Showing 33001 words to 36000 words out of 101986 words
su a matsayin ƙanwar sa ta jini kuma twin sister ɗin macen da ya fi so a rayuwar sa..
Ana haka suna soyayyar su a ɓoye ba tare da sun bayyana ba akan suna jiran right time su kuma basu sani ba ashe iyayen nasu na hango masu wani abu ne daban..
A cewar Khalid,ranar da labarin ya riske su ne shi da Hamida suka hau nemar hanyar hana faruwar auren amma lokaci ya ƙure ba yadda suka iya sama da bariwa Allah komai dan in suka ɗaukaka maganar toh hankalin fifi zai tashi kuma ba lallai bane a yarda a bar su su mallaki junan su ba,shi yasa suka yi shiru kawai but ganin lokaci na ta gabatowa kuma ba lallai bane su mallaki junan su ba sai kawai suka yanke shawarar guduwa a rana bikin ba tare da sun bari an gano su ba dan kar a yi yunkurin nemo su ba tare da sun mallaki junan su ba..
A jiyan bayan gudun su ne suka tafi wani wuri aka ɗaura masu aure kuma yanzu da haka suna a matsayin mata da miji ne..
Yana rufe bakin sa hawayen dake maƙale idanun Ammy ya zubo Hajja kuwa kasa ko da motsi tayi sai Ammyn ce ta kalli Khalid ta ce da shi ya matsa mata ta ga fuskar Hamida,cikin sanyin jiki ya matsa mata sai ta ɗan tako kusa da ita ta tsaya ta ƙare mata kallo sannan ta buɗi baki cikin sanyi ta ce
"Ta ya aka yi ke kika fita kika bar gidan nan ba tare da mun sani ba"?shiru Hamida tayi daddy na kallon ta da sauraron ta,sai da Ammy ta kuma maimaita tambayar ta sannan Hamida ta ce mata
"Ammy a lokacin da ake ƙara yiwa fifi kwaliyya ne bayan an gama yi min nawa,toh na ga hankulan mutani na kan ta ana ta ɗaukar hotuna sai na ɗau hijabin ta na saka na janyo shi ya rufe min fuska,shine na sauko na bi hanyar ƙofar baya na fita a nan na ga yaya Khalid cikin wani taxi sai ya ɗaga min hannu na tafi na same shi muka tafi inda aka ɗaura mana auren toh a gidan limamin muka kwana ni na kwanta a ɗakin matar sa shi kuma ya kwana a ɗakin baƙi,sai yau da safe muka ɗau hanyar dawowa gida dan mu nemi yafiyar ku"!!kai ayar bayanin ta yayi daidai da isowar daddy gaban ta a harzuƙe abin da bai taɓa yin sa ba,ɗaga hannun sa yayi da nufin marin Hamida cikin ɓacin rai da raɗaɗin zuciya yayin da ita kuma ta runtse idanun ta tana jiran saukar marin dan ta shirya masa tuntuni..
Muryar fifi ne ya dakatar da daddy daga aiwatar da abin da yayi niya..
"Daddy dakata...,please"!!muryar ta a karye ta jawo hankalin sa abin da basu sani ba tun zuwar su Hamida gidan akan idon ta ne har kawo wannan warwararriyar bayani nasu duk tana ji kuma tana kallon su..
Ƙarasa saukowa tayi sai Khalid ya kawar da kan sa gefe Hamida kuma ta saci kallon fuskar fifi amma sai ta ga babu hawaye face tawakkali..
Riƙo hannun daddyn nasu tayi ta saukar tana girgiza mai kai alamar kar yayi komai ya bar shi kawai..
"Daddy babu abin da zaka yi da zai sauya destiny ɗin mu,ko ka manta jiya da kan ka ka min nasihar matar mutum bata wuce sa dan haka ƴar uwa ta Hamida ita ce matar yaya Khalid ba ni ba kuma Allah ya san da haka dan shi ya tsaro mana hakan a rayuwar mu dan haka daddy,Ammy da Hajja ku yi haƙuri abin da zai faru ya faru bamu isa mu sauya sa ba ok"?ta ƙarasa da murmushin dole wanda ya karya zuciyar Khalid sai ta kalle su ta ce da su
"Na taya ku murna ubangiji ya dawwamar da farinciki a rayuwar ku"!!tana kaiwa nan ta juya ta koma ciki,duk jikin su sai yayi sanyi fifi dake haba haba da mutani babu ruwan ta da damuwa dan ta san ko ta sakawa kan ta ba lafiya ce da ita ba,wai yau ita ce ta komo haka...
Kasa aiwatar da komai suka yi dan duk inda maganar kamun hankali yake Mufida tayi sa,hukuncin su ba komai zai gyara ba sai dai ya ɓata dan haka Ammy ta kalle su ta kuma tana girgiza kan ta kafin ta ce da su
"Sai ku tafi apartment ɗin shi Khalid ɗin Allah ya bada zaman lafiya"!!dama an gyare two apartments ɗin da na Khalid da na yayan sa Saheeb so amare kawai ake jira su tare...
Bayan Ammy ta gama magana ta juya abin ta daddyn su kam baya jin ganin fuskar Hamida bare ya mata fatar da Ammy ta masu dan haka wucewar sa yayi haka Hajja ta tashi itama ta bi su da kallon ta girgiza kai sannan ta wuce..
Ƙarshe komawa apartment ɗin Khalid ɗin suka yi inda suka tare a matsayin ma'aurata even though akwai matsalar family dake kan su hakan bai hana su raya daren ranar ba...
A fannin fifi kuwa wuni tayi cikin zugin zuciya da rarrashin kan ta wanda abin ya ishi su Hajja har Ammy ta ce mata
"Mufida ki ɗau shawara ta a ɗaura maki aure da yayan ku Saheeb dan kina buƙatar mai kula da ke fiye da wanda mu muke maki a yanzu duk da ya zo jiya amma ya koma immediately auren ku na iya faruwa in ya so daga baya in ya dawo sai kuyi assuming duties ɗin ku ko ke ki bi sa can inda yake kin ji"?Hajja tayi na'am da wannan shawarar dan haka ta gyaɗa kai ita kam fifi ba a hayyacin ta take ba sai ta saka murmushin dai mai galabaitar da zuciya ta ce
"Ammy duk yadda kika yi zaɓin ki daidai ne a gare ni kuma ni zan maki biyayya sbd nariga na rasa zabina har abada Don kuwa ko mutuwa hameeda tayi Khalid ya haramta ga rayuwata har abada,
Farin ciki da rayuwar auren danake fata da buri har abada na rasashi"!!?rungume ta Ammy tayi ba tare da ta bar hawayen idon ta ya fito ba tace"
Khadija da yardar Allah aurenki da SAHEEB sai kinyi kukan farin ciki domin saikin kasance cikin Mata masu Saar aure.
'dan juyowa tayi takalli hajjn idanuwanta na cikowa da hawaye tana maidawa tayi murmushi mai tsananin ciwo ahankali can qasan maqoshi ta furta"
Mai matan???
Nida bantaba Sharing komai arayuwataba sai iyayenmu shine yanzu zance cikin tsofi muna gogayyar miji nida matarsa.
Har dare suna tare da ita suna bata magana da ƙyar dai bacci ya ɗauke ta,Ammy ta sanar da daddyn su tunanin da shawarar datayi da alhaji Abbas wani qaninta namiji daya rage Mata shima ya manyanta sosai
Akan mganar auren saheeb da fifin
ya ce in dai ta yarda shi bai da matsala Dan shima kam zaiso auren fifin da saheeb dama tun farko shi sukaso hadata dashi Amma ganin yanda take da Khalid yasa sukace shi din sbd ganinsu so ne atsanakin nasu Ashe ashe,
albarka Hajja ta saka mai dan yayi jarumta da tawakkali..
Washegari a cikin gida misalin ƙarfe goma na safe aka ɗaura auren MARSHALL MUHAMMAD SAHEEB Maƙarfi da KHADIJA NUHU MANDE ɗaurin auren da aka yi sa cikin shiru ba tare da hayaniya ba ko gayyata dan basu buƙatar kowa sai su...
A ranar bayan an ɗaura auren Mufida ta ƙulle kan ta a ɗaki ta sami damar fitar da damuwar zuciyar ta dan kuka tayi sosai har sai da numfashin ta ya rinƙa sama sama sannan ta sararawa kan ta ta watsa ruwa ta fito da alwala tayi nafila raka'a biyu tayi addu'ar da zata yi sannan ta kwanata bisa sallayar.
Tunani takeyi aranta gameda yanda rayuwar ta juya cikin sauri,
Itace da auren tsohon datakeyiwa 'yaruwarta maganar aurensa,
Shin ita wane farin ciki ko Jin dadin rayuwar aure zata samu a auren Wanda ya tsofeta?
QADDARA TA RABATA DA WANDA TAKE TUNANIN SHINE ABOKI MAHADAR RAYUWARTA,
MIJINDA 'YAR UWARTA DASUKA FITO CIKI DAYA,
RANA DAYA,
AWA DAYA MINTINA BIYARNE A TSAKANINSU ZATA AURA AURENSA YADAWO KANTA BAYAN TANA TUNANIN BATADA WANI ABOKIN RAYUWA KAMAR KHALID,
WACE QADDARACE WANNAN?
SHIN MENENE MAKOMAR RAYUWAR AURENTA DA WANDA HARYAU BATAGA KALARSABA.
Ahankali ta rintse idanuwanta dasuka fara bushewa da kuka tana Kiran sunayen ubangiji sbd yanda zuciyarta ke zafi da nauyi.
a nan bacci ya ɗauke ta dan ta sami sassaucin cunkushewar zuciyar ta..
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*15*
Da safe aka kawo abinci sashen su Hamida daga Hajja kuma saboda Khalid ba dan Hamida ba dan halin da Hamida ta nuna a shekaranjiya ya saka Hajja jin wani iri tana mace amma tunanin ta irin na da namiji har yau abin bai bar kan ta ba..
Bayan an kawo abincin a ajiye masu aka fita dan basu tashi daga bacci ba sai wuraren 11am tun sallar subhi da suka yi suka koma sai yanzu suka farka kenan an yi ɗaurin auren Mufida da Saheeb ba tare da an gayyace su ba musamman shi Khalid ɗin..
Cikin shigar atamfa riga da zani haɗe da babban mayafi Hamida ta fito ta tarar da angon nata yana jiran ta sun je su gaida su Ammy su kuma yiwa Hajja godiyar abincin da ta aiko masu da shi dan sun san dama Ammy na fushi da su ƙila sai anjima zata saurare su..
Shima Khalid din a yau yayi shigar alfarma ya fito a angon shi half kaftan da hula shirin da bai taba yi ba kenan tunda ta san shi dan ko a ranar bikin nasu wani irin kaftan ya saka da bai fiddo sa ba..
Murmushi shimfiɗe saman fuskar su suka nufi sashen Ammy inda ta amsa gaisuwa kawai ba tare da ta kuma tanka masu ba har suka ƙaraci zaman su suka wuce zuwa sashen Hajja da tunanin ita zata tarbe su da sanyin fuska tunda ta aiko masu da abinci sai dai ba yadda suka yi tsammani bane dan yadda ta ɗaure fuska ta kawar da kan ta gefe kaɗai ya tabbatar masu har yanzu fushin take yi da su kuma fuskar su kan sa bata jin ganin sa..
Tashi suka yi suka nufi sashen daddyn su,inda aka sami bambanci kenan dan shi ya amsa gaisuwar tasu ba yabo ba fallasa kuma ya masu fatar alkhairi haɗe da sanar da Khalid batun ɗaurin auren da aka yi na ɗan uwan sa da ƙanwar sa yana mai ce da shi ya kira ɗan uwan nasa ya masa fatar alkhairi..
Ko da Khalid ya ji wannan zance babu inda bai yi sanyi ba a jikin sa dan bai yi tsammanin farat ɗaya za a ɗau hukunci mai zafi haka ba,yayi tunanin za a ba Mufidar damar zaɓar abokin rayuwar ta ne dan har ya fara tunanin haɗa ta da wani abokin sa na kusa mai ɗabi'u kusan irin nasa amma an riga an gama tunda aka aura mata yayan sa sai dai matsalar shin tana son yayan nasa kuwa ko dai haɗin iyaye ne?
Tambayar da ya rinƙa kai kawo kenan a zuciyar sa amma ya san bai da wannan ƙimar na tambayar daddyn dan laifin sa na nan bai goge ba da saura ko da zai gogen amma sai ya ɗau lokaci shi ya sani,wannan dalili ya sa ya ja bakin sa yayi shiru har daddyn ya gama nasihar sa a gare su ya sallame su suka fita bai bar tunanin ya lafiyar fifi ba kuma a wani hali take...
Suna fita Hamida ta ja hannun sa zuwa old room ɗin ta tayi saurin saka lock ta cire mayafin ta da dama ya ishe ta sbd rashin sabo..
Dariyar ta da ta rinƙa dannewa ne ya fito fili sai da ta dara har tana riƙe cikin ta mijin nata na kallon ta sannan ta matso kusa da shi ta rungume sa tana mai cigaba da ƙarasa ƴar dariyar da ta rage mata..
Shi dai Khalid bai san me ya saka ta dariyar ba kuma hankalin sa da tunanin sa na ga fifi ko a wani hali take,wannan dalili ya sa bai ce mata komai ba har ta zo ta rungume sa sannan ya sami damar tambayar ta..
"Me ya faru ne love kike dariya haka tun ɗazu"?jujjuya kai ta shiga yi tana murmushi sannan ta ce
"Miji na dariya ta manufofi biyu gare ta,na farko aurar da fifi da aka yi ga wannan tsohon da aka so a haɗa ni da shi,na biyu kuma murnar samin ka da nayi a matsayin miji na da na rasa ka in har a ranar nan an aura maka fifi ni kuma aka aura min wannan tsohon amma Allah na amfani da zuciyar mutum ne ba kalaman sa ba shi ya sa ya bamu ikon mallakar junan mu a matsayin ma'aurata bai bar mu mun zalunci wani ko wata ko wasu ba ya bar mu tare dan Allah kaɗai ya san abinda ke zuciya ta da ban mallake ka ba miji na,na godewa Allah da ya bani kai kuma ya mallaka min kai please don't ever leave me i will die if you forsake our love"!!da ɗan muryar kuka ta ƙarasa maganar dan wani irin azababben so ƙauna da shauƙin mijin nata dake shigar ta bata san ya zata iya rayuwa a doron ƙasar nan ba tare da shi ba..
Khalid dake sauraron ta cikin mamaki da jimami sai ya kasa faɗin abin da yayi niyar faɗi musamman da ya ji yanayin muryar ta ya sauya kamar kuka take yi sai shima ya ƙara tightening hug ɗin yana mata alƙawarin duk wuya duk runtse suna tare babu mai raba su sai hukuncin ubangiji..
Cikin zurfi a tunanin maganarta cikin ransa nazarin maganarta,
Shin sunkuwa San waye Marshall dasuke kiransa da tsoho?
Tabbas basuda masaniyar waye Marshall Amma bazai fadaba zai Bari su gani a idanuwansu.
Kusan mintuna sama da biyar suka kwashe suna a haka sannan ya raba jiki da ita ya ɗauko mata mayafin ta ya yafa mata dan su koma sashen su su ci abinci..
Har sun fito hannun sa cikin nata sun zo giftawa sai ta ji zuciyar ta na raya mata yin wani abu a ɗakin da suka wuce yanzun nan dan haka ta ɗan ja da baya tana ce ma Khalid
"Baby ka tafi ina so in gana da ƴar uwa ta zan zo in a jiffy"!!shi babu abinda ya zo mai rai jin ta ce zata gana da ƴar uwar ta sai ya gyaɗa mata kai ya ce zai raka ta amma ta ce ta yafe mai ya tafi ita zata zo daga baya.
Sai da ta tabbatar ya tafi gabaɗaya sannan ta koma da baya ta nufi ɗakin fifi bakin ta ɗauke da sallama sai dai bata ji an amsa ba so ta tura ƙofar ta shiga..
Hango fifi tayi kwance saman sallaya tana bacci fuskar ta ya ɓaci da hawaye sai tayi murmushi tana jin wani sanyi a ran ta..
Ƙarasawa gare ta tayi tana taku ɗai ɗai har ta zo ta tsuguna tana ƙare mata kallo,tunowa tayi da ranar da fifin ta kawo mata ziyara ta gama tsokanar ta sannan ta gaya mata wai tausayin ta take ji duk kyawun jikin ta wannan tsohon ne zai mora,sai tayi murmushi haɗe da lumshe idanun ta sannan ta cigaba da maganar zucin ta tana faɗin yanzu wa yayi asarar kyau da da surar jiki?ke Mufida dan ke kika ƙare da tsohon da kike murnar ni zan aura oh na tausaya maki dama haka rayuwa take yau kayi dariya gobe ko anjima ka yi kuka...
Ina tsananin sonki yar uwata fiyeda komai da kowa a duniya
Sai zuciya Batada qashi bansan ya zanyi na Hana zuciyata tsanarki ko kishinki ba sbd sune sukeda haqqin sakamin qiyayyarki yar uwata duk da nasan ba laifinmu bane Amma we'll have to pay the price for abinda iyayenmu keyi,
Zan nuna baqin cikin danai shekaru Ina boyewa tareda dannewa Ina qunsa kodan Su girba abinda suka shuka
I'm sorry my Fifi.
Kuma murmusawa Hamida tayi tana sauke ajiyar zuciya haɗe da furzar da iska daga bakin ta..
Tapping bayan fifi tayi ba tare da ta ce mata komai ba har sai da fifi ta buɗe heavy eyes ɗin ta ta ɗora su kan fuskar Hamida dake ta baza murmushi..
Tashi zaune Mufida tayi tana gyara hijabin jikin ta sannan ta zauna bayan ta matsa nesa kaɗan da Hamida..
Kallon behaviours ɗin ta Hamida tayi sai ta taɓe baki tana ɗan yin fari da ido unexpectedly sai kalmar zuciyar ta ya fito sarari..
"Na ji an ɗaura auren ki da...yaya Saheeb wai ko"!?ɗago kai Mufida tayi ta kalli Hamida sai ta ga sai murmushi take ta yi babu alamar damuwa a fuskar ta..
"Toh nothing big,kawai zuwa nayi na musamman dan in maki fatar alkhairi da samin miji irin naki wanda ban taɓa gani ba tunda nake a rayuwa ta ina maku fatar samun zaman lafiya mai ɗorewa har ƙarshen rayuwar ku"!!tana kaiwa nan sai ta miƙe tsaye ta juya leaving fifi to be staring at her kamar stranger..
Ɗan dakatawa tayi bata fitan ba sai ta juyo irin surprisingly ɗin nan ta kalli fuskar fifi,cikin son ƙure haƙurin ta ta ce
"Oh na manta,kina cikin jimami ne shi ya sa kika kasa yi min ni fatar alkhairi da nawa auren amma ba komai na fahimta ai na san ba zaki min baƙin ciki ba da nawa mijin dan bai zamo namijin da ya kwana biyu kuma second hand ba,jini ne ke yawo a jikin shi sabo fil yana ji da ƙarfi dan akan gaɓar sa yake lafiyayye ne ya haɗa duk abinda nake burin miji na na aure ya haɗa and guess what?i have been appreciate him for everything,though na tausaya maki ƴar uwa ta da kika yi rashi rashin da har abada kin yi