Showing 27001 words to 30000 words out of 101986 words
da shekarun sa,toh ana haka ne wata tarzomar ta kuma tasowa a ƙasar south africa inda a nan ne kuma ya ƙara samin ɗaukakar fiye da na farin,toh kuma tun daga wannan sai suka buƙaci da ya cigaba da zama a can dan ƙasar na fuskantar barazana ta maƙiya kusan akai akai,zaman yayan ku a ƙasar ya sauƙaƙa yawa yawan faɗace faɗacen da ake samu akai akai dan sun haɗa kai da sojojin ƙasar ta yadda da zarar an sami ɓaraka ko ana gab da samu toh zasu baza battalions ɗin su nan kuma za a fito da nasara"!!kuma jan fasali Hajja tayi Hamida na sauraron ta kamar tana sauraron wa'azi..
"A shekarar da suka fito da wata nasara ce Allah ya nufa suka haɗu da matar sa Muhibbah wacce itama aiki ne ya kai ta can ɗin dan businesses ɗin mahaifin ta ya kasance mai faɗi ne ƙasashe daban daban take zuwa yin sa, a wannan karon sai suka haɗu suka saba,toh mu a nan gida dama a matse muke da yayi auren dan ya fara manyanta amma bai maida hankalin sa a nan sai da ya haɗu da ita ɗin ne sannan ya kawo maganar,ba a ɗau lokaci ba aka yi auren zaman su a nan wata guda suka tattara suka koma south africa da zama,bayan shekara ɗaya kuma sai ya kawo mana ziyara duk muka ga kamar ba shi ba,yin duniyar nan mun yi ya fayyace mana matsalar sa amma ya ƙi,ko da muka tuntuɓe sa da maganar inda matar take sai ya ce ai tana ƙasar Los Angeles wai tana kula da businesses ɗin mahaifin ta da ya rasu ya bar mata.a wannan lokacin hankali na ya gama tashi nayi tunanin samin mahaifiyar ta dan mu zauna a warware matsalar amma haka Saheeb ya hana ni ya ce min shi bai da matsala da wannan haka na ƙyale ba dan ina so ba"..
"Bayan ya koma da shekaru biyu ya kuma dawowa shi kaɗai nan ma da aka yi tambayar duk ɗaya ce,tana wata ƙasar tana kula da businesses ɗin mahaifin ta,a lokacin na san Saheeb bai yi dacen macen aure ba dan bata da niyar zama da shi bare ta haihu,daga ni har Ammyn ku duk mun matsu mu ga jinin sa a duniyar nan amma shi a wurin sa ba haka bane,a lokacin na ɗaga hankali na akan zancen ina ta nemar haɗa sa da jikokin aminai na amma haka zai ce duk basu mai ba shi hasalima bai da matsalar komai da matar sa akan me zai kuma yin wani auren,a ƙarshe dai komawa can south africa yayi kuma tun daga wannan komawar ne bai sake dawowa ba kusan shekaru shida da rabi kenan kullum sai dai a yi magana da shi ta waya in muka matsu da son ganin sa sai dai ta video call abin na damu na yana damu na a zuciya ta,yana jika na amma ya nesanta da ni ga mahaifiyar sa ya tsallake ta ya gwammaci zaman wata ƙasar duk dan baya so a ba matar sa laifi"..
"A ranar da mahaifin ku ya sanar da ni kun cika shekaru goma sha tara a duniya a ranar ne na saka sa gaba akan ya turo ku ku dawo tunda shi ɗin bai da niyar dawowa dan tun bayan rasuwar mahaifiyar ku shima ya ƙi yarda a mai maganar aure ya zaɓi zaman can germany akan nan,tun lokacin nake damin sa akai akai dan na san ba za a rasa wacce za a haɗa ta da Saheeb ba amma ya min nuni da cewa ai karatu kuke yi sai dai kuna gab da kammalawa kuma da zarar kun kammala zaku taho"..
"Kasancewar takwara ta ta fi yawan magana da ni ya sa na rinƙa damin ta da ta dawo gida,ku dawo gida kar ku gama yin girman ku a ƙasar da ba taku ba,toh alhamdulillah kun kammala karatun naku kun dawo gida Allah ya tsara maku mabambantan rayuwa ita Mufida ta dace da Khalid ke kuma muka maki sha'awar Saheeb sbd ɗabi'un ku kusan ɗaya,ke tamu ce muna da iko akan ki ba kamar matar sa ba da ikon da muke da shi a kan ta ƙalilan ne"!!..
"Dan haka muka ga dacewar ku kuma mun san kema a yanzu da kika ji labarin sa kika san ko shi ɗin waye zaki ga hangen da muka yi kuma ba zaki taɓa yin nadamar zaɓin mu ba"..
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Hamida ta sauke bayan ta gama sauraton Hajja,ajiyar zuciyar na ɗauke ne da abubuwa masu wuyar fassaruwa amma dai ta barwa kan ta duk da zuciyar ta na mata zafi ganin irin mizanin da aka ɗora nata martabar akai,ƙasƙancin sa ya ɗare abin misali..
Wani baƙin cikin ta haɗiya sannan ta saka murmushin da ya fi kuka zafi da ciwo tana faɗin.
"InshaAllah zaku same ni mai bin umarnin nan naku da amana da gaskiya Hajja"!!.wani sanyi Ammy ta ji a zuciyar ta har ta fidda ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya haɗe da tashi cikin sauri ta rungumo Hamida jikin ta..
Abin mamaki yanzu dan na yarda da auren nan ne ya sa Ammy ta rungume ni haka?abin da tun da muka iso ƙasar nan bata taɓa yunƙurin yi min ba akasin fifi da ba zata iya ƙirga yawan hugs ɗin da ta samu daga wurin Ammy ba,oh ita Aysha yanzu wai ba dan ta cancanci hug ɗin ba aka bata shi ba sai dan ta yarda da zaɓin su..
Hawaye ne ya sauko mata daga idanun ta tayi saurin gogewa tana jan hancin ta sai muryar Ammy ta ji tana ta yi mata addu'a haɗe da bata tabbacin ba zata taɓa nadamar wannan haɗin da zasu mata ba.
Jin Ammyn kawai take ta yi har ta gama ta kuma jaddada mata ta tabbatar ta tafi inda ake ma fifi gyaran jiki dan itama a mata..
Gyaɗa kai kawai tayi ta sallame su suka rinƙa saka mata albarka tana jin su ita dai tayi gaba..
Tana hanya tana ta nazarin kalamomin su har ta zo ta wuce apartment ɗin da ake wa fifi gyara sai kuma ta dawo tayi peeping ta hango ta tana ta danna waya tana murmushi..
Komawa da baya tayi ta nufi nata ɗakin ta kwanta dan zuciyar ta bai mata daɗi,kasa baccin tayi sai ta tashi ta ɗau maganin ta ta zazzago guda biyu ta nemo bottle water ta haɗiye maganin..
Bata jima ba bacci ya sace ta bata farka ba sai 7pm kasancewar bata sallah sai ta sauko zuwa ƙasa dan a yi dinner da ita inda a nan fifi ta rinƙa mitar Hamida ta manta da ita yanzu sai dai su haɗu a wurin cin abinci in ta zo kenan bayan haka basu haɗuwa kuma ita a hana ta fita a apartment ɗin sai dai in ya zama dole..
Nan ma duk jin ta Hamida ke yi kowa ya kwaso blame ɗin sa kan ta ake sauke sa ba komai in yanzu sun mata wataran ba zasu yi ba..
A haka aka cigaba da shirin bikin su Hamida da fifi wanda tun a washegari Hamida tayi joining fifi aka cigaba da yi masu gyaran jikin sai dai bata tsira ba still akan nuna bambancin dan bayan an gama sai Ammy ta kira fifi separately ko me suke girkawa Allah ne masani ita dai ta san babu wani ƙaunar Mufida a zuciyar ta ko na ɗigo ne but su sun kasa ganewa,bambancin da suke nuna mata bai haddasa komai sai ƙiyayyar masoyiyar tasu wato Mufida...
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*13*
Ana saura kwanaki biyar da bikin su fifi sai shaƙuwar su da Hamida ya ninku ya fi da duk da ita Mufida ta fi alaƙanta shaƙuwar tasu da yanayin bambancin rayuwar auren da zasu fuskanta,duk dama ta san cewa gida ɗaya zasu zauna amma apartment ɗin kowa daban ba lallai bane su rinƙa haɗuwa kullum ba in an gama bikin..
Lokaci zuwa lokaci sukan zauna zama ta musamman tsakanin su su zanta mafi yawan hirar tasu takan karkata ne a ɓangaren kewar junan su da zasu yi bayan bikin,though sau da yawa hirar ta su takan ƙare ne da faɗa wanda fifi ce mai yawan janyo sa dan takan so ƙure Hamida akan zaɓen mijin ta ita kuma Hamida bata ba fifi hankalinta ɗin ta iyakar in an gama masu gyaran jikin sai ta tashi tayi gaba abin ta ƙarshe Mufidar ce ke zuwa ɗakin Hamida ta bata haƙuri sai su shirya hakan bai hana washegari in sun kuma haɗuwa ta ƙara tsokanar ta ba sai dai Hamidar da girgiza kai ta ce mata Allah ya shirye ki fifi..
A yau ne suke saka ran zuwan daddyn su dan kusan one week ago suke ta waya da shi ya sanar da su zai zo inshaAllah cikin kwanakin nan..
Tun safe suka kasa sukuni musamman fifi da ta fi zumuɗin ganin daddyn nasu dan dama tayi kewar sa fiye da tunani..
Har kasa natsuwa tayi saboda zumuɗi sai da Khalid ya ja hankalin ta da hira sannan ta sami natsuwa shima ya tafi ɗauko daddyn..
A cikin gida kuwa har girke girken da aka yi fifi na a ciki dan sosai ta ce tanaso daddyn ta yayi tasting abin da ta girka da kan ta..
A lokacin da daddyn su ya iso gida tare da Khalid haka fifi ta kanainaye sa ta ki barin sa ya sha iska tana ta yi mai surutai akan yadda tayi kewar sa,hakama su Ammy da Hajja da suka matsu da ganin sa sai dariya suke ta yiwa fifi akan yanzu kenan da take da ƴancin ganawa da daddyn nata take mai haka ina ga in ta yi aure kuma ita da mijin and da zarar sun tsokane ta da haka sai ta saka kukan shagwaɓa tana kallon Khalid da kwana biyun nan sam tadena gane masa
Sau dayawa ta rinƙa tambayar sa ai ba zai bari ta rabu da daddyn ta ba ko? shi kuma da dariyar sa zai amsa ta yana ce mata ai babu mai raba ta da daddy da su Ammy..
Azuciyarta tana dannewa ne kawai amma Halaye khalid gaba daya ya sauya mata in ya amsa ta se tanajin kamar ba shiba
Sai da aka ci abinci aka natsu sannan aka dawo parlor domin cigaba da hirar da aka faro tun akan dinning,sam Hamida takasa sakin jiki tayi da su sai ta nemo excuse ɗin da ta san zai bada babbar muhimmanci ta gudu zuwa ɗakin ta ta kwanta sabida duk yadda kwanakin bikin na ƙaratowa the more fargabar ta na ninkuwa..
Kusan raba dare suka yi suna hirar su duk kuma saboda fifi ne dan ta ce wannan shi ne best moment ɗin rayuwar ta da ba zata yarda ya tafi haka nan ba sabida ita dai tun tasowar ta daga ita sai daddyn su sai Hamida suke rayuwa a cikin gidan banda ma'aikata,a yau da suka haɗu duka with exception of saheeb wato mijin ƴar uwar ta da ita kan ta ƴar uwar nata sai ta ga wannan kamar dama ne babba da zata yi amfani da shi dan barin memories ɗin ta a zukatan ahalin nata...
Wasa da dariya anata hira Sai kusan 11pm fifi ta raka daddyn su masaukin sa inda nan ma ta rinƙa labarta mai abubuwan da Khalid ke mata tun zuwan su da irin kula ta musamman da yake bata tun zuwan su,shi kam daddy bai da abin cewa sama da yiwa Allah godiya dan ya kawo mai saka ɗiyar sa farinciki a rayuwar ta ba kuma zuwa kaɗai yayi ba tsayawa ma zai yi na har abada..
Da ta dawo ɗakin ta kuwa sabon babin hira taso ta buɗe ta musamman ita da angon nata Khalid dan kiran da ta mai ya kai sau uku bai dauka ba,can yazo yadauka bata gane masa ba in sun yi good night sai ta sake kiran sa a haka dai har aka yi final good night duk suka kwanta bacci..
A washegari suka haɗu a ɗakin Ammy ta saka su gwada ɗinkunan su na bikin har ma da na events ɗin da za a yi,duk babu wacce kayan nan bai yiwa kyau ba dan dirin jiki da kyan halitta Allah ya hore masu shi..
Ita fifi da ta gwada na ƙarshen ƙin cirewa tayi ta bar shi a jikin ta sai da aka shigo ɗakin da sallama ta ɗago kai ta ga Khalid ne nan take ta fara nemar abin da zata rufe jikin ta da shi da alamr bata so ya ga kayan dan in ya gani toh ba wani birge sa da take son yi da zata yi a ranar event ɗin kayan..
Dariya Ammy ta mata itama Hamida ta ɗan dara tana mata gwalon Allah ya kara wai angon ta ya ga kwalliyar ta tun kafin ranar bikin,abin sai ya ba fifi haushi amma da yake bayan ya shigo Ammy ta kora sa waje dan kar ya ga kayan fifin sai ta ji sauƙin abin bata saka tsokanar ƴar uwar nata a ka ba...
****
Da safe yau ma family breakfast aka yi dan an san daga yau ɗin ba lallai bane a kuma haɗuwa on special breakfast haka ba sai dai in bayan biki..
Ana cin abinci ana hirar yaushe rabo Hamida dai bata yi gigin saka masu baki a hirar tasu ba dan ta san ko ta saka toh ba wani ƙwarjinin da zata yi duk hankali na ga fifi..
Suna gama breakfast ɗin tayi gaba abin ta sai dai a yau Hajja ta yi magana akan ƙyaliyar Hamida na damin ta,toh ana ta fifi sai kawai aka ce hala yanayin fargabar ta kenan ita tunda ko wacce amarya na da nata sigar fargabar in bikin ta ya zo toh maybe nata a haka ya zo na son kaɗaicewa ita kaɗai..
Bayan an gama hirar fifi ta tafi ɗakin Hamida wacce ke kishingiɗe tana danna wayar ta da hannu ɗaya babu wani sutura a jikin ta sai ƙaramar armless top marar kauri ƙafar ta tayi crossing ɗaya kan ɗaya,hakan ya bada damar viewing elegant well groomed skin ɗin ta da ya sha gyara yana ta ƙyalli da walwal..jin fifi abayan ta ya sa ta boye abunda takeyi a wayar tana me cusawa a kasan fillow
Ƙare mata kallo fifi tayi sannan ta ƙaraso ciki tana murmushi ta zauna kusa da Hamidar ta taɓa ta..
Kallon ta Hamida tayi sannan ta tashi ta zauna sai fifi ta kuma kallon ta har abin ya saka Hamida tsarguwa sai ta nemo outer top ɗin rigar ta saka tana kallon Mufidar haɗe da tambayar ta ko lafiya da irin wannan kallon..
Murmushi kawai fifi ta mata sannan ta fara magana cikin gaskiya da gaskiya..
"Hamee ni kin san me ke dami na ne,wallahi ba komai ke dami na ba sai ganin irin wannan gyarar da aka maki kika fito tas da ke amma wai a ce wannan tsohon ne zai ga gyaran abin na taɓa min zuciya ƴar uwa ta,ban da yadda zan yi ne da na taimaka maki,ba ƙaramin tausaya maki nake yi ba,duk yanayin ki ina ankare da su kawai ƙyalewa nake yi dan na ga kamar kin fi buƙatar ki zauna ke kaɗai ne dan ki jajanta rayuwar da zaki shiga ciki,wannan dalili ya sa nake barin ki ki bar mu ko da hira ake yi sai dai a yau na ga damuwar taki har ta ɗare na kullum shi ya sa na biyo ki,shin Hamida akwai wata matsalar dake damin ki ne a zuciyar ki da baki son sanar da kowa"?.
Kallon ta Hamida ke yi cikin wani yanayi me wuyar fassara da sa tsoro wanda babu alaman shi akan fuskan ta sai a ziciyarta
har fifi ta gama maganar ta sai ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana girgiza kan ta cikin halin ni ban da wani damuwa..
Hakan bai gamsar da fifi ba sai da ta kuma nanata mata tambayar a wannan karon sai Hamida ta yi magana da bakin ta bayan riƙo hannuwan fifi da tayi cikin nata.
Tace"Fifi na kar ki damu kan ki akan matsalar da bata nan,ni ban da matsalar komai dan dai kawai a ƴan kwanakin nan nakan yi tunanin irin kewar ki da zan yi bayan bikin nan dole dama wataran duk shaƙuwar mu dole mu rabu in ba mutuwa akwai aure kuma auren babu inda baya kai mutum hala mu rabu wata rana,alaƙar dake tsakanin mu ba ta fuska bace kaɗai,Mufida alaƙar mu ta jini ce wacce ko bayan rabuwar mu in an yi bikin nan wannan alaƙar tamu ta jini ita zata cigaba da ƙarfafa _Ƙaunarmu_ dan haka ƴar uwa ta kar ki damu advantage ɗin auren mazajen namu kenan,gida ɗaya zamu zauna kuma in muka so a rana sai mu haɗu fiye da ɗaya,so calm down my dear auren nan ba zai raba mu ba ok"?ta ida maganar tana ɗage girar ta..
Gyaɗa kai fifi tayi dan duk abin da Hamida ta faɗa mata a yanzu gaskiya ne babu ƙarya cikin ta..
Rungume junan su suka yi Mufida ƴar shagwaɓa sai kuka take ta yi ita kuma Hamida na rarrashin ta dan ita danne nata hawayen tayi...
Sai da suka natsa suka ɗan yi hira Hamida na kuma jaddada mata kar fa ta ɗaga hankalin ta akan behaviours ɗin ta ba komai bane kawai kewar ta da zata yi ne da na su daddyn su,da hakan fifi ta sami relief ta saka a ran ta in ma an gama bikin ba zata yarda su gudu zuwa honeymoon ɗin ba har sai sun jima sbd ƴar uwar ta kar ta yi zaman kaɗaici...
****
Yau ce ranar da za a yi family get together inda a cikin gidan farfajiyar gidan aka taru aka gabatar