Showing 39001 words to 42000 words out of 101986 words

Chapter 14 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15646

ta tafi...
#Mamuh*17*

Ammy na shigowa ta taso ta zo ta faɗa jikin ta tana murmushi,da murmushin itama Ammy ta tarbe ta tana mamakin farincikin ta na yau dan a kwanakin nan ba kasafai ta fiye sakin jiki tana dariya ko fara'a ba sai ya zama dole.
"Baby me ya faru na ga yau kamar annashuwa kike ji"!gyaɗawa Ammy kai tayi tana lumshe idanun ta har suka zauna kafin ta tafi straight to the point ta bayyana Ammy abinda take so..
"Ammy so nake in koma makaranta tunda zaman wurin ɗayan yakan ɗan ishe ni ba dan bana jin daɗin kasancewa tare da ku ba sai dan ina tunanin tunda ban da wani abin da nake yi a nan sai zaman gida kuma baki yarda in taya ki aiki,so please kar ki hana Ammy komawa ta makaranta zai kawo min cigaba a rayuwa ta fiye da da tunda kin ga bana komai kuma dama ina manta wasu abubuwan amma in na koma makaranta na maida hankali na sai in fito da sakamako mai kyau ko Ammy na"?tayi maganar tana daɗa kwantar da kan ta a jikin Ammyn..

Shiru Ammy tayi tana sauraron ta har ta gama,ba hana ta take son yi ba hasalima jin dadin shawarar nata tayi ko ba komai ba zata rinƙa ƙarar da lokutan ta cikin tunani ba,matsalar yanzu shine wa zai rinƙa kula da ita a makarantar kuma wani irin makaranta ya fi dacewa da ita inda ba za a rinƙa ɗaga mata hankali ba..
Shiru ta sai ya saka fifi jin wani iri a tunanin ta ko Ammy bata yi na'am da shawarar ta bane sai ta kuma lafewa jikin Ammyn tana shirin shagwaɓa..
Murmushi Ammy tayi ta shafo kan ta ta bayyana mata fargabar ta amma fifi na nuna mata ai ba komai ita ɗin ai ta girma ba zata yarda hankalin ta ya rinƙa tashi ba zata kula da kan ta..

Da ƙyar Ammy ta yarda da kalaman ta dan cewa tayi sai an samo mata masu kula da ita amma ta tuɓure akan ita kan ta tayi girman da zata iya kula da kan ta,sai Ammy ta ce mata ba komai dama lokacin siyar da form ne sai cewa fifi zata yi magana da daddyn su duk yadda ake ciki zuwa nan da 2 weeks ta san komai zai kammalu...
Runguma sosai fifi ta kaiwa Ammy tana ta yi mata godiya da fatar gamawa da duniya lafiya,sai da Ammy ta dara ganin yadda fifi ta karɓi ragamar Ammyn ita kuma ta zamo kamar ita ce fifin dan irin adduo'in da fifi ke mata bai da maraba da addu'ar da uwa ke wa ƴaƴan ta..

Throughout ranar fifi ta yi sa ne cikin annashuwa da jin daɗi bata yarda ta saka damuwar Hamida ko wani a ran ta ba,kiran Dr Fatima Yonas tayi ta faɗa mata ai zata koma makaranta kuma burin ta na son zama cikakkiyar ƙwararriyar mai kare rajin haƙƙin ɗan adam wato Human right archivist na gab da cika,murna sosai Dr Fatima ta mata haɗe da fatar alheri da samin nasara a ƙarshe ta tambaye ta ya Hamida take dan sun ɗan jima basu yi magana ba ko ta waya..
Wani abu ne ya ziyarci zuciyar fifi jin sunan Hamida da Dr Fatima ta kira amma sai ta danne zuciyar ta ta amsa mata da tana nan lafiya ƙalau a haka suka ƙarasa hirar tasu suka yi sallama..

Kiran Ameed tayi shima ta faɗa masa ya mata murna da barka tun kafin abin ya kasance,Meena ce mutum na ƙarshe da ta sanarwa shima sai bayan hirar su da suka yi suka gama..
A iya nazari da lissafi fifi ta lissafa kwanaki goma sha huɗu kenan rabon ta da Hamida abin da ko a mafarki aka faɗa mata zata ƙaryata wai ita da ƴar uwar ta ta jini sun zamo ko ga maciji basu yi kuma suna zaune gida ɗaya..

Tun ranar da Ammy ta sa aka yi musayar kayan ɗakin su akan ai kayan fifin aka kai ɗakin da Hamida ke ciki presently ita kuma na Hamida na sashen fifi sai ta sa aka je aka kwashe kaf hatta da akwatinan fifi sai da ta sa aka musanya akwatinan da yake sashen Hamida da ta ƙi aka kwasa aka kai mata wanda su Ammyn ne suka yi na fifi kuma aka dawo mata da su amma waɗanda angwayen suka yi sai ba'a canza ba dan dama an sami sauyin angwayen,toh ranar da Ammy ta saka aka yi wannan kwashen ba ƙaramin ƙiyayyar fifi ta jefa a zuciyar Hamida ba wato ita bata yi deserving abu mai kyau ba kenan,tun ranar da fifi da ta fito ta leƙa ta ga abinda ke faruwa ta ce da Ammy ai ba wani amfani sauya kaya amma Ammy ta ce no sai an sauya ai ita Hamidar rufe ido tayi ta aure Khalid so dan me tunda yanzu itama da nata mijin ba za a saka mata kayan da yake mallakin ta bane,tun ranar da ta hangi Hamida bata kuma ganin ta ba har rana mai kamar ta yau..

Da maganar su da Ammy yanzu ya kai kwanaki tara bata dai san ya ake ciki ba but tana ankare da kwanakin kuma takan yiwa Ammy godiyar ƙoƙarin da take yi akan ta time to time ita kam Ammy bata cika son jin hakan ba dan gani take kamar fifi bata gama sakin jiki da ita ba..

****
Fannin rayuwar su Hamida ita da mijin ta soyayya ake yi ba ji ba gani kamar akan su aka fara soyayya,duk damuwar family ɗin nasu baya hana su nunawa junan su kulawa da soyayya dan shirin tafiya zuwa wani wurin shaƙatawa ma suke tunda plan ɗin su yayi failing ba yadda suka tsara sa ba akan bayan bikin zasu tafi honeymoon toh yanayin bikin ya sa suka ɗan dakata har sai yanzu da abubuwa suka ɗan yi masu sauƙi..

A kullum dai kafin Khalid ya tafi aikin sa zai shiga ya gaida Ammyn sa da Hajja but iyakar amshin su bai wuce lafiya ba bayan haka babu canji tun faruwar lamarin har kawo yanzu,haka zai tafi aikin sa ya dawo ya kuma shiga gaida su da gida babu bambanci abin na damin sa ba kaɗan ba.
Ko ga kan matar sa Hamida duk haka ne basu sauraron ta ita dai abin bai wani ɗaɗa ta da ƙasa dan mijin ta ya gama yi mata komai tunda ya ɗaukaka soyayya da ƙaunar ta a zuciyar sa da ruhin sa,she doesn't care about irin attitude da suke bata a gidan..

Tana ƙoƙarin yiwa mijin nata hidima da sauke haƙƙoƙin da ya rataya akan ta na aure,a wannan fannin kam Khalid bai da matsala dan bayan matsalar family ɗin sa da irin ƙibar da zai yi sai ya fi wanda yayi a yanzu.
Bai cire rai ba ya san watan wataran iyayen nasu zasu yi accepting relationship ɗib su da auren su kuma su yafe masu,yana buri da addu'ar zuwar wannan ranar...

Sun shirya tafiyar su dai dai ƙarshen wata wanda yake daidai da lokacin da fifi zata fara zuwa makarantar ta,burin Hamida bai wuce su kai ziyara ɗakin Allah ba a matsayin umara after that sai su zarce zuwa ƙasar Oman dan jin daɗin honeymoon ɗin su.
Zaɓin ta ya zamo na Khalid dan haka ya amince aka yi processing masu visa suka haɗa kayayyakin su ɗan kaɗan a cewar Khalid ta bari in suka tafi can zasu sayi wasu kayayyakin...

Ana washegari zasu tafi Khalid ɗin da kan sa ya shiga sashen Ammyn sa ya gaida ta ta amsa mai kamar kullum sai ya fara nemar yafiya da afuwar ta akan tafiya zasu yi shi da matar sa ya san tana fushi da shi amma ta yafe mai dan ya ga haske a wannan tafiyar tasu duka su biyu tunda tafiyar hanya ce ba lallai bane su dawo a raye in kuma ta Allah ta kasance akan su yayin da take fushi da su ba zai ga rahamar ubangiji ba..
Ba ƙaramin shigar ta kalaman sa yayi ba sai ta ji zuciyar ta na gaza cigaba da fushin da shi abu ne da bata saba yi masa ba,bata da wani zaɓin da ya wuce sassauta fushin nata ta mai addu'a shi da matar nasa ta masu fatar alkhairi da farinciki mai ɗorewa a rayuwar su..
Kasa natsuwa yayi sai ya je ya rungume ta yana murna kimanin watanni uku kusan na huɗu kenan Ammyn sa bata sauraron sa yau ta saurare sa sai ya ji kamar an sauke mai nauyi a zuciyar sa..

Ko da aka sanar da Hajja bata wani yi freaking out ba sai addu'ar Allah ya kai su lafiya ya dawo da su lafiya that's all so duk da bata sauya ba amma ya ji daɗin addu'ar ta gare su..
Next target ɗin sa shine ya gana da fifi ya roƙe ta dan gani yake ko Ammy ta yafe masa haƙƙin fifi dake kan sa kaɗai ya isa ya hana sa jin daɗin rayuwar sa da Hamida amma duk iya ƙoƙarin sa na son su haɗu haƙar sa bata cinma ruwa ba dan Mufida bata da lokacin su tana can tana murnar samin gurbin karatun ta a Abuja university da lectures date ɗin ta fixed sati ɗaya mai zuwa,jin daɗin wannan gurbi da ta samu bai bar ta ta saurari labarun su Ammy ba bare ta san me labarun nasu ya ƙunsa ba..

A washegari tun asubahi jirgin su Khalid ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki sun tafi cike taf da adduo'in Ammy da na daddyn su Hamida da Khalid ɗin ne dai ya kira ya sanar da shi dan jin ko zai sassauto shima duk da dai dama ba wani ɗaukar zafi yayi sosai ba irin na su Ammy ba...

****
Wuraren 8am fifi ta fito cikin shirin ta na tafiya makaranta inda ta sami su Ammy zazzaune ana cin breakfast ga nata nan rufe ana jiran zuwar ta..
Fuskar ta ɗauke da fara'a ta ƙaraso tana gaida su,suna amsawa tana zama cikin sauri ta tambaye su ya daren su suka amsa da lafiya..
Sauri sauri ta ci abincin ta tashi wai zata tafi sai Ammy ta aje spoon ɗin ta tana kallon ta da mamaki
"Baby ina zaki tafi ba ki kammala cin abincin ki ba fah"!dariya ta ɗan yi ta zo ta bayan Ammyn ta rungume ta tana mata kiss ta ce
"Ammy na duba lokaci ki gani tara saura kuma ina da first lectures ɗi na by 10am beside na ƙoshi sosai kuma in ma yunwar na ji ai zan nemi school cafeteria in ci abinci sannan in cigaba da attending lectures ɗi na"!!a dame Ammy ta miƙe tana faɗin
"Wait for me ina zuwa"!bin ta da kallo fifi tayi tana jinjina irin ƙaunar da take mata sai Hajja ta yafito ta da hannu,saurin ƙarasawa tayi sai tayi murya ƙasa ƙasa ta ce
"Kin san Ammyn ku,abinci ta je kawo maki,kar fah ki bari karatu ya sha maki hankali ki ƙi cin abincin dan tun jiya take ta haɗa maki ta ce ƴar ta zata fara zuwa school dole ranar farkon ta ya zama abin tarihi a rayuwar ta dan haka ta dage ta maki girki mai daɗi so ki tabbatar kin ci abincin kar ki dawo da shi ta gani kin ga ai ran ta ba zai yi daɗi ba ko"?gyaɗa kai fifi tayi tana murmushi haɗe da jin son Ammy na kuma shigar ta..
Suna haka sai Ammy ta fito da wata ƙaramar basket mai cover ɗauke da food warmer da wani watter bottle kamar na ƴan primary school..
Yau da Mufidar da ne da ta tsaya ta yi dariyar ta son ran ta dan wannan shirin Ammyn shirin ƴan primary ne amma kasancewar rayuwa ta sauya ta zuwa ɗaya fannin ta sai kawai ta murmusa ta ƙarasa ga Ammyn ta amshi basket ɗin tana mata godiya da alƙawarin zata cinye abincin duka..
Har bakin mota Ammy ta rako ta da Hajja suna mata addu'ar nasara a ranar farkon ta sai da Ammy ta gargaɗi drivern da yayi tuƙi a hankali daga nan gida zuwa cikin university ɗin ba doguwar tafiya bace dan haka kar yayi gudu da fifi su tafi a hankali...
Murmushi kawai Mufida ke ta yi masu dan suna bata dariya da over protectiveness ɗin su,waving nasu tayi suka maida mata motar ya tashi suka fita su kuma suka dawo gidan suna tattauna yanayin rayuwar gidan da ya sauya ba yadda suka so ya tafi ba kafin bikin..
A nan Ammy ke ɗago zancen Saheeb akan ya kamata ya zo su ga juna da fifi ko da sau ɗaya ne in komawar zai yi sai ya koma amma ya zo ya gan ta damuwar ta kenan,Hajja ma ta matsu ya dawo dan tayi kewar sa ba kaɗan ba..

****
A fannin fifi kuwa tana iya cewa ranar ta na farko a makaranta rana ce da ba zata taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwar ta dan abubuwan al'ajabi,ban mamaki da ban dariya ta rinƙa gani wanda a germany bata taɓa experiencing irin wannan school life ɗin ba kasancewar can kowa minding business ɗin sa yake yi amma nab ko baka da niyar magana wani sai ya saka ka yi..
Ƙalau ta ida lectures ɗin ta aka dawo da ita gida,tun daga farfajiyar gidan Ammy ta san an sami nasara a makaranta..
Biyewa fifi tayi ta fito tana amsa kiran ta,rungume Ammy tayi ta hau labarta mata abubuwan ban mamakin da suka faru a idon ta yau,ita da Ammy suka rinƙa dariya sai farincikin Ammy ya ninku ya ɗare na fifi duba da yadda yau kaɗai ta sake tana dariya abin da ta jima rabon ta da yin sa..

Har dare in fifi ta tuno wani abin sai ta rinƙa dariya ita kaɗai kusan kaso saba'in cikin ɗari na damuwar ta ya tafi kuma tayi farinciki da faruwar hakan..
Bayan sun gama dinner ta je ta kwanta har ta riga Ammyn bacci a cewar ta ta zamo ƴar makaranta dole ta rinƙa minimizing time ɗin ta kar ya rinƙa tafiya ba tare da ta aiwatar da abu mai muhimmamci ba..

A kwana a tashi ga mai rai ba wuya,fifi ta cinye semester ɗaya har tana gab da zana jarabawar ta saura sati ɗaya hankalin ta duk ya karkata ne ga karatun ta bata son disappointing Ammy da Hajja duba da irin so da ƙaunar da suke mata she want to make them proud...
Ko da Ammy ta sanar da ita tafiyar su Hamida sai ta share zancen ta masu fatar more tafiyar tasu lafiya ita kuma tayi facing damuwar ta dan bata so ta fara jarabawa da layin baya duk da ma bata san nature ɗin jarabawar nan ba amma ta dage sosai sai shirya mai take da makaman karatu..

Rannan da dare tana karatun ta misalin ƙarfe ɗaya na dare sai Ammy ta farka ta gan ta gaban littafi saman table abin sai ya dami Ammy ta taso ta zo ta rufe littafin,ɗago kai fifi tayi sai ta ga Ammy ta ɗan ɗaure fuska sigar kar ma fifin tayi tambayar dalili ko magiyar a bari ta ƙarasa..
Bata jira ta cewar ta ba ta ja hannun ta ita kuma tana murmushi ta bi Ammyn,Ammy bata dakata ba sai kan gadon ta inda ta saka fifi kwanciyar dole ta rufe ta ta je ta kashe wutar ɗakin ta bar na gefen gadon ta ce da fifi
"Go to sleep dare yayi"gyaɗa mata kai tayi tana murmushi mai sauti sai kuma ko me Ammyn ta tuno bayan ta juya baya ta kuma Juyowa ta kalli fifi da idanun ta biyu ta ce
"Baby yayan ku zai dawo nan da kwanaki uku kuma sashen sa na buƙatar gyara ina tunanin assigning wasu su mai gyaran amma babu yarjewar ki shi ya sa nayi delaying dan na ga hankalin ki na kan karatu kar in takura ki ya kika gani kin yarda su shiga su yi gyaran"?kasa fahimtar Ammy fifi tayi ita meye haɗin ta da Khalid da ake nemar permission ɗin ta wurin gyara masa sashe sai ta dubi ta ce
"Ammy ai matar sa zaki tambaya ni ina ruwa na da sashen su"!kallon ta Ammy ta yi sai ta ce
"Da zan so hakan amma matar nasa ba sanin wurin baccin sa tayi ba bare lafiyar sa tana can wani ƙasar daban but ke da kike nan nake nemar yarjewar ki"gaban Mufida ne ya faɗi jin zancen Ammy..
Wai ashe da ita ake yi da aka ce yayan su zai dawo,kaf tunanin ta ya ta'alaƙa akan Khalid ne,ashe wai nata mijin ake nufi.
Dafe goshi tayi ta kalli Ammy sai ta juya mata baya kuma gaban ta na cigaba da faɗi,Ammy sai tayi tunanin hala kunya ce ta kama fifi sai ta ƙyale ta ta kashe hasken dake gefen ta ba jimawa bacci ya ɗauke ta,ita kam ko gyangyaɗin kasa zuwar mata yayi fargaba ne tattare da it da alhinin irin yanayin mijin nata da zata gani in ya zo ohh ita Mufida auren tsoho bata taɓa mafarki ba da ƙyar dai baccin ya ɗauke ta bayan doguwar tunane tunane...
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*18*

Zazzaune suke bisa dinning suna breakfast Ammy sai bin fifi da kallo take dan son gano wani abu amma haƙar ta bata cin ma ruwa ba dan ƙeƙashewa Mufida tayi bata yarda sun haɗa ido ba sai abincin ta da take ta ci tana hira da Hajja suna ɗan ɗariya ƙasa ƙasa.
Suna yunƙurin kammala cin abincin sai Mufida ta ji kamar an tsikare ta wuf ta tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login