Showing 21001 words to 24000 words out of 101986 words

Chapter 8 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15631

za a ba Hamida dama da tace babu wanda yakai hajja iya nuna fifiko da sonkai dan babu cigaba a cikin lafuzan ta hala nata tsufar a haka ya zo mata da hauka,tana tambayar ta tun ma bata amsa ba ta kuma jefo wata tambayar da bata san ma'anar sa ba ikon Allah...Hajja..?wai waye na saheeb din nan tsoho shekaru aruru?Allah tir..Allah ya sawwaka itace za'ace ta auri wanda yazo duniya tunma kafin a aure mahaifiyar su?

Dariyar bazata Hamida tayi tana girgiza kai tana mai raba hannun ta daga na Hajja haɗe da furta

"Hajja kenan,zokije fifi na ɗakin ta ɗazu ta wuce ni zuwa ɗakin ta,sannan maganar ki ta biyu Hajja ni ban gane mata ba zai fi kyau in na raka ki ɗakin ki kika huta dan da alama kin gaji da yawa bayan tsawon lokacin da kika ɗauka baki ci abinci ba kina jiran dawowar....,fifi ko?"a kalmar Hamida ta ƙarshe sai da ta ja misali kafin ta ƙarasa sakamakon wani baƙin cikin da ya mamaye mata zuciyar ta tuno da cewa saura ƙiris ta yarda ɗan kada yayi girma a gaban ta ba dan tayi saurin yiwa tufkar hanci ba...

Ko jiran jin ta cewar Hajja Hamida bata yi ba ta janyo hannun ta ta kai ta ɗakin ta tana mai dangana ta da gadon ta haɗe da ƙare ma ɗakin kallo dan sai yanzu take shiga,duk da ba mai yawan magana ce ba ita,ta tsinci kan ta da complimenting ɗakin Hajjan..

A nan kuma Hajja ta kasa haƙura ta so ta kuma tado da maganar da ke ran ta amma Hamida bata bata damar yin maganar ba sai ta juya tayi ficewar ta..

Tuntuni Tana ɗakin ta tana shan banana smoothie tana tunano zantukar Hajja na ɗazu abin na mugun bata dariya dan ta fi danganta rashin natsuwar zuciyar Hajja da yanayin tsufa inba haka ba ina ita ina auren wani wai saheeb?

Nan take kuma tunanin zagayen su na ɗazu ya bijiro mata a lokacin da suka kai sashen sa,wani dariya ne ya taso mata nan ta tuno da yadda mama hasiya ke mata tayin shiga sashen tana ko, dariyar ce ta taso mata a fili ta furta
"Wai in shiga in gani?kaji munafurci suce kawai dama ni an zabamin shine ita kuma an zaba mata kyakkawa,toh me nake da buƙatar gani a sashen tsoho sama da karikitai?gaskiya mama hasiya da abin ban dariya take sosai, ni dai na san wannan babban ɗan Ammyn in har yanzu bai yi aure bama toh lallai akwai matsala dan bana jin akwai macen da zata wani aure sa wa ke son tsoho,lallai..sanda ya gama zamawo asalin tsohon za'a kuma bada hamida?.."dariyar hasashen kamannin sa tayi haka ta rinƙa ƙyaƙyatawa har ta ji dariyar ta ishe ta sai ta miƙe tana faɗin
"Ya zama dole in sanar da fifi wannan abin dariyar na san ta sarai ko son binciken ta kaɗai zai saka ta shiga sashen in ya so bayan ta dawo sai ta faɗa min ya sashen yake..

Ko tsayawa batayi ba ta fita ta nufi ɗakin fifi,babu doguwar sallama ta shigo kawai..

Fifi dake duƙunƙune cikin bargo ta ɗago kai dan ganin wa ya shigo mata,sai ta ga Hamida ce nan take ta kuma rufe fuskar ta..

By now attitude ɗin fifin shikansa na son shiga sahun abubuwan ban dariyar da Hamida take cin karo da su a yau..

"Tace hjiya fifi taso ki faɗa min menene ke faruwa na ga kamar ke da Hajja wasan ɓuya kuke yi"!!da sauri fifi ta taso ta zauna yayin da Hamida ke gyara zamanta bisa kan gadon..

Saurin tambayar Hamida tayi halan me Hajja ta ce mata,ita kam Hamida da dariya a fuskar ta ta hau yi mata bayanin yadda suka yi da Hajja ita kan ta fifi sai da tayi dariyar Hajjan amma ta ba maganar Hajjan ma'ana akan ko dai Hamida itama yi mata za a yi irin nata.. ?

"Faɗa min ƴar uwa ta,ina jin ki shin me Hajja ta faɗa maki ne da kike ta jin kunyar ta?Hamida tayi tambayar tana mugun danne dariyar takaicin ta..

Sai da fifi ta ɗau lokaci sannan ta riƙo hannun Hamida ta hau bayyana mata komai da ya faru ɗazu tsakanin ta da Hajja ta kuma ɗora da bayyana mata ko wanene wannan mai sa'ar da ta kasa bayyanawa Hajja shi ta gudo,still da yadda zancen ɗin da suka yi a tsarin su na cewa ita za'abawa khaleed ita kuma saheeb

Dan Fizge hannu Hamida tayi daga riƙon da fifi ta mata ta tashi tsaye dan take take ganin kamar duhu ya fara ziyartar idanun ta,bugun zuciyar ta ya ɗan dakata sannan ya cigaba a bugu fiye da ƙima,take ta ji kamar zata faɗi,ba shiri ta juya ma fifi baya tana tare hawayen dake shirin zubo mata da hannun ta,ɗaya hannun ta na bakin ta tana kare bakin ta daga sakin kukar da ke shirin fin ƙarfin ta..

Cikin dauriya Tace"Na taya ki murna fa Allah ya tabbatar da alkhairi"
iya abin da Hamida ta iya faɗi kenan daga haka ta tura ƙofar ɗakin Mufida ta fita da sauri tana haɗa hanya burin ta ta tsinci kan ta a ɗakin ta..

Har ta wuce sai ta dawo da baya jin wani irin baƙin tattaunawa dake tashi daga ɗakin Hajja tsakanin ta da Ammy..

Natsuwa tayi ta kasa kunnen ta tana sauraron su ba tare da sun san tana wurin ba,har suka gama zantukar su mai ɗauke da nazarorin su da fasahohin su suka yi jawo bakin zaren aka tsaya a matsaya ɗaya...

Juyawa tayi ta ga gidan na mata juyin fanka,kan ta ta dafe da hannuwar ta biyu ta hau dube dube a balcony ɗin ko zata hango ruwa dan ta sha ko zata sami damar kashe wutar da ya banku a ciki cikin zuciyar,amma bata gani ba kuma babu alamar zata samu...

Kusan da dafe dafen bango ta ƙarasa ɗakin ta,tana shiga ta saka lock ta zame a ƙasa tana ta juye juye tana fifita da hannuwar ta biyu sai shakar numfashi take kamar mai matsalar asthma ganin hakan bai gamsar da ita ba sai ta hau zubda hawaye tana numfashi cikin sauri sauri,tari ne ya sarƙe mata nan take ta hau yin sa babu ƙaƙƙautawa idanun ta sun canza launi daga farare zuwa jajazir.

Kwanciya tayi a ƙasa ta hau birgima dan har yanzu bata ji numfashin ta ya mata yadda take so ba..

Kimanin mintuna ashirin Hamida bata samu daidaituwar numfashin ta da ƙyar dai ta sami ikon sakin wani kuka

tun da ta ji kamar zuciyar ta ya ɗan sassauta sai ta cigaba da kukan,yi take yi tana tuno lokutan datayi sadaukarwa da yawa a rayuwar su ita da fifi har kawo yanzu...

Ƙirjin ta ne ta ji yana mata nauyi da zafi nan ma ta rasa ina zata saka kan ta ta sami sassauci,danne ƙirjin tayi da hannayen ta biyu tana jan numfashi hawaye na fitowa wani na korar wani...

A nan ɗakin Mufida kuwa ba ƙaramin kaɗuwa tayi da mamkin hamida ba,taga ta shigo tana yar fara'a batayi tsammanin zata ga shauƙi da zumuɗin ya yanke bayan ta bayyanawa Hamida sirrin dake zuciyar ta amma sai ta sha mamaki ta ga akasin haka.. Seta ke gani kamar mufida bata ji dadin zabin ba?

Dama wazai so tsoho?wani damuwar tuno da cewa ko itace na bayarda zatayi ba to amma me zatayi?wannan ai duk shirin su ammy da hajja ne.

Miƙewa tayi ta tsaya a tsaye tana kallon inda Hamidar ta tsaya daxun a yayin da ta juya mata baya tana mata wani irin amsar da bai yi kama da kalaman da kawai ya dace su fito daga bakin ta ba..

Mamaki kan mamaki ne ya saka fifi a gaba,duk iya inda hankalin ta da tunanin ta zai kai akan wannan abin da ya faru yanzu yanzun nan tayi ƙokarin kai hankalin ta nan amma bata sami abin da take so ba..

Juyawa tayi ta ɗauko gyalen ta ta yafa a kan ta ta saka takalmin ta ta fito da sauri dan zuwa jin matsalar Hamida gani take wannan reaction ɗin nata bai yi kama da abunda da mutum zai gani ya kawar da kai ya ƙyale ba dole ne dai akwai matsala dan Hamida ba haka take ba...

Cikin saurin ta ta fito tana tafiya sai ta ji a jawo ta ko da ta duba sai ta ga Ammy ce,cikin inda inda ta fara yunƙurin yin magana amma Ammy ta riga ta da fara'ar ta tana gyaɗa mata kai..

"Na sani,na sani,Hajja ta faɗa min komai,kuma na kasa haƙuri har sai kin bayyana mana da bakinki wanene wannan ɗin dan ni duk hankali na ga mutum ɗaya ya koma and i know it's that person,yanzu kin ga ba batun kunyar Hajja ko ni zaki ji ba,ki zo mu tafi sashe na dan ki bayyana min abin dake zuciyar ki a matsayi na na uwa a gare ki ai na cancanci jin ra'ayin ki,so come let's go my dear"Ammy na gama faɗin haka ta riƙo fifi da karfib tsiya suka hau tafiya ita kuma ba zancen kunyar ce ke damin ta ba a yanzu abin da ya fi damin ta shine ta san wani hali yar uwarta Hamida ke ciki..

Ɗan ja da baya Mufida tayi tana rau da ido cikin rashin jin dadi tace ma Ammy akan itafah ga inda ta fito da niyar zuwa amma amsar da Ammy ta bata shine
"Kibar wannan Hamida zata zo anjima itama aiko?itama akwai maganar da muka yi akan ta duk zan mata bayani amma bayanzu ba.let's concentrate on yours.."daga haka ta kuma riƙo hannun fifi suka cigaba da tafiya..

Duk da zuciyar ta na faɗa mata a'a ta fara zuwa ta ji damuwar ƴar uwar ta amma maganar Ammy na daɗa buga mata ƙararrawa akan ai ta ce zasu yi wata magana akan Hamidar tare,sai kawai tayi shiru ta cigaba da bin Ammy har suka isa ɗakin ta...
#Mamuh_*Mamuhgee*_

*11*

Zaunar da Fifi Ammy tayi tana kallon fuskar ta nadan wani lokaci sannan ta fara magana cikin kwantar da murya dan ta sami cikakkiyar hankalin fifin..

Ita kam fifi na ta bin Ammyn da kallon mamaki dan a zuciyar ta tambayoyi ne kala kala sai dai Ammyn bata bar ta ta sami ikon yin sa..

"Mufida kina ji na?,ɗazu Hajja ta kirawo ni ta sanar da ni matakin da ta ɗauka akan ki na haɗa auren ku sai dai ko kafin ta furta maki wanda ta zaɓar maki ke har kin nuna ta hanyar yin na'am da shawarar ta a ƙarshe har kika fita cikin kunya hakan ya tabnatar mata da cewa kina son abin da take maki sha'awar samu,toh ni yanzu ina so in kuma tabbatarwa ne,da gaske kin yarda da alakar dake tsakanin ku da yayan ku Khalid ya shiga wata matakin rayuwa wato matakin aure"?
karasa maganar tayi tana janyo hannayen fifi dan samin hankalin ta da yaddan ta dan basa so su yi mata ba dai dai ba..

Yin ƙasa da kai Mufida tayi cikin jin nauyin Ammy da tambayar da ta aiko mata..

  "Mufida amsa min bana son kina jin nauyi na ko kin manta ni ɗin Ammyn ki ce"?girgiza kai fifi tayi tana mai buɗe bakin ta cikin jin nauyin Ammyn ta ce
  "Ammy ai shi bai ce komai ba"!!shiru Ammy tayi tana sauraron ta a zaton ta akwai cigaban maganar amma ta ji shiru sai ta ɗago ta kalli Mufidar cikin jin daɗi dan ta san in har ita tayi na'am da zancen toh shima Khalid ɗin ya zama dole ya amince dan bai da matsala dama sun jima da jiran ganin ya kawo masu mace da sunan matar da zai aura anma babu labari shi yasa da Hajja ta tunkare ta da maganar kawai ta ji hankalin ta itama ya kwanta da shi dan ta matsu ta ga jikokin ta ko zata mori albarkar ƴaƴa itama tunda auren na danta na farin bai yi working out ba toh yanzu addu'ar ta bai wuce ta sami jikokin daga tsatson Mufida ba...

Hajja Tace..."In dai Khalid ne wannan ba abin da zaki ɗaga hankalin ki bane saboda ya jima da bari mana zaɓin matar sa a hannun mu,yanzu dai menene kike son sani game da shi da baki sani ba wanda bai faɗa maki ba"!?

murmushi fifi tayi tana daɗa sunkuyar da kan ta ƙasa kafin ta amsa kamar da Ammy takeyi..
"Ammy kaɗan na sani daga rayuwar sa kin ga kamar ban san komai bane so kusan komai akan sa nake son sani"cikin jin nauyin su duka ta ƙarasa maganar nata.

Ajiyar zuciya Ammy tayi sannan ta kuma faɗaɗa murmushin ta tana gyara zaman ta..
"Kamar dai yadda kika ji ana kiran sa da Khalid,toh asalin sunan nasa kenan Khalid,kwata kwata shekarun sa bazasu wuce 27 years ba bai ma gama kaiwa ba sannan shi ne ɗa na biyu a cikin gidan nan babban yayan sa shine Saheeb wanda ba a nan yake ba,Khalid yayi karatun su both primary and secondary schools ɗin sa a nan ƙasar ne so bayan ya kammala ya nuna interest ɗin sa a fanin karatun gynaecology wato ya zaɓi ya zurfafa karatun sa a fannin sanin matsalolin mata.

duk da ban raine su tare da Abban su ba sakamakon barin mu da yayi a daidai lokacin da muke buƙatar sa dan kuwa Allahn da ya bamu shi ya karɓe sa,hakan bai sa nayi ƙasa a gwiwa ba kakar ku Hajja ita ta ƙara ƙarfafa karatun Khalid ɗin sai ya zaɓi ƙasar Cyprus a inda yake son zuwa yin karatun,bamu hana sa ba iya fatar alkhairi da muka mai,wani abu shine Khalid ya kammala karatun sa ne a dan kankanin lokaci dan ya karasa yana da shekaru ashirin da biyar abin da ba kasafai ya fiye faruwa ba,so ya dawo kuma alhamdulillah ya sami aikin sa yana aiki a nan cikin gari sai dai ba ko da yaushe yake zuwa ba sai har in shine on call kuma a halin yanzu yana kan cigaba da karatun sa dan zama cikakken consultant so zuwan ku ne ya sa yake zaune a gida kuma ya haɗu da hutun sa da ya shigo..

Kuma he really wants you to feel at home that was why ya zaɓi kai ki wurare daban daban tun dawowar ki kuma daga dukkan alamu shima ya gamsu da ke dan naga kamar jinin ku ya zo ɗaya daga yanayin da yake sake maki"..ɗan dakatawa Ammy tayi tana sauraron jin ta bakin fifi..

Fifi sai ji tayi kamar an kara rura mata wutar ƙaunar Khalid a zuciyar ta ina ma a ce karantar fannin zuciya yayi da sai ya magance mata damuwar ta amma duk da hakan bata ji ƙaunar sa da ya mata shigar farat ɗaya ya ragu ba..

Can Tace "Ammy, baki sanar da ni komai akan social life ɗin sa ba irin meyafi so,abokan sa da dai wasu abubuwa da suka shafi personal life ɗin sa"..
murmushi Ammy tayi tana shafo fuskar fifi sannan ta cigaba..

"Well,Khalid...,ina ga ba sai na tsaya faɗa maki tsarin rayuwar sa ba dan ke kan ki shaida ce akan hakan kin gani kuma kina iya faɗawa wasu,sannan akan abokan sa...,Khalid na da abokai but mostly sai lokaci zuwa lokaci suke haɗuwa kinsan yanayin aikin nasu kowa na concentrating ne akan aikin sa,game da abincin da Khalid ya fi so kuwa,ina iya faɗa maki Khalid is a simple person komai yana ci muddin abin nan na ci ne,ba kamar yayan sa Saheeb da ba komai yake ci ba"...

Kallon Ammy fifi tayi tana gyaɗa kai alamar ta gamsu da duk bayanan Ammy tace Hamida fa,itama ai tare zaayi mana auren ko?sai tayi shiru aranta tana tunanin
"ya ita kuma zata kasance in aka ce ita zata yi aure ba tare da Hamida ba?bata taɓa mafarkin hakan ba ta fi planning ranar auren su ya zo daidai komai su yi tare amma ba a rabe ba..

Yin wannan tunani sai ta ɗago ta kalli Ammy directly ta jefo mata tambayar dake zuciyar ta...

"Ammy ya labarin na Hamida"?shiru Ammy tayi tana ɗan kasaƙe for a while sannan ta amsa tambayar..
"Dear ban manta da Hamida ba ai dama na faɗa maki za mu yi maganar nata bayan naki so yanzu bari in fayyace maki nata dan surprise ɗin da Hajja ta mata ne

"..nan take fifi ta zaƙu a faɗa mata dan sanin ko wa ita kuma aka zaɓar mata dan dan tasan bazata taba yin aure ba tare da ƴar uwar ta ba..

"Kin ga kasancewar Hamida mai ɗauke kai ne ga duk wani al'amurar rayuwa,ba ni kaɗai na hango hakan ba har kakar ku Hajja ta hango hakan,tana da shiru shiru bata cika magana ba babu ruwan ta,so haɗa ku da za a yi da yayan ku Khalid sai Hajja ta ga me zai hana itama a mata hakan dan ɗabi'un ta ya zo sak irin na wanda take hasashen haɗa sun,sedai shi ba anan yake ba

kuma...."!!!sai tayi shiru sai fifi ta girgiza mata hannu cikin zaƙuwa tana son Ammy ta ƙarasa mata bayanin...

Kawar da kai Ammy tayi tana takaicin furucin da zata furtawa fifi dan bata san yadda zata ɗau maganar ba amma dai dole ta sanar da ita dan ba zai yiwu ta ɓoye wani sirri ba alhalin haɗin da suke son yi haɗi ne na har abada..

"Mufida wanda muke son haɗa sa aure da ƴar uwar ki Hamida yana da mata,kuma sun share shekaru da yawa suna tare sai dai..."!!nan ma Ammy tayi shiru sai fifi ta ƙyale ta bata ce mata komai ba...
Sai da suka ɗau lokaci a hakan sannan fifi ta sake tambayar su haɗe menene matsalar da ajiyar zuciya Ammy ta furta bakomai sunan sa..
"Muhammad Saheeb,yayan Khalid ne, shine mutumin da muke son haɗa Hamida aure da"!!fata na hadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login