Showing 87001 words to 90000 words out of 101986 words

Chapter 30 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15648

da tayi tare da fifi kwance cikin tsantsar jin daɗij yanayin su..

Juyawa tayi idanun ta rufe da kishin mijin ta da ɓacin rai ta bar sashen tana ta nanata dama yana son yarinyar nan amma kullum baya admitting ya saka ta ta rinƙa jin kamar daga ita sai ita a rayuwar sa dama ƙarya yake mata..

Bata tsaya ko ina ba sai a sashen Hamida da yanzu ta dawo daga rakiyar mijin ta zai tafi aiki..

Sallama tayi a bakin ƙofar parlorn,bata jira an bata izini ba ta saka kai ta shiga,daidai Hamida zata zauna kenan ta ga Muhibba kuma da ganin ta ka ga wacce ke cikin tashin hnkl..

Bata ba Hamida damar yin mgn ba ko uffan bata ce ba Muhibba ta riga ta da baki cikin fushi da ɗan zafin rai..

"Ke Hamida tare da ke muke komai Amma ashe wannan ƴar yarinyar mai ƙoƙarin amsa sunan matar Saheeb na can na kalaikaye min miji ni ina nan ina tinƙahon miji nawa ne ni kaɗai nagama da shi?,for goodness sake is that girl so dump and foolish just look at me na yi kama da wacce zan haɗa miji na da wannan ƴar yarinyar"?

Hamida na shiru tana jin zafin kalaman Muhibba ga ƴar uwar ta..

"Kina ji na kuwa Hamida?ki bani mafita ta yaya zan ɓullowa wannam yarinyar na ƙi jinin in gan ta kusa da miji na"!

Dakatar da ita Hamida tayi ta hanyar ce mata
"Me ya sa"?rai ɓace ta bata amsa da

"Because he is mine and all mine alone"!

Murmushi Hamida tayi ta koma ta zauna tayi crossing ƙafar ta ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa tana duban Muhibba dake tsaye tana bin Hamida da kallon mamaki..
"Meye haka ina nemar mafita ta yadda zamu kawar da lbrn wannan yarinyar a rayuwar miji na ke kuma kin zauna kamar ba kya ji na"!da ɗan ɗagon murya Hamida ta ce

"And why should i help you Muhibba?for crying out loud ke baki da brain ɗin tunanin kan ki ne sai na baki mafita?waini nace miki tsanarta nayi ne uhm?shawara fa nabaki..go ahead and use ur head mana..kema ki samowa kan ki mafita as far as am concern ke ɗin ai babba ce kin girme mu so use ur big head and find a proper solution for ur self


"Arazane Muhibba ta bi Hamida da kallon mamaki..

Karkaɗa ƙafa ta cigaba da yi tana duban Muhibba sai kawai Muhibba ta mata wani tsawa itama ta miƙe tsaye ta mayar mata da martanin tsawar nata.

"ai ban yi ƙarya ba ki je ki samowa kan ki mafita na gaji da duk wannan abin am out...kiyi waje

ɗora hannu a ƙwanƙwaso Muhibba tayi tana kallon Hamida da tsantsar mamakin ta..

Kalamai marasa daɗi ne ya fara fitowa daga bakin Muhibba zuwa ga Hamida,itama Hamida cikin rashin haƙuri ta hau maida mata martani har da gori da tunatar da ita ita ta kasa bada farinciki a rayuwar mijin nata sai hassada dan ta ga nata twin sister ɗin ta bashi farinciki..

A sannu duk suka gama tonewa kan su asirin shirin su da suka yi ta yi a ɓoye ba tare d wani ya sani ba gori akan gori,faɗa sosai suka yi mai muni,tas suka tonawa kan su asiri kamar ba a taɓa zaman mutunci ba..

Turo ƙofar parlorn aka yi da ƙarfi alamar duk wanda ya turo ƙofar ya ji every single part of their conversation,a tsorace Hamida ta juyo hakama Muhibba duban su suka kai ga wanda ya shigo dan ganin sa..

Zazzaro ido Hamida tayi sakamakon ganin wanda ya shigo ta juya ta kalli Muhibba da itama ita take kallo lokaci guda suka juya kallon ƙofar..
#Mamuh*35*

Ƙarasa shigowa yayi take Hamida ta shiga taitayin ta ta ɗan koma da baya yayin da Muhibba ta ƙare masa kallo ta juya ta kalli Hamida ta ɗan ja ƙaramin tsaki ta sa kai ta fice ta bar sashen..

Gaban ta ya zo ya tsaya cak yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa,irin wannan disgusting looks da yake mata na ruɗa ta..

Da ƙarfi ya riƙo kafaɗar ta cikin tsantsar ɓacin rai da tir da halin matar nasa ya fara mgna cikin bacin rai, cikin ɗagon murya da hargowa..

"Ki Tabbatar min da gaskiyan wannan hirar naku da na gama ji yanzu da bakin ki"!!

a tsorace Hamida ta dundunce cikin tsoro da fargabar me zai biyo baya ta hau in'ina tana ƙoƙarin fizgewa khalid ya kuma matso ta dab da shi..

"Khalid you are hurting me let go off me"!.kamar zatayi kuka ta furta hakan

daka mata tsawa yayi yana ce mata
"Yes i wanna hurt u so that u will feel d pain u hv been making ur own blood twin sister experiencing,hamida ba zan ga laifin ki ba dan dama wanda bai so ka ba tun asali ba zai taɓa son ka ba har abada ko ya zo ya ce yana son ka toh da manufa ne,now i get it,you are a selfish person,kin cika son kan ki da yawa,just imagine,Hamida haka kike ashe?ki haɗa kai da wata wai Muhibba da duk kusancin ku bai kai girman kusancin ki da ƴar uwar ki ta jini ba,hnkl kwance ki yarda tana cin ma burin ta akan ƴar uwar ki and d most provoking part of all shine da sanayyar ki hakan ke ta faruwa"..?

Zafafan Hawayen sa daya ke dannewa su suka kwace mishi suna gangarowa a hankali muryn sa yayi wani irin sanyi yace

"Hamida Me ya sa kika canza halayyar ki kika zamo kamar wata muguwa marar imani?huh?sbd Allah Hamida duk waɗannan munanan abubuwan da kan ki da hannun ki kika yi su?in fact ke ce mai coming up da idea ɗin?.ƴar uwar ki ta jini kika haɗawa waɗannan abubuwan?common Hamida u weren't lyk dis. meye ne ya sauya ki kika zamo haka?duk ƙoƙarin da nayi ta maki ashe abinda kika saka kanki a kai kenan?

Kuka ta fashe dashi batace dashi uffan ba

shiru yayi yana watsa mata kallon banza ita kuwa banda kukan babu abinda take yi..

Haɗa ta da wall ɗin parlorn yayi yana kallon ƙwayar idanun ta,tas tana hango tsantsar ɓacin ran da yake ciki..

"So u two have been blackmailing my brother huh?kai Hamida how many evil hv u done?ashe tuntuni kun daɗe da sanin juna ma sanin da yayi zurfi har ke kina iya bada shawarar ga abinda ya dace a yi?kun saka shi zama cikin zargin kan sa akan laifin da bai sani ba ku kuna nan kuna arranging plans ɗin ku shi yana can yana kwantar mata da hnkl yana nesanta kan sa da ƴar uwar ki matar sa kuma kina ankare?ke ce a gaba mai jagorantar komai ma"!!

A raunne ta dago Zatayi magana yace baison ji

Sosai Hamida ke kuka tana nadamar wannan rana da ya zo mata a haka
kwata kwata ba haka ta shirya faruwar Abun ba so tayi daga wannan argument ɗin da suka samu tsakanin ta da Muhibba shikenan ta fitar da ita a rayuwar ta ta koma ga ƴar uwar ta but unfortunately Khalid ya gama jin komai bata da yadda zata kare kan ta komai ya ƙwace mata...

Sakin ta Khalid yayi ya juya baya yana furzar da iskar takaico da ɓacin rai,yana mamakin yadda zuciyar Hamida ya ƙeƙashe ya bushe haka har akan kishin ƴar uwar ta take iya haɗa kai da Muhibba su cuci ƴar uwar nata...

Nade hannayen sa yayi a ƙirji ya juyo ya dube ta da kyau sannan ya ce mata cikin murya mai firgitarwa da tsoratarwa.

"Tun yaushe kika fara zaluntar Mufidan?saurin duban sa tayi gaban ta na faɗi cikin kuka sai ta girgiza mai kai tana faɗin

"Wlhy ban taɓa shirya zaluntar ta ba ruɗin zuciya ne ya shiga tsakani na da Mufida amma Ƙaunarmu na nan a zuciya ta"!!shutting nata yayi ta hanyar ce mata

"Ƙarya kike yi karki ce min akwai ƙauna a tsakanin ki da Mufida after all these conversation da na ji da kunne na,har kin ba Muhibba shawarar karɓar wannan maganin da take sha,well for ur information maganin nan na nan na haddasa mata illa,illah mai tsanani,ɓoye ɓoyen ku wata rana zai ƙare but kin san me?

"am leaving,am leaving u na har abada.. coz ba zan iya cigaba da zama da mace irin ki ba, duka soyayyar da na nuna maki,da irin zaryar kai komon da Mufida ta rinƙa yi maki duk dan ki yafe mata ku shirya amma tun asali da yake ba son ta kike ba sai kika rufe idanun ki kika rinƙa bin abinda zuciyar ki ke raya maki yake bijiro maki,so am getting out of ur life hamida ki je Muhibba ta zame maki abinda ni da ƴar uwar ki muka kasa zame maki"!!yana kaiwa nan ya ingiza ta ya wuce ya shiga tattara kayan sa..

Faɗi ƙasa tayi tana kuka mai haɗe da shesheƙa tana maganganu ita kaɗai tana nemar yafiyar Khalid bai kulata ba har ya gama yaja jakar sa ya fita..

Bata kuma tsorata ba sai da ta ga da gaske tafiyar zai yi dan ya fito da akwatin san rai ɓace ya xubasu s booth ya rufe..

Tana kuka ta taso ta zo zata riƙe shi,wani tsawar da ya mata sai da ta ja da baya jikin ta na ɓari tana kuka mai tsanani tana nemar yafiyar sa haka ya ya shige ya ja motr sa ya fita a gidan..

Kamar zata haukace haka ta rinƙa yi ita kaɗai tana aibata ranar da tunanin haɗa kai da Muhibba ya bijiro mata,tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin Khalid yayi fushi mai tsanani irin wannan ba sai yau,kenan ya tafi ya bar ta kenan?hukuncin da ya zaɓi yi mata kenan?..

Surutai dai babu wanda Hamida bata yi ba tun tana ganin abin kamar hasashe har dai ya tabbat Khalid ya tafi ya bar ta shikenan ita bata da wani gata,garin nemar gira ta rasa ido,ita ina zata kalla ta ji daɗi a ran ta...

Haka ta yini tun safen nan har dare bata sami kan ta ba abin kamar wacce ta rasa hankalin ta haka tayi ta yi,kiran tayi har ta gode

Allah bai ɗaga ba daga bisani ma kashe wayar yayi gabaɗaya,text msgs kuwa sun fi a ƙirga da ta aika mai da shi but babu reply,kwanar kuka da nadama tayi tana da ta sanin rayuwar ta...

*****
A fannin Muhibba da ta bar sashen Hamida bayan kallon banzan da ta ma Khalid,sashen ta ta nufa ta shige ɗakin ta ta saka mai lock..

She is weak already bata da wata dabara da ta rage mata tunda dai har Khalid yaji abin da ya faru tsakanin ta da Hamida toh ta san Saheeb ya gama jin komai...

Kai kawo ta shiga yi a ɗakin tana saƙa da warwara,rikicewa ƙwaƙwalwar ta yayi ta kasa lissafin komai dan dama in dai irin wannan ne toh Hamida ce mai bata mafita toh yanzu sun ɓaci babu jituwa a tsakanin su..

Furzar da iska tayi tana cigaba da kai kawo at same tym da take takura brain ɗin ta ya bata mafita a same time ciwon cikin ta na addabar ta dama daurewa tayi ta tsaya ta yi wannan faɗar da Hamida amma tana jin ciwon sosai...

Zama tayi a kan sofa ɗin ɗakin nata tana ta nemawa kan ta mafita but sam bata samo komai ba haka ta ɗau wayar ta ta rinƙa kokarin kiran Saheeb sai tayi dialing sai ta kashe dan bata san me zata ce mai ba in ya ɗaga kiran.

Gabaɗaya Muhibba ta rasa natsuwar ta da tunanij ta a ranar ga Saheeb ɗin bai ko waiwayo ta ba bare ya san halin da take ciki

Daɗin daɗawa ma ga fifi ta dawo part ɗin dan ta ji hayaniyar mai aikin su Ammy na tmbyr ta ko ta tsaya ta taya ta girki amma ta ce a'a ta tafi kenan shi Saheeb ɗin ne ya ce mata ta dawo dan ya rinƙa ganin ta da kyau yana nuna mata so da kulawar sa ita kuma ko oho..

Har dare tana part ɗin ta bata fito ba haka Mufida bata haura ta duba ko lafiya bata gan ta ba toh dama babu ruwan ta da Muhibban,mijin ta ne a gaban ta kuma duk inda yayi nan itama zata yi bata jin tana da lkcn wata Muhibba bare ta sakawa ran ta damuwar ta,ta san days ɗin ta are numbered dan sarai doctor ɗin ta ya faɗa mata komai game da rayuwar ta da na babyn ta sai dai bata sanar da Saheeb ba dan bai san tana da wani doctorn ba all he knows shine Khalid ke kula da ita bayan hakan bai san komai ba...

*****
Kusan kimanin sati biyu kenan rabon Khalid da Hamida sai dai ya zo ya gaida mahaifiyar sa da kakar sa,in yayan sa na kusa su gaisa in baya nan yayi tafiyar sa.

Duk wannan mu'amalar nasu da Saheeb ko da wasa bai bayyanawa ɗan uwan nasa abinda ya jiyo Hamida da Muhibba suka aikata ba haka bai sanar da mahaifiyar sa ba bare kakar sa Hajja..

Hakama Hamida na nan na ta targeting nasa in ya zo amma bata taɓa sanin lkcn da yake zuwa har ya tafi sai dai ta ji an ce ai Khalid ya zo har ya wuce..

Kwanar kuka take yi a ranar da ta ji hakan sai dai bata san wa zata tunkara da damuwar ta ba ƴar uwar ta da ta ha'inta zata tunkara ko wa,bata sani ba amma matuƙa abin na damin ta a ran ta...

Wata ran tana kan share hawayen ta bayan 111 missed calls da ta bar wa Khalid sai ta tashi wuf kamar an tsungule ta ta yafa ƙaramin mayafin ta ta nufi sashen Mufida dan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba fifi na zuwar mata hira sai dai bata taɓa faɗa mata abinda ke damin ta ba hasalima in ta zauna sai ita ta tashi ta ce bata jin daɗi zata kwanta,tmbyr inda Khalid yake kuwa fifi ta mata shi sau nawa amma amsarta shine ya tafi aiki so daga haka fifi zata ja bakin ta tayi shiru..

Haka ko da Saheeb da Ammy suka so sanin me ya sa ya tafi aikin ba tare da matar sa ba sai ya nuna masu so yake y barta da fifi tunda sun fara shiri yanzu,so kowa ya yarda da dalilin sa ban da Muhibba da ta san kwanan zancen..

Waya take yi da daddyn su tana ta murmushi sai ta an turo mata ƙofa dan haka ta kai duban ta ga ƙofar sai ta ga Hamida duk hnkl tashe idanun ta cike taf da hawaye ta ƙarasa shigowa bedroom ɗin Mufidar abinda bata taɓa yi ba kenan tunda aka masu aure sai yau..

"Daddy i will call u back ina zuwa"fifi ta faɗa tana kashe wayar haɗe da dubar ƴar uwar nata..

Hnkl tashe ta tashi ta ƙarasa gare ta tana tmbyr ta lfy,kuka ne ya ci ƙarfin Hamida sai kawai ta ɓalle da kukan sosai,hnkl fifi ya tashi sosai sai ta riƙo ta suka zauna a gadon ta saka hannun ta cikin nata tana tmbyr ta me ya same ta..

Da kunya ciki a zuciyar ta ta zayyanewa Mufida dalilin tafiyar Khalid sakamakon abinda ya jiyo,da mamaki fifi ta tmby ta me ya jiyo nan matsanancin kunyar fifi ya mamaye Hamida amma haka ta daure din dai ta fayyace mata komai daga fari har ƙarshe...

Wani mamaki ne ya kama xuciyar Mufida sai da ta ɗau lkc tana ƙaryata kunnuwar ta amma Hamida tayi ta nanata mata ai hakan ne ita dai ta yi kuskure babba Mufida ta dube ta da idon rahama ta yafe mata ba zata ƙara ba...

Kallon ta kawai fifi tayi ta yi ta rasa me zata ce,ƙirjin ta ne ya mata wani irin nauyi sai tayi shiru har Hamida ta gama surutan ta tana kuka...


Rungumo ta fifi tayi tana fidda hawaye daga idanun ta tana jin zafi a ƙirjin ta sai dai ta kasa furta komai har sai bayan wasu lokuta sannan ta rarrashi Hamidan a nitse.

"Is ok Hamee na maki alƙawarin zan taimaka maki mijin ki ya dawo maki InshaAllah!

a firgice Hamida ta ɗago tana kallon fifi da mamaki
murmushin da ya fi kuka ciwo fifi ta mata tana gyaɗa mata kai ta kuma rungume ta batace komai ba..

Ba ƙaramin guilty conscious ne ya addabi Hamida ba tunanin ta in ta gama faɗawa fifi gaskiyar ƙulalliyar da suka mata from a-z fifin zata bada negative reaction sai ta ga akasin hakan..

A nan part ɗin fifi Hamida ta yini dan tayi yadda zata yi ta sa Hamidan ta sake jikin ta kafin daga bisani ta raka ta har sashen ta suka yi sai da safe ta dawo part ɗin ta...

Kuka ne mai ƙarfi ya kama Mufida tana yi tana danne ƙirjin ta dan nauyin da ya mata ba kaɗan bane,tana ta son ta karyta zancen cewa Hamida ce ta aikata mata hakan sai dai ya faru ko saura a gyara gaba..

Ciwon ta ne ya so tashi cikin dare dan Saheeb baya nan ya ɗan je wani tafiya haka tana jin nauyin faɗawa Ammy wannan abin so ta barwa kan ta,in da wanda zata faɗawa bai wuce saheeb ba toh baya nan dole ta jira har ya dawo sannan dan kar ta ɗaga mai hnkl,kuma daga baya tayi tunanin kawai ta fasa faɗa mai ɗin ita tayi yadda zata yi dan Khalid ya dawo ga matar sa...

****

Washegari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login