Showing 9001 words to 12000 words out of 101986 words
furta
"Hamida ki yafe ni ban nuna maki hanya zuwa ciki ba ko?kiyi hakr yar uwar kin nan is so attractive,waidama dagaske ku yan biyu ne?dana ganta hankali na duk ya koma gare ta shi yasa na manta in nuna maki hanyar shiga cikin gida im deeply sorry"..
Wani fushi me hade da Faduwar gaba ne ya riske ta toh me yake nufi da yar uwar ita is attractive kuma?mswww fifi fifi fifi and ffi again,ji tayi kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ga bata nan cikin gidan...
Janyo mata trolley din ta yayi zuwa ciki yana mai dan jan ta da hira,gabadaya zuciyar ta na ayyana mata cewa kar ta sake Khalid ya kufce mata sabida fifi wannan kuma nata ne ba zata barwa Mufida shi ba,dan duk cikin su shi kadai ya dan nuna ma ya san da ita...
Wani babbar bacin rai dataci karo da shi kuma shine ganin hanyar dakin da aka kai ta nan kusa da wani new abandoned room da yake shiru shiru kamar babu kowa sai ita kadai...
Dannewa haushin ta tayi Bayan ta mai godiya garin boye damuwar tane yasa tayi saurin rufe kofar dakin da key ta jingina bayan ta da kofar tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya akai akai wasu zafafab hawayen kunci na diga,jin kamar zuciyar ta zai fashe at any moment ya sa ta dauko karamar jakar ta ta hau lalubar maganin da Dr Fatima Yonas ta bata wanda dama kullum in ta tafi ta fadi mata damuwar ta shi take bata ta sha,bude robar maganin tayi ta zuba guda biyu ta hau nemar bottle water din da ta sha a jirgi ta rage,tana ganin sa ta bude bakin murfin ta jefo maganin ta bi da ruwa...
Gadon dake gyare a dakin ta hau ta kwanta a kai idanun ta na kallon gefe daya hawaye na silalo mata har bacci ya dauke ta bata sani ba.
#Mamuh*_Mamuhgee_*
_*Zafafa biyar na kudine ka nemi wannan numbern ka biya kudinka ko katinka*_
07067124863
09032345899
*6*
A nan fannin su Fifi tunda ta shigo cikin dakin nata da ya sha kayan alatu taji sam takasa zama dan tamkar wata sarauniya haka aka tsantsara mata dakin sai da ta karewa dakin kallo ta yaba kyaun sa hade da maimaita kalmar "_wow cancadi"_.
Cire kayan jikin nata tayi ta nufi hanyar bandaki dan watsa ruwa,nan ma duk abubuwan bukata an tanadar mata wanda diya mace da ta amsa sunan ta mace yar gata ke alfahari da shi,haka tayi wankan a karkashin shower ta gama ta fito daure da fari kal din towel..
Sallah ta fara gabatarwa sannan ta hau kan kujerar gaban madubin ta,dama tayi tunanin jere cosmetics din ta gaban madubin ne amma zuwan ta dakin sai ta ga wadanda aka jere mata ma sun dame nata sun sha dan kuwa kaf babu cosmetics din da suka fito daga wani kamfanin kwalliya dake african
hatta jam baki da hoda duk products din La pariso ne daga kasar Persia hka komai suka fito ras dan a jeren su suke suffar su daban da na kasar nan..
Nan ma sai da ta yaba da kyaun koma ta kuma kara yarda da kaunar da ake mata a cikin zuri'ar nasu,lallai duk soyayyar da tayi tsammanin samun shi daga gare su ya wuce yadda ta tarar dan tun a wurin dauko su ta gasgata hakan..
Kwaliyyar ta ta cancanɗa mai daukar hankali dama akwai kyaun sai ga adon zamanin da ta dora a fuskar nata me sanyin haske..
Duk dakin nata ya gama amsawa da kamshin designers perfs din ta na matron daga haka ta saka suturar ta irin ta kullum bata canza ba wato shigar kananan kaya riga da wando ta kamfanin Dior sai ta dau kimono deep red ta dora a sama hade da saka head hoodies kalar rigar cikin da ta saka,flat foot wear ta saka ta dauko wayar ta cikin kazar kazar da karfin jiki ta fito da nufin tambayar inda yar uwar ta take..
Kicibis tayi da Khalid da shima fitowar sa kenan da zumar zuwa duba ta,anan suka shiga zagowa dan su hade a hanya wanda yake half way a balcony din gaban dakin hamida...
Dakatawa yayi ya tsaya kusan inch biyar da inda fifi take yana mata kallon da bai san yana yin sa ba
kwata kwata bai san yadda aka yi yake kasancewa a zauce ba musamman a duk lokacin da ya hada ido da ita...
Kasa karasowa kusa yayi yana tsaye ita kuma ganin sa sai da ya saukar mata da kasala domin kuwa white shaped long sleeves shirt ne a jikin sa mai two black straight line mai dauke da botara masu matukar tsada
wannan rigar ta shi ta bayyana asalin ginannen jijiyoyin muscles dinsa dan dama bai saka botins din duka ba ya bar na sama da mai bi mai a bude,kusan quarter daga sirrin faffadan kirjin sa a waje suke
ga wani irin glowing da haske da bared chest din nasa ke yi,kan sa ya sha gyara da mayuka har fiye dana dazu da ta gan sa..
Tace.."Ya rabbi"abin da ta furta kenan a zuciyar ta ganin kawai ya amsa sunan namijin da ta dade tana mafarkin mallaka a matsayin saurayi kuma miji a gare ta dan sak yanayin jikin sa bai da doguwar bambamci da Ameed abokin ta kuma dan Dr Fatima Yonas a germany...
Kasa boye abin dake zuciyar ta tayi kawai ta sanar da shi ya mata cikin sakin fuska dan ita bata iya boye abin da ya birge ta ko ya bata mata rai..
"You are looking good mr Khalid"
..wani dadi ya ji a ran sa yayi ado ta yaba dan dama dan ita yayi adon kuma kwalliya ta biya kudin sabulu data yaba,jin kan sa yayi kamar yau din rana ce ta musamman a gare sa...
Karasowa yayi gare ta yana mata murmushin manyan maza masu ji da kan su akan gabar su..
"Na gode Khadijatul Mufida"!ya fada hakan yana mai karkata kan sa wanda ita kuma ta ji kamar babu wanda ya iya furta sunan nata sama da shi
dan babu mai kiran sunan nata a haka gabadaya sai dai ko Mufida ko Fifi ko Fifi Mande..
Tambayar sa tayi inda yar uwar ta Hamida take,shi kan sa sai yanzu ya tuno da Hamidar sai ya mata jagora zuwa chan dakin Hamidar inda yake da doguwar tazarar gaske tsakanin matakakan dakin ta da na yar uwar nata..
Shi ya rinka yin sallama amma ba'a amsa ba kuma ya san bai gan ta ba a nan kasa tun bayan barin sa dakin da ya kawo ta mata kaya..
Kallon fifi yayi yana fada mata cewa hamida bata amsa ba sai fifin ta matso adame kusa da kofar ta mannu da nufin yin sallamar da kan ta, nan ma kamshin turaren tane ya kusan sumar da khalid a tsaye wani sanyin yanayi yaji wanda har cikin zuciyar sa yake jin dirinsa,bai san menene yake ji game da ita ba amma yana mutunta wannan abin ko ma menene shi...
Haka fifi ta rinka doka sallama wani na bin wani kusan sau hudu but babu amsa daga ciki,nazari tayi ta kira ta da pet name da ta saba kiran ta da shi koda zata gane itace dan haka ta hau kiran sunan _"Hamee"hamee,hamida_
Sai shiru nan ma duk haka bata sami amsa ba..
Da rashin jin dadi a fuskar ta ta juyo ta kalli Khalid da shi ba sunan Hamidar ko amsa sallamar ta ke gaban sa ba illa ita mai yin sallamar da kiran sunan wato ita kanta fifi..
Cikin matukar yanayin damuwa Tace hamida
"Bata amsa ba ko bacci take yi ne"?kallon ta yayi yana fadin.
"Kila baccin take yi"!!gyada kai tayi tana dan juyi tana dada kallon kofar daga haka har suka juya zuwa kasa nan main parlor din gidan inda a nan Mufida ta ga tsantsar gata dan abinci kala kala aka baza a babbar dardumar cin abinci duk dan saboda ita..
Farinciki ne ya buwayi zuciyar ta ta rasa ina zata saka kan ta da irin wannan soyayyar da ake nuna mata duk ita daya...
Ammy ce ta taso cikin fara'a ta tarbe ta tana mai yaba kyaun da tayi hade da yaba kamshin ta ita kuma ta rungume Ammyn tana fadin
"Ammy ai duk ke ce silar kyaun da nayi dan kaf kayayyakin dake gaban mirror din daki na ban taba ganin irin su ba ko da nayi amfani da su sai na ga ashe ni din bakuwa ce a fannin kayan ado,Ammy nagode da soyayyar ki gare ni na san ko da a yau na mutu na bar duniya na ga masoya na kuma na yarda da kaunar da suke min suke kuma nuna min"!!
jin kalmar mutuwar da ta kira sai da Ammy ta ji bugun zuciyar ta ya dadu dan sam bata son jin wannan kalmar bare har ya kasance ya alakantu ne da fifi...
Dada rungume ta tayi tana danne hawayen dake kokarin fin karfin ta ya fito murya na rawa ta ce.
"A'a Mufida ta kidena cewa hakan ba zaki mutu ba har sai kin ga yayan ki,sai kin more su mu ma mun gan su,tare zaki rayu da yayan ki har girman su,da yardar mai rahama yayan ki ba zasu yi maraicin rashin uwa ba kamar yadda ke kika taso cikin ta ba Allah ya jikan mahaifiyar ki"..
Hajja da ta rigada ta ta fara hawaye tun bayan jin kalmar mutuwar da fifi tayi sai ta kasa hakura ta yi magana..
Tace"A'a Mufida ba yanzu zaki mutu ba kuma bana son kara jin kalmar nan ta fito daga bakin ki"..
Kallon ta fifi tayi ta kuma kallon Ammy da yanzu ta raba jiki da ita,ta kuma juyawa ta kalli Khalid da shima ya dan shiga wani yanayi sai ta basar da zancen duk da ta san ita din ba mai tsawon rai bane rayuwar ta mai iya datsewa ne any moment kuma ita so take ta saka murmushi a fuskokin kowa kafin ta rabu da su ba wai ta rinka saka su a damuwa ba,abaxata ta hau yin dariya tana fadin
"Ammy,Hajja, Khalid kun bani dariya,ashe haka kuke?wasa fah kawai nake maku dama gwada ku na yi dan in ga yawan son da kuke min kuma na gani,ta gwalo ido cikin wasa"sai dai Hajja ban gane miki bafa,fada min gaskiya hala dama kin matsu ne in tafi in baki wuri dan ki kwace min saurayi"?
da sigar tsokana tayi maganar..inda Duk ta saka su dariya ba kadan ba
duk da akwai kalmar rabuwar nan dai a wannan zancen nata but ta saka su nishadi..
Ganin duk sun sake ran su ya sa itama ta taya su dariyar har dai suka zazzauna aka hau serving nasu abinci..
Sosai fifi ta ci abincin dan ba zata iya tuno rabon ta da cin abincin gargajiya irin ta kasar ta Nigeria ba sai yanzu kuma da yake abincin da cikakkiyar soyayya aka bata shi sai ta ji kawai kaunar family din nata na kara ninkuwa a zuciyar ta fiye da da kafin ta san su in person..
Da suka gama cin abincin ne Khalid ya mata tayin fita zaga gari kafin dare,ai kuwa bata ja da tayin sa ba dan ita kan ta ta fi son haka,ko ba komai ta san zata fara ajiye tarihi da memories masu wuyar mantawa musanman tare da dan uwan ta kuma wani bangare na rayuwar ta wanda bata san ya zata fassara sa ba..
Da kazar kazar din ta ta tashi daga kan dardumar tana mai yi ma Ammy da Hajja godiyar saka ta jin ita din wata ce a gare su hade da yi masu sallamar sai sun dawo..
Sosai Hajja ta rinka gargadin Khalid akan kar ya kuskura yayi tukin ganganci da zai jijjiga jikin Mufida,shi dariya ma Hajjan ta bashi ganin yadda duk hankalin ta ya bi ya tashi akan kar a taba lafiyar takwarar ta,ita fifi in ta nata ne bata ki a yi ta rough driving din ba dan ta fi son hakan sbd ya fi dadi da saka annashuwa a gare ta a kuma zuciyar ta...
Juyawar su kenan da nufin fita Hamida ta bayyana a gaban su tana saukowa daga sama..
Tun daga kan babbar dardumar idanun ta ya nuna mata har an yi family lunch an gama kuma cikin nishadi aka yi sa dan ga yadda abinci ya barbarzu alamar mutani daban daban ke ba mutum daya abincin..
Babu inda hankalin ta ya kai sai ga fifi,wani abu ne ya taso ya tsaya mata a kirjin ta rasa abin yi tayi...
Idanun ta ne ya dawo kan yar uwar ta da mutumin da ta jima da mai masauki a zuciyar ta,bayan an gama cin lunch ba tare da ita ba yanzu kuma fita za'a yi ba tare da an damu da nemar ta ba...?
Idanun fifi ne ya sauka kan Hamida da ta tsaya cak a fourth to the last step ta kasa karasowa tsabar daurewar kan da ta tsinci kan ta a ciki...
"Hamee tun dazu nake ta nemar ki sai da fa Khalid ya zo ya nuna min dakin ki muka zo tare,kinyi bacci ne? munyi ta yin sallama baki amsa mu ba hope you are ok dan yanzu fita zamu yi ni da Khalid ya ce zai kai ni in zaga gari kafin dare,na san ba zaki taho ba ko na ce ki inaso dan haka mu sai mun dawo,go ahead am sure you will love the lunch da Ammy ta hada mana....na gargajiya ne mai dadi,just enjoy har mu dawo ok sis"!
karasa maganar tayi tana mai dan buga kafadar ta alamar comforting din ta take son yi cikin nuna tsananin damuwarta akan ta..
Hamida kuwa batace uffan ba
Bayan haka fifi ta juya ta fita Khalid na bin ta a baya suna magana kasa kasa suna dariya wanda ya kuma kunna wutar kiyayyar fifin a zuciyar Hamida...
Su Ammy dake daga cikin parlor din ne ta tsaya kare ma kallo,cikin kitsa maganganu ganin wai duk wannan abin da ya faru babu wanda ya lura da ita kuma ba a aika a kirawo ta ba haka suka ci abincin su cikin farinciki,ita kadai ce ake wa wariyar launin fata dan bata cancanci kaunar kowa daga cikin family members din nata ba,wannan bakin ciki da me yayi kama...?
Fasa saukowar tayi kawai ta koma dakin ta duk da haka bata sami natsuwar zuci ba sai kai kawo take ta yi a karshe zuciyar ta ya saka mata ta tafi dakin fifi dan ganin ko nan ma an nuna bambancin kamar ko da yaushe..
Fitowa tayi ta nufi hanyar babbar balcony din dake upstairs da nufin tambayar ma'aikatan gidan dakin fifi..
Tana tafe ta ga gilmawar wata sai tayi saurin kiran ta ta tambaye ta dakin Mufida ai kuwa ta kai ta har dakin inda da shigar ta ta ga abin da ya girgiza mata zuciya da ruhin ta dan in akwai aljannar duniya toh dakin fifi ya dace da wannan sunan...
Komai yayi ne kusan dukan abunda take muradi su aka zuba a dakin fifi abin nan ya sake tayar mata da hankali..
Danne damuwar ta tayi ta fita a dakin ta koma nata dakin,bata jin marmarin dandanar abincin gidan ma dan haka cookies din ta da ta zo da shi a jaka ta fiddo ta hau ci tana jin ciwo a zuciyar ta..
A haka tun tana dannewa kar tayi kukar bambancin da ake nuna mata har ta bar hawayen suka zubo,shaidan kam sai dada tunzira zuciyar ta yake yi ta rinka saƙe saƙe kala kala akan yar uwar nata daga baya ta dauko laptop din ta dan rage zugin da zuciyar ta ke mata dab wayar ta kam bai da amfanin komai dan in dai wai dan a kira ta ne dan jin ya take bayan ta bar kasar germany toh tasan yaudarar kan ta zata yi dan ba kiran nata za a yi ba
Ita kanta ta san izuwa yanzu favourite din kowa da kowa ta amsa kira ya fi sau a kirga daga saukar su hala har yanzu da suka fita da mutumin da take jin shi a zuciyar ta ma hakan ne...
Tunowa da yanayin farincikin da suka fita ciki dazu ya sa ta ji kamar ta masu mummunar addu'a amma haka ta daure ta maida idanun ta ga kallon da ba wani gane shi take yi ba dan hankalin nata ba a kan kallon yake ba...
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*_zafafa biyar na kudine ka nemi wannan numbern ka biya kudinka ko katinka_*
07067124863
09032345899
*7*
fitar su agidan Khalid yafara tukinsa a hankali gudun kar ma wani ya gani aje a fadawa hajja,yana hawa kan titi ya kalli fifi ya ce da ita ta gyara zamanki da kyau yan mata zamu fara tukin mu ko?.. Murmushi suka maida ma juna
Ita a dadin ta dan dama hakan ta fi so,tun daga haka sai ya kara speed din motar yana tukin juye juye in yayi sai ya kalle ta ya ce speed din yayi sai ta girgiza kai suna dariya ahaka sai ya kara gudun,a haka a haka ya rinka kara speed har ya kure zuwa last speeding point din inda fifi sai ihun murna da dadi take ta yi dan tunowa takeyi da last drive din su a germany tare da kawayen ta.
Wurare da dama ya kai ta ya kuma bata dukkan lokacin sa cikin sukuni,bai yi rushing din ta ba komai a natse ya bar ta tayi,tun daga gidajen ganin kayan al'ajabi da aka bar su su bude a wannan lokacin dan har wuraren shakatawa sai da Khalid ya kai fifi kuma bai gajiya duk wani tambayar da zata mai akan abin da ta gani haka zai bata cikakkiyar amsa mai gamsarwa...
Su da suka ce zasu dawo kafin magrib sai gashi sai 7:24pm dai dai Khalid ya ja birkin motar da suka fita da shi.
Hannun sa cike da shopping bags da packaged eatery leathers duk na fifi Khalid dinne ya siyo mata dan kawai ya faranta mata..
Dawowar su yayi daidai da lekowar Hamida ta windown ta dan tun