Showing 87001 words to 90000 words out of 124287 words

Chapter 30 - MAJANUN HAUSA NOVEL

18 Nov 2024

16701

'kugu na da hannunsa. cikin kunnena ya ce." Na san dole ki bukaci abinci ban san wane irin hali gare ki ba.

Murmushi kawai nayi ina d'an janye jikina daga nasa, domin ganin kamar yana so ya zarme! bai damu da abinda nayi ba ya fito da wayarsa ya kira Shukura tare da bata umarnin kawo abinci.

Minti biyar a tsakani ta buga 'kofar dakin. ya tashi ya bud'e mata amma bai yarda ta shiga d'akin ba, ya kar'bi kayan abincin itama ba tace komai ba ta juya ta tafi jikinta duk a sanyaye! wai yau ita ce ta zama tamkar 'yar aiki a gidan ubanta, ita takewa wata 'kask'antanciyya bauta! kuka mai 'karfi ya kwace mata da gudu! ta shige Hajiya dake zaune a falo ta bude dakinta ta zube a gado tana kukan b'akin ciki! yanda dadyn nata ke rawar jiki a kan musakar yarinyar shine abinda ya fi tsaya mata a rai! ko a mafarki bata ta'ba tsammanin hakan zata faru ba, 'Yar talakawa kuma muskiniya ita ce take juya kowa a gidan, gaskiya dole suyi wa tufkar hanci.

Wayarta ta d'auka ta kira Mommynta duk ta sheda mata abinda yake faruwa. Hajiya Fatima Hankalinta ya tashi ainun! nan ta ajiye a ranta cewa; yarinyar shiga tayi ta fita har ta sami nasarar mallake zuciyarsa, a yanda ta san halinsa a can baya mutum ne shi mai tsare gira, wanda baya son raini, amma yau 'kan'kanuwar yarinya mara galihu ita ke juya shi a gidansa. lallai da sake dole ta shiryawa al'amarin.


Tare muka ci abincin yana ta tsokanata, ni dai umm kawai nake iya cewa, saboda gabad'aya! jikina a mace yake ga bacci da gajiya sun dabaibaye ni.

Wanka ya shiga ya fito ina kwance ina kallonsa, ya shirya cikin suit wanda sukayi masa kyau ainun, kasa dauke idona nayi daga kansa har ya k'araso kusa dani yana gyara gilashin dake sakaye da idonsa, yayi murmushi tare da fad'in" Nayi kyau ne?"

Ajiyar zuciya kawai na sauke na tashi zaune tare da ri'ke hannunsa a marairaice na ce" Zaka tafi kano ka barni."

Ya sassauta fuska da fad'in" Ki kwantar da hankalinki don Allah kada kiyi min asarar hawayen nan, kar ki bari su zuba kinji ko nayi miki alkawari in sha Allahu za kije Kano a kurkusa domin ni kaina tafiyar dole ce, amma komai dare a gida zan kwana."

Jin abinda yace yasa na sassauta fuskata tare da k'ok'arin mayar da hawayen dake 'kokarin zuba, na ce" Shikkenan Allah ya kiyaye hanya."

Ya amsa da "ameen fuska a sake ya ce." Ba ki da sa'ko gurin Baban-baba?"

Dariya ya bani na ce" Ga ka nan a zaune a gabana, zan dai sake jadadda maka cewa; ka kula da kanka, kuma banda kallon mata."

Dariya yasa tare da jan karan hancina, ya ce." Ni mata basa damuna tunda ina dake bana ganin kowa."

Tsira masa ido nayi ina nazarin maganarsa, mafi akasarin mazan nan basu da al'kawari, bana so na saba da dad'in bakinsa na saki jikina dashi ya aikata min halinsu.

Ganin kamar ina masa kallon zargi ne yasa ya dubi agogon dake d'aure a hannunsa 9:30 na safe da sauri ya mi'ke tare da ri'ke hannuna muka sauka 'kasa.

Hajiya na zaune ita kad'ai tana kallon sunnah tv. zuwanmu gurin yasa ta fad'ad'a fuskarta da fara'a.

Na tsuguna har 'kasa na gaisheta, ta amsa cike da farin ciki. kafin ta kalle shi da cewa" Na ganka a shirye da fatan dai ba wani guri za kaje ba?"

Ya ce." Kano na nufa In sha Allahu. amma ba kwana zanyi ba, zan dawo yau idan Allah ya nufa".

Ta ce. " To ko da naji ai ya kamata ka d'auki hutu, domin ka samu nutsuwar gabatar da komai! domin so nake na samu jiki da wuri"
Tsakani da Allah ta fadi maganar.

Maganarta ta bashi dariya ya ce" Hajiya ai haihuwa ta Allah ce, zamana a gida ba shi zai kawo haihuwa da wuri ba komai lokaci ne, amma muna ta addu'a in sha Allahu rabon a kusa yake.

Cikin damuwa ta ce" Alhaji Habu halinka na sani da son kud'in tsiya kai kenan yawo a sama kaje nan kaje can, ai gwara kuma ka zauna a gida ka samu 'ya'yan da zaka tarawa dukiyar.

Ya dinga kyalkyala dariya yana kallonta. nima na shagala gurin kallonsa da mamakin yanda yake dariya, nan na gasgata maganar da suke bata shafe ni ba, domin da na ga damuwa a fuskar Hajiyan sai jikina yayi sanyi, duk da ban ji abinda suke tattaunawa ba, na tsargu shiyasa na kasa sakin jikina a gurin, amma yanzu ganin yana dariya yasa na samu kwanciyar hankali tabbas maganar da suke bata shafeni ba.

Ya kalle ta tare da fad'in" Ina Shukura ne? ban ji motsinta ba.

Ta ce." Au! kaga na manta wallahi ta bani sallahu ganin baka fito ba ta ce na fad'a maka cewa ta je filin jirgi d'auko mamanta wai ta dawo "


Ya 'bata fuska da fad'in"Shukura bata jin magana Hajiya na rabata da Fatima amma ta raina maganata"

Murmushi tayi ta ce" Ai hakan ba zai yuwu ba, domin dai babu wanda ya isa ya raba uwa da d'a, addua kawai zaka cigaba da yi mata Allah ya shirya mana ita, amma yana da kyau ka zauna da ita lallai ta fitar da miji daga cikin masu neman auranta"


Ya ce." Kwanaki na zauna da ita akan hakan, amma in sha Allahu a karo na biyu zan sake zama da ita domin na ji a wace matsaya ta tsaya domin ba zata mayar dani 'karamin mutum ba.

Ta ce." Hakan yayi, Allah ya za'ba abinda ya fi alheri.

Ya amsa da ''ameen tare da kallona ya ce" Sai na dawo ko."

Cikin nutsuwa nayi masa fatan alheri tare da dawowa lafiya ya kama hanyar fita sai duk muka bi shi da kallo har ya bude 'kofa ya fita.

Ganin fitowarsa yasa escorts d'insa gaishe shi ya amsa da kulawa d'aya ya kar'bi 'yar jakar dake hannunsa ya wuce sai suka rufa masa baya, kafin ya shiga mota sai duk ya gaisa da ma'aikatan dake harabar gidan, Sule da shi za a yi tafiyar domin amintaccen yaronsa ne kuma direbansa, shi ya bude masa motar ya shiga, escorts din suka zauna kusa dashi. sannan Sule ya zauna a mazauninsa ya ja motar. masu tsaron 'kofar su kayi masa fatan alheri tare da dawowa gida lafiya.

Kusan zaman kurame! mu kayi ni da Hajiya domin biye min tayi ganin duk maganar da tayi min bana iya tanka mata sai da umm ko a'a domin gabadaya nauyi da kunyarta sun hana ni sakat! a gurin, har gwara zama a saman na d'an fi sakewa! ganin haka yasa tayi min shiru ta cigaba da kallon tv amma da murmushi a fuskarta.

Shigowarsu falon yasa gabad'aya muka kalli Bakin k'ofa, hamsha'kiyar maca ce tana sanye da suttura ta alfarma, kallo daya nayi mata gabana ya fad'i! ganin Shukura rike da akwatin kayanta yasa na gazgata cewa Mamanta ce, gabadaya falon ya cika da masifaffan 'kamshin turaranta.

Ta 'karaso ta zauna kan kujera tana ya tsine fuska. ta kasan ido nake kallon duk motsinta, magana suke da Hajiya wacce ban fahimci komai ba tunda a hankali suke kawai dai naga bakinsu yana motsi.

Kallonta nayi a karo na biyu tun bayan zamanta a gurin, wayayya ce daga gani, ga ha'koran maka nan 'kasa da sama, wuya da hannuwanta uban gold ne masu nauyi, mayafi da d'ankwalin kanta ta cire ta ajiye, nan naga uban gashin doki a kanta anyi mata kitso dashi, duk sai na raina wayonta, domin ni a rayuwata na tsani 'karin gashi, da alama kuma tana shafe-shafe, domin farin gaskiya ya fita daban, gajera ce don na fita tsayi, amma a cike take ta ko'ina, hakan bai dameni ba saboda na san babu abinda za ta nuna min na daga suffah.


Hajiya ce ta katse tunanin da nake ta hanyar fad'in " Shukura Fatima tana magana.

Sai nayi saurin kallonta tare da aro jarumta na ce" Sannu da zuwa."

Ta amsa tana min wani banzan kallo kafin ta d'auke kanta ta ce" Hajiya don girman Allah meye abin so a tare da wannan muskiniyar"?

Kalmar k'arshe kawai na iya tsinta a cikin maganarta, raina ya 'baci mutuka amma ban ce komai ba, kawai nayi shiru ne domin naga matakin da Hajiyan zata dauka.

Babu walwala a fuskarta ta ce" Fatima bana son neman fitina don Allah ki kama girmanki, babu ruwanki da yarinyar nan zaman aure take.

Ta she'ka da dariya tana kallonta ta ce"Ai fa zaman aure manya ayi ma gani." Na sake tsintar karshen maganarta, domin ban ji abinda Hajiyan tace mata ba har ta fad'i wannan maganar, na dai fuskanci damuwa da a tare da ita.

Yun'kurin tashi nayi domin na bar gurin, saboda bana so na zauna matar ta fusata ni mu zo muyi abinda bai dace ba. da sauri ta ce"Shukura ina zakije kuma ki zauna mana.
Tafad'a tana 'boye damuwarta.

Na ce" Hajiya zan hau sama ne na kwanta bacci ne a idona."

Ta ce"To shikkenan idan kina bu'katar wani abu kiyi magana kada kiyi shiru."

Na ce"In sha Allahu Hajiya." da sauri nayi nufin barin gurin, sai kawai na ji shewarsu Shukura da Mamanta, nayi saurin juyawa domin naga abinda sukewa dariya, kawai Shukura sai tayi min maganar bebaye da hannunta, wai tambaye ta take menene tana kwaikwayon irin maganata.

Wasu zafafan! hawaye suka ciko idona, da sauri na mayar dasu cikin sassarfa na hau saman na bude daki na shiga na zube! kan gado. lokacin kukan ba'kin cikin da nake dannewa ya 'kwace! min, tun ina yarinya nake da kishin kaina, na tsani wani ya kushe hallitata ko ya kwaikwayi maganata hakan yana min ciwo sosai! kuma duk dauriyata bana iya jurewa sai na zubar da hawaye, haka na kwanta ina ta sharar hawayen takaici.



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*
96&97
KANO
Cikin manyan kaya ya fito daga d'akinsa yana ta zabga 'kamshin turare mai tsadar gaske. Ya tsikara hula gaban goshi da alama dai wani muhimmin guri za shi duba da irin adon da yayi, ko da yake dama can tuntuni shi d'an fafah ne! bai yarda da tu'ammali da 'kananun sutturu ba, har yanzu yana nan da halinsa zai yi kwalliya ya fita shar-shar sai ka rantse da Allah cewa; wani mugun attajiri ne saboda yanda yake kashewa kansa kud'i, amma gidansa kuma ko za a kwana da yunwa wannan bai dame shi ba, domin dai a 'koshe yake dawowa gida, Hujaj yana nan da mugwayen d'abi'unsa sai abinda ma ya yi gaba.

Talatu na gurfane! gaban murhu tana fifita wuta da mafici! duk tayi wujiga-wujiga! ta jigata! zani daban riga daban, daka gani tana fuskantar rayuwa! idonta sai tsiyayar da ruwa yake sakamakon haya'kin wutar da ya turnuke! gidan.

Kallonsa tayi a lokacin da ya tsaya a gabanta fuskarsa babu fara'a domin mugun haushinta yake ji ganin yanda ta mayar da kanta jakar mata, duk ta mokad'e! ta ko'ina babu wata mamora, shiyasa ya daina kwamciya da ita ko ta nemashi a shimfid'a sai ya wulakanta ta sannan zai bata hakkinta na aure, wannan shine dalilin da yasa ya fara neman wata 'yar duma-duma aure zai 'kara domin ya huce takaici!

Tasa gefen zaninta ta goge hawayen fuskarta kafin ta ce" Ka san Allah yau ba zaka fita ba sai ka biya bashin dake kanka."


Tsaki ya ja ya kalleta a wulakance kafin ya ce." Idan kuma na'ki fa?" da hanzari ta ce" Sai na d'auki mataki a kanka, domin na gaji da wannan wulakancin da kake mana ni da yarana. Wallahi Jamilu baka da imani ko kad'an, kuma na fada maka cewa; tun shekaran jiya rabon Hadiza da gidan nan, na bincika gidajen 'yan uwa nawa da naka bata nan amma Jamilu kayi biris da maganata, wallah ka kiyayi had'uwarka da Ubangiji domin tilas ya tuhumeka akan amanar da ya baka."


Babu wata damuwa a tare dashi ya ce."Wannan kuma matsalarki ce, ai ke ki ka lalata yarinyar, don haka sai kiyi hakuri da sakamakon da zaki gani, ni dai ba zan lamunci cikin shege a gidana ba."


Rushewa tayi da kuka! da fad'in " Yanzu fatan da kake wa 'yar cikin ka kenan? cikin shege fa kake magana Allah ya kiyaye."

Yayi tsaki da cewa; Ai ni Shahida ta fi yaranki sau dubu a guri na, tana can tana zaman aure, duk da mijinta talaka ne mai rangwamin gata, amma tsayin wata hud'u wata matsala bata faru ba, abinda ki ke nufi a kanta na sharri, sai gashi ya afku a kan 'yarki"

Zubewa tayi a gurin tana kukan bakin ciki da takaici, ya d'auko dari biyar daga aljihunsa ya jefe mata a jiki kafin yasa kafa ya fita daga gidan babu abinda ya dame shi.


Ganin fitowar Hujaj daga gidansa yasa Sule dake cikin mota yayi saurin fitowa ya riske shi. hannu ya bashi suka gaisa kafin ya ce." Kai ne Jamilu Hujaj ko?"

Ya ce." Eh 'kwarai kuwa ni ne Allah dai yasa lafia."

Sule ya ce."Lafiya lou ina fatan kasan Attajirin dan kasuwar nan Alhaji Habu Dangaske."

Da sauri ya ce." Eh na san shi a hoto da kuma kafafan watsa labarai amma ban ta'ba ganinsa a zahiri ba,ina fatan dai lafiya?" ya 'karasa maganar cikin fargaba."


Sule yayi murmushi tare da cewa" Alhamdulillhi dama shine ya turo ni gurinka domin yana bukatar magana da kai yanzu za mu je ofis d'insa tare "

Hujaj hantar cikinsa ta kad'a! baki na rawa ya ce." Me ya faru kuma? ni wata alaka bata ta'ba had'ani dashi ba wallahi."


Sule ya dafa kafad'arsa ya ce'' Ka kwantar da hankalinka ba wani abu bane sai alheri in sha Allahu."

A sanyaye ya ce."To shikkenan tunda kace haka mu je babu komai."


Hujaj tsuru-tsuru yayi a mota gabadaya jikinsa ya mutu jin cewar ga wanda yake nemansa sosai ya zurfafa tunani domin gano dalilin neman. amma bai hasaso komai ba, haka dai ya hakura sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa har suka isa zooroad in da babban ofis dinsa yake.



Ofis ne babban wanda aka 'kawata shi da kujeru na alfarma! tare da komai na bu'kata akwai hotonan Sarki shugaban 'kasa tare dana gwamna da kuma hoton mamalakin ofis din, wanda yake sanye da manyan kaya yayi kyau sosai.

Cike da fargaba Hujaj yayi sallama ya shiga jikinsa in banda rawa babu abinda yake.

Wayar dake hannunsa ya ajiye fuska a sake ya amsa sallamar tare da nuna masa gurin zama.


Hujaj kasa zaman kujerar yayi ya tsuguna gabansa tare da mi'ka hannunsa da fadin"Barka da yamma yallabai."

Ya ri'ke hannunsa a lokacin da yake amsawa da "Barka kadai Babana."

Jamilu ya kama ya'ke jin sunan da ya kira shi da shi "Babana." yayi ta nazarin sunan a cikin ransa.


Ya ce."Ba zan yi wata magana da kai ba sai ka zauna kan kujera domin girmanka ya wuce a ce ka tsuguna a gabana, ni ya dace nayi hakan amma ban yi ba.


Hujaj ya tsira masa ido jin irin maganar da yake wai shin me yake shirin faruwa ne.


Ofis din yayi shuru na minti biyu, kafin ya sake nuna masa gurin zama a karo na biyu ya ce."Ka zauna ka samu nutsuwa sai mu tattauna maganar da ta had'a mu.

Ya tashi ya zauna kan kujerar kamar yanda ya umarce shi, amma fa gabadaya jikinsa ya mutu! tunaninsa ya tsaya cak.


Sai da ya tabbatar da cewa; ya samu 'yar nutsuwa sannan ya mi'ka masa wayarsa da fad'in" Ko zaka sheda waye a jikin wannan hoton."

Hannu na rawa ya kar'bi wayar yana dubawa. hoton mijin 'yarsa ne Shahida wanda ya tafi da ita abuja.

Da sauri ya ce." Wannan ai Baban-Baba ne mijin yarinyata Shahida ina fatan ba wani abu su kayi maka ba domin dai mutumin yana da 'yar matsalar 'kwa'kwalwa."

Ya ce." Me yasa ka san yana da ta'bin hankali ka dauki 'yarka ka bashi har ya tafi uwa duniya da ita kuma baka taba bibiyarsu ba.

A sanyaye ya ce" Wallahi dole ce tasa hakan, a lokacin babu yanda zanyi ne domin ina cikin masifa, to sai ya zo da maganar yana sonta zai aureta, ni kuma nayi al'kawarin bashi auranta mutukar yayi sanadiyar fita ta daga cikin masifar da nake ciki."


Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce."Ba kowa bane wannan mutumin face ni da nake zaune a gabanka, ni ne Alhaji Saddiku Dangaske, kuma ni ne Baban-Baba mahaukacin nan dake rayuwa a 'kasan mota."


Hujaj fitsari ya kusa kwace masa a gurin, bakinsa ya shiga rawa da k'yar ya iya furta "Alhaji ya akayi hakan ta faru innalillahi wa'ina ilahi raji'un! ya k'arasa maganar da kiran sunan Allah.


Murmushi yayi kafin ya tashi a nutse ya je ya bud'e wata dirowa wata leda ya dauk'o mai d'an girma ya zo ya zauna k'asan kafet!

Hujaj tsuru! yayi kawai ya zuba masa ido a lokacin da yake sanjawa kansa hallita.


Abinda ya faru shine: Wato tunda ya kudiri aniyar neman matar aure ta wannan sigar, sai ya shirya ya nufi india dama kuma a garin shi ba 'bako bane, yana da jama'a sosai a garin wanda harkokin kasuwanci ya had'a su, akwai wani abokinsa mazaunin 'kasar babban likita ne, tare da had'in gwiwarsa komai ya tafi dai-dai, fuska akayi masa wacce tayi kamanceceniya da tasa, amma sabuwar fuskar tasa tayi tsufa sannan da kuma gemu mai tafe da furfura, akwai wasu sinadarai da yake shafawa a jikinsa gabadaya sai fatarsa ta bushe! ta yamushe ta kuma sauya kala, hatta da fartansa da tafukan hannu da kafafunsa suma sanjawa suke, amma yana zuba ruwa a jikinsa komai zai wanke

29, August 2025
Mohamed Amina Nyam

Pls I want to download

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login