Showing 69001 words to 72000 words out of 101986 words
Hawaye ne taf a idanun ta wanda bata hana su zubowa ba ta bar su suna zubowa ita kuma tayi shiru dan zafin da ran ta ke mata in ba nutsar da zuciyar ta tayi ba kalaman da zasu fito bakin ta ba zasu yiwa su Ammy daɗin ji ba shiyasa ta ɗan tsaya na wasu lokutan sannan ta dubi wayar dake ƙasan sannan ta dubi Ammy ta kuma dubi hajja kana ta ce.
"Kun ga wannan wayar da ta tarwatse a wurin nan"?gyaɗa mata kai suka yi sai ta girgiza kan ta ta ja hanci sannan ta cigaba da mgn
Tace "nima Haka zuciya ta ta tarwatsewa,haka rayuwa ta ta tarwatse,haka dreams ɗi na ya tarwatse its all because of u people,ku kuka bada gudunmawa mai ƙarfi a lalacewar komai da ya lalace a rayuwa ta,nayi tsammanin da zuciya ɗaya kuke so da ƙauna ta har na saki jiki da ku ashe ba haka bane,kuna nan kuna koya min abinda ku kuka san ba daidai bane,menene laifi na?yarinya ce ni ban san komai ba ku ya kamata ku nuna min hanya mai kyau a layin rayuwa ta amma baku min haka ba,kuna ji kuna gani na rinƙa aikata laifi amma abinda kuka kira da "So" sai ya hana ku nuna min laifi na?
duk akan ku komai nawa ya zama wani iri na rasa abu mafi girma a rayuwa ta,gani nan ina rayuwa a duniyar nan amma kamar ban da zuciya a ƙirji na,komai nayi dan gyara kurakuran ku bai yi sai taɓarɓarewar da al'amura ke ta yi,a dalilin ku...ƴar uwar ta,jini na wacce take a matsayin komai a gare ni ta guje ni ta tsane ni ta tsani gani na duk wani abu da ya shafe ni bata son gani ko ji,kuma ku kuka jawo hakan,da gudunmawar ku kuka nesanta ni da ƴar uwa ta,da sanin ku tsana ta ya ɗarsu a zuciyar ƴar uwa ta,a yanzu,a yau Hamida ta dubi tsabar ido na ta faɗa min ta daɗe da manta ni a rayuwar ta a matsayin ƴar uwar ta ta jini kuma tana umarta ta da in manta da ita nima,wa ya janyo min??
wa ya janyo min wannan abin?me ya sa kuka min haka?kunsan soyayyar ku na iya rikiɗewa ya dawo ƙiyayya a gare ni a idon ƴar uwa ta me ya sa baku ankarar da ni ba kuka rinƙa nuna min so da bambanci a gaban Hamida?
babu abinda ni na sani akan wannan abin amma ƙiyayya ta ta gama mamaye jikin Hamida is this just?ya dace?for all those years bata taɓa nuna ɓacin ran ta ba ku kuma baku taɓa nuna damuwar ku akan ta ba sai ni ni ɗaya what if i die right now zaku iya gyara guraben da kuka ƙirƙira ne a zuciyar Hamida?
zaku iya dawo da ni ku cigaba da bani kulawar taku ne dan kar in mutu kuma?no u can't do anything kun rigada kun ɓata komai kun ɓata min matsay na a wajen ƴar uwa ta kun dasa mata baƙin tambari a game da ni a zuciyar ta da zai yi wuyar goguwa,yau an zo ƙarshe.. idan har ba zan iya gyara alaƙa ta da ƴar uwa ta ba toh i see no reason why i should continue leaving on this earth kun san me??ku manta da ni kawai i don't need u all in my life..
babu abinda soyayyar ku ta janyo wa _Ƙaunarmu_ ni da Hamidata yau bamu da wata rayuwa sai acikin ƙiyayyar mu.
dan haka ku bar ni ku rabu da ni ni na san yadda zan yi da rayuwa ta"..tana kaiwa nan ta juya da gudu ta fita..
Tana fitowa daidai balcony ɗin su Ammy sai ta ga Saheeb tsaye da alama ya ji komai,kallon sa ta tsaya yi tana numfarfashi da sauri da sauri tana jan iska da ƙyar dan ba ƙaramin nauyi zuciyar ta ya mata ba ji take kamar zai faɗo ya fito amma bata so ta cigaba da tsayuwa a sashen su Ammy bare har ciwon da take ji ya bayyana su gani su kawo mata agaji danbata nemar taimako ko kulawar kowa a halin da take ciki..
Kallon sa take yi tana kokawa da numfashin ta dake sama sama kamar zai ɗauke,ƙarasowa kusa da ita yayi sai kawai ta hau girgiza mai kai ta faɗa jikin sa cikin daƙiƙu kaɗan nan take kukan ta ya fito fili sosai sai ta sake jiki tana ta yi..
Kasa cigaba da tsayuwar wurin suka yi ta lalaɓa ya taimaka mata suka koma sashen su tana ta kuka..
Kuka sosai fifi ke yi sa sai da ruɗar da Saheeb dan bai taɓa ganin mace ma kuka irin haka dake fitowa daga zuciyar ta ba,tana a jikin sa tana kukan kamar ba zata daina ba ta rinƙa tmbyr sa
"Ina da laifi ne?sun saka tsana ta a zuciyar ƴar uwa ta ta ce bata sonta sake gani na,ta ce ta daɗe da goge ni a rayuwar ta a matsayin ƴar uwar ta i swear it wasn't my fault ya zan yi da rayuwa ta"!?da shesheƙa mai ƙarfi ta ƙarasa mgnr sai ya ji tausayin ta dama yakan lura da shigi da ficin ta kawai dai jiran lkcn da ya dace ya tunkari abin yake yi..
A jikin sa zazzaɓin ta ya tsananta dole ya nemi Dr ɗin su ya zo cikin gaggawa dan har kamar ta fara convulsing,da zuwan Dr kuwa ya ce abin ya fara tsanani dan any moment tana iya samin cardiac arrest na biyu kuma dan ta ɗan jima tana danne rashin lfyr..
Wannan abin sai da ya saka zuciyar Saheeb bugawa ya kuma duban ta tana bacci sakamakon allurar da aka mata dan yayi calming nata..
Tambayar Dr yayi ko wani abu za a zaman yi mata da zai taimaka kar ya janyo rashin lfyr nata,nan dai doctorn ya ɗan yi briefing mai abubuwan da suka dace a rinƙa yi mata..
Godiya yayiwa doctorn ya raka sa shi kuma ya dawo ciki ya tasa ta gaba yana kallon ta yana tunane tunane a zuciyar sa game da yadda zai magance wannan abin..
_4 hours later_
Daidai 6pm fifi ta farka daga doguwar baccin allurar da aka mata sai ta ɗan zauna tana tunanin abinda ya faru da ita nan kuwa ta fara tunowa sai hawaye ya cike mata ido..
Kamar ya sani dama yanzu ya shiga wanka a ɗakin sa sai ya fito da ɗaurin towel ɗin ya nufi ɗakin ta,da shigar sa hawayen na dropping daga idon ta..
Kallon ta yayi sai suka haɗa ido take ta ji kamar an ingiza zuciyar ta sai ta fara sabon kukan..
Ɗan ajiyar zuciya ya sauke ya ƙarasa ciki yana mai gyara ɗaurin towel ɗin ya zo har gadon ya zauna haɗe da jawo ta jikin sa ya rungume ta tsam dan ya san tana wani hali mai wuyar fassarawa..
Kukan ta cigaba da yi a jikin sa ta manta a inda take kuma a situation ɗin da shi Saheeb ɗin yake na rashin sutura a jikin sa,haka ta yi ta rusa kukan ta shi kuma yana rarrashin ta har ta ɗan tsagaita sai ya ɗago da ita ya dubi fuskar ta dake dab da nasa ya haɗa ido da ita suna kallon juna har na wasu lokuta sannan ya fara mgn cikin sanyaya murya a hankali
"Am sorry i couldn't understand ur pain".
cigaba da kukan tayi tana shesheƙa sai da tayi mai isar ta sannan ta ɗaga daga jikin sa tana share hawayen fuskar ta..
Yana kallon ta sai kuma ta ruɗe ta fara yunƙurin kawar da kan ta a yanzu da ta dawo hayyacin ta,murmushi kawai yayi ya tashi ya bar ɗakin zuwa nashi..
Around 8pm na daren still ya dawo daga masallaci ya ga bai gan ta a nan parlorn ba sai ya shiga dan duba ta,nan ya ga yadda take rawar sanyi ƙudindine cikin blanket tana ta numfashi sama sama..
A hanzarce ya ƙaraso ya zo ya taɓa goshin ta ya ji zafi rau,duba magungunan ta yayi ya ga bata sha ba sai shine yau yayi jinyar nata ya kawo mata warm tea ta sha kaɗan sannan ya ɓallo mata magungunan ya miƙo mata ta sha..
A jikin sa tayi baccin bayan wuyar da ta sha a cikin jikin ta,jingina da gadon yayi yana tunanin mafita ɗaya sahihiya dan wannan lamarin nata ya munana..
*****
Da safe ya riga ta tashi yataimaka mata ta yi wanka ta sauya kayan ta dan jikin nata da sauƙi,ya koma ɗakin sa da zumar zai je ya dawo sai ta kama hanya ta fita kamar dole tana kakkame jikin ta dan sanyi sanyin da take ji ta nufi sashen Hamida..
Yau kam Hamidar da kan ta ta buɗe mata ƙofa,tana ganin ta sai tayi wani irin murmushin is this girl for real sannan ta riƙe ƙofar nata tana duban fifin har na wasu lokuta..
"Hamida ki yi haƙuri jiya ban ji daɗin jiki na bane na so in zo da dare but ban da lfy ne shi ya sa ban zo ba"ko da Hamida ta ji fifi ta ce bata da lfy sai ta kuma duban ta a ɗan tsorace amma ta basar ta cigaba da kallon ta har ta cigaba da bata haƙuri tana tuno mata yarintar su yadda suke komai tare akan tayi haƙuri yanzu ma is not late zata gyara komai sai su dawo kamar lkcn suna yara ba tare da wasu sun masu karan tsaye a rayuwar su ba kuma..
Hamida abin na taɓa ta a zuciyar ta amma ta rasa ya zata yi da kishin ƴar uwar ta da ya mata dabaibayi a zuciyar ta sai kawai ta kawar da tausayin da ya ɗan bijiro mata ta gayawa fifi mgn son ran ta haɗe da rufe ƙofar ta a fuskar Mufida..
Da rashin jin dadi Mufida ta juyo zata fara kukan sai ta ga mijin ta na ƙarasowa da zuwan sa ya riƙo hannun ta bai ce da ita ƙala ba dama da sutura a jikin ta ya kai ta hanyar shiga motar sa tana bin sa bata ce mai komai ba har ya buɗe mata ƙofar ta shiga bata fahimci komai ba shi kuma ya zaga ya shiga..
Tada motar yayi sai ta ga yayi hanyar fita a sannan ta tmby sa ina zasu cikin kuka sai ya amsa mata da..
"Somewhere far from here"!!
daga haka ya ja bakin sa yayi shiru itama tayi shiru amma kukan zuci take yi mai ciwo haka a zahiri takan goge hawaye time to time,har suka yi doguwar tafiyar da a ƙa'idance ya isa ya saka mutum bacci sbd nisan sa amma da yake ba a cikin normal self ɗin ta take ba sai bata ga nisar tafiyar ba..
Wani gida ne babba ya tura motar nasa ciki bayan an buɗe gate ɗin gidan yayi parking ya kashe motar ya dube ta yana faɗin
"Shall we"?gyaɗa mai kai tayi sai ya fito itama ta fito sai ta ga ya bada umarnin a buɗe booth a fito da kayan dake ciki nan ta ga akwatunan ta har biyu aka zo aka wuce da su ciki suna tsaye..
Daga bisani ya mata jagora zuwa cikin main house ɗin tana bin sa a baya zuciyar ta na mata wani iri kamar ba ita ba...
#Mamuh*27*
Tun da fifi ta gama maganganun ta ta tafi kaf jikin su yayi sanyi sun rasa ya zasu yi sun san su suka lalata komai kuma suna nadamar abubuwan da ya faru a sanadiyar su dan sun bada gudunmawa mai karfi a faruwar halin da ake ciki..
Hajja ce ta fara zama kan kujera tana mai dafe kan ta in soyayya na siyar komai da sun yi amfani da shi sun siyowa fifi soyayyar Hamida amma duk gatancin da suka nuna mata bai haifar mata da komai ba sama da nisanta ta da ƴar uwar ta da yayi ina amfanin irin wannan gatar da soyayyar?..
Ammy ce ta zo ta zauna kusa da Hajja itama tana nata nazarin da yadda zasu ɓullowa lamarin dan Hamida ta hau dokin fushi da su sam bata sauraron su ko sun tafi kuma sun san laifin su ne.
Abin ya masu yawa sai Ammy ta kirayi layin Khalid dan abin ya ishe ta haka nan duk laifin kan ta da Hajja yake dawowa..
Bugu uku Khalid ya ɗaga sai ta ce mai ya zo Hamida yanzu tana son ganin ta..
Ko da ta sauke wayar sai da aka ɗau lkc kafin Khalid ya dawo gidan sakamakon rushing da yayi ya dawo daga asibiti ya je ya tasa Hamida a gaba dan su zo nan ɗin..
Rai a haɗe ta shigo tana kawar da kan ta dan kar ma ta ji wani batun daga bakin Ammy ko Hajja game da fifi..
Gaida su tayi kamar an saka ta dole sai suka amsa mata suna kallon ta,Ammy ce ta fara bata haƙurin abinda ya faru sannan Hajja ta saka baki but duk wannan abinda suke yi bai ɗara Hamida ba so take su kai aya ta tashi ta tafi ta gaji da jin fifi fifi,imagine yardar ta da ƙaunar ta ma fifin kasa nemar sa tayi sai da ta zo ta haɗa da su..
Hajja na gama nasihar ta Khalid na sauraron su Hamida ta ce ta gode ta miƙe ta fita ta bar su da jimami,kasa haƙuri Khalid yayi ya tashi ya bi bayan ta rai ɓace ya same ta a parlor zata shiga kitchen ya fizgo ta suna kallon juna rai ɓace ya ce
"What was that Hamida"?kallon ƙwayar idanun sa tayi ta ce
"A ina"?wani scoff yayi na raina mai tunanin da tayi sai ya kuma matso ta da ƙarfi ya ce
"Hamida ki min duk abinda kika ga ya maki amma don't u ever include my mother and my grandmother,ashe haka kike?har kina iya rufe idon ki ki ma waɗannan mutanin wannan abin?duk girman laifin da aka maki baki saukowa ki dawo yadda ake so ki dawo?ke da su wa ke nemar albarkar wani dan gama da duniya lfy?ke ko su?wacece ke da har za a maki laifi a rinƙa bibiyar ki ana baki haƙuri amma kina turjewa?
.
zatayi magana ya dakatar da ita yace
Hameeda wai meye laifin Mufida a wannan abin?ita ta maki laifin ta hana kan ta sukuni ta rinƙa zarya a nan sashen dan baki haƙuri but kullum da ɓacin ran ki take komawa yet bata haƙura ba ta cigaba da zuwa wai kuma baki ji tausayin ta ba,,my god Hamida ko wanda ya halicce mu a ko wani daƙiƙa muna masa laifi kuma da baya yafe mana ko numfashin da muke shaƙa ta iska da ba zamu shaƙa ba toh dan me ke ba zaki fahimci ƴaruwar ki ki yafe mata ba"?kallon idon sa Hamida tayi tana jin zafin yadda yake son ɗora mata laifin komai alhalin ya san ba yin kan ta bane su suka ingiza ta yin hakan..
"Khalid ka je ka auri Mufida in ya so sai ka yi defending nata da kyau a idanu na amma wannan ba zai yi ba"! tana kaiwa nan ta buge hannun sa daga jikin ta ta wuce sa ba tare da ta juyo ba..
Abin ya ɗaure mai kai,wannan wace iriyar tsana da kishi ne ya ɗarsu a zuciyar Hamida game da Mufida?ta fara rasa tunanin ta dan tana furta kalaman da ya fita daga na masu hankali..
Ɗaga kafaɗun sa yayi ya juya ya shiga motar sa ya tada dan komawa bakin aikin sa zaman sa gidan nan bai da amfani sai dai ɓata abubuwa da zaman zai jawo dan Hamida tayi nisa ba fahimtar sa zata yi ba..
****
A natse take ta kallon parlorn kamar bata taɓa ganin gini mai kyau da tsari da ya kai wannan ba sai ya kalle ta ya mana iso zuwa wani ɗaki inda nan ma ƙarshe ne a kyau dan ya tsaru yayi kyau..
Kayan su ne a cikin ɗakin sai ta zauna bisa sofa ɗin ɗakin ta rinƙa kallon ɗakin komai maroon and cream colour tana ta kallo shi kuma yana mata murmushi..
"It's beautiful"!ta furta sai ya mata murmushin gamsarwa ya gyaɗa kan sa sannan ya koma waje dan ɗauko wasu abubuwan sa ita kuma ta cigaba da kallon ɗakin tana yaba sa..
Har ya dawo bata tashi ta ɗaga komai ba sai da ya fara gyara kayan dan kan sa sai ta tashi ta fara taya sa..
Kamar kurame suka yi gyaran ɗakin ta kalle shi tana son tmbyr sa kitchen dan ta samo masu abinda zasu ci..
Nuna mata kitchen ɗin yayi ta shiga ta ga komai na nan kamar dama akwai mace a gidan..
Nemo abinda zata dafa tayi ta fara aiki,duka duka bata ɗau awa ba ta haɗa jollof pasta da garnishing vegetables ta zuba masu a plate biyu ta saka folk da abin sha da kofuna ta fito da su zuwa parlorn..
Baya nan sai ta shiga cikin ɗakin ta mai mgn akan ta kammala girkin,barin abinda yake yi yayi ya biyo ta zuwa parlorn..
Zama suka yi a ƙasa kowa ya fara cin abincin sa,shi dai yana ci yana mamakin dama ta iya girki ne,shi yayi tunanin duk girkin da take yi ana zuwa taya ta yin sa ne toh amma yau da babu wanda ta sani a nan ɗin kuma tayi girkin sai yayi ta mamaki har ya kasa ɓoyewa ya tmby ta..
Dariya ta yi dan tmbyr ta bata dariya sai ta dube shi ta ce
"Ni na dafa da kaina"gyaɗa kai yayi ya cigaba da cin abincin har suka kammala babu wanda ya ce komai..
Kwashe kayan tayi ta gyara wurin ta dawo tana