Showing 90001 words to 93000 words out of 101986 words
fifi da kan ta ta kira Khalid bata bari ya riga ta da baki ba ta nemi alfarmar da take nema daga gare sa sai ya rasa abin faɗi kawai ya ce mata ya ji zai dawo nan da kwanaki uku,gudun kar ta takura mai da yawa sai ta mai godiya kawai suka yi sallama ta fita dan zuwa ta ma Hamida albishir..
#Mamuh*36*
Kamar yadda Khalid ya faɗa haka ya cika,danna daidai 3rd day ɗin da suka yi waya da Mufida ya dawo gidan..
Ranar Hamida sai da tayi kukan murna ta rasa me zata mai dan ya ji daɗi sai dai bai bi ta kan ta ba ya bar ta kamar bai yi kewar ta ba..
Kasa aiwatar da komai Hamida tayi har dai ta kira Mufida a waya wacce daidai lkcn kuma tana waya da mijin ta,ganin kiran ƴar uwar ta ya sa ta katse nasa kiran ta ɗau na Hamida..
Da shesheƙa Hamida ta fara mata bayanin ƙyaliyar da Khalid ke mata,haƙuri kawai fifi ta iya bata ta ce ta ɗan bar sa zuwa washegari hala ya sauko..
A haka dai Khalid da Hamida suka kwana a part ɗin su,shi ya kwana a ɗakin sa ita kuma ta kwana a ɗakin ta abinda basu taɓa yi ba tun auren su..
Ita dai bata yi baccin kirki ba dan kewar mijin nata ne kawai ke mamayar ta but bata da yadda zata yi haka nan ta kwana cikin kewar sa idanun ta buɗe duk sun kumburo...
Da safe misalin ƙarfe shida ta farka ta haɗa ma Khalid breakfast duk da ciwon da kan ta ke yi haka ta daure ta girka mai wani da zai tafi da shi office ta je tayi wanka ta dawo ta shirya cikin shigar atamfa ja mai ratsin fari fari ya mata kyau ta ɗan yi makeup kaɗan tayi ɗaurin ta ta fito ta zauna a dinning table ɗin tana jiran sa...
Fitowar sa kenan cikin shigar tafiyar aiki yana gyara necktie ɗin sa sai ya hango ta kan ta haɗe da table ta tallafe kan da hannayen ta biyu tana bacci..
Wani tausayin ta ne ya ratsa sa sai ya ƙaraso gare ta,a hnkl ya saka hannun sa yana shafa bayan ta but kamar yana petting nata ne..
Cikin baccin ta ta ji abinda yake mata sai ta ɗan ɗago da baccu bacci a idon ta,ganin sa sai ta wartsake gabaɗaya ta tashi..
Saurin maida ta yayi ta zauna shima ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna suna fuskantar juna,for a while bai ce komai ba sai daga bisani ya fara mgn..
"Na san na maki hukunci mai tsauri ta hanyar ƙaurace maki but ki sani,hakan ba yana nufin ban yi kewar ki bane ko ban damu da rashin ki a kusa da ni bane,i did what i did to wake u up from ur challenged future,ba zaki cigaba da rayuwa a duniyar nan da ƙiyayyar ƴar uwar ki ba,but am happy ganin abubuwa sun daidaita a tsakanin ku kuma kuna getting along da juna,i pray that it will continue all through"!!gyaɗa mai kai tayi da sauri tana jin sanyi a ran ta..
Hawayen dake tseren zubo mata ne suka sauko sai ta share da yatsar hannun ta tana kallon sa..
Murmushi ya mata sannan ya nemi da ta mai alƙawarin ba zata kuma ƙulla wata alaƙa da Muhibba ba..
Alƙawarin ta mai tana tabbatar mai da cewar in har ya ga tana kusantar hakan toh ya jawo hnkln ta but bata fatar kusantar hakan kuma..
Daɗi ya ji da ya iya tsawatarwa matar nasa ta dawo kan hanya,maida duban sa yayi ga abincin ya umarce ta da tayi serving nasa..
Da sauri tayi hakan,fried chips ne da scrambled egg sai quacker oath da ta haɗa masu..
Ya ji daɗin breakfast ɗin dan haka ya cinye duka yana santi haɗe da yabawa hannun nata da ya girka abincin,daɗi sosai Hamida ta ji har ta rasa ina zata saka kan ta...
Tare suka fito bayan yayi feeding nata itama ta ƙoshi sai ta ɗauko mai food flask ɗin sa na abincin da ta mai..
Nan ma wani yabon ta sha shine ta rako sa har mota,suka yi warmly goodbye sannan ya tafi ita kuma ta nufi sashen fifi...
Da sallamar ta a baki ta shiga parlorn sai tayi tozali da Muhibba dake fitowa daga kitchen cikin sauri cikin shigar blazers da wando ta ɗora wani summer cardigan,kan nan babu mayafi sai wani turban,handbag ne a hannun ta da car key,ƙafar ta ya sha heels ne baƙaƙe..
Kallon wofi Hamida ta mata itama ta maida mata da matarni har da ɗorawa da
"Ina cikin hanzari ne amma ki bari in dawo zan yi fixing naki inda kika dace"!!ta faɗa tana tafiya..
Cikin sauri Hamida ta maida mata amsar da ya saka ta juyawa dan kallon Hamidar da kyau but sai ta ga har ta wuce ta..
Abinda ta ce mata kuwa ba wani abu mai tsayi bane sama da
"Kullum cikin hanzari kike shi ya sa kika kasa ba mijin ki farinciki har ya samo wacce ke bashi,that's why u always behind,hanzari!!!hanzari!!hanzari,too bad"..
Ba ƙaramin ƙonawa Muhibba rai waɗannan kalaman Hamida suka yi ba sai dai bata ce komai ba illa ƙwafa da ta yi ta juya ta fice...
Kai tsaye Hamida ta shige bedroom ɗin fifi sai ta gan ta zaune da towel babu kaya a jikin ta tana ta positioning wayar ta kamar dai video call zata yi..
Murmushi tayi ta ƙaraso ciki,sai a sannan fifi ta gan ta sai ta kife wayar a kan gadon ta fara yunƙurin tashi dan tarbo Hamida but Hamida ta hana ta ta hanyar ƙarasowa ɗakin da sauri tana riƙo hannun ta game da furta..
"Don't take d trouble sweet"faɗaɗa murmushi fifi tayi sai ta zauna suna fuskantar juna..
Gaisawa suka yi irin ta ƴan uwa a nan Hamida ke shaida mata yadda suka yi da Khalid sai fifi tayi murmushi kawai tana sha'awar rayuwar su dan suna burge ta,kullum suna tare da juna unlike ita da suke raba mijin sannan bai cika zama ba,a ƙalla cikin sati biyu yayi tafiya ya kai uku,bai da wani lkcn isasshe da yake spending ɗin sa da ita..
Hirar su suka yi har Hamida ta taya fifi gyare gyaren inda bata gyara ba kafin ta koma apartment ɗin ta tayi girki mai ƙara lfy a jiki da kyaun kallo ta cika sa cikin food warmer tayi blending fruits ta tace ya zamo kamar fruit juice sannan ta haɗa su a wani basket ta dawo sashen fifi da su...
Abin ya ma fifi daɗi dan dama ƙiwar girkin take yi dan a ƴan kwanakin nan aiki na mata wuyar yi kuma ta ƙi yarda Ammy ta turo mata ɗaya daga cikin ma'aikatan ta haka ta ƙi yarda a rinƙa kawo mata abinci daga sashen...
Har dare suna nan tare suna ta hirar su,wanda cikin hirar ne Hamida ta kawo wata shawara da tayi tasiri a zuciyar fifi har tayi tunanin ɗabbaƙa shawarar immediately sai dai ta bari har mijin ta ya dawo sannan ayi mai yiwuwa..
Shawarar akan daddyn su ne da rayuwar zaman kaɗaicin da yake yi na rashin mace,sun gama tsara komai yadda zai kasance,lkc kawai suke jira su fara aiwatar da plan ɗin nasu...
Wayar Hamida ne yayi ƙara kamar ba zata ɗaga ba sai ta ɗaga ta kai idanun ta kan wayar..
Sunan dake haskowa ne a screen ɗin wayar ya saka ta buɗe baƙi cikin mamaki tayi saurin ɗaga wayar tana faɗin
"Am on my way luv ina wurin Mufida ne"!!tana gama faɗin hakan fifi ta saka mata dariya ganin duk ta ruɗe..
Bata bi ta kan ta ba ta tashi abin ta tana mata sai da safe,sauri sauri ta dawo apartment ɗin ta inda ta gan sa yana cire necktie ɗin sa a gajiye..
Saurin ƙarasowa gare sa tayi tana bashi haƙuri haɗe da taimaka mai ya cire necktie ɗin ta kwashe duk kayan da ya cire da hannun ta ɗaya,ɗayan kuma tayi wrapping round his waist tana mai yi mai sannu.
A haka suka ƙarasa sama inda bedroom ɗin su yake ta taya sa yayi wanka itama ya saka ta yi na dole,tare suka ƙarasa wankan bayan an gama romancing kamar ba za a bari ba sannan suka fito...
Abinci ma yanzu tare suka ci suna feeding junan su da love and care,a wurin kwanciya kuwa,yau sai da Hamida ta tabbatar mijin nata yayi kewar ta itama haka,dan basu wani runtsa da wuri ba sai cikin dare sannan baccin ya ɗauke su...
****
Yadda Allah ya so haka yake kasancewa,yau da gobe sai mai duka,a kwana a tashi ga mai tsawon rai cikin Mufida ya shiga wata takwas cif cif sakamakon scanning ɗin da tayi na ƙarshe ya tabbatar da hakan...
A lot has happened kamar yadda Hamida ta tsayawa Muhibba a ido kamar matsala ta ƙi yarda a cigaba da cutar da ƴar uwar ta,dan har threatening Muhibba Hamida tayi akan in ta ja abin da nisa toh kaf zata zayyanewa Marshall gaskiyar zance dan Khalid bai faɗawa kowa abinda ya ji suna discussing akai ba ranar...
Sosai tsoron Hamida ya ɗarsu a zuciyar Muhibba dan ta san da zarar bakin ta ya buɗe shikenan maybe ta rasa Saheeb ɗin na har abada kenan because in har yayi realizing cewa she has been blackmailing him for long toh ba ƙaramin zafi zai ɗauka da ita ba sai dai ta kasance cikin matsalar ita ɗaya
Sannan a fanni ɗaya tana fama da health condition ɗin ta,dan duk da tayi stopping maganin da take sha completely,babu abinda ya sauya game da lfyr ta,yanzu tana normal anjima zata rikiɗe kamar ba zata yi rai ba...
In ta zauna takan ji mamakin yadda ita Muhibba Hamida ke wa gashin ƙuma da mummuƙe,tana ganin Hamida is too small for her to handle amma ashe mightiness da Hamida ke da shi ya sha gaban tunanin ta...
Dai dai da pretence ɗaya in Muhibba tayi Hamida na wurin toh sai ta razana ta da kalamai masu tsoratarwa dan Hamida gani take yadda fifi ta dawo mata da annashuwar ta rayuwar ta wic is her husband,toh duk wani abinda zata mata a yanzu bai biya fifin ba shi ya sa take dagewa da strength ɗin ra take sokawa Muhibba mgn cikin mgn dan ba zata yarda ƴar uwar ta ta cigaba da fuskantar cin zarafin kishiya ba alhalin ta san komai na kishiyar...
Ga Muhibba kuwa babbar regret ɗin ta a rayuwa shine yarda da tayi da Hamida har Hamida ta san sirrin ta yanzu gashi tana mata barazana,abin kan dame ta ba kaɗan ba...
_Thursday morning_
Duk suna zaune ana breakfast a part ɗin su Ammy as family,kowa cin abincin sa yake yi ba tare da ya tanka ba,sai da aka yi nisa sai Muhibba ta fara jin wani iri a jikin ta,sincerely tana jin pains kamar kullum but fear ɗin ta shine kar ta buɗe baki ta furta Hamida ta taso ta gaba akan she is lying,dan yau ɗin girkin fifi ne wacce ita duk wannan bidirin da ke faruwa tsakanin Hamida da Muhibba bata da masaniya all she is after shine rainon cikin ta da lfyr jikin ta kafin ranar haihuwar ta dan ta sani,Dr ya sanar da ita bai ɓoye mata ba akan zai yi wuya ta rayu in har tayi experiencing labour pains,but ya bata option akan ana iya yi mata surgery a ciro babyn in kamar saura satittuka kafin EDD ɗin ta but sai ta ƙi yarda ta ce tana so ta ji zafin da mahaifiyar ta ta ji a yayin da ta haife ta kafin ta bar duniya,sbd believe ɗin ta shine duk mace da bata san zafin haihuwa ba toh ba zata mutunta kyauta da baiwar da Allah ya mata ba na bata kyautar haihuwar,so she choose to undergo the labour pains...
Duk motsin Muhibba a kan idon Hamida har dai Muhibban ta gaji da mutsu mutsu ta tashi ta bar wurin,murmushi Hamida tayi ta cigaba da cin abincin ta yayin da ake tmbyr ko lfy ta tafi,Ammy ce ta tashi ta bi bayan ta dan duba ko lfy su kuma sauran suka cigaba da cin abincin su except Saheeb da ya bar abincin ya bi Ammy dan duba Muhibba bcoz yana da tafiya yau mai muhimmanci..
Kasa natsuwa fifi tayi sai ta tashi da ƙyar ta bi sa,a hanya suka haɗe sai ya ruƙo ta a jikin sa suna takawa a sannu har suka ƙaraso ciki...
Ganin Ammy a parlor tana ta kiran sunan Muhibba ya saka Saheeb tmbyr me ya faru nan Ammy ke shaida mai wai Muhibban ce ta ce ta tafi bata son ganin ta...
Abin ya ɓatawa Saheeb rai mahaifiyar sa ce matar sa bata son gani,so annoying sai ya ja ƙaramin tsaki,ya ce da Ammyn ta tafi bayan bata haƙurin da yayi,shi da fifi suka shige ɗakin fifin inda ya ɗau bag ɗin sa da ba zata iya ɗaukar mai ba,suka fito da ƙyar ta raka sa ya shiga mota,ya ɗan leƙo da kan sa ya manna mata kiss a goshi a sannan yayi waving nata ya tafi itama tana waving nasa kafin ta koma ciki cikin tafiyar ɗai ɗai tana mai jin kewar sa tun yanzu..
#Mamuh*37*
Rayuwa ta sauya sosai a cikin gidan dan komai na tafiya normal fiye da tunanin mai tunani,rayuwar farin ciki ne kawai ke wakana a cikin gidan..
Soyayya kam tsakanin fifi da Marshall sai abinda yayi gaba,har ga Allah basu taɓa tsammanin shaƙuwar su tayi ƙarfi haka ba da komai ya faru da ɗaya sai ɗaya ya ji alama a jikin sa..
Wasa wasa ƙauna mai ƙarfi ta shige su sosai,duk da fifi ta fi dangana kusancin nasu a matsayin shaƙuwar rabuwa dan ta san days ɗin ta are numbered already..
Yayin da shi Saheeb yanzu yake kuma jin soyayyar ta a ran sa sai dai bai da wani tym na nuna mata ɗumbin soyayyar sa gare ta sakamakon yanayin aikin sa da bai ba shi isasshen lkcn spending tym ɗin sa da ita ba..
Ita kuma gani take kamar rashin amincewa da ita da bai yi bane a zuciyar sa har yanzu ya sa baya wani nuna mata soyayya ƙarara yadda ta daɗe tana dreaming...
A rayuwar Muhibba kuma lamuran ta ta fawwalawa mai duka bcos komai ya tsaya mata cak,bata isa ta bugi ƙirji ta ce zata yi wani abu ba sai Hamida ta ɗora alamar tmby a behaviour ɗin ta..
Sannan Saheeb,ba wani daɗin sa take ji ba dan yadda take stressing nasa in suna tare ko kuma suna waya,abin dai sai a hnkl..
Hamida kuma da Khalid zaman su abij sha'awa dan tun wannan matsalar da suka samu bata kuma yarda wata kafa ta shiga tsakanin su ba,kullum tana kafa kafa da gudun zuciyar sa musamman in mgn ta kama irin ta argument ɗin nan,toh bata wani ja sai ta karɓi laifin dan dai kar su sami saɓani..
Khalid bai da wani complain sosai yanzu a rayuwa dan matar sa na masa duk wasu abin da ya kamata,haka akwai fahimtar juna sosai tsakanin sa da fifi haka nan ma tsakanin matar sa Hamida da ƴar uwar ta fifi..
Duk da tight schedule na Saheeb,hakan bai hana sa yin alherin da ya saba ba ga mabuƙata in buƙatar hakan ta taso ba,kuma yana ƙoƙarin sauke haƙƙoƙin sa as a husband of two wives...
Ammy da Hajja ba abinda ya fi masu wannan daɗi ganin kawunan yaran a haɗe,kuskuren da suka yi a baya ba su fatar kuma tafka wannan kuskuren ever again a rayuwar su,dan duk inda mutum ya kai ga hassadar sa toh in ya ga bond dake tsakanin family members ɗin nan toh dole ya kawar da kan sa dan relationship ne mai ƙarfi..
Cikin fifi na shiga watar haihuwar sa wato wata na tara,Ammy ta fara bata special care kusan yini take yi a sashen fifi,wacce tayi nauyi zama da ƙyar tashi da ƙyar,bata fuskanci matsalolin early pregnancy ba but yanzu da ta shiga last trimester ɗin ta sai ta ga kamar yanzu take fuskantar matsalolin early pregnancy ɗin..
Kama daga ruwan wanka,abinci,kula da ita,komai Ammy ke mata shi bcos Hamida have to take care of her husband as well,in aka bar ta da ɗawainiyar fifi da na mijin ta abin zai mata yawa,dalilin da ya sa Ammy ke kai kawo a sashen fifi kenan,moreover Saheeb is always busy a ƴan kwanakin sai da ƙyar ma take iya ganin sa kuma baya kwana a tare da ita,ko girkin ta ne ko ba nata ba dan Muhibba na fuskantar matsanancin ciwo mai barazanarwa ga rayuwar ta...
Ita dai fifi ta san musabbabin matsalar Muhibba but da yake ba saka kan ta take a lamuran ta ba,sai ta ƙyale ta maida hnkl ta ga nata health ɗin dan tayi alƙawarin kula da babyn ta har ranar da zata haifin babyn kafin ta bar duniya...
Fargaba sosai ke sabunta a zuciyar fifi a duk ranar da ta farka a sabon rana ta tuna kwanakin haihuwar ta matsowa yake which is equivalent to ranakun mutuwar ta dake gab..
Ba kasafai Saheeb ke bibiyar scanning ɗin ta ba wanda hakan ya bata damar ganawa da likitan ta secretly bcos shi Saheeb ya san ya damƙawa Khalid ne kula da lfyr ta