Showing 63001 words to 66000 words out of 101986 words
fito shi ya sauya kayan sa zuwa jallabiya ya fita zuwa masallaci ita kuma tayi nata sallar a ɗaki...
Ko kafin ya dawo har ta yi yan kimtse kimtsen ta ɗin ta ta masu breakfast tayi wanka ta fito cikin ƙananan kaya da maroon kimono kan ta ta yafawa ƙaramin mayafi ta ɗan yi kwalliya ta hakimce saman dinning ɗin su tana latsa wayar ta..
Bai shigo ba sai misalin 8:30am sakamakon zama sashen Ammy da yayi suka gaisa ya kuma kai ziyara wa Hajja wacce ita ta ja sa da hira har ya daɗe..
Da shigar sa ta tare sa abin sai ya burge sa kenan kalaman sa gare ta na safiyar yau yayi tasiri a zuciyar ta lallai da haka zai rinƙa sanyaya mata zuciya har yayi nasarar yaƙice mata kishin ƴar uwar ta a zuciyar ta ya gyara alaƙar su..
Brush kaɗai ta bar sa yayi sai wanka sannan suka dawo suka fara cin abincin nasu cikin so da ƙaunar juna,yana iya faɗin rabon sa da fuskantar hakan daga gare ta wanda ba komai ya sa ta rikiɗe masa ba sai kishin fifi da ta sakawa ran ta..
Da suka kammala shi ya kwashe kayan tunda yana hutu baya on call sai ya shashance akan matar sa through out yau babu inda ya tafi yana tare da ita soyayya yake gwada mata na fitar hankali so yake ta gama yarda da shi har zuciyar ta dan hakan zai taimaka ta cire batun fifi daga ran ta dan suyi rayuwar su..
Yau Komai tare suka yi sa abin gwanin sha'awa,duk da wannan abin da Khalid ya rinƙa yiwa Hamida bai hana ta ware seconds 30 ƙwarara ba wurin son ganin baƙin Mufidah da kasawar ta,haka kawai ta rinƙa tursasa zuciyar ta da kan ta kan sai ta samo wani abu da Mufida ke lacking da zata rinƙa alaƙanta ta da shi,sai dai bata samu dama sosai dan da zarar zata fara tunanin abin sai mijin ta ya ɗau hankalin ta..
Ko da dare yayi bai bar ta tayi zaman tunanin ba ya rinƙa gaya mata sunayen wuraren da yake son su tafi a washegari sannan yana hiran yana showering nata da kisses da tickling dake saka ta dariya,da haka har tayi bacci a jikin sa shima yayi baccin cikin farincikin ganin first move ɗin sa an samu nasara.
****
A ɓangaren su fifi da Marshall kuwa da safe yayi kamar an tsungule sa ya farka ya buɗe idon sa sai ya ga haske daga curtains,juyowa yayi sai ya ga sleeping fifi,ƙura mata ido yayi yana ta kallon ta yana tunanin abinda ya faru a daren jiya,mamaki ya rinƙa yi yana ayyanawa hala Ammy ce ta saka ta yin aikin..
Ɗan taɓe baki yayi ya yunƙura ya tashi zaune yana hamma,ya ɗan sami ƙarfi kaɗan dan dole sai ya haɗa da pills but normal emergency care da ta bashi jiya ma ya taimaka masa.
Zaman kallon ta yayi yana ƙarawa sai da ta motsa a hankali sai yayi saurin kawar da kan sa yana tari..
Tarin nasa ne ya ƙarasa farkar da ita ta tashi tana kallon sa a firgice tana tmbyr me ya same sa sai ya nuna mata hanyar window..
Nan ta kai duban ta sai ta ga haske da sauri baki buɗe ta sauko daga kan drawer ɗin tana mai zuwa kusa da shi..
"Bamu yi sallah ba safe yayi"!!kallon ta yayi sai ta kawo hannu tana son taimaka masa ya tashi ba musu ya karɓi taimakon nata,suka shiga toilet da ƙyar yayi alwalar suka fito ta nemo darduma bayan ta tmby sa inda yake ya nuna mata. ...
Ta shimfiɗa mai ta miƙo mai jallabiya ita kuma ta koma ciki tayi alwalar da sauri ta fito lkcn har ya fara sallah sai ta tada nata iƙamar a ɗan nesa da shi..
Da suka idar sai tsaya jiran sa har ya shafa addu'ar sa,kawai ta ji ya kamata ta gaida sa sai ta yi ƙasa da kai..
"Ina kwana"!mamakin ta duk ya gama cika sa amma ya amsa mata sai ta kuma faɗin.
"Ya jikin naka"!gyaɗa kai yayi yana faɗin
"Alhamdulillah"fatar samin lfy ta mai tayi shiru sai can shi ya ce
"How was ur night"?kallon shi tayi ta saukar da kan ta ƙasa sai yayi murmushi dan ya fi kowa sanin ya night ɗin nasa ya kasance..
Da taimakon ta ya koma ya kwanta ita kuma ta ce mai tana zuwa..
Fitar ta bata zarce ko ina ba sai sashen su Ammy..
Ko da ta shiga sai ta gan su zaune gaida su tayi kawai ta sanar da su Marshall ba lfy daga haka ta haura ta ɗau wayar ta ta fito bayan wasu minutes har ta sauya kayan jikin ta zuwa simple gown mai ɗan kauri sbd yanayin sanyi na garin..
Mamakin ta suka ji ganin bata yi shagwaɓa ko ta tsaya tmbyr su dalilin ƙin buɗe mata ƙofa ba jiya wanda intentionally suka yi hakan duk wai dan ƙaunar ta da Marshall ya girmama..
Dawowa sashen Marshall tayi ta same sa kwance sai ta buƙaci ya bata numbern family doctor ɗin su tana so ta kira sa ya zo ya duba sa..
Miƙo mata wayar yayi bayan ya fiddo da numbern sai ta kwasa a wayar ta tayi dialing,bayan an ɗaga ne suka gaisa ta mai bayanin abinda ke damin Marshall but kasa kiran sunan sa tayi sai cewa take "yaya soldier wai dan doctorn ya gane da wanda take referring..
Shi dariya ta bashi har ta sauke wayar ta miƙo mai yana kallon ta sannan daga bisani ya ce da ita
"Ammy told u to do this right"!?shiru ta mai tana kallon sa,sai ya girgiza kai yayi shirun shi ma..
Ba jimawa Ammy da Hajja suka zo duba sa sai a nan yake jin wai rashin lafiyar nasa yanzu suke ji daga bakin fifi abin ya bashi mamaki wato ita ce dan kan ta ta ji tayi hakan kenan?lallai ashe tana da tunani mai zurfi ba yadda yayi tsammanin ta ba..
Suna zazzaune doctor ya zo ya duba sa ya mai abinda ya dace Ammy ta koma ta kawo masu abinci dan ta lura kamar fushi fifi ke yi da su ganin yadda duk ta maida hankalin ta ga mijin ta sai suka yi ta mamaki haka shima Marshall ɗin sai da suka jima sannan suka tafi ita kuma ta maida hankalin ta gare sa ta bashi magani yana karɓa yana tunanin ɗabi'un ta..
Ita kam ko a jikin ta kula da shi ta saka a gaba a matsayin abunda ya dace ba tunanin abinda Ammy take mata ba..
Ranar dai ta ƙauracewa su Ammy a nan part ɗin ta kwana dan bashi kula ta musamman kamar yadda doctor yayi ta nanatawa wanda tun su Ammy na damuwa har suka daina suka haƙura suka zuba mata ido.
Chan cikin dare tana kwance a parlor kamar jiya sai ta rinƙa tunanin rayuwar ta da na ƴar uwar ta Hamida numfasawa tayi ta juya tana mai cigaba da tunanin ta,rasa yadda aka yi ta kasa fahimtar halin kuci da zafi da Hamida ta shiga ciki tun yarintar su tayi har kawo girman su..
Ji tayi kwata kwata bata kyautawa kan ta ba ita tana ta kwace soyayya Hamida na can cikin damuwa da rashin kulawa wai amma bata taba sani ba,a duk lkcn da ta tuno wannan abin ran ta kan sosu ba kaɗan ba..
Daga wannan ranan Ta ma kan ta alƙawarin safiyar gobe a sashen Hamida zai mata tunani tayi da hala halin da take ciki rashin sauraron ta da Hamida bata yi ne ya sa take fuskantar wannan abin hakan ya sa ta yanke zuwa duba ta gobe ita ko zagin ta Hamidar zata yi ta yi in dai zata furta mata kalmar yafiya toh ita tayi alƙawarin cike mata gurbobin da ta rasa na soyayya a rayuwar ta..
*****
Da safe bayan ta gama abinda zata yiwa Marshall ta ce mai tana zuwa sai bai ce mata komai ba dan sabbin ɗabi'un nata na mai shammaki..
Gaban ta na faɗuwa ta iso part ɗin su Hamida ta tsaya ta rasa ya zata yi sai dai ta ɗan natsu ta yi sallama a hankali,sau uku tana yin sallama sannan aka zo aka buɗe ƙofar wanda fuskar Khalid ne ya bayyana..
Da mamaki ya gaida ta sai itama ta gaida sa tana tmbyr sa ko Hamida na ciki,cikin tausayin ta ya amsa mata da eh..
Hamida dake tsaye bakin kitchen tana rige rigen ɗora breakfast ita da Khalid da kamar competition ne sai kawai ta gan sa tare da fifi..
Take ta ɗaure fuska ta haɗe rai,yana kallon sauyin yanayin ta fifi kuwa da zuwa tayi saurin ƙarasawa gare ta murya na rawa ta buɗe baki zata yi mgn sai Hamida ta kawar da kan ta gefe..
Kallon ta fifi tayi
sai ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta kuma yunƙura ta ce
"Ina kwana Hamee"!wani kallon ƙiyayya Hamida ta watso mata ta ja tsaki ta juya zata tafi sai muryar fifi ya mata amo a kunne da ɗan ƙarfi
Tace "Hamida kiyi hakuri ki sassauta min dan Allah am sorry,am deeply sorry ki yafe min,wlhy wlhy ban san ya zan hukunta kai na akan laifin da na maki ba,na kasa samin sukuni a zuciya ta am deeply blaming myself for this mistake and i swear i want to make it up to u am ready to make u happy just listen to me ko da sau ɗaya ne"!!
juyowa Hamida tayi ta kalle ta ranta na ɓaci ba kaɗan ba sai ta watsawa Khalid ɗin kallo shima sannan ta ja doguwar tsaki tayi wucewar ta..
Gwiwar fifi ne yayi sanyi nan da nan hawaye ya kawo mata sai ta dubi Khalid da idanun ta dake cike taf da hawaye ta ce mai
"Am sorry,,i truly am"...!!duk tausayin ta ya ishe sa ya san abin na damin ta sannan ba laifin ta bane laifin iyayen su ne but da alama Hamida ta gaji, wa ke da laifi waye baida shi bata dubawa for all she cares shine tana jin mummunar kishin Mufida kuma kishin nata ya fara rikiɗewa zuwa ƙiyayya...
Fita fifi tayi ta koma sashen Marshall inda a nan ta riƙe ƙirjin ta ta fara zubar da hawaye a hankali ko da Marshall ya fito a bazata dan haɗawa kan sa tea ganin bata dawo da wuri ba sai ya gan ta tana kuka..
Kallon ta yake yi daga bisani ta ji muryar sa a kan ta sai tayi saurin ɗagowa ta dube sa,da sauri ta goge hawayen ta tana tmbyr sa me yake so..
Da kamar ya kuma tmbyr ta me ke damin ta amma sai kawai ya faɗa mata abinda yake buƙata haka ta je ta haɗo mai ta dawo da shi ta bashi.
Yana ankare da ita through out yau bata da walwala duk da dai ba sanin halayyar ta yayi ba amma daga shekaranjiya zuwa yau ya ɗan karance ta..
Da damuwar Hamida Mufida tayi bacci yau kuka kam kamar yau ya fara bijiro mata dan sosai ta yi sa tana yi tana tunano lifetime ɗin su a baya,ta dai san ko dukan ta Hamida zata yi ba zata daina bibiyar ta da nemar yafiyar ta ba har sai ta yafe mata dan ita kaɗai ta san irin halin damuwar da zuciyar ta ke ciki haɗe da nauyin da zuciyar nata ke mata akan rashin kula ta da Hamida ke yi..
#Mamuh*25*
Da safiyar washegari fifi ta kuma maimaita abinda ta yi a safiyar jiya na yau ma Marshall bai da masaniya a kai ta tafi sashen su Hamida,har Khalid ya buɗe mata ƙofa sai ya tuno abinda ya faru a jiya da irin rarrashin da ya rinƙa yi wa Hamida akan ta saurari fifi ko da sau daya ne amma ta rufe idon ta ta nuna mai bata jin zata iya yin hakan duk kuwa da shi kan sa ya san abin na taɓa ta kawai rinjayar ta da kishin yayi ne ya sa take ɗauke kan ta akan abubuwan..
"Ina kwana Khalid"ta gaida sa ya amsa sai ta tmby sa lfyr Hamida nan ya ɗan yi shiru wanda ya bata amsar ta akan ba lfy ba kuma har yanzu fushi Hamida ke yi da ita..
Hawaye ne ya cicciko mata a idanun ta na tausayin kan ta da fushin da ƴar uwar ta ke yi da ita..
Kallon Khalid tayi sai ta ji zuciyar ta na mata zafi tana buƙatar wani wanda zai fahimci halin da take ciki..
"Khalid ai ka san manufa ta ko?ina so in gyara tsakanin mu da Hamida am deeply sorry for all my mistakes i really want to clear her mind akan alaƙar mu,na roƙe ka ka haɗa ni da ita i hv to talk to her"!!kuka me sanyi ne ya kusa cin ƙarfin ta sai Khalid ya kasa cigaba da kallon ta a haka kawai ya juya wai dan ya je ya ma Hamida mgn ta fito..
Juyawar sa ke da wuya ya hango ta tsaye bayan su tana bin su da kallo sai Khalid ya ƙarasa gare ta da sigar rarrashi..
"Hamida...Pls ki bada ƴar uwar ki ta gyara abinda ya faru kar fah ki manta ba itace kawai ta maki wannan laifin ba gashi ta ɗau laifin kuma ta yarda zata gyara ita kaɗai toh me zai sa ke kuma ba zaki fahimce ta ba?uhm"?kallonsa Hamida ta yi ta kuma kalli fifi dake tsaye tana hawaye ji tayi kamar tazo ta rungumeta amma tana tsoro..
Duk halin da fifi ke ciki abin na taɓa Hamida a zuciyar ta sai dai ta rasa ya zata yi controlling fushi da kishin ta akan fifi hakan ya rikiɗe ya zama kishin fifi ƴar uwar ta ya rinjaye ta har bata iya fasalta ƙarfin kishin nata..
Tsawon lokacin nan ace bata san da nemo min farinciki na ba sai yanzu?
In dagaske tana so na kuma ina da muhimmanci arayuwarta meyasa da chan bata iya bambamce bacin rai na da jin dadi na ba?meyasa bata karance zafi da kunan dake yawo acikin fushi na ba a duk sanda aka ware ni aka nuna min ni ba komai bane sai ita,....saida na furta?
Wannan ba kaunar mu bane,kowa kansa yafi so ya tafi kauna,dan haka nima kaunata ni kadaice bazan sake shi ba...
Kawar da tunanin da tayi yanzu ta yi ta dubi fifi dake kuka ta gasa mata kalmar nan da ke ma fifi zafi a zuciya.
"I hate liars and pretenders ki fitar min daga apartment"!
A hankli ta faɗa so calm and gentle ta yadda ta san zai taba fifin emotionally..
Ta kuwa yi nasara dan sosai fifi ta fashe da kuka mai ban tausayi haka ta juya ta fita ita kuma Hamida ta jingina bayanta da staircase har sai da Khalid ya matso ta ya rungume ta yana bata sassayanr runguma,shidai ba wai yana ƙoƙarin tursasa mata zuciya akan sai ta yafewa fifi bane a'a yana gudun kar kishin yayi yawa ya fi haka ne har ya zo ya taɓa martabar gidajen auren su gaba daya..
Gabaɗaya ranar Khalid aikin ban haƙuri da nuna ƙauna ya rinƙa yi wa Hamida tun tana ɗan kawar da kai har dai ta fara sauraron sa suka dawo daidai Yayin da fifi ta kasa samin kwanciyar hnkl tun bayan fitar ta daga sashen su Hamida daurewa tayi ta bincika kitchen ɗin ta ga abubuwan dafawa ta zaɓi wanda ya dace ta girkawa Marshall dan yanayin rashin lfyr sa..
Haka yau ma ya gan ta tana kuka amma ɗabi'ar nan ta bana shiga abinda babu ruwa na,jin kanshi yake kamar ai fifi yarinya ce ita shi kam ya haife ta ya juya ya dubeta baya jin wani tsaurara mata tambayoyi akan dalilin kukan ta zai ƙara mai mutuncin sa instead sai dai ta raina sa dan zata ga ya damu da ita..
Haka nan itama tayi ranar kaf cikin damuwa da kuka akai akai,abu kamar wasa zazzaɓi ya fara shigar ta a hankali amma ta yi ta dannewa tana kama jikin ta tana ma Marshall ayyukan da ya dace..
Sam bata cika damuwa da auren bata kamar yadda t sa lamarin hamida aranta,tasan sun ma hamida rashin adalci kuma bata ganin laifin kowa sai kanta ayanzu
Ba abu ne mai sauƙi ba a gare ta tun tana ganin zata iya gyara komai ita kaɗai har ta fara fiddo damuwar ta sarari in Marshall ya fita zai dawo ya same ta tana kuka,ba zata jira ya tmby ta ba zata fara tmbyr sa shin bata da hali mai kyau ne,abin na ɗaure masa kai dan shi bai san sanadin kuka da damuwar ta ba kuma baiyi lokacin tambayarta ba..
Kimanin sati biyu kenan masu kyau Mufida ta ɗauka tana ƙoƙarin ɗinke tsakanin ta da Hamida amma a duk lkcn da ta kusanci inda Hamida take sai Hamida ta bata wasu irin halayyar
Munana masu zafi
Hamida ce wacce bata rasa komai daga wurin mijin ta ba dan ba ƙaramin kula da ita yake yi ba
haka fifi take ziriyar sashen ta zuwa na Hamida a kullum a ƙalla sau uku ko huɗu a rana amma zuciyar Hamida ya mata dauri me wuyan kuncewa...
Abubuwa dayawa inta tuna takanji tsanan fifi da duk wani wanda ya lalata mata zuciyan ta ya dawo baki
Rayuwa ba ƙaramin sauyawa fifi ta yi ba ba dan komai ba