Showing 15001 words to 18000 words out of 101986 words

Chapter 6 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15639

cigaba dan samo asalin amsoshin da take so...

"Fifi yar uwa ta...,na so a ce ni ce ke cikin wannan matsalar sai dai a'a..ba ni ba ce,saidai na yarda da wannan kalmar ta masoyin ka masoyi ne ko a ina yake haka makiyin ka makiyin ka ne ko a ina yake, _*KAUNARMU*_ ta asali ce,yadda nake son ki nake kokarin ganin farincikin ki kema haka din ne,da wuya ake samin yar uwa mai kyakyawar zuciya irin taki"..nan ma tana kawowa ta ja tayi shiru..

Dulmiyewa fifi tayi cikin kogin tunanin inda kalamar Hamida suka dosa dan ta matsu ta ji matsalar yar uwar nata ba dan ta gaji da jin yabon da yar uwar nata ta mata ba sai dan ta damu da son magancewa yar uwar nata matsalar ta..

Zata yi magana Hamida ta riga ta dan bata son shirin ta ya wargaje bata so fifi ta fahimce ta dan ba halin ta bane bata saba ba,ko da tana da matsala yana damin ta bata iya tunkarar fifi da shi dan bata da lokacin ta is either tana yawon bude ido da kawayen ta,ko tana gidan Dr Fatima Yonas,so yau na cikin kwanakin da zata iya kirgawa ta zauna one on one su yi wata muhimmiyar magana,and wannan ya kasance rana daya da ba zata so tayi sake ya kufce mata ba..

"A jiya bayan mun diro kasar nan na iske sakon wata aminiya ta a inbox di na sai na share dai har muka iso nan gida,bayan na yi wanka na bude na karanta tun daga farko har karshe,kusan sau uku ina karanta sakon nan nata,sai da na kammala kai na ya kulle na rasa ya zan yi dan tana tsaka mai wuya

kuma taimako take nema na gaggawa daga gare ni,fifi ko kin san menene wannan damuwar nata"?da sauri fifi ta girgiza kai tana son jin menene..

Murmushi Hamida tayi wanda a ido da zuciyar fifi gani tayi kamar murmushin da hausawa kewa lakabi da ya fi kuka ciwo ne sai ta ji ta kara tausayawa yar uwar nata dan ta shiga damuwa sosai...

Hamida tace
"Kawata Tana da yar uwa wacce suke ciki daya mahaifin su daya haka mahaifiyar su daya,tun yarintar su sun taso ne cikin kauna da kulawar junan su,suna kafa kafa da bacin ran junan su,basu son abin da zai taba dayan su,a haka suka taso cikin rayuwa mai inganci har girman su,ana haka sai yaruwar kawar tawa ta tsinci kan ta cikin son kula wani masoyi wanda wannan masoyin kuwa ba masoyin kowa ba face masoyin wannan aminiyar tawa,bata da masaniya akai tana chan tana dakon soyayyar sa tun haduwar ta da shi ta farko sai dai bata sami damar sanar da shi ba sbd alkunya irin ta mace,abin da bata sani ba shine,tun ranar da ta hadu da wannan masoyin nata yaruwar ta ta hadu da shi itama

Amma ita aminiyar tawa ita ta fara ganin sa kafin yaruwar nata ta gan sa,nauyin baki ya sa ba a jima ba ta gano cewa yaruwar nan nata ta gama fadawa soyayyar wannan masoyi nata kuma da alama shima yana shirin fadawa a tarkon soyayyar ta,duk yadda aminiyar nan tawa tayi dan ganin ta hana faruwar hakan ta yi amma abin ya ci tura dan tana chan tana tunanin madafa yaruwar nan nata ta fara niyar kawo mata labarin kusancin ta da wannan masoyin aminiyar tawa,bata kai ga kawo mata ba sai tayi tunanin sanar da ni dan in bata mafita,..iya tunani na yi fifi,ta bani tausayi kar fah ki manta masoyi ne da ta jima da soyayyar sa a zuciyar ta kuma take ta dakon sa sai dai alkunya da nauyin baki ya sa tayi delay akan fallasa masa sirrin dake ran ta,kuma kar ki manta,yar uwar nan nata ta riga da ta gama shirya sanar da ita abin dake tsakanin su da masoyin nan nata,tunani na ya ƙafe ƙaf,hankali na ya gama hango min iya mahanga,nazari na ya tsaya akan hanya,kai na ya kulle,tausayin ta ya gama mamaye ni dan shirun da tayi na nemar cutar da ita cuta ta har abada da in tayi wasa lallai zata zanawa kan ta tambari mai wuyar goguwa har abada dan tana ji tana gani yar uwar nan nata zata kasance cikin rayuwar da ya dace ita ce ta kasance ciki amma hakan bai yiwu ba, .

Mufida ina mafitar ki kan wannan matsala ta aminiya ta da yar uwar ta?me cece gudunmawar ki akan wannan labarin rayuwur tasu"?..

Kakkarfar ajiyar zuciya fifi ta sauke mai abubuwa da dama dan ba karamin tausayin aminiyar yaruwar nan tata tayi ba,labarin ya fi mata kama da irin labarun da ake sakawa a fina finai dan da wata ce ta bata wannan labarin toh nan take zata karyata ta dan bata ga ta yadda za a ce kana son mutum kayi shiru ka ki sanar da shi ka rinka boye abin dake zuciyar ka wai dan kar wata ta ji zafi da wani abu wai shi sunan shi alkunya?ita ba zata iya yarda hakan ya faru da ita ba,kasancewar yar uwar ta ce ta sanar da ita wannan labarin sai ta gasgata dan yar uwar ta ba zata taba tsara mata karya ba..

Rau da idanu fifi tayi tana jijjiga kai hade da alhinin wannan labari sannan ta yi nata maganar.

"Hamida yau da ba ke kika sanar da ni wannan labari ba,ba zan taba yarda da dan na fi ganin irin sa cikin fina finai,amma na san ba zaki zauna ki tsara min karya ba shi yasa na gasgata zantukar ki"!jin wannan kalama ta karshe da ya fito daga bakin fifi wato _"Gasgata"_ sai Hamida ta ji wani dadi ya mamaye ta dan ko da ta fara bada labarin tayi zaton fifi zata ki amincewa da labarin sai kuma ta sha mamaki dan haka ba karamin dadi ta ji ba..

Kara kyabe fuska Hamida tayi kalar tausayi ta tsurawa fifi ido tana jiran jin amsar ta..

Sai da fifi ta rinka shafa bayan Hamida tana bata magana akan komai zai wuce sannan ta cigaba da magana..

"Hamida kin ga dai rayuwar nan ita daya ce gare mu in aka bar ta ba dawowa ake yi ba sannan baya ga hakan akwai ƴancin kai,ƴanci zaben abin da kake so a rayuwar ka,toh dan me wannan aminiyar taki take daukar lokacii wajen yin wasu tunani?in ta zuba ido tana kallo yaruwar nan nata ta mallaki muradin rayuwar ta kuma suka kasance cikin farinciki shi kenan burin ta na son yin Tarayya da wannan masoyin nata a matsayin abokin rayuwar ta ya tafi kenan ba tare da ya sani ba?

matukar ta bari wannan damar nata ya tafi tabbas rayuwa ce zata yi amma cikin kadaici da rashin ingancin abokin da ya dace dan babu wani da namiji da zai zauna mata a zuciya sama da wannan masoyin nata,sbd haka tun kafin wannan yaruwar nata ta tunkare ta da zancen ita yakamata ta dau mataki dan kare faruwar hakan,ba sai ta bayyana mata ba amma dabi'un ta su zasu nunawa yar uwar nata cewa akwai wani sirri tsakanin ta da masoyin nata kin ga daga haka ita kan ta yar uwar zata rabu da su ba sai an yi hayaniya ba,let her go for what she want,ko ba haka bane yaruwa ta"?..

Kallon ta Hamida tayi tana hadiye shawarwarin ta tana kada kai daga bisani ta rungume ta cikin tsananin murna da farinciki tana fadin
"Tabbas _Kaunarmu_ daga min indallahi ne fifi,ni da ke din jini ne kuma Tarayyar mu tayi min amfani,yadda kika samo min maganin wannan damuwar wacce na dau tsawon awanni ina ta bugawa a kwakwalwa ta amma ban samo amsa ba,na yarda shi yasa kike da kaifin basira kike zuwa a layin farko ta fannin karatu,you are a genius twin sis i love you"!!

daɗa faɗaɗa murmushin dake saman fuskar ta fifi tayi tana jin dadin ta samowa aminiyar yar uwar ta maslaha mafi sauki kuma tayi kokari akan damuwar yar uwar nata..

Dagowa Hamida tayi ta shafa fuskar fifi tana kara gode mata da taimakon da ta mata sannan ta kara jaddada mata zata sanar da aminiyar nan nata shawarar kuma zata fada mata cewa nata yaruwar ce ta bata wannan shawarar..

Daga karshe bayan ta ma fifi godiya ta tashi da nufin fita sai kuma ta juyo ta kalle ta da murmushi mai ratsa zuciya sannan ta ce
"Na gode yar uwa ta Allah ya bar zumunci ya bar mu tare ba zan taba manta wannan abin da kika min ba yar uwa ta,InshaAllah wataran zan rama maki wannan kyakyawar ranar da kika min,kafin nan,ki koma baccin ki kin san daddy ni zai rike in har baki sami isasshiyar hutu ba

dan haka go back to bed twin sis sai mun hadu a wurin breakfast anjima"!gyada mata kai fifi tayi daga haka Hamida ta juya tana mata wani irin kallo..

Har cikin zuciyar Mufida ba karamin jin dadi tayi ba ganin ta warwarewa yar uwar ta damuwar ta,dama Hamida zurfin ciki ne da ita dan kullum shiru shiru haka take har takan yi mamakin yadda Allah ya halicci zuciya irin ta Hamida kamar bata da damuwa dan bata cika shiga sabgar da ba nata ba bayan ita da take yar uwar tama kan ta ita din irin mutanin nan ne da ake kira da extrovert masu son magana

Hamida kuma ta kasance kullum shiru sai abin da ya shafe ta take saka kan ta...

Komawa tayi ta kwanta dan cigaba da baccin dan dama bai ishe ta ba,bata dade ba baccin ya dauke ta..

A nan fannin Hamida kuwa duniya sabuwa dan ta samo abin da take so kuma ta samo facts da shaidar da ko da tace ga abin da take so babu yadda yar uwar ta zata ce ta mata kwace dan da kan ta ta bata shawarar kwato abin da yake nata ne..

Farincikin ta a ranar baya misaltuwa dan kasa bacci tayi har gari ya gama wayewa tayi abin da zata yi,wani hali da ba nata ba sai tayi sa a yau wato cancaɗa kwaliyya na zamani irin na yan mata masu ilimi da wayewa,shigar mutunci tayi ta dohuwar Asmaa abaya plain black mai kyau da tsada,tayi rolling veil din abayar ta saka loafas mai taushi ta fito kamar wata wacce bata taba zaman damuwa da kadaici ba...

Bata tsaya duba fifi ba dan ta san an zo an dauke ta zuwa dinning table,haka da fara'ar ta ta sauko ai kuwa ta fara hango su suna breakfast din su cikin walwala,ɗage kafadun ta tayi alamar abin bai dame ta ba ta karasa saukowa kasar..

Da zuwar ta ta sa hannu ta ja daya daga cikin kujerun dinning din ta zauna tana mai gaida su(cikin jama'u)..

Mamaki Ammy tayi ganin walwala a fuskar ta yayin da Hajja kuwa ta tsaya tunanin hala wa ya kirawo ta zuwa breakfast din tunda sun ga alamar ita din mai son kadaicewa ne ita kadai ko me ya faru yau ta zo tayi joining din su..

Shi kuma Khalid kallon ta yayi yana yaba kwalliyarta har ya furta mata..
"You look beautiful "wani dadi ne ya mamaye zuciyar Hamida amma tsabar rike aji irin nata sai ta dan murmusa kawai ta ce
"Nagode brother".daga haka ta kalli fifi tana mata faffadar murmushi itama ta maida mata da martani..

Abinci suka ci cikin jin dadi da walwala as family har suka kammala babu tashin hankali bayan yar hirar da aka rinka yi da fifi ba a sako ta ciki ita kam ko a jikin ta dan damuwar su yanzu ta maida shi gefen hagun ta ta dabbaƙa damuwar Khalid a gefen damar ta dan ganin bata yi sake ta rasa shi ba...

Sallamar ta fifi tayi akan zasu tafi yawon bude ido tare da Khalid har ta mata tayin tafiya amma ta ce a'a su tafi sai dai kar su manta su dau hotuna da dama dan in sun dawo ta kalla..

Allah sarki fifi sai ta dawo ta rungume yar uwarta tana mata sai sun dawo ita kam ban da murmushi babu abin da take mata,bayan tafiyar su ma bata koma dinning din ta zauna ba sai ta sallami su Ammy akan zata tafi kallon gidan tare da ma'aikatan gidan,basu hana ta ba suka kirawo wata amintacciyar ma'aikaciyar gidan suka umarce ta da ta raka Hamida su zagaya gidan..

Daga haka ta masu godiya suka fita,barin su Ammy da Hajja tayi cikin mamakin dalilin walwalar ta na yau amma da yake bata wani yi jiki da su ba sai suka share kawai suka cigaba da sabgogin su...
#Mamuh*_Mamuhgee_*


*9*

Sannu a hankali yar aikin nan ta rinƙa zagaye gidan nan da Hamida tana nuna mata sashe sashen dake cikin gidan ko wanne kuma sai ta mata bayanin mammalakin sashen, dan akalla mai aikin wanda aka fi sani da mama hasiya ta jima tare da su a cikin gidan zata kai sama da shekaru ashirin da shida zuwa da bakwai tana aiki a gidan kuma bata zamba da cin amana wannan ya daukaka darajar ta a idanun yan gidan ya sa aka yarda da ita har in abu na sirri ya taso ana iya yi a gaban ta dan an san sirrin nan zai kasance a killace..

Wani sashe suka zo mai bala'in kyau da tsari wanda bata taba ganin irin sa ba sai ta ja ta tsaya ahankli ta kalli matar ta ce
"Mama hasiya nan kuma sashen na waye ne?amsa ta bata kai tsaye ta ce
"Wannan sashen shine sashen ɗan uwan ku Khalid kuma tun yarintar sa har kawo girman sa a nan sashen yayi sa"..

Gyaɗa kai Hamida tayi tana tunanin ta shiga ne ko a'a, wani tunani tayi sai tayi shiru ta kyale ta dai cigaba da ƙare ma sashen kallo.

Muryar matar ne ya fargar da ita a inda take tambayar ta ko tana son a bude mata sashen ne ta shiga..

Tace "A'a mama hasiya,bana bukatar ganin yanayin sashen a yanzu,amma watarana nice aciki. cikin ranta tace ba iya gani zan yi ba har shiga cikin sa zan yi in zauna na har abada dani da khalid.
"da fara'a a fuskar ta ta ida maganar wanda ya so ya ɗan ɗaurewa mama hasiya kai ganin kamar jefa magana Hamidar tayi cikin magana amma lura da tayi da yanayin Hamidar na ba mai son hayaniya bane sai bata daukaka maganar ba ta basar..

Daga haka suka cigaba da bin sauran sashe sashe na gidan suna dubawa suna ƴar hira kaɗan kaɗan wanda a cikin hirar ne Hamida ke ƙaruwa sosai dan kusan a 100% ta san kusan 60% na halayyar ƴan gidan musamman inda ta fi buƙatar sani wato fannin labarin rayuwar Khalid dan shine ta fi bukata sama da komai..

Suna zuwa wani sashen kuma sai Hamida ta ja ta tsaya tana kallon mama hasiya tambayoyi cike taf a bakin ta da zuciyar ta amma bata furta ba tayi shiru..

Fuskantar hakan sai mama hasiya tayi murmushi dan ita kan ta tana da ɗiya mace mai hali kusan na Hamidar wato halin kau da kai ga abin da ba'a saka ta ciki ba kuma bata tambaya in har ba abin ya zame mata abin dole bane da zata sami ƙaruwa ba,dan haka sai ta hau yiwa Hamidar bayanin wannan sashen da mamallakin sa.

"Wannan shine sashen babban ɗan gidan nan kuma jigo jagorar gidan nan,magaji kuma masanin sirrin cikin gidan nan wato marshall MUHAMMAD SAHEEB kuma a halin yanzu baya ƙasar yana can South Africa inda ya fi yawan zama dan business din sa da kusan komai na rayuwar sa sun fi ƙarfi a can ɗin,amma duk lokacin da ya kawo ziyara nan ƙasar toh a nan sashen yake zama"!!

gyaɗa kai kawai Hamida tayi dan ko ba a faɗa mata ba ta san wannan shine old eldest son ɗin Ammy da daddyn su ke basu labarin sa,lallai wannan tsohon shine wai har yanzu yana zaune awata ƙasar gaskiya su Ammy sun mai sake da yawa..

Ko da mama hasiya ta kuma yi mata tayin shiga wannan sashen sai ta ce a'a bata so,a zuciyar ta kuwa faɗi take ita me zata shiga ta gani a sashen tsoho sama da tarikicen kaya irin tasu ta tsoffi,sashen yaro mai zamani ma wato Khalid an mata tayin sa bata karɓa ba sai na wannan da ta san da ta shiga zata fito da babbar story da zata faɗawa fifi in ta dawo su yi dariya dan ta san fifi ta fi ta wauta tana iya cewa zata zo sashen da kan ta dan ganin me ke ciki ko dan ta sha dariyar mai dalili..

Zagaye farfajiyar gidan suka yi har suka ɓullo ta asalin kofar babban falon suka shige tare ita mama hasiya ta wuce sashen ta ita kuma Hamida ta haura zuwa nata ɗakin dan ko da suka dawo babu wanda suka tarar a parlorn..

Hamida ta kai kusan mintuna talatin tana ta saƙa da warwara akan yadda game ɗin ta zai kasance dan a jiya ta rasa courage ɗin komai amma safiyar yau da tayi magana da fifi sai kawai ta ji kamar an yi tursasa mata wani karfin gwiwa ne tun safen har ya kawo iyanzu bata da shakku a zuciyar ta game da alaƙar da take shirin ƙullawa tsakanin ta da Khalid dan ta san Tarayyar su zata zamo abin alfahari..

Ko da rana yayi bata tsaya jiran ganin saƙon su na ta zo a ci abinci ko a aiko mata da shi ba ta sauko da kan ta ta kuwa same su zazzaune suna jiran dawowar su fifi..

Babu wata damuwa a fuskar ta ta sauko ta tunkare su tana fara'a ta jawo kujerar ta zauna sai duk suka bi ta da kallon mamaki dan yau gabaɗaya kamar an sauya ta daga Hamidar jiya da suka yi welcoming daga filin saukar jirgi ba..

Ganin irin kallon da suke bin ta da shi ya sa ta ɗan yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login