Showing 57001 words to 60000 words out of 101986 words
cin abincin sa cikin kwamciyar hankali banda fifi da tsananin tsarguwa ya gama addabar ta kamar wacce tayi wani illegal act..
Sarai ya fuskanci halin da take ciki na rashin sakewar ta amma abin mamaki sai ya ɗaure fuska ya ƙi tashi ya ƙi yin hira da su Ammy ko dannita ta sami chance na cin abincin..
Sai da ta ga bai da niyar tashi a wurin kuma ba zai yi mgn da kowa ba bare ta sami damar cin abincin sai ta yi shahada ta sunkuyar da kan ta ƙasa tana cin abincin a hankali..
Ko sau ɗaya bata ɗago kan ba bare ya takura ta ta kasa samin natsuwar cin abincin..
Sai da ya ga ta ɗan sake tana cin abincin sannan ya matsar da nasa plate ɗin yana goge baki haɗe da faɗin
"Ammy zamu fita ni da Khalid zamu duba site ɗin nan na ga kamar basu saurin aikin ne"sai Ammy tayi murmushin manya tana faɗin
"Allah ya kiyaye min ku kai da shi ya sa ku je lafiya ku dawo lafiya,ka kula kar ka bari Khalid yayi tuƙin ganganci da kai dan ya saba ka ji"!?gyaɗa mata kai yayi yana tuno ranar da suka fita shi da Khalid ɗin irin tuƙin da ya rinƙa yi da shi...
Har ya juya zai tafi Hajja ta saka baki tana faɗin
"Ga takwara ta kawai ku tafi tare da ita ka rabu da Khalid itama tana buƙatar buɗe ido rabon ta da fita ya jima"!!bai juyo ba bare ya amsa shawarar Hajja,ita kuma fifi gaban ta ne ya faɗi ai da ta fita da shi gwara ta zauna a gidan,he is a matured man ba wani daɗin da zata ji ko ta fita da shi,ba sanin shi tayi ba kuma from all indications kamar moon face shi ya fi fitting nasa sama da murmushi toh ita ta yaya zata ji daɗin fita da shi?.tsintar kan ta tayi da faɗawa Hajja
"Ina da online review class by 10:30 da safen nan"!already 10:20am ne ssi ya dubi agogon sa ya ga lkc kawai girgiza kai yayi ya fice abin sa shi dama bai ɗau shawarar Hajjan da muhimmanci ba...
Kallon ta Ammy da Hajja suka yi,za su yi mgn ta tashi ta nufi hanyar sama,suka bi ta da kallo har ta shige,murmushin manya kawai suka yi suka ƙada kai musamman Hajja dake ankare da duk motsin su...
Juye juye kawai take ta yi a kan gadon tana jin yadda bugun zuciyar ta ke ƙaruwa sai dai bata san dalili ba..
Muryar Ammy ne ya saka ta tashi zaune ta dube ta,daga tsaye Ammy ta ce mata
"Baby mijin ki fita zai yi zuwa duba wani uncompleted building ɗin Abban su kuma ina tunanin sai dare zasu dawo dan ya matsu a kammala wurin kasancewar yanayin aikin sa ba sosai yake zama a nan ba kuma shi Khalid bai da wani isasshen lkcn zagawa zuwa wurin sai dai in shi mijin naki ya dawo sai ya tafi da kan sa,dan haks ina ga ki je ku gana kafin ya fita ba dawowa da wuri zai yi ba sai dare"!!abin mamaki abin dariya me ya sa Ammy ta sauya mata ne haka da yawa?kalmar "mijin ki mijin ki" duk ya addabe ta ta gaji da jin sa daga bakin Ammy sannan Ammyn ta daina bata kula ta musamman kamar yadda ta saba a baya yanzu sai dai sama sama in ta ɗan ɓata fuska sai ta rarrashe ta hakan bai hana anjima ta kuma janye jiki da ita ba...
Bata saba da yi ma Ammy musu ba sai kawai ta tashi ta nufi hanyar fita amma ta ji ƙarar abu kamar ana fetsa perf,juyawa tayi sai ta ga Ammy gab da ita tana fetsa mata turare tana murmushi,rasa ta cewa tayi sai itama ta maida mata murmushin daga haka ta fita abin ta...
A natse take takun ta har ta iso part ɗin nasa tayi sallama ta shiga,bata tsaya a waje ba ta ƙarasa ciki ta kuwa yi sa'ar samin sa a parlor yana zaune yana sipping wani abu a matsakaicin cup sai ta mai sallama ya amsa yana kallon ta..
Ganin yadda ya tsare ta da kallo sai ta gaida shi,abin sai ya ɗan bashi dariya but bai bayyana dariyar ba ya gyaɗa mata kai alamar ya ji kuma ya amsa..
Tana tsaye bata iya ce mai komai ba shi kuma bai yi offering nata kujerar zama ba,for a moment sai ya dube ta a fizge ya kawar da kai ya ce
"Lafiya"?sai ta dube sa cikin sanyin murya ta ce
"Eh"!!kallon ta yayi sai ya ƙyale ta tana tsayen shi kuma yana sipping abin kofin sai da ta gaji kuma ta zauna abin nata kamar har da yarinta a ciki ya faɗa a zuciyar sa,if not ta yaya mutum zai zo ya tsaya maka a tsaye ya ce ba komai ya kawo sa ba amma yana nan tsaye sannan yanzu ta zauna bai ce mata ya bata dama ba..
Muryar sa ne cikin sigar gar da gar babu wasa ya ce
"Ke,shekarun ki nawa"?sai tayi mamaki ta ɗago kai ta dube sa ta ga babu wasa a tare da shi kawai ta ce
"20"!!scoffing yayi na mamaki yayi tsammanin ta kai irin 25years ɗin nan ma dan mantawa yayi da lissafin sa yana ta ɗaukar ta to be a 25years old girl..
Ganin abinda yayi sai ta ayyana a zuciyar ta hala ta girma ne da yawa shi ya sa ya bata wannan look ɗin mamakin sai ta ji ina ma 19 ta ce mai dan ya san ba babba ba ce ita ɗin..
Bata san ya aka yi ba sai tsintar kan ta tayi da sha'awar tmbyr sa haka kawai bakin ta ya furta
"Kai fah"?sai ta ga ya kalle ta rai a haɗe yana ajiye kofin hannun sa,sai ta ji tsoro dan yanzu ta tuno abinda bakin ta ya furta..
Tashi zata yi sai ya umarce ta da ta zauna kar ta matsa,haka ta koma ta zauna sai ya kafe ta da ido har ta ji ta tsargu fiye da misali kamar ba zai ce komai ba sai ya ce
"Are u asking for my age"!?ya tmby yana ɗage gira ɗaya sama sai ta ji fargaba ya tsirga ta ta kasa amsa mata,yana kallon ta yana jiran amsar ta amma bata amsa ba sai ya murmusa ya ce
"Am 45"!wani irin firgita fifi tayi tayi saurin tashi tsaye tana rufe bakin ta idanu a waje ta dube sa shi kuma sai ya tsaya yi mata kallon mamaki menene na firgita?..
"What?me ya faru"?saurin girgiza mai kai tayi tana juyawa da zumar fita,ai ko ya taso ya juyo da ita da sauri suka fuskanci juna,hannun ta rufe da bakin ta har yanzu,hannun sa ya saka ya cire nata hannun daga bakin ta ya zama bata kare fuskar da komai ba..
Kallon juna suka tsaya suna yi sai da suka ɗau daƙiƙu sannan ya ce
"Me ya faru"!?cikin separate sentence ta ce
"Ba...ba..b..komai"sai ya kuma kallon ta sannan ya sake ta ta fita cikin sauri shi kuma ya tsaya hannun sa a ƙugun sa yana tunanin me ya sa ta firgita,bai sani ba amma yana mamaki..
Sallamar Khalid ne ya farkar da shi daga tunanin abinda fifi tayi sai ya juya ya ɗau wayar sa ya fito suka wuce..
A motar bai daina nemo dalilin da ya saka fifi yin abinda tayi ba haka Khalid ya rinƙa yi mai mgn amma bai bashi doguwar amsa hankalin sa na kan son samo dalilin reaction ɗin fifi..
Kawai sai hankalin sa yayi hitting nasa akan maybe shekarun sa da ya faɗa mata ne,yana wannan tunanin sai kawai ya hau yin murmushi shi kaɗai tun Khalid bai lura ba har ya fara ganewa ya rinƙa mamakin yayan nasa sai dai bai ce mai komai ba suka cigaba da tafiya..
Har suka kai inda zasu tafi suka yi abinda ya dace suka kamo hanyar dawowa around 6pm tunanin fifi da reaction ɗin ta bai daina bijiro mai ba kuma a duk sa'in da ya tuno ta toh fah dole sai ya murmusa shi dai Khalid yau ya ga ikon Allah..
Yanzu burin Marshall bai wuce su koma gidan lfy ba ya san yadda yayi Ammy ta sako ta zuwa dan ya turke ta a gaba ya tmby ta dalilin yi mai wannan abin ba alhalin ita ta mai tmbyr dan ya lura tana da tsoro sai dai kafiyar zuciya ya sa ba a cika gane tsoron nata ba,shi kuwa yau sai ya tsorata ta dan ya ga abin dariya indeed yarinyar na tattare da abubuwan ban dariya kuma yau yana son ganin iya inda nata kalar tsoron ya tsaya...
#Mamuh*23*
Fifi da tun bayan fitar ta daga sashen Marshall ta ɗan tsaya a gefe ta rinƙa dariya kamar wata sabuwar kamu,haka har ta ƙarasa sashen Ammy bata daina dariyar ba sai da Ammy ta tasa ta gaba da tmby sannan cikin dariyar da ta jima rabon ta da yi ta hau labartawa Ammy abinda ya faru tsakanin ta da Marshall nan itama Ammyn ta ɗan dara tana kuma kallon fifi da mamaki ta tmby ta dalilin ta na dariyar amsar ta shine
"Ammy he is old kamar yadda ya faɗi but he doesn't look lyk an old man wai fah 45years Ammy ki ji fah,ta yaya zan yarda?ni na san da gangar ya faɗa min shi gani yake kamar shekaru na da na faɗa mai ba gaske bane shi ya sa da na tmby shi ya amsa min haka nan amma ni na san bai kai 45 ba right Ammy"?ta tmby Ammy tana murmushi sai Ammyn ta murmusa itama tana dariyar yarintar fifi a zuciyar ta..
"Ke kuwa baby me ya sa kike tunanin zai maki ƙarya?ai duk abinda Saheeb ya faɗa haka yake baya ƙarya iya gaskiyar sa ne dan haka ki daina ɗaukar zantukar sa da wasa iya gaskiyar sa kenan"!shiru fifi tayi tana nazarin zantukan Ammy,toh in dai da gaske shekarun sa 45 ne saura 5years ya cike 50years kenan..
Lallai Allah mai halitta wani bai kai 45 ɗin ba ma amma sai ka gan sa kamar ɗan 50 yayin da wani ɗan 50 ɗin sai yayi kamar bai ko taka layin 50 ba..
Tana iya cewa Marshall yana cikin layin waɗannan mutanin da ke da shekaru amma shekarun nasu bai nunawa ko kaɗan,but me ya sa hakan ta kasance a nasa case ɗin?shiru tayi tana tunanin rashin dacewar dariyar da ta rinƙa mai ɗazu..
Kalkon ta Ammy tayi tayi shiru tana jiran jin ko zata kuma yin wata mgn amma sai ta ga tayi shiru dan haka ta kuma jaddada mata cewar duk abinda Marshall ya faɗa mata ta ɗauka gaskiya ce dan baya ƙarya ko wasa in har akan muhimmin mgn ce,daga nan fifi ta rinƙa wasu tunane tunane kala kala har dai lkc ya rinƙa tafiya tana abubuwa ne amma hankalin ta na ga tunanin Marshall tana ganin kamar bata mai daidai ba kamar ta mai rashin kunya ne a matsayin sa na babba dake gaba da ita..
Haka dai ta ƙarar da ranar cikin tunanin rashin kyautawar ta ga Marshall har yamma tayi wankar yamma ta dawo ta natsu wuri ɗaya tana saƙa abinda zai haɗa su ta ba shi haƙurin abinda ta mai ko da zai ɗaure fuska ne...
Ammy dai ido take ta bin ta da shi tana observing ɗin ta amma bata nuna mata ta san halin da take ciki ba bare ta saka ran zata sami encouraging words daga gare ta..
Yamma lis suka iso gida duk a gajiye amma hakan bai hana Marshall saka Ammy ta aiko mai da abincin sa na dare ba a cewar sa ya gaji baya jin yana iya zuwa nan part ɗin ta sai dai ko gobe...
Tayar da fifi Ammy tayi daga ɗan taƙaitacciyar baccin da ta fara yi yanzu tana kiran ta a hankali,sai ta ɗan buɗe idon ta ta dubi Ammy..
"Tashi ki kaiwa mijin ki abinci yanzu ya dawo kuma a gajiye yake ba zai iya ƙarasowa nan ba ki je ki haɗa mai abincin sa pls yi sauri bai da jimirin yunwa"!!tashi fifi tayi zaune tana duba bed side clock ta ga 8:45pm sai ta sauko daga gadon ta ɗau hijabin ta ta saka sannan ta nufi hanyar kitchen dan haɗa mai abincin..
Dama akwai abincin a food warmers sai ta jere a saman tray sannan ta haɗa mai coffee mai ɗumi ta fito,ta hanyar baya ta fita dan ya fi sauƙi..
Da sallama ta shiga sashen nasa tayi sa'ar ganin sa a parlor yana ƙoƙarin zama..
Da ganin sa ka san yayi wanka ne dan kayan bacci ne a jikin sa sai dai akwai Cardigan a saman rigar baccin nasa sai abin ya ɗan ɗaurewa fifi kai tana tunanin yanayin garin ba wani sanyi ake yi sosai ba bare ya ce sanyin ne ya saka sa saka Cardigan ba,wata sashe na zuciyar ta ya ce mata kin sani ko shi sanyin yake ji tunda tun safe a waje suke ke kuma kina cikin gida?..
Yin wannan tunanin sai kawai ta kawar da abinda ya bijiro mata ta ƙaraso cikin parlorn tana kuma yin sallama..
Amsa mata yayi ba yabo ba fallasa kamar ba shi ba sai ta kalle sa a karkace sai kuma tayi ƙasa da kan ta tana gaida sa..
Amsa mata yayi yana kallon ta yana tuno abinda ta mai da safe sai ta riga sa fara mgn..
"Ammy ce ta ce in kawo maka abinci"!kallon ta yayi na wasu daƙiƙi sai ya buɗi baki ya tambaye ta
"Ke kullum aiko ki ake yi baki zuwa dan kan ki"?sai tayi shiru bata ce komai ba har dai ya ce da ita ta zauna,ba musu ta zauna tana ɗan kame jikin ta..
Janyo abincin yayi gaban sa ya bubbuɗe ya mayar ya rufe sannan ya dube ta ya ce
"Wa yayi girkin nan"?mamakin tmbyr nasa tayi sai dai ta amsa mai da
"Ammy ce"!ga mamakin ta sai ta ji ya kuma tmbyr ta
"Ke fah me kika yi"?a wannan karon kasa cigaba da kallon ƙasa tayi sai da ta ɗago ta kalli fuskar sa tana mamakin sa sai ta ce
"Na taya ta hira a lkcn da take girkin"!!abin dariya but ba damar yi sai ya gimtse ya buɗe food warmer ɗin ya tsaya yana kallon abincin yana kallon ta..
Tun kallon nata baya affecting ɗin ta har ya fara,ta rasa ya zata yi kuma ta rasa me yake nufi da irin wannan kallon sai da ya mata wata tmby sannan ta fahimce sa
" Je ki kirawo min masu girkin nan"!wato su su zo su yi serving ɗin sa kenan lallai al'amarim soldier sai shi..
Tsam ta tashi ta ƙarasa gare sa ta tsuguna ta fara serving ɗin sa tana yi tana tmbyr sa ko yayi,da ƙyar ma take tmbyr dan jin wani iri da ta rinƙa yi bata saba ba..
Shi dai bai amsa mata ba amma yana kallon yawan abincin da take zuba mai yana jiran ta ya ga ko zata tsaya ko cigaba da zubawan zata yi.
Dan kan ta ta tsaya dan ta san duk cin abincin sa wannan zai ishe sa sai ya maida kan sa gare ta daidai tana yunƙurin zama dan ta gaji da tsugunen..
"Na gama"!!ya kuma kafe ta da ido yana ɗage mata gira ɗaya sama wai bai fahimce ta ba sai ta dage ta kuma ce mai
"Na gama zuba abincin yayi"?sai a sannan ya dubi abincin ya dube ta ya ɗau spoon ya fara ci ba tare da ya tanka ta ba..
Ajiyar zuciya ta sauke tana jiran ya ɗan ƙara yin nisa da cin abincin sai ta sako mai mgnr dake ran ta,amma tana shakkar sa tana ganin ya wani yi mata ƙwarjinin da ba zata iya tunkarar sa kai tsaye ba amma da zama da abin a ran ta gwara ta ba shi haƙuri.
Kawai sai ta daure ta fiddo mgnr kai tsaye bayan doguwar wasi wasin da zuciyar ta ya gama yi..
"Ka yi haƙuri da childishness ɗi na da na maka da safe"!!kasa cigaba da cin abincin yayi ya tsaya yana kallon ta sai ya ce
"Ban gane ba"!oh ya salam yanzu waye zai ce bai fahimci wannan hausar nata ba?tmbyr da fifi ta yiwa kan ta kenan sai ta kuma yi mai fashin baƙi..
"Na tmby ka kuma bayan ka amsa min sai na saka dariya ka yi haƙuri Ammy ta ce min gaskiya ka faɗa min"!a wannan karon sai da ta ba Marshall dariya amma yayi murmushi mai sauti ita kan ta sai da ta ji mamakin murmushin sa dan bata taɓa gani ba tunda ta ssn shi fa ya dawo..
"Dama kin yi zaton wasa nake maki?na maki kama da mai wasa a mgn?me ya sa ke komai Ammy ce ke maki?wato ni na faɗa maki amsar tmbyr ki amma Ammy ce ta tabbatar maki da gaskiyar amsa ta unbelievable"!ya ƙarasa mgnr yana cigaba da cin abincin sa..
Shiru ta mai tana sauraron sa ganin bai wani ɗaga mata murya ba sannan in ta natsu tayi tunani kamar akwai alamar rashin lfy tattare da shi dan muryar sa ya nuna..
Bata kuma faɗin komai ba kamar yadda shima bai ce komai ɗin ba,zaman