Showing 99001 words to 101986 words out of 101986 words
yake ta yi yana kuma matse likitan,a taƙaice dai da ƙyar aka ƙwaci likitan yana ta faman tari..
Rai ɓace Saheeb ya hau shi da faɗa yana ta yi kamar ce mai aka yi fifin ma ta rasu..
"Wani irin daƙiƙi ne kai?how om earth zaka zo ma mutani da irin wannan banzar mgn as ur surgery outcome?haka kai aka koya maka ana conveying saƙo!?ko naku da dokoki ne da sigar conveying ma mutum ko patients relatives saƙon outcome ne?ta yaya zaka zo ka ba mu wannan incomplete answer ba tare da ka ƙarasa ba?dubi nan ka gani,that is her blood sister her twin sister,kana gani ai bayan ia gama faɗin banzan sakamakon ka ta sume,what if akwai mai hawan jini ko cardiac disorder kuma ya ji wannan shirmen naka ya yanke jiki ya faɗi ya mutu fah?kana fah ganin halin da muke ciki na nemar sanin mafitar wannan aikin but shi ne ka zo kana bamu irin wannan shashashar amsar"??..
Ammy ce ta tsawatar mai dan yadda yayi ta yi kamar shine mahaifin likitan ma abin was awkward..
Da ƙyar Saheeb ya daina aika ma likitan mugayen kallon da yayi ta aika mai da shi sannan ya ingiza sa ya shige cikin ɗakin da ba a gama gyara fifi ba..
Idanun sa a kan ta yana ta ƙure ta da kallo,daga inda ake gyare ta ne aka hango sa sai ya ɗaga hannu alamar su tsaya ba sai sun zo ba zai tafi..
Kusan 10 minutes yana tsaye yana kallon ta daga bisani ya bar wurin ya fito waje inda ya tarar har Hamida ta farka tana ta kuka tana kallon babyn..
Glancing fuskar babyn yayi ya sallame su akan zai je a kai Muhibba gida dan a mata wanka a kai ta gidan ta na gaskiya..
It's so touching dan haka Khalid ya bi shi suka bar asibitin dan sosai Saheeb ke buƙatar comfort amma baya cikin hayyacin sa..
Fitar su da mintuna aka turo fifi kan wheel zuwa ɗakin hutu inda aka ba su Ammy damar ganawa da ita a ɗan taƙaitacciyar lkc dan tana tsaka mai wuya ne presently yaƙi take yi da ran ta..
Da shigar su ɗakin Hamida ta zo ta zauna kusa da ita ta hau yi mata mgn tana kuka tana kallon babyn dake ta mutsu mutsu da baki,inda kusan a kashi ɗari toh kaso arba'in kawai ya kwaso na kamannin mahaifiyar sa duk kaso sittin ɗin mahaifin sa ne..
Haka Ammy da Hajja suka yi ta rarrashin ta suna bata mgn,daga bisani da kukan nata yayi tsanani ma karɓan babyn Hajja tayi ta ja gefe ta zauna tana rarrashin ɗan dan ya fara kukan yunwa...
****
An kai Muhibba gida an sanar da rasuwar ta,toh dama ba wasu ƴan uwa a kusa gare ta ba dole sai a washegari ko da zasu zo dan haka suka ce a mata sutura kawai a kai ta..
Haka aka mata wanka aka mata sallah aka suturta ta aka kai ta final destination ɗin ta..
Sai da Saheeb ya ƙulle kan sa a ɗakin Muhibba yayi ta kuka tuƙuru yana yi yana mata addu'ar rahamar ubangiji..
Sai misalin ƙarfe shida na yamma ya bar gidan ya nufi asibiti dan ganin halin da fifi ke ciki..
Dama su Ammy sun dawo gida dan karɓar gaisuwa tunda fifi na ɗaki ne na musamman ba a so a dame ta sosai sai Hamida ta tsaya tare da ita while Ammy da Hajja suka dawo gidan da babyn dan a mai wanka...
Ranar dai an ga samu an ga rashi,a wurin Saheeb da a ce babyn mace ce toh da tabbas sunan marigayiya zai maida mata wato Muhibba..
Haka nan tun ranar da Muhibba ta rasu fifi kuma ta shige comma,rayuwa ta sauya ma ahalin,wata walwala dai babu ita duk ta kau..
Rayuwar su ta sauya sosai dan daga ranar zuwa yanzu kusan sati biyu kenan fifi bata wani yi ƙwaƙwarar motsi ba sai dai in aka zo yi mata allura ta ɗan juya,da zarar an cire kuma zata cigaba da baccin wahalar da take ta yi...
Likitocin sun sanar da family ɗin fifi cewa wannan miracle ne mace mai cardiac disorder tun a yarintar ta kuma ma da shi aka haife ta ita kuma ta haihu ba tare da ta rasa ran ta ba,toh ba ƙaramin miracle bane...
Asibiti ya zama wurin zaman Saheeb har ranar da aka sallame su suka dawo gida ana bata kula ta musamman,bayan doctor dake zuwa yana duba ta,akwai wasu domiciliary nurses dake kula da ita a gida.
Duk wannan kular bai ma Hamida ba sai da ta ɗora da nata kular,bayan kula da babyn da take yi da har an raɗa mai suna while fifi is in comma..
Babu shagali da aka yi ko ɗaya duk da an yi ɗokin haihuwar amma yadda haihuwar ta zo,sai kowa yayi sanyi aka bari in har Allah ya tashi kafaɗun fifi sai ta zaɓi yadda take so a yi celebrating naming ceremony ɗin...
Babyn madara yake sha tunda ya zo duniya dan babu wani abu mafi sauƙi da zai fi zama a cikin babyn ba tare da ya mai illah ba sama da madarar..
Sunan babyn shine Abdulrahman but aka masa inkiya da Maheer duk da shi Saheeb ya ce in fifi ta farfaɗo kuma sunan bai mata ba toh dole za a sauya sunan..
Ba ƙaramin kula Maheer ke samu daga wurin aunty ɗin nasa ba wato Hamida,ita ke mai wanka ta saka mai kaya ta bashi abinci,tana yi tana kuka,tun mitsitsin babyn nan bai fahimtar Hamida har ya fara dan in yana hannun ta wani lafewa yake yi yayi ta sucking yatsar sa,alamar madarar bata isar sa..
A duk lkcn da yayi hakan toh fah Hamida kuka take yi ta daɗa rungume sa a jikin ta tana addu'ar samin lfy ga ƴar uwar ta..
Shi dama Saheeb ya tare a ɗakin da fifi take take samin kula,duk yadda Ammy ke kula da ita in har ta ga shigowar Saheeb haka zata haƙura ta bashi wuri dan sai yayi ta kushe kular da take ma fifi,daga ya ce nan bai yi ba sai ya ce can bai gogu ba,duk kamar zautacce haka ya dawo gwanin tausayi...
Mgn kuwa ba iyaka,in fara zuba mgn shi kaɗai dan fifin dai ba jin sa take ba,abin sai ya ba mutum tausayi,dan har barin sumar fuska da na kai yayi babu gyara,duk ya sauya dan yanzu be asalin ƙaunar matar sa ke shigar sa,a yanzu da yake ganin kamar rasa ta zai yi dan kullum in ya zo toh burin sa bai wuce a ce ta farka ba amma haka zai yi zaman sa har ya tashi,ko motsu fifi ba zata yi ba...
Kalaman soyayya ya faɗe su wanda da fifi na hayyacin ta toh da zata ce maybe wani Saheeb ɗin ne ba wanda ta sani a matsayin mijin ta mai kawar da kai ba..
Kalaman ƙauna da so kala kala ko da yaushe sai ya faɗawa fifi su,duk ya zauce,ƙaunar ta mai zafi ke shigar sa..
Hamida kan yi kuka im ta gan sa a wannan yanayi,tausayin sa kan kama ta sai dai a halin yanzu,kula da babyn fifi da yi ma fifin addu'a shine abu mafi kusanci da fifin ke buƙata...
Kamar kullum yau ma yana zaune rungume da Maheer a jikin sa yaron na bacci shi kuma yana riƙe da hannun fifi yana mata kalaman soyayya da gwada mata irin ƙaunar ta da yake yi,har da alƙawarin sa na in ta farfaɗo bai kuma matsawa ko da nan da can ne sai ta yarda ta bashi izini...
Idanun sa sun rikiɗe sun yi ja dama su Hajja da Ammy basu jima da barin ɗakin ba,a kullum sai sun sanar da daddyn su fifin halin da ake ciki dan hnkln sa ya kwanta,duk da shima shirin dawowa gida nan Nigeria yake yi dan ya kasance da family ɗin sa gabaɗaya..
Dai dai yana mata surutan nasa kenan hannun ta riƙe cikin nasa sai ya ga kamar hannun na motsi,ɗan tsayawa yayi sannan ya kuma kallon hannun sai ya ga da gaske moving hannun ke yi daga haka ta fara motsawa tana nishi da ƙyar..
A 360 Saheeb ya tashi rungume da ɗan sa ya matso kusa da ita yana ta dariya mai ɗauke da kuka..
Sunan ta ya shiga kira hawaye na zubo mai kamar ba namiji ba namijin ma soldier mai matsayi kamar sa...
Da ƙarfi ya fara kiran sunan nata at same tym yana kiran sunan Ammy akan ta zo da sauri..
Ammy da zata wuce ɗakin dan duba lfyr Hajja dake fama da ciwon kai sai ta ji ana kiran ta da murya mai nuna zumuɗi..
Da sauri ta ƙarasa ta shiga ɗakin,dai dai fifi na tari mai ƙarfi kenan,da ganin haka sai Ammy tayi ƙasa tayi sujjada tana ma Allah godiya sannan ta taso a hnkl ta ƙaraso ga fifi ta riƙo hannun ta cikin nata tana kallon ta..
Rasa abin faɗi Ammy tayi sai murmushi shi kuma already ya fito daga ɗakin ya sauko yana ta faɗin ai Khadija ta farka his wife is awake,she is back to life again...
Kafin a sani tuni gidan ya hargitse da hayani ana ta murnar farkawar fifi,bayan kimanin wasu awowi aka ɗan sarara a ɗakin dan kula da ita da Hamida ke son yi kamar wanka da gyaran jikin ta...
Bata sami damar tmbyr abinda ta haifa ba,tunda dai ta gana da ƴar uwar ta sai ta ji duniyar ta mata daɗi not as she expected kamar da irin mutuwa zata yi ba zata kuma ganin su ba...
Ranar Hamida ce ta kula da ita ta bata abinci sannan ta je ta karɓo Maheer daga hannun Saheeb ta kawo ma fifi,sai daga baya su Ammy suka shigo ɗakin tare da Saheeb dake ta kallon ta kamar zai haɗiye ta tsabar kewar ta da ƙaunar sa da suka kasa barin zuciyar sa yayi saƙat...
Kallon babyn tayi ta yi tana mamakin wai ita ta haife sa kuma take riƙe da shi as his mother,me kuma zata nema a wurim ubangijin ta sama da gode mai da wannan baiwa da ya mata,dan baiwa ce,a lkcn da bata yi tunani ba bata yi tsammani ba sai gashi ta kasance tare da ahalin ta da ɗan da ta haifa da kan ta...
Har dare Hamida bata bar ƴar uwar ta ba sai da Khalid ya ja ra'ayin ta akan ta ɗan bar Saheeb ya gana da matar sa shima tunda tun bayan farkawar ta bai wani sami sararin zama tare da ita ba sakamakon cika da aka yi a ɗakin..
A lkcn itama tayi zurfin tunani sai ta ce ma fifi ta kawo babyn su tafi sai ta ce mata za a maido mata da babyn so take ta kuma kallon babyn kuma..
Da fara'a shimfiɗe saman fuskar Hamida ta fita ta bar ɗakin while fifi ta ƙurawa babyn ido tana ta kallon sa tana admiring babyn...
Tana haka sai Saheeb ya shigo bakin sa ɗauke da sallama sai ta amsa tana kallon sa..
Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita suka ƙurawa babyn ido sai suka yi murmushi a lkcn ɗaya,ce mata yayi
"Welcome back mon amour"!kallon sa tayi tana mai gyaɗa mai kai kawai..
Daga haka suka cigaba da kallon ɗan har dai bacci ya fara ɗaukar ta tana rungume da Maheer,dabara Saheeb yayi ya gyara mata kwanciya bayan ya ɗauke babyn daga jikin ta..
Shima kwanciyar yayi kusa da ita sai ɗan space da ya bayar kaɗan inda ya shimfiɗe babyn a tsakiyar su ya ƙura mai ido yana ta kallon sa har shima baccin ya ɗauke sa..
Sai a washegari fifi ke sanin rasuwar Muhibba ai kuwa ta mata addu'a sosai da fatar samin rahamar ubangiji a nan kuma aka sanar da ita sunan ɗan ta sai ta ce sunan ya mata daɗi kuma bata buƙatar sauyawa babyn suna daga wanda mahaifin sa ya saka masa..
A cikin kwanakin aka rinƙa taimaka mata tana doguwar tafiya har jikin ta ya warware gabaɗaya ta fara shayar da ɗan ta da kan ta in ta gama ta aika ma Hamida da babyn..
A haka rayuwar gidan ya cigaba da tafiya cikin fahimta da kula da sanin ya kamata..
Ba a cire rai ba,itama Hamida ana mata addu'ar samin nata ƴaƴan in da rai da rabo..
*****
_5 months later_
Abubuwa da dama sun wanzu cikin waɗannan watannin kama daga haɗa daddyn su Fifi da Dr Fatima Yonas da su fifin suka yi dan su zama ma'aurata wanda dama dreams ɗin fifi kenan har ta bar wasiyar in ta mutu toh Hamida ta taimaka mata ta cika mata wannan buri nata,as she is still alive,sai ita da Hamida suka ɗaukaka mgnr har dai su Ammy suka ga dacewar hakan su ma..
Abu dai kamar wasa mutuntakar dake tsakanin daddyn su fifi da Dr Fatima ya ɗaukaka ya dawo babba,dan presently batun bikin su ake yi wanda ya rage nan da sati kaɗan..
A can fannin Dr Fatima kuwa da ƴaƴan ta biyu,bata da matsala ko damuwa da auren dan sun bata support ɗin su 100% as daddyn su fifi is a nice man Throughout his stay a ƙasar tare da su...
Maheer ya fara wayo kuma yanzu ne Allah ya azurta Hamida da Khalid da ƙaruwa dan she is 4 months pregnant,lbrn da ya ma kaf ahalin daɗi,dan sun fara yawa kamar yadda suke buri..
Saheeb dai dama jira yake komai yayi settling na bikin uncle ɗin nasa sai ya ɗau matar sa su koma South Africa tare in ya so sai su rinƙa zuwa visit ko vacation a nan Nigeria tunda a can yake aiki..
Bayan komai ya kammalu suka shirya dan tafiya,sosai fifi da Hamida suka yi kuka kamar sun rabu kenan na har abada,dan kuwa irin shaƙuwa da kusancin da suke yi a yanzu,ko zaman su na da da suka yi suna ƴan mata,basu taɓa yin sa ba,lokuta da dama ba Saheeb ba har Khalid yakan ji mamakin irin ƙarfin kusancin su sai dai in ya tuna ƙarfin jini ya fi gaban wasa sai ya share..
A haka rayuwa ta basu second chance suka fuskanci juna tsakanin su da kuma tsakanin su da iyayen su,a yanzu ne suke zaman so da ƙauna da fahimtar juna fiye da da da aka sami tangarɗa as result of ignorance da negligence ɗin su wanda basu fatar ko a wani gidan ne haka ya faru dan babbar illah ce su sun gani da idanun su..
After alk d luv and care da suka rinƙa nunawa Mufida har ya ma Hamida illah a zuciya ta so kauce hanya a ƙarshe Allah bai dubi halin da suka jefa Hamidar a ciki ba ya saka ƙaunar Mufida a zuciyar ta bayan so many attempt to get rid of Mufida..
Wannan shine clear definition na ƙauna da ake kiran sa da jini,dan ƙauna a jini yake ba kamar so ba da a baki ake faɗan sa ba wataran yana iya gushewa..
****
Bayan wasu shekaru kamar biyar a rayuwar su fifi,Allah ya azurta Hamida da ƴaƴa biyu na farkon itace mai sunan fifi na biyun kuma mai sunan daddyn su Khalid marigayi,while fifi kuma tun bayan Abdulrahman bata kuma haihuwa ba sai bayan shekaru uku inda ta haihu still through surgery kafin ma ranar haihuwar dan lfyr ta da na babyn,a wannan karon sai Allah ya bata ƴan biyu mata ɗaya ta ci sunan Ammy suna kiran ta da mami,ɗayar kuma sunan Hamida suna kiran ta Rayhan...
Tsakanin fifi da Nigeria shine ziyara dan tun bayan bikin dadyn su da Dr Fatima da ta zo,bata kuma zuwa ta jima ba sai dai ta zo ta ɗan yi kwanaki ita da Saheeb su koma..
Akwai shaƙuwa a tsakanin ƴaƴan su wanda hakan ya masu daɗi dan basu so rashin ƙaunar da ta so ta samo asali a nasu rayuwar ta faru a tsakanin ƴaƴan su...
Fifi kam bata da abin cewa sai godiya ga Allah swt da ya mallaka miji irin nata mijin wanda da ta so butulcewa Allah da zaɓin da ya mata but da yake matar wani bata auren mijin wata shi ɗin ne dai nata ƙaddarar sai Allah ya jefa mata so da ƙaunar sa a zuciyar ta tun bata sauraron zuciyar ta har ta natsu ta zauna da shi gashi a yau Allah ya albarkaci rayuwar auren su da abu mafi tsada da ko kuɗi bai isa ya siya maka shi ba,wato ƴaƴa..
Hamida ma na cikin gode ma Allah da ya bata nata zaɓin mijin ya kuma saka ƙaunar junan su cikin zukatan su,rayuwa mai daɗi da tsafta suke yi,kula da juna kuwa ba a mgn dan kullum cikin yin sa suke,ƴaƴa ko aikin Khalid ko nata ita kan ta aikin baya hana ta ba mijin ta kula yadda ya kamata,kamar yadda a kullum Saheeb baya gajiya da gwada ma Khadijatul Mufidah salon son da yake mata,toh haka Khalid baya gajiyawa gurin ganin ya kuma dasa ƙaunar sa a zuciyar matar sa Ayshatul Hamida...
*Duka duka a nan na kawo ƙarshen wannan lbr nawa mai suna Ƙaunarmu,inda nayi kuskure rabbi ya gafarta min inda nayi daidai Allah ya bani ladar sa,ubangiji Allah ya bar ƙauna da zumunci,taku ce*
#Mamuhgee