Showing 12001 words to 15000 words out of 101986 words
dazu ta damu tana ta duba lokaci tana leko window sabida bata ji muryar kowa cikin yan gidan ba,.
alama ne na cewa yar lelen tasu bata nan dan haka annurin gidan ma dole ya dauke na dan wucin gadi..
Tana kawo kan ta kuwa ta hango Khalid na bude ma fifi mota har fito tana mai dariya hannun sa ya saka a motar yana kwaso tsarabar outing din da suka futo..
Sosai hamida take ganin cikakken view din na duk abunda dake faruwa a nan farfajiyar gidan sakamakon hasken kwayayen lantarkin da ya dallare gidan ya haska ko ina..
Tsaye take tana kallon su wayar dake hannun ta ta dada damkewa dan saura kiris ya fado daga sama zuwa kasa kasa rike hawayen ta tayi kawai ta bar su suka rinka fitowa,babu murya bare wani reaction da tayi,wannan tsantsar hawayen bakin ciki da takaici ne ke bin fuskar ta wanda ya samo asali ne daga ciki cikin zuciyar ta..
Kasa cigaba tayi da kallon nasu kawai ta koma ciki hade da buga kofar window din wanda su kuma daga kasan suka ji karar bugun dan da karfi tayi kuma dama windown asalin metal ne mai kyaun gani da tsada..
A hanzarce duka suka dago kai suka dubi windown wanda babu alaman kowa,Kallon junan su suka yi suna mamakin wa zai aikata hakan?amma da yake abin dake gaban su ya fi karfin wannan yar hayaniyar sai suka cigaba da hirar su kamar ba gida daya zasu kwana su tashi ba..
"...Sai da aka fara kiran sallar isha'i sannan suka karasa ciki inda suka tarar da abinci shake saman dinning table alamar ba a ma ci abincin ba dan komai a shirye yake neat babu kowa,aranta tace kenan sun shiga yin sallar isha'i .
Murmushi tayi tana mai karbar wasu daga cikin kayayyakin nata shi kuma yana rike da wasu,haka ya raka ta har dakin ta ya ajiye mata kayan yana mai nuna mata kar tayi lattin fitowa dinner ta amsa ta hanyar gyada mai kai...
Bayan fitar sa ne ta sakawa kofar lock tawani daka tsalle da dariya dan yau is one of the best day da zata iya kirgawa na sakawa har cikin tarihin rayuwar ta
"kusan duk abubuwan da take bukatar sani a rayuwar Khalid din nata yau ta san kaso tamanin kuma ta san da sannu zata gama sanin sauran halayyar sa..
A tunanin ta da nazarin ta gaba kadan ita da Khalid din zasu yi sabon da ba a yi zato ba dan hallayar su kusan iri daya ne yadda take son morewa ta ji dadin rayuwa haka shima yake,ire iren suturun da take sha'awar sakawa shima haka ne..
Bata san ina zata saka kan ta dan tsananin farinciki da annashuwar da Khalid din ya saka ta ciki yau ba,mannewa tayi da jikin wardrobe din ta tana ta yiwa kan ta murmushi tana kara tuno awannin da suka gabata kafin yanzu..
Jin ana sallame salla ya sa tayi wuf ta shige toilet dan yin alwala dan dama ko magrib bata yi ba ga isha'i tayi har an idar...
Sai da tayi wanka ta kimtsa kan ta tayi sallolin nan ta fito ta nufi hanyar sashen yar uwar ta hamida dan ganin ya lafiyar ta yake dan a dazu da suka fita rabin hankalin ta na ga tunanin yar uwar tawainiyar ta
ganin yadda duk ta bi ta kasa sake jikin ta kamar ba cikin family din ta take ba abun na matukar damun fifi..
"....Tsayuwar ta da sallamar ta a bakin kofar dakin Hamida ya kai kusan mintuna biyar tana ta sallama da dan bubbuga kofar dakin amma ba a bude ba kuma ba wai dan ba a ji bane a'a kawai jin budewar ne kawai mai dakin bata jin yi..
Har fifi tagaji ta dubo number din Hamidar da zumar kiran ta aganin ta ko bacci take yi amma in ta ji karar wayar kila ta farka,sai kuma ta ga wani kiran ya shigo wayar ta,duba numbern tayi ta ga daddyn su ne dan haka cikin sauri ta daga kiran kuma a dai dai wannan lokacin ne aka bude kofar..
Ta karasa shiga dakin ne wayar na sagale a kunnen ta tana gaida daddyn nasu cikin shagwaba.
Ita dai Hamida tun da ta bude mata kofar ta koma ta zauna bisa sofa dake dakin bata kuma dago kan ta ta kalli Mufidar ba dan ta san wanda take wayar da shi ba kowa bane face daddyn su wanda ita ko digon missed call din sa bata sami arzikin samu ba..
Dadin mamakin Hamida shine lokacin da ta ji fifi tana cewa"Daddy ai gashi yanzu na daga kiran,dazu ma da ka kira muna tare ne da Khalid ya kai ni zagayan gari kuma ma ai daddy tun bayan saukowar mu in ban manta ba maganar mu da juna sau takwas fa ka kirani kenan and i have been ok tun dazu har yanz kadena damuwa kaji daddyna am fine wallhy...,ko ka manta tare da Ammy da Hajja da Khalid nake?duk fah cikin family nake sannan ga yar uwa ta abin alfahari na Hamida"
..dan shiru ne ya biyo bayan maganar da fifi tayi..
Hamida kan ta a kasa tana auna irin tsabar kiyayyar da ake mata a cikin ahalin ta kamar ba zama tare suka yi da Mufidar cikin cikin mahaifiyar su sannan aka haifo tare har suke rayuwa yau atare ba,ita ce ta zamo bare da ba a san tana raye ba?ko dai ta mace ne da har ba'a lura ba,8 calls daddyn su ya ma fifi ita tana nan tana ta jiran ganin kiran sa sau daya bai kira ba
even after seeing her 3 missed calls bai bi kiran ba sai fifi da ya kira ta har sau takwas..abun yanacin mata rai matuka
Waya ta ji a kunnen ta kuma shine ya ankarar da ita cewa a take muryar daddyn su ta ji yana ce mata
"Hamida ta yaya kuke?kina lura da yar uwanki kuwa? na ga kiran ki har uku amma bana kusa kuma da na dawo na gani sai nayi tunanin tare kuke da yar uwar ki dan haka na kira ta in ya so ita sai ta baki mu gaisa kawai,hamida tace hmmm.yace da fatar kema kina jin dadin gidan su Ammyn naku?murmushi mai ciwo tayi jin wai ashe ya ga missed calls din nata ma, amma bai biyo ta ba sai ya kira wacce ta fiye mai soyuwa a zuciyar sa sannan sai yanzu ne zaina tambayar ta akan jin dadin zaman gidan wanda in da zata sami dama da mutumin da ya cancanta toh da zata samar da shi irin rayuwar da ta fara ginawa a yan awannin da ta tsinci kan ta a ciki a cikin gidan da take ganin tana iya bugun kirji tayi alfahari da shi..
"Daddy komai alhamdulillah"iya kalmar da ya iya fitowa daga bakin ta kenan sai tayi shiru,ko me ya kuma ce mata sai ta mikowa fifi wayar tana tashi daga wurin dan bata muradin jin cigaban hirar tasu..
Sai da ta tabbatar sun gama sannan ta fito da fake face ta fuskanci fifin tana fadin
"So,ya outing din naku ya kasance"?ita kadai ta san karfin halin da tayi kafin tayi tambayar nan,tunanin ta kamar kullum fifi zata hau zayyano mata komai da ya faru ne dalla dalla sai dai yau ta ga akasin hakan
Dan fifi yi tayi kamar bata ji tambayar ba ita ta aiko mata da nata tambayar..
"Hameda meye ne wai ni kam, me ke faruwa da ke ne tun zuwar mu kasar nan?duk yanayin ki ya sauya kamar baki ji dadin tahowar mu ko dan nan kasar batamu bane ko?duk fah fara'ar ki ta dauke baki walwala hamida, baki sakin jikin ki dani na rasa gane maki Hamee
Please dan Allah ki sanar da ni damuwar ki kin ga duk duniyar nan baki da wata wacce zaki iya bayyanawa damuwar ki sama da ni,hamida ta a tare muka taho duniya, duk da ni din ba mai cikakkiyar lafiya ba ce kuma ina iya barin duniyar ma ako wani lokaci,
toh in baki fada min damuwar ki ba ta yaya kike so in taya ki saka farinciki a rayuwar ki, da fuskar ki wanda ba zaki taba mantawa da shi ba ko bayan na bar duniyar uhum?..fifi kamar zata yi kuka haka ta karasa maganar..
Kallon ta Hamida tayi tana jin maganganun yar uwar nata tsanake har yana son yin tasiri a zuciyar ta dan ta san bayan matsalar ciwon nan dake damin ta,inba don aan ware ta ba to da rayuwar su ba a haka zai ginu ba
dan sarai ta san Mufida bata da son kai bata da kyashi,amma wasu lokutan abubuwan dake faruwan be sai take ganin kamar fifin na da son kan ta da yawa wajen janye komai da kowa..
Matsowa fifi tayi ta riko hannuwar ta biyu cikin nata tana kallon cikin idanun ta hade da kuma yi mata tambayar
"Ko dai nan dakin bai maki bane mu yi musayar daki ke ki koma wancan nawa ni in dawo nan"?
kallon ta Hamida ta cigaba da yi kafin ta cire hannun ta cikin na Mufida ta mike tsaye tana fadin
"A'a fifi na,ko daya cikin tambayoyin ki babu wanda ke dami na,yanzu ki zo mu je mu ci abinci dan kin ga sai da daddy ya kuma min gargadin kar in rinka barin ki da yunwa in kular masa da ke,so mis Khadijah Mufida Mande can we go for our dinner now"?
sunan da ta kira ta da shi ne ya saka ta murmusawa dan da sigar tsokana ta fadi sunan..
Fifi Tana son sanar da mufida sirrin zuciyar ta game da Khalid amma sai ta ga kamar lokaci baiyi ba,gani take zai fi in ta bari abin ya kara karfi sai ta fadawa yar uwar nata...
Tare suka fito suna dan hira kadan kadan har suka karaso main parlor suka nufi dinning table..
Hajja ce ta fara ankara da Hamida sai ta dafe kai cikin jimami tana fadin
"Hamida kina gidan nan amma aka yi ta sha'ani amma baki fito an yi da ke ba kuma baki aiko kowa ya kawo maki abincin rana ba?ni dai bani son irin wannan dabi'ar taki da kika dauko ta turawa a ce mutum na cikin ahalin sa amma yana jan jiki da su kamar ba shine nasu ba"?kasa karasa zaman Hamida tayi ta tsaya a tsaye tana kallon Hajja har ta gama maganar ta sannan Ammy ta dora nata..
"Hajja ni wallahi mantawa nayi da ita da na aika mata da nata dazu, kin san sam yaran nan na zamani ba cika son takurawa rayuwar su suke son ana yi ba kin ga bai dace ana yawan shiga harkar su ba"!
kamewa Hamida tayi a tsaye tana nazarin zantukar nasu,da kamar ta juya ta koma amma sai ta ji hannun fifi a kan hannun ta da ta saka ta janyo kujera da niyar zama amma ta kasa...
Kallon ta tayi sai ta ga ita murmushi ma take yi dan haka sai ta fasa komawar kawai ta zauna ba tare da ta ce kala ma maganganun su ba..
Serving din su abincin Ammy tayi suka zazzauna har sun fara ci sannan Khalid ya zo shima yayi joining din su saidai duk hankalin sa akan fifi ita kdai yake,bayan ita kuma Hamida hankalin ta akan shi yake tana mai ambaton kaunar sa a ran ta..
Abubuwa kala kala sun faru a gun cin abincin sai dai duk ba a sako Hamida ciki ba sai ita fifi,dannewa Hamida ta rinka yi har aka kammala cin abincin ta mike tana masu sai da safe,bata jira amsar su ba tayi gaba dan ta san kara mata damuwa zasu yi..
Ammy ce ta bi ta da kallo kamar ta so dago wani abu game da hamida karar da fifi ta saki ne ya sa tayi saurin maida hankalin ta ga tana tambayar ta lafiya..
Ashe spoon Khalid ya saka cikin abincin ta ya dauke mata last sliced of cucumber din dake cikin abincin shine ta sake kara dan har ya kai baki zai saka..
Fada Ammy ta mai akan yana babba amma madadin ya faranta mata a matsayin ta na kanwar sa shine yake kuma tsokanarta...
Hajja kuwa ta kasa hakura da dabi'ar Hamida dan tayi ma abun bahaguwar fahimta gani take hamida miskila ce marar saurin sabo..
Tace "Wannan yarinya dai dabi'ar ta daban take,ana zaune ana hira amma ta tashi ta wuce ciki anya bata da wata damuwa kuwa?karasa tambayar tayi tana kallon Ammy..
Dage kafada Ammyn tayi alamar oho bata sani ba,daga haka suka maida hankalin su ga shirmen Mufida da Khalid har suna tambayar ta ina take son zuwa gobe dan bude ido..
Kasancewar bata san ko ina ba sai Khalid ya rinka zayyano mata wuraren bude ido da daukar hankali,daga nan ta rinka zabar inda zata kai ziyarar a washegarin..
A haka dai suka karasa hirar ta sallame su akan zata koma ta kwanta dan kan ta ya fara ciwo,ai jin kalmar ciwon nan ya sa suka daga hankulan su har abin ya ba fifi tausayi dan ta san duk son da suke mata da kaunar da suke mata dole watan wata rana haka zata mutu ta bar masu duniyar..
Rungume su tayi tana furta masu kalaman so da kauna hade da godiyar kulawar su akan ta,sannan ta wuce su suma suka wuce zuwa makwamcin su..
Anan ma Bata tafi dakin direct ba sai da ta fara duba dkin Hamida ta zauna tare da ita ta rinka jan ta da hira mai ban dariya sannan ta bata sassanyar runguma dacewa kar ta manta in tana da damuwa ko tana jin tana bukatar shawara kar tayi kasa a gwiwa wurin sanar da ita ita kuma ta mata alkawarin bata dukkan lokacin ta da hankalin ta dan ganin ta taya ta magance damuwar ta..
Da haka suka rabu Hamida na ta nazarin kalaman yar uwar nata,taji dama dama sosai kamar dai ta dauka tayi amfani da shi,can sai kuma ta fasa dan karfin kiyayyar da take ma yar uwar nata kamar ya fara rinjayar karfin soyayyar da take mata..
kuma ko ba dan haka ba tasan ita ba zata taba zuba ido ta rasa Khalid ba,tace makanta enough is enough fifi,fifi,fifi,kowa fifi toh abin ya isa haka
Anan ko da ace mutum daya ne zai saurare ta tasaka aranta Khalid ne.
Da Hakan zai fiye mata kallon su da saurarar irin kalar son da suke ma Mufida..
A fannin fifi kuwa kasa runtsawa tayi har sai da ta karema hotunan da suka yi tare da Khalid kallo,ta kalli hotunan nan sun fi a kirga sannan daga bisani ta kashe bed side lamp din dakin ta runtse idanun ta tana me sa kan ta baccin dole dan ba baccin take ji ba ta fi jin kamar begen Khalid ne ya fi dacewa da ta yi a daren ba bacci ba shi ya sa ta runtse idanun dan dole koda bacci zai sace ta in ya so ko a mafarki ne ta lazumci begen sa..
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*8*
Da sassafe Hamida ta tashi ta bar sashen ta ta nufi
sashen Mufida dan aiwatar da wata kudiri da zuciyar ta tayi ta ayyana mata akan ta aiwatar da zarar ta farka daga bacci..
Kamar marar gaskiya haka tayi ta sanda tana bin hanya a hankali har ta zo kofar dakin nata ta ja ta tsaya ta hau bubbuga kofar a hankali tana kiran sunan ta a hankali kamar bata son a ji ta..
Sai da ta dan jima sannan ta ji an zo bude kofar dakin,ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala dan bata so a zo a riske ta a wurin a fara jero mata ka'idoji dan ta zo da sassafe tada diyar gwal..
Ganin Hamida ce sai ta kuma murtsike idanun ta tana mata kallon mamaki dan bata fiye ganin Hamidar ta farka da sassafe haka ba..
"Lafiya me ya faru Hamee"?tura ta ciki Hamida tayi itama ta karasa ciki tana maida kofar ta rufe sannan ta jawo hannun fifi ta rike cikin nata suka samu wuri a kan gadon fifin suka zauna...
Kallon kurilla Hamida ta mata tana ta nazarin yadda zata kasance a tsakanin su bayan ta gama fada mata abin da ta nufo ta da shi..
Ganin kallon yayi yawa sai fifi ta tambaye ta ko lafiya,sai Hamida ta sauya fuska zuwa kalar damuwa ta saka idanun ta cikin na fifi sannan ta fara magana kamar haka..
"Fifi na matsala ce ta dumfaro ni babba amma ban san ya zan magance wannan matsalar ba, tun jiya toh bayan tafiyar ki sai na kasa samo mafita amma hankali na ya kawo min ke,tuno da karfin gwiwar da kika bani nasanar da ke matsala ta sai kawai na yanke hukuncin tunkarar ki sai dai kash,ko da na duba agogo,sai na ga har daya da mintuna talatin da tara ya buga,sai na fasa zuwa sanin cewa kin dade da yin bacci kuma baccin mai dadi ne dan baccin gajiya ne"!!
Hamida na kawowa nan sai ta ja tayi shiru tana kallon fuskar fifi dan samin amsoshi daga sauyin fuskar ta..
A ruɗe fifi ta kuma riko hannun Hamida tana jin babu dadi,saurin tambayar Hamidar tayi.
"Hamee dan Allah ki yi saurin sanar da ni wannan matsala da damuwar da ta dumfaro ki,ni dama na sani,sam akwai damuwa a tattare da ke amma kika ki sanar da ni,yanzu Hamida har kina iya boye min damuwar ki ba tare da kin sanar da ni ba?ina yar uwar ki jini daya"?..
Wani irin murmushi Hamida tayi haka dama ta tsara ganin fuskar fifi bayan ta tunkare ta da wannan batun..
Dada langaɓar da kai Hamida tayi kalar tausayi ta kuma matsowa kusa da fifi ta