a duk sanda zamu had'u a wani guri

Tunda ake maganar auran ban taka k'afa na je gurin yarinyar ba, komai suke ina kallonsu ne kawai, nayi iyakar abunda zan iya na lefe da sauran abubuwan bukata na aure.


Sai ga ta tazo ta same ni a gurin aiki na tare da 'kawarta, kallo daya nayi musu na kawar da kaina domin raina ya 'baci da ganin sutturar dake jikinsu, komai a bayyane.

''Magana na zo nayi da kai" tafada a lokacin da take tsaye a kaina.

Na kalleta tare da fadin."Me yake tafe dake?" kai tsaye ta ce."Kudin 'kunshi da kitso nake bukata.

Dubu uku na bata amma na gargade ta kan cewa; kada ta kuskura ta zo min gida da gashin doki, domin gwanar 'karin gashi ce da tara farce, ga uban bilicin da take, duk ta lalata fatarta!

Ta'be bakinta tayi ta ja hannun 'kawarta suka tafi, tana maganganu kasa-kasa wanda na san dani take.


'Daki da rumfa kawai na samu na kammala, na dan kwaskware! dai-dai gwargwado. amma kicin da band'aki da sauran aiki, dan babu fulasta ballanatana rufi, haka nan na hakura, saboda yanda wahala tayi yawa, ga bikin ya matso komai ya kacame! babu mataimaki sai Allah.


To tunda aka d'aura auran, ban wani saki jikina da ita ba, na dai sanya mata ido ne kawai ina nazari a kanta.

Duk wani hakkinta da ya rataya a wuya na, ina kokarin ganin na sauke shi, amma kuma ban ta'ba had'a shimfida da ita ba, a falo nake kwanciyata ita kuma a cikin uwar daki, haka nan, za tayi shigar fitar da tsaraici a gabana tayi ta juyawa, amma cikin ikon Allah ba ta iya jan ra'ayi na zuwa gare ta.

Sai kawai ta je ta fad'awa Hajiya cewa; bani da lafiya domin tunda akayi auranmu wata hud'u ban ta'ba kwanciya da ita ba.

Hajiya ta samu abin yi ta je har d'akin mamana ta rufe ta da fad'a, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cin mutumci iri-iri abin mamaki! Fatima har tana sanya baki, anan ne Sadiya ta gaza hakuri ta fara mayar da martani, Hajiya ta gaura mata mari tana fadin" Wato za ta goyi da bayan uwarta kenan! to shikkenan zata sanya kafar wando daya dasu gabad'aya!

Sai da nazo gidan Sadiya ke sheda min abinda ya faru, sosai raina ya 'baci! idan Hajiya ta ci zarafin mamana na rabu da ita to babu shakka Fatima ba zata wanye lafiya ba, domin bani da hakuri a kan mahaifiyata da nake jinta a cikin ko'kon raina!


Sosai ta ga 'bacin raina akan abinda tayi, na ce kuma lallai in tana bukatar zama dani to ta je ta bata hakuri, idan ta'ki wallahi sai na sake ta. wannan shine hukuncin dana yanke mata.

'Kwana d'aya biyu shuru ba tabi umarnina ba, a cikin kwana na ukun, na rubuta mata saki daya a takarda na ce lallai kafin na dawo ta fice min daga gida.

Yanda na fahimta al'amarin ya bata tsoro sosai, domin ba tayi tunanin zan iya sakinta ba, haka na fita na barta cikin damuwa mai tsanani, wanda ni hakan bai dameni ba, mutukar zata ta'ba martabar mahaifiyata to wallahi na gama zama da ita.



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*ABACHE POULTRY FARM*??????
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*



*AKWAI VIP GRUOP POSTING SAU UKU A RANA MASU BUKATA SUYI MINI MAGANA*
71&72
"Ina gurin aiki sai ganin Sadiya nayi a kaina. Na san dama hakan zata faru, ko ga yanayin da naga yarinyar, idanuwanta sunyi jawur! da alama ta ci kuka ta 'koshi. na ce" Menene? nan take sheda min cewa gida babu lafiya na je ana nema na." hankalina na kan babur din da nake gyarawa, na ce "taje kawai gani nan zuwa."

Koda na shiga gidan hayaniya hayaniya ce kawai take tashi. muryar Hajiya tafi ta kowa sai sababi take, ta inda take shiga ba tanan take fita ba. shigowata yasa suka saurara, Inna Samira ce 'kanwar mamana, suke musayar yawu da Hajiyan, yayin da mahaifiyartawa ke cikin d'aki tana zubar da hawaye, wannan shine abinda ya d'aga min hankali, kuma nayi nadamar abinda na aikata, wanda na san shine musabbabin tashin hankalin da yake afkuwa a gidan.

" Ka shige ciki zanyi magana da kai." Hajiya ce ta bani wannan umarnin, ban yi mata jayayya ba, na bi bayanta. nan na gan su a zaune ita da mahaifinta wato Baba Auta fuskarsa a murtuke! ina mika masa hannu domin mu gaisa amma bai ko kalle ni ba.

Na samu gefe na tsuguna ina sauraran abinda zai biyo baya.

Ta fashe! da kuka! fuskarta kaca-kaca da hawaye! take fadin" Saddiku cin mutuncin da za kayi mana kenan? saboda 'kasa ta rufe idon ubanka, shiyasa kake nuna min iyakata, babu damar na yanke hukunci a gidan nan, sai kasa kafa ka tsallake, amma kara wannan, idan mahaifiyarka ta ajiye baka iya tsallakewa saboda kana gudin 'bacin ranta, amma ni dana haifi ubanka ka raina ni, Sadiya ta shirya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zauna, shin yaushe Fatima ta zagi uwarka da har zaka sake ta, akan wannan dalilin da bashi da tushe ballanatana maka ma."

Zanyi magana ya daga min hannu da fad'in" Dakata" sai nayi shuru ina kallonsa. yayi 'kwafa! yana girgiza kansa da fadin" Aure duka wata hud'u da 'yan kwanaki har ka soma wulakanta min yarinyata! menene abin jin haushi anan, saboda kawai ta nemi hakkinta na aure shine zaka sake ta, idan baka da lafiya ba sai ka fada mana ba, a nema maka magani."

Murmushin takaici nayi na ce" Lafiyata lau, kawai ban yarda da nayi kwanan aure da ita kai tsaye ba, sai mun je asibiti likita ya aunta, domin gabad'ayanku kun san abinda yake faruwa.

Sai ya fusata! ya rufe ni da fad'a zagi ta uwa ta uba! duk ina kallonsa ina kuma 'kara jin haushin 'yarsa a cikin zuciyata, an aura min ita ba don ina sonta ba, amma ana bina da cin mutunci.

Ta sassauta murya da fad'in" Saddiku kada ka bani kunya mana kayi wa Allah da annabi ka dau aniya a zuciyarka ka mayar da matarka dakinta, kada ka manta fa 'yar uwarka ce, duk abubuwan da suka faru a baya ka daina tunawa, ka fuskanci abinda abinda yake gabanka.

Ganin ta sassauta yasa na ce"To shikkenan zanyi shawara akan al'amarin... ya katse ni ta hanyar fadin." Kada ma Allah yasa ka mayar da ita mana, ko ka d'auka kai kad'ai ne namiji a duniya shashasha mara mutunci kawai"

Na ce" Baba auta idan an ciza a hura! kai babba ne kuma kanin mahaifina, ka dinga sanin irin maganar da zaka fada a kaina, domin ina tsoron watarana ka fusatani na mayar maka da martani"

Da kumfar baki ya ce" Ka mayar mana, ai babu lefi tunda kana ganin ka isa"

Ta ce" Ya isa haka Auta abi komai a sannu a hankali, domin shima duk abinda yake yana da hujja akai saboda haka rarrashinsa za ayi"

Shuru yayi yana cin magani. ita kuma Fatiman sai ta hau kuka! tana fadin" Sai Allah ya saka mata a kan zargin da ake mata, tunda ita dai bata ta'ba sanin wani d'a namiji ba.

Ni dai tashi nayi na bar su a gurin suna mayar da magana, na shiga dakin Mamana na same su a zaune jigum! Inna Samira na kwantar mata da hankali, itama zuwanta gidan kenan, sai ta riski irin cin zarafin da akewa 'yar uwarta, wannan dalilin yasa ta shiga ciki fad'an, domin kare mutuncin yar uwarta.


Ta kalle ni kafin ta ce" 'Dan gaske, wannan ya zama na farko kuma ya zama na 'karshe! kada ka kuskura wani sa'bani ya sake had'aka da matarka ka sake ta, ko bayan raina ban amince da hakan ba.

Na ce" Umma ba zan iya zama da matar da zata zage ki ba, wallahi duk son da nake mata zan rabu da ita, muddun ba zata martabaki ba, to ballantana wannan da kin san ba sonta nake ba, akan me zata ci mutuncinki ba."

Ta ce" Wannan ba hujja bace, ba kuma dalili ne da zai sanya ka saki matarka a kai ba."

Na ce" Wallahi Umma kin fi karfin komai a guri na, kamar yanda na fada miki da farko ba zan zauna da matar da zata ci zarafinki ba."

Ta ce" A gaban idonka Fatima ta zage ni?" na girgiza kai da fadin" A'a amma Sadiya ta tabbatar min, kuma na san ba za tayi k'arya ba."


Ta 'bata rai da fadin" To na gargad'e ka, ka daina yanke hukunci sai ka tabbatar da gaskiyar lamari, domin sakin Fatima na nufin abubuwa da yawa a gidan nan, ciki kuwa har da rashin kwanciyar hankalina, bayan haka kuma ina mai baka umarni yanzu-yanzu ka mayar da matarka, wannan shine farin ciki na"
Cikin 'bacin rai ta kai k'arshen maganar .

Na ce" Shikkenan Umma na mayar da ita kamar yanda ki ka bukata.

Ta ce" Allah yayi maka albarka, ka je ka d'auke ta ku tafi gida, kuma ka tabbatar da cewa ka bata hakkinta na aure, kada ta sake zuwa gidan nan, da wata matsala."

Na ce" Insha Allahu komai ya wuce zanyi k'ok'arin bin umarninki.

Addua sosai tayi min kafin na tashi daga gurin.


To wannan shine abinda ya faru, hakan yasa na kwanta da Fatima kwanciya irin ta sunnah, amma kash! ban same ta cikakkiyar mace ba, wanda dama na san hakan zata iya faruwa.

Koda na tsira ta a d'aki domin ta fad'a min iyakacin mazan da take mu'amula dasu, sai ta rushe! da kuka ta dinga ranste-rantse! kan cewa; babu wani namiji da ta kwanta dashi, na ce

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login