Showing 93001 words to 96000 words out of 101986 words

Chapter 32 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15654

wanda daga shi har Khalid ɗin babu wanda ke da masaniya akan likitan da take gani a ɓoy,duk kuwa da Khalid yana iya ƙoƙarin sa na ganin ya bata extra care but bata yarda ko secretly ba tare da sanin Hamida ko mijin ta ta sanar da shi conditions da doctorn nata ya bata ba game da yiwuwar haihuwar ta...

Lyk always yau ma tayi shirin ta cikin maternity gown ɗin ta ta saka ƙaramin hijabi ta tako da ƙyar ta fito zuwa farfajiyar gidan tana duba motar da driver ke jiran ta dan zata tafi ganin likitan ta sbd Saheeb baya nan kuma a nan gidan ta sallame su ne akan wurin Khalid zata tafi dan a mata dubiya ta musamman dan ta ƙi yarda a kawo mata scanning machine ɗin gidan dan in hakan ya faru ta san zai yi wuya ta haɗu da likitan ta da suka haɗu a yawon binciken ta ta waya har dai abin ya kai su ga haɗuwa concurrently...

Motar ta nufa ta shiga tana ajiyar zuciya kamar tayi gudun tsere dan cikin ya mata nauyi ga matsalar cardiac disorder dake damin ta wato health issue ɗin ta..
Jan motar yayi suka fita,sai dai yau bata bari sun fara zuwa wurin Khalid ba ta ce mai ya kai ta ɗaya wurin da yake kai ta in sun baro wurin Khalid..

Juya kan motar yayi suka nufi asibitin likitan ta inda ya duba ta ya kuma bata shawarwari da gargaɗin kar ta rinƙa ɗaga hnkl ta dan the more tana ɗaga hnkl ta the more damuwar ta zai yi muni,haka dai ta karɓi drugs ɗin ta ta koma mota suka tafi asibitin du Khalid inda nan ma ya bata kula ta musamman kafin su dawo gida...

****
Tunda fifi ta shiga satin haihuwar ta fargabar ta ke gaba gaba,ba laifi tana samin kula daga wurin Hamida da mijin ta Saheeb sai dai kular ragagge ne dan ba wani enough tym gare sa ba,a wannan yanayi ta fi buƙatar sa sai dai ya mata nisa dole ta haƙura wasu lokutan ya rinƙa attending travelling ɗin sa dan suna da muhimmanci duba da matsayin sa...

Suna zaune a parlor suna hira,Hamida,Ammy da fifi wacce jefi jefi take saka masu baki dan bacci baccin dake ɗibar ta..
La'akari da baccin da ta fara yi ne ya sa Ammy yi ma Hamida alama da su ƙyale ta ta huta,daga nan suka fita suka bar mata parlorn inda ta cigaba da baccin nata bisa wani ƙaramin mattress da ta maida sa abin kwanciya in ba ɗakin ta take ba...

Cikin baccin nata ta ji muryar Muhibba na maganganu wanda bata gane ba sai ta daure ta buɗe idanun ta,nan ta ga tana ta kai tana komowa ita ɗaya,waya sagale a kunnen ta tana mgn da alamar damuwa a muryar ta...
Bin ta da kallo fifi tayi kawai ta maida idon ta ta rufe dan in da sabo ta saba da halin i don't care da Muhibba ke nuna mata ita da unborn baby ɗin ta,duk da tana ganin kamar Muhibban ta san very soon zata mutu ta bar mata mijin nata su cigaba da rayuwar su kamar yadda kullum take nanatawa kan ta...

Jin muryar ta tayi tana faɗin
"Ban sani ba amma zafin da nake ji yanzu ya fi na da doctor,ka taimake ni pls,i don't wanna die soon"..
Gaban fifi ne ya buga jin kalmar mutuwa daga bakin Muhibba wic means ciwon da take yi yana iya yin sanadin rasa ran ta kenan...

Kamar ta tashi amma ta fasa ta bari akan zata ma Hamida mgn in ya so sai a sanar da su Ammy abinda Muhibba ke fuskanta dan kar ayi rashi biyu..
Ta tausayawa Marshall ba kaɗan ba tayi zaton ita kaɗai ce ke cikin matsala da damuwa ashe damuwar Muhibba ke ciki itama kawai dai nata tana ɓoye sa ne dan ita babba ce kuma babu wanda ya sani cikin iyayen su...

A daren ranar suka yi waya da Saheeb ta ji kamar ta sanar da shi amma ta fasa,sai da suka gama sannan ta kira Hamida ta mata bayani sai dai to her greatest surprise sai ta ji Hamida ta ce mata
"Sweetheart pls ki kula da kan ki before anyone else,it's all about u and no one but u,ok so good nit je ki kwanta"daga haka ta kashe wayar..
Haka fifi ta kwanta cikin jimami da zullumin me zai zamo sakamakon rashin lafiyar su su duka kuma ya Saheeb zai ji in ya san duk ciwon da suke yi na ajali ne..
#Mamuh[8/24, 8:12 AM] +234 808 540 5215: *38*

Tun daren jiya fifi ke jin ta aani iri wanda ba komai bane sama da labour pains dan kuwa ranar ta gabato but sai tayi ta sharewa dan da ya mata sai ya tsaya,ganin haka ya sa ta kyale abin kawai ta sha pain relief ta kwanta tayi baccin ta..

Da gari ya waye sai ta ji sayau babu ciwon babu alamar sa sai ta ɗan yi ayyukan da zata iya yi kafin daga bisani ta tafi tayi wanka..

As always yau ma maternity gown ɗin ta ta saka na atamfa ta saka hijab ta fito tana tafiya a hnkl har ta iso sashen su Ammy...
Da Hajja ta fara cin karo wacce take zaune bisa three seaters tana danna counter dake hannun ta,tana sanye da hijabi..

Saurin taro ta tayi tana mata faɗar karambanin da tayi na zuwa nan sashen alhalin ta san ba wani lafiya ne da ita ba..
Murmushi kawai tayi ta zauna da ƙyar suka gaisa da kakar nata inda ta tmby ta me take buƙatar ci sai ta ce mata duk abinda ta ci itama shi zata ci..

Kiran mai girkin su tayi ta umarce ta da ta kawo ma fifi kunun accan da ta mata da alale kuma ta saka man shanun da ta saka mata..
Murmushi fifi tayi ta shiga zolayar kakan nata tana ce mata ta fiye kwaɗayi duk ita kaɗai ta ci wannan abin..

Dariya kawai Hajjan ta mata tana ce mata lallai tayi ƙwari tunda ta iya tsokanar faɗa.
Suna zaune a wurin aka kawo mata abincin ta zauna ta ci sosai har ta kammala sannan ta dubi Hajja ta ce mata

"Hajja ƙila fah abinci na na ƙarshe kenan a duniyar nan,kamar ta ƙaro min"!!wani faɗi gaban Hajja yayi dan straight foward person ce fifi bata ɓoye ɓoye shi ya sa ta faɗi abinda ke ran ta...

Matsowa kusa da ita Hajja tayi sai ta rungumo ta ta gefe tana mata kul da kuma nanata wannan kalmar but fifi insisted ta cigaba da furta mata kalmar rabuwa..
Sosai ta karya zuciyar Hajja har hawaye ya cicciko mata a ido but bata bari sun zubo ba sai ta aika a kirawo mata Ammy...

Ammy na zuwa da ƴar fara'ar ta sai ta ga mahaifiyar ta na ɓoye fuskar ta kamar kuka take yi..
Da sauri ta ƙaraso ta hau tmbyr ba'asi inda Hajja ta nuna mata fifi,ita kuma ta maida idon ta ga fifi...

Ko kafin ta ce zata ce wani abin har fifi ta fara yi mata mgnr mutuwa kamar dai yadda ta ma Hajja..
Zuciya a karye Ammy ta matso ta rungume ta tana kuka tana faɗa mata InshaAllah she will pass through da yardar ubangiji,kuma zata raini ƴar ta ko ɗan ta da kan ta..

Ita dai jin su kawai take but ta san abu ne mai wuya bcos likitan ta ya faɗa mata kuma ita kan ta ta san tana ji a jikin ta komai ba lfy bane sai dai ganin halin da suka shiga ciki sai bata cigaba da kira masu kalmar mutuwar ba ta dai yi shiru...

Ta jima a nan wurin su Ammy suna ta nan nan da ita dan dai kar ta kuma tado mgnr mutuwar nan,Ammy kam sai da ta ɓoye kan ta a ɗakin ta tayi kuka sosai dan ta san gaskiya fifi ke faɗa,bcos an sanar da su,Khalid ya faɗa masu a scanning ɗin ta an gano tana da matsalar zuciya kuma ba lallai bane ta iya haihuwa da kan ta ba but ita ta ce ta fi so a bar ta tayi labour da kan ta..

"Wannan masifa da me yayi kama,tun haihuwar yarinyar nan har yanzu rayuwar ta a stalk yake,rayuwa take yi a duniya amma lfyr ta bai da inganci,yanzu da ta ɗan fara jin daɗin rayuwar nata kuma,mutuwa zai yanke mata shi"..Ammy ce ke kuka tana mgnr ita kaɗai bayan fifi ta bar su ta nufi sashen Hamida..

Har dare dai bata wani sami sauyi ba dan jikin ta duk yayi sanyi,tsoro ya shige ta,fargabar rabuwa da fifi bai bar ta ba,sai a yanzu ma take jin sabon shaƙuwa na shigar ta akan fifi..

Sallar dare tayi ta musamman dama ta saba amma na yau daban ne,ta jima tana roƙon Allah akan ya rangwama ma fifi ya ji ƙan ta ya kawo mata komai cikin sauƙi ya shigo lamarin su..
Haka ma Hajja ta kwana tana ma fifi addu'a dan zuciyar ta ya karye akan wannan abin..

Bayan fifi ta fita daga sashen su Ammy sai ta nufi sashen Hamida inda nan ma duk kalmar mutuwar ce,sai dai ita Hamida bata yarda memory ɗin yayi lasting a kan ta ba dan bata yarda fifi zata mutu ta bar su ba,ta yarda cewa in har fifi zata iya riƙe babyn ta for good 9 months toh ta san da hukuncin ubangiji she will pass through her labour successfully..

Ƙarfafa mata gwiwa Hamida tayi ta yi har Khalid da ya dawo daga aiki yayi joining nata suna ta ba fifi mgn da ya sanyaya mata zuciya but a can ciki,ta san me zai faru a ƙarshe...

Har bedroom Hamida ta rako fifi ta taimaka mata ta sauya kayan ta zuwa comfortable night wears sannan ta mata duk abinda ya dace kafin ta tafi dan ta ce a nan zata kwana but fifi ta ƙi yarda ta ce ta tafi kawai in ba haka ba toh kuka zata saka mata,jin haka sai Hamida ta rarrashi fifi ta ce amma ba bacci zata yi ba zata je ne ta rinƙa leƙo ta..

A hakan ma da ƙyar fifi ta yarda sannan Hamida ta kashe mata wutar ɗakin ta tafi..
Bayan tafiyar Hamida ne fifi ta ciro wayar ta tayi dialing numbern daddyn su inda bayan ringing huɗu ya ɗaga suka gaisa ya tmby ta ya jiki ta ce mai lfy take..

Suka ɗan yi hira kafin daga bisani suka yi sallama,instead tayi bacci sai ta hau kiran layin mijin ta but duk ringing ɗin da yayi ta yi ba a ɗaga ba,haka hnkl ta ya tashi har ta tura mai saƙonni babu iyaka ko zai kira ta ko ya maido mata da reply but bai turo ba bai kuma kira ba sai ta daure ta ajiye wayar ta rufe idanun ta dan yin bacci...

****
Misalin ƙarfe uku na dare ta ji wani abu ya murɗa mata cikin baccin ta but bata buɗe idanun ta ba sai ta ɗan gyara kwanciyar..
Can kuma ta ji wani azababben ciwo a ƙasan marar ta nan take ta buɗe idanun ta ta fara salati a ran ta,tana nan a haka kafin ta tashi ciwon baya ya riƙe ta,tun tana iya resisting ciwon har ta kasa ta fara addu'ar a bayyane,da abin yayi tsanani ko ina ya amsa yana mata ciwo da raɗaɗi sai kawai ta tsala ihu..

Ihun nata ne ya doki kunnen Muhibba dake faman murƙususun ta a ɗakin ta dan dare ne kuma babu hayaniya so ko spoon ne aka yi dropping mutum na iya jin ƙarar sa bare wannan ƙara ce mai sauti...

Ɗan dakatawa tayi daga juye juyen ta ta tsaya shiru duk da zafin da take ji haka ta tako a duƙe ta fito zuwa hanyar ɗakin fifi..

Ihun ta kuma ji a karo na huɗu nan take ta ruɗe ta fara yunƙurin kai hannun ta ƙofar ɗakin amma ina,juyi cikin ta yayi wanda ya haddasa mata faɗi wurin ƙasa tana ta riƙe cikin tana numfashi sama sama...

A nan ɗakin fifi kuwa zafin da take ji bata taɓa jin sa ba tun da ta shigo duniyar nan sbd zafin is irresistible..
Hannun ta ta kai ga side drawer ɗin ta ta laluɓo wayar ta,ga ba haske ga halin da take ciki...

Bata ma san numbern wa ta kira ba ita dai tayi dialing number,wayar na ta ringing sai daga baya aka ɗaga..

Tana jin an ɗaga sai ta fara mgn a wahalce da rashin sabo da yanayin dan har ta fara kuka,tunanin ta mutuwar ce zata yi

"Hamee...ham...Hamee ki zo. Pls ki zo..am gonna die..pls come"ta ƙarasa mgnr tana jan kalmar come ɗin haɗe da tsala wani ihun...

Wayar ta wurgar ta faɗo ƙasa tana ta juye juye tana kuka tana nemar agaji da tallafin mutani...

Kusan 5 minutes bayan ta yi kiran tana durƙushe sai ta ji hayaniya daga haka ta ga an buɗe ƙofar an kunna wuta..

Already ta fara fita hayyacin ta dan haka bata san wa da wa suka shigo ba sai dai ta ji ana kinkimar ta ta mutani biyu a hanzarce...

Muhibba dake sume a ƙasa bakin ƙofar ɗakin fifi Khalid ya kira mai gadin su da ya je ya buɗe mai gate haka ya kai ta motar sa bayan motar su fifi ya tafi wanda Hamida ce ke jan motar dan ba zasu iya jiran driver ya zo ba..

Wsni irin speedy driving Hamida ke yi a kan titin cikin wannan tsakiyar daren tana yi tana kuka tana juyowa tana kallon fifi dake ta juye juye..

Ammy da Hajja dake riƙe da ita kuwa cikin su babu wanda gwiwar sa bai sage da al'amarin ba sai tofa mat addu'a suke ta yi...

Haka Khalid ma yayi ta banka gudu a kan titi yana bayan su Hamida,dai dai inda hanya ta raba nan suka rabu,motar su Hamida yayi dama nasa kuma yayi hagu..
Suka cigaba da gudu har dai motar su Hamida ya iso wani babbar asibiti inda nan Khalid ke aiki wato National hospital dake garin abuja...

Da sauri Hamida ta fito a birkice ta shiga ta kirawo su su zo emergency ne,sannan suka zo da gadon ɗaukar patient aka fito da fifi daga motat aka ɗora saman gadon aka yi wheeling nata zuwa ciki..

Shigar da ita E&O unit aka yi aka dakatar da su Ammy dake yunƙurin shiga ciki...

Card aka buɗe mata sabo fil sannan aka tmby Hamida wasu informations ɗin fifi while ana ciki ana ƙoƙarin stabilizing fifi...

Duk a rikice Hamida take sai kai kawo take ta yi a nan ta nemi da a ara mata waya zata kira mijin ta a nan yake aiki ta faɗa masu sunan sa sannan suka bata waya...

Kiran layin Khalid tayi wanda shima yana can wani asibitin an shigar da Muhibba ɗakin emergency tana numfashi sama sama da ƙyar...

Haɗa sa da likitan da aka kira tayi inda ya mai bayanin komai dangane da fifi sannan suka ajiye wayar...

Duk inda natsuwa take toh ta ƙauracewa wannan ahali a wannan dare..
It's already 4:50am kusan 5am na asuba but babu wani improvement a condition ɗin fifi abinda ya tsorata su kenan dan sau biyu ana so a mata shirin shiga theater dan ceto rayuwar babyn but ta tmby su har wani lkc bavyn zai rayu suka faɗa mata sannan ta tmby har wani lkc labour ɗin zai kai ta suka faɗa mata sai ta ce toh su bar ta dan tana so ta haihu da kan ta...

Duk yadda suka nuna mata haɗarin hakan sai ta nuna masu ta fi su sani dan ita ke da ciwon a jikin ta kuma ko a yi aiki ko ta haihu da kan ta ta san mutuwa zata yi dan haka ta ce su kirawo mata ƴar uwar ta...

Duk wannan mgnr ya gudana ne bayan ciwon ya ɗan lafa mata but sai basu kira Hamida ba dan suna ganin hnkl ta zai tashi in ta ga condition ɗin ta...

Ai kuwa ciwon na dawo mata ta fara kiran sunan Hamida,sai nanata sunan take yi har dai suka fito suka yi requesting Hamida ta shigo...

Da gudu ta shigo ɗakin ta ƙarasa ta rungume fifi dake kwance akan couch ɗin haihuwa ta fashe da kuka tana faɗin
"Mufida pls fight it...ki yi yaƙi ki tashi kar ki bar mu,..ki tuna fah yanzu Ƙaunarmu ke ƙaruwa,yanzu ne Ƙaunarmu ya kamata ya taimaka mana ya kawo mu kusa da juna ba wai mu rabe ba,Mufida ki tuna fah in baki yi fighting ma rayuwar ki ba this baby will be motherless ya kike so babyn nan ta ji ko ya ji?kina son babyn ya taso ko ta taso cikin rashin mahaifiya ne?ki duba ɗumbin mutanin dake son ki pls Mufida ki tashi kar ki bar mu"!!kuka sosai Hamida ke yi wanda fifi ke taya ta dan ta san ba rai zata yi ba tana ji a jikin ta...

Riƙo hannun Hamida tayi cikim azaban raɗɗin da take ji ta fara mgn
"Ko na mutu Hamee..na baki kyautar abinda zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login