Showing 1 words to 3000 words out of 101986 words
https://www.youtube.com/channel/UCMylPCg0TCgTWAmy6HHvcEQ
_*'KAUNARMU*_
_Mamuhgee_...
_*1*_
https://youtu.be/MJxY0y_SrOc
Labarin qaunarmu labarine akan soyayyar data shigi mutane biyu batareda sun ankareba duk da kasancewar banbancin dake tsakaninsu na kasancewar kowannensu nada abokin rayuwarsa Wanda suke ganin sune rayuwarsu saidai so yayi musu shigar sauri Dan kuwa tuni suka daina kallon waincan amatsayin abokan rayuwarsu.....SO NE WANDA BAIDA KATANGA YAYI MUSU SHIGAR SAURI...YAYA ZASUYI DA ABOKAN RAYUWARSU NA FARKO...
Zata sadaukar da farin cikinta dominsa,
Zai sadaukar da rayuwarsa dominta,
Zasu sadaukar da komai domin juna,
'yar uwarta wadda suka fito ciki daya,
Rana daya, awa daya saidai bambamcin mintuna biyarne a tsakanin fitowarsu duniya
'yar uwar tata zai aura Amma qaddara ta juyo da auren akanta bayan tanada nata abokin rayuwar dataiwa kanta tanada Kuma a uba suke kallonsa shikuma atasa duniyar baimasan dasuba
saidai qaddarar so ta sauya musu akalar rayuwarsu zuwa ga zazzafar qauna da bazasu iya juyowa su kalli bayansu ba bare abinda yayi sanadin auren nasu......sun shirya yaqar maqiyan soyayyarsu batareda sun tabbatarda qauna da zazzafar soyayyar dasukewa junansuba...
*_BRG MUHD SAHEEB MARSHALL MAKARFI_*
And
*_KHADIJA MUFIDA NUHU MANDE FIFI_*
*_'KAUNARMU_*
_Mamuhgee_
*_1_*
BismillahirRahmanir Raheem.
👇👇👇👇👇👇👇
https://youtu.be/MJxY0y_SrOc
HAMBURG garmany.
10:30am
Gyara zamanta tayi akan kujerar dake fuskantar ta Dr Fatima Omar yonas tareda gyara zaman glasses na idonta ta bude bakinta dake mata nauyi aduk lokacinda zatayi maganar 'yar uwarta sbd jin kunyar kanta da takaicin kanta akan yanda konyaushe 'yar uwartace ciwon ranta da damuwarta,
Duk yanda taso dauke Kai da danne alamarin ako yaushe sabo abin ke dawo mata sbd tsoron meyene zata samu agaba 'yar uwarta ta rabata dashi sbd wannan shine asalin dumuwarta da tsoronta sbd batasan mezata iya zama agaba ba itama akan hakan.
Kamar yanda tasaba kullum idan tazo gurin Dr Fatima yonas yauma farawa tayi da cewa"
Sunana AYSHAT HAMEEDA NUHU MANDE sunan Tawainiyar haihuwata KHADIJA MUFEEDA NUHU MANDE,
yan biyu mahaifiyarmu ta haifemu shekara ashirin dasuka wuce,
Mintuna biyarne kacal atsakanin haihuwar tamu,
Nice nafara fitowa duniyar kafin ita,
Nice na cancanci mafi yawan soyayya da qauna daga iyayenmu da danginmu kafin ita sbd nice nafara haskaka idanuwansu dasuka jima da jiran ganin wannan Rana dazasu rungumi nasu 'yayan suma kasancewar sun jima harsun fara manyanta babu haihuwa,
Bayan fitowata duniya iyayena sunyi farin ciki mara misali na samuwata Saidai SO da QAUNA Dana samu daga garesu na mintuna biyarne kacal sbd fitowar 'yar uwata duniya ya sauyamin komai har zuwa yanzu,
Itace sanyin idanuwansu,
Itace farin cikin gidansu da wajensu,
Saidai Allah dayafisu iko da ita bai sakota a duniyarba sai daukeda cuta ta *_RAUNIN ZUCIYA_* ma'ana _*WEAK HEART*_ _*(CARDIOMYOPATHY)*_
Wannan cuta datake daukeda ita ta qara rage kaifin qauna dake tsakanina da iyayenmu,yan uwanmu,likitocin da duniyama gabaki daya.,
Ciwon raunin zuciyarta yasa ba'a qaunar bacin ranta,baa mata fada,baa ganin laifinta,kowa qaunarta yakeyi,kowa sonta yakeyi Wanda tuni gata yayi mata yawa tako wane bangare musamman Kai tsaye mahaifiyar dadynmu ta yanke cewa asakawa 'yar uwata sunanta tanason ta gajeta
Ba 6ata lokaci taci sunan kakarmu da mahaifiyarmu wato KHADIJA MUFEEDA inda ni naci sunan Mahaifiyar mamanmu wato AYSHAT HAMEEDA.
Ta karbe soyayyar iyayenmu,
Ta karbe soyayyar kakanni da danginmu haka ta karbe sunan Mahaifiyar da rayuwarta Dan kuwa tun bayan fitowarta duniya mahaifiyarmu Bata qara lafiyaba munada shekara daya ta rasu tabarmu da dibbin kewa da maraicinta,
Anyiwa mufeeda aikin zuciya Wanda akayi cikin nasara da saa Saidai likitocin sun tabbatarda akwai yiyuwar asake mata wani aikin agaba wanda sukeda tabbacim ba lallai ta rayuba idan anyi.,
Wannan shine yaqara assasa wata sabuwar qaunarta mai tsananin qarfi a zuciyar kowa.
Muntaso cikin gata da kulawar mahaifinmu da kakarmu wadda tsufa yasa tuni Takoma gidan babbar yarta yayar dadynmu dake zaune a Lagos mukuma mahaifinmu ya daukemu muka dawo wannan qasar da zama,
Soyayya da qauna wadda mahaifinmu kewa mufeeda ta dabance wadda baa hadata da komai,
Ummy yayar mahaifinmu da hajja baza hada qaunarta da komai Dan kuwa ummy ko 'yayanta biyu maza kacal da Allah yabata Bata musu qaunar datakewa mufeeda,
Mufeeda Allah yayi mata gatanda bazance nasamu irinsaba Dan kuwa tako wane fanni Allah ya Bata duk wani Abu dakowa ke buqata,
Dukiya,
Arziki,
Gata,
Kyawu,
Kyawun jiki,
Farin jini,
Haiba,
Ilimi da wayewar rayuwa Amma Abu dayane bai horeta dashiba shine lafiya.,
Takasance lafiyarta qarantattace duk yanda takaiga holewa arayuwarta to lafiyace ke kawo mata tsaiko Dan kuwa ita mutumce mai tsananin son more rayuwa tareda abokai na wayewa dajin dadi,
Tun muna primary kowa da mufeeda yakeson qawance,
Kowa mufeeda yakeso haryanxu da muke a matsayin 'yan mata haka rayuwar take,
Nazama tamkar tsohuwa ko uwa sbd duwa da kishin 'yar uwata dake cin Raina tun ina qanqanuwata,
Ayanzu zuciyata cike takeda kishi tareda qaunar yar uwata Saidai abinda bansaniba shine tsakanin qaunarta da kishinta wanne yafi yawa cikin Raina??????
Wanne ne zai rinjayi waninsa acikin Raina Dan kuwa ayanzu nafara jin tsoron yanda tarabani da kamai na rayuwa mezata rabani dashi anan gaba????
Zan iya jurewa qaunarta ta rinjayi kishinta da jin zafinta kuwa kokuwa kishintane zai rinjayi qaunarta.????
Cikin sakin dogon numfashi Dr Fatima ta dakatar da ita ta hanyar miqa mata magani tareda glass cup na ruwa tana cewa"
It's time for break hameeda.
Jeki ki huta zamu Dora next time
Karki manta duk lokacinda kikaji zuciyarki na zafi gameda hakan Zaki iya zuwa ki sameni
I'm always here for you and always ready to listen to you okk?????
Gyada Kai tayi tareda sakin ajiyar zuciya Yana sake kurba ruwan ahankali kafin ta aje glass din tana kallon Dr Fatima ahankali ta furta"
Thank you mss yonas.
Murmushi Dr Fatima tayi tareda dafa hannunta tace"
Idan nadawo gida zanshigo
Karki Bari shedan tashiga tsakaninki da qaunar da kikewa 'yar uwarki,
Kece yakamata ace kinfi kowa qaunarta da tausayinta a duniya sbd kece twin dinta.
Gyada Kai tayi tareda miqewa tana sake cewa"
Thank you..ta dauki handbag dinta da wayarta dake kan table ta miqe ta nufi qofa ta fice.
Numfashi Dr Fatima tasauke sbd tausayin hameeda din da kishin yat uwarta yayiwa zuciyarta mugun kamu hartakai tanajin tsananin tsanaar 'yar uwarta wani lokacin wanda lura da hakan yasa tafara kulawa da mufeeda din ta hanyar sakata amayar da damuwarta kullum wanda Kuma hakan ba qaramin taimakawa mufeedan yakeba Dan tanajin sassauci idan tayi hakan Tasha mgani tana zuwa gida bacci yake sata maganin tana tashi zataji zuciyarta sakayau.
Dr Fatima Omar yonas maqwafciyarsu ce Kuma consultant ce ta bangaren tunani da karantar Dan Adam sune irin likitocin da idan Dan Adam baisan meke damunsaba idan ankaika gurinsu daga yanayin yanda kake amsa musu tambayoyinsu suke gano matsalarka.
Asalin 'yar qasar Ethiopia ce Batada miji ya dade da rasuwa yabarta da 'yaya biyu rak namiji da mace
Ameed da meena,
Ameed saurayine wanda shima Dr ne be wani jima da zama Dr dinba and ko shekara beyiba
Dan gayu me ji da kyau da gata da dukiya shima gashi dason rayuwar hutu da wayewa shiyasa aduniya Babu wadda yakeso kamar mufeeda wadda qawayenta da duk yawanci ma da FIFI MANDE,
Ameed na matuqar son Fifi itakuma amatsayin aboki Kuma Dan uwa ta daukesa sbd Dr Fatima data zamar musu tamkar uwa Dan kuwa ita kanta irin gata da qauna da Dr Fatima ke nuna mata yasa ma take kallonta tamkar mahaifiyarta haka take zuba mata shagwaba musamman idan ciwon na Fifi din yataso to tabbas kowa hankalinsa tashi yakeyi har mutanen Nigeria haka Dr Fatima zata tsaya tsayin daka a asibiti tamkar uwarta.
Meena ma Batada qawar datafi mata Fifi shiyasa kusan koyaushe suna tare musamman gurin yawon guraren shaqatawa sbd hameeda Bata shiga cikinsu.
Fifi a duniya bayan mahaifinta Babu Wanda takeso arayuwarta sama da 'yar uwarta hameeda wadda takewa kallon uwa Kuma 'yar uwa,
Qaunar datakewa hameeda qaunace irin wadda Allah ne kawai ya isa ya cire mata ita cikin ranta musamman sbd sanin ba lallai tayi doguwar rayuwa sbd ciwonta,
Tana Jim dadin rayuwarta da shaqatawartane sbd tunanin tabbas ita bamai jimawa bace a duniyar shiyasa Batada abokin fada Bata saka komai na damuwa aranta kowa natane sbd wata Rana Babu ita.
Ita mutumce mai tsananin son life musamman idan ta zauna takance idan har Allah yasa zata jima a duniya hartayi aure to Sam Babu abinda zai hanata auren miji irin ameed sbd itadai duk namijinda bai wayewaba ya iya rayuwar turawa Yana geaming ya handa muscles da abs to tabbas bazata iya aurensaba ita dai mijinta dole zai kasance kamarta Kuma wanda baifi yabata shekara uku zuwa huduba idan yabata shekaru to kardai su wuce biyar sbd me qarancin shekaru kamarta shine zai fahimci rayuwar Jin dadi yabarta suyi rayuwa yanda suke so kafin ta mutu tabarsa.
Ahankali ta bude idanuwanta dasuka Sha bacci ta miqe da sauri tareda cewa"
Oh shitt nayi latti sosai inada practical 10:00 and it's 9:40 yanxu.
Da sauri ta sauko daga kan gadon tana mayarda hular baccinta data zame gurin bacci ta nufi toilet da sauri tana adduar shiga toilet din ta fada tana cewa"
Maheeda zata kasheni da masifa wannan lattin danayi.
Sharp sharp tafito ta shirya cikin Marron Turkish gown me hadeda hula me gyale dazakayi rolling tayi rolling dinsa ta fesa turarenta na possess ta dauki Maroon channels handbag da loafers na Clark ta fito da sauri tana Kiran nurat me aikinsu akan takawo mata robar guava shake
Tana kawo mata ta karba da sauri ta bude zata saka a bakinta aka riqe robar tayi saurin juyowa taga hameeda ce tayi saurin Bata fuska tace"
Hameeda please kibarni Mana wlh nayi latti sosai fa....
Dadynsu ne yafito Yana waya idanuwansa suka sauka kan robar guava shake din sai hayaqin sanyi takeyi
Ya datse wayar Yana qarasowa gurinsu ya kalli robar yaga harda qanqara yakai hannu ya karba Yana kallon hameeda yace"
Hameeda kina kallo Zaki Bari Tasha wannan sanyin?
Kinmanta wayece itane?
Kallonsa tayi Takoma kallon Fifi din tana cewa"
Dady zan hanatane ka taho.
Kallon Fifi yayi Yasake kallon hameedar yace"
Ki ringa kiyayewa hameeda dukanmu bamason komai qanqantar ciwo yasamu mufeeda ok?
Miqa mata robar yayi Yana kallon Fifi datayi fuskar tausayi tace"
Dady nayi latti bazan iya tsayawa breakfast bafa.
Table ya nuna mata Yana cewa"
Ko exams ne mamana bazan taba barinki ki fita bakici komaiba indai I'm around.
Suna zama table din su duka hameeda datakai drink din fridge itama tazo ta zauna sai alokacin suke gaidasa ya amsa cikin kulawa Yana cewa"
Ummy takirani hajja ta sake 'dago rigimar wai sai andawo dake agabanta so takeyi taga aurenki kafin ta mutu.
Dariya tayi tareda kallon hameeda tace"
Hamee kinji nice hajja keson ganin aurena kifada mata raayina idan kunyi waya sbd dady yanzu ina kiranta ko ummy zata fara min kukan tanason ganina dady ba'a Nigeria zanyi aurebafa anan bana tunanin zan samu choice dina acan.
Murmushi yayi yace"
Mamana kifara zuwa Nigeria din tukuna zakisan choices naki duka suna can bama choice kadaiba,
And idan kina maganar life ne kije idan kinje Zaki bani labari sbd KHALID is also gonna be around.
Kallon Hameeda tayi tana dariya tace"
Hameeda ki shirya bazan iya zuwa badake ba I think it's time muje mu zauna dasu ammy right.
Chips hameeda ta tura cikin baki badan tanajin taste dinsa ba ta daga Kai tana qaqalo murmushi sbd yanda dadyn ke fira da fifin cikin tsananin kulawa sai can can yake jefota.
Cikin qarfin hali tace"
Dady 'yayan ammy shima wannan Khalid din Yana ciki???
Kallonta yayi cikin kulawa yace"
Hameeda yanzu duk bakusan 'yayan ammynku ba I tot kuna tambayarsu idan kunyi waya da ammyn.,
To dady ai bamusansu bane.
Babban danta tun kafin na auri mamanku ta haifesa MUHD SAHEEB MAKARFI yanzu baya Nigeria Amma Yana south Africa acan yake zama sai KHALID MAKARFI sukadaine yayanta so gskia yakamata kusan yan uwanku shiyasama dole ku koma gurin ummyn sbd abubuwa ma da yawa kamar wannan din.
#mamuh.
KU nunamin qaunarku ta hanyar dannamin subscribe @lafazitv👇👇👇👇
https://youtu.be/MJxY0y_SrOc
Littafin QAUNARMU na kudi ne akan naira 200 kacal.
Katura kudinka zuwa wannan account din...
2260792279
Maryam sani
Zenith Bank
Ka tura shedan biyanka ga wannan numbern
07067124863
Kokuma katura katin wayarka zuwa wannan numbern
.0903 234 5899*_ZAFAFA BIYAR NA KUDINE KA NEMI WAINNAN NUMBERS DIN KA BIYA KA KARANTA CIKIN AMINCI_*
07067124863
OR
09032345899
*2*
cigaba da cin abincin fifi tayi tana sauraran hirar su batace uffan ba da dan sauri take dan tuttura abincin tana lura da time,tana aje fork jakarta ta soma jawowa a gurguje ta mike tsaye tace dady pls can i go now?waaro idanun sa waje yay,a shagwabe tace pls,se ya rankwafo kai yana kallon ta kamar me tunanin wani abu can yace emmm not until u give ne a hug,da yar dariyar ta ta taho ta rungume sa sosai yana me sakar mata murmushi cikin tsananin nuna kulawar sa yace akula ok?tace ok bye..dad i love u..bai amsa ba wani irin kallon kauna me fallasa tsananin so yake biyota da shi.. taku dayan biyu tayi sai ta juyo kamar wanda aka tsakure ta tace,"hamee?dago kai hamida tayi ta bita da sassanyar murmushi me ciwon datake jin shi har can kasar zuciar ta.."tace natafi schl..bye..Gyada kai Hameeda tayi Bata ce uffan ba ta mayar mata da murmushi
Me dan fadi..
tun kan ta maida kallon ta kan dinninh table taga dady shima yana shirin mikewa da alaman zai bar wajen cike da mamaki tace"dady har ka koshi?yace yes dear dama na zauna ne sabida mufida ta samu ta ci abinci,u go ahead ni zanje daki..
murmushin karfin hali ta kwakwalo tace ok Nan ya wuce ya haura sama tayi jugum tana bin bayan sa da kallo
In akwai abunda yake mata ciwo bai
Wuce wannan yanayin datake shiga ciki,nobody have her time,rabon dady yay zama na musamman akan dining table domin ta ita kadai bazata iya tunawa..."oh Allah its always about fifi nikam ko oho..wani lumshe idanun tayi hade da sauke nannauyan ajiyan zuciya can ta mike tayi wicewar ta daki..
Classic bentley stance code shiya sauke ta a kofar makarantar su batare da ta maida hanklin ta kan kowa ba ta haura fifth floor inda ake gabatar da practical din sun
Ta riga da tayi lattin mintuna talatin amma dake ta saba da halin ta na creating drama so tana bude kofar ajin tayi lumui cikin sanda tace hey guys,"anan kusan duka ajin suka juyo suka kalle ta,ganib hakan ya sata ta boye fuskanta ta tana toshe bakin ta ridicoliusly.
Kawarta maheeda ce ta watsa mata harara tana mata alaman shushhhh da hannu..kwabe fuska tayi a shashance tana duban lecturer da sauran daliban da duk suka tsura mata ido tace sorry tazo ta wuce sadaf sadaf ta nemi waje ta tsaya,sauke ajiyan zucia lab co-odinator yayi yace "and that was mufida mande, now lets get back to business. ,jin haka wani dariya ne ya kufce mata inda hanklin kowa ya sake dawo kan ta tun kan malamin sun yy magana ta mike tsaye ta rike kunnen ta kamar marainiya tana cewa sorry sir..rasa abun cewa yyi yana girgiza kai ya rasa ta meyasa fifi taki sa seriousness arayuwan ta
" ya bita da hararar jan kunne yace sit down,tana xama kuwa ta fashe da dariya duk ajin suma suka dauka da dariyar.
Wani hakurin ta sake bayarwa wannan karon da kyar dai aka agama practical din nan tare da ita cikin lumana...
Khadijat mufida nuhu mande,itace dalibar data fi kowa kokari a set dinsu duk dama bata dauki duniyar nan abakin komai ba,rayuwar ta kawai takeyi bata taba tsaurara tsanani akan dukkan lamarin ta ba.
Duk abunda xai bata nishadi da jin dadin rayuwa bata wasa da shi,great sense of humourn ta wajen iya mu'amala da mutane ya sa kusan kowani dalibi a makarntar ya san da zaman ta.
"Fifi mande" shine nick name din da kowa yake kiranta da shi tun suna shekarar su na farko,sosai sunan ya zaga ko ina in baka san ta dan wani abu ba dole zaka san ta dan wani abun dan duk inda shakatawa dajin dadin rayuwa yake to ita ne akan gaba
Aguje take biyo maheeda abaya dake tafiyar ta cikin masifa tana kukkuni
Mahee..maheeda pls now,juyowa maheeda tayi a masife Tace da Allah malama dakata min
Sau nawa na kira wayar ki?
Tace sau takwas..
Wani angry face maheeda ta sa tace and?...
matsowa kusa da ita tayi ta kama cheeks din ta tana mata murmushi tace and dady ne ya jawo komai wallahy...kinsan wani abu mahee?
Maheeda dake mugun son jin gulma tace what?..yatsinawa fifi tayi cikin iya zolaya tace nothing..in kina son ji ki biyo ni cike da takun ta na rigima ta wice gaba maheeda taja tsuka ta shiga biyo bayan ta..
Hadadden student cofee stall ta nufa nan take tayi odering kofuna biyu na shayin dayafi kowanne jin kayan hadi da dadi da tsada..
suna sha suna yar hirar su ahaka basa yin minti 10 batare da wani ko wata ta katse su da gaisuwa ba
dake mufida kusan favourite din kowa ne a makarantar so duk inda ta xauna sekaga mutane suna son mata magana in one way or the other,wani ajiyayyan numfashi ta saki tace wa maheeda gurl friend saura kwana nawa mugama karatun nan ma?Mahee ta yatsina idanun ta ta zuki shayin ta da alaman rashin kulawa,can tace 1 month i ques,wai meye ne zaki fada min kinsan na matsu inji kike ja min rai?..,dariya fifi tayi tace calm down dama nasan matsalar ki ai sarauniyar son jin gulma ..mahee tace whateva nan mufida ta matso kusa kamar me neman mata yar tsegumi tace ke maheeda ki shirya wannan karon ina so muyi abun da babu wanda ya taba yi a ranar graduation dinsa
Maheeda Tace kamar yay fa?
Tace i mean party ina son in hada babban get togher da ni da dukan abokai na amma kafin nan ina son muje yawon
Shakatawa ina son sauran ragowar college time dina ya zamto wanda bazan taba mancewa da shi arayuwata ba
..Maheee ta ce ehem?karatun fa?tace ohhh mance da wannan zamuyi catch up,.mahee dagaske nake miki
I want to go wild maheeda tace ure alwys wild,tayi kwafa ta maida bayan ta kan kujeran cikin dauke numfashi tace wannan karon ina nufin"wildest"..
Mahee tace hmmm to me kike shirya mana ne haka? shiru tayi sanda ta karashe shanye shayin ta tas sannan tace alot. Starting from today?..maheeda ta dan dube ta tace and hamida?
Tace oho wallhy bansan ko zata amince ba amma zan tabo ta inji,tace i hope she did nan suka gama yar hirarrakin su suka watse kowa ta nufi gida
Kafin satin ya kare ita da kawarta maheeda da meena yar gidan dr fatima yonas datake daukar ta kamar yar uwan ta da duk sauran gang na friends din ta suka taru suka harhada
Nau'i nau'i na shirye shiryen yadda zasu more rayuwar su a cikin wayannan kwanaki.
Ameed dake shi doctor ne so bai ciika samun lokacin kansa ba amma da shike yana matukar kaunar fifi hakan ya kukkusa ya