Showing 48001 words to 51000 words out of 101986 words

Chapter 17 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15652

gigin tada ta daga baccin ba dan ta san labarin gizo baya wuce koƙi dole kukan baƙin cikin ƴar uwar ta ne ya saka ta baccin dole..
Fitowa Ammy tayi tana share hawayen ta dan abin na damin ta ganin da hanun ta ta taimaka wurin nesanta Hamida da Mufida wanda a matsayin ta na uwa a gare su bai kamata ta bayyana soyayyar ɗaya akan ɗaya a fili haka ba kamar yadda ta rinƙa nunawa a baya..
Ta kan zauna tayi kuka cikin dare idan fifi tayi bacci ba dan komai ba sai tuno irin wariya da bambancin da ta rinƙa nunawa Hamida kamar ba tare aka haife su da Mufidar ba..
Tabbas da ace Khadija na Raye da bazata bambamta yayanta ba sbd ita ta haifesu,
To su yanxu me kenan sukayi???.


Tun ranar ita da Hajja suka rinƙa zaryar zuwa duba ta dan nemar afuwar ta amma sai ta tsiro da hanyar guje masu kar na su haɗu bare su karanta mata fake love ɗin su gare ta...
Musamman yanxu dataga mijinda suka zabarwa Fifi tasake tabbatarda sun qara fifita fifin,

Sashen Hamida Ammy ta nufa bayan doguwar sallamar da ta tsaya tana yi a bakin ƙofa ba tare da an amsa mata ba sai ta yanke kawai bari ta shiga ciki..
Da shigar ta sai ta hango Hamida zaune a ɗan kishingiɗe kunnen ta sagale da earpiece bakin ta na nanata abinda take sauraro a earpiece ɗin wanda waƙar maher zain ne na number one for me cikin album ɗin sa,shigowar Ammy daidai inda yake baitin _"my mamma is alright is a brand new day i will like to put a smile on your face every day"_..

Sanyi gwiwar Ammy yayi zuciyar ta ya karye duk wannan maraicin ita da Hajja ce sanadin faruwar sa dan tun yarinta da suka taso tare da daddyn su basu damu da son jin ya lafiyar ta yake ba sai dai na Mufida..
Kasa cigaba da tsayuwa Ammy tayi haka ta fita ta koma sashen ta tana nadamar ƙiyayyar da suka dasa a zuciyar Hamida game da su sannan inda abin ya fi muni shine ƙiyayyar ƴar uwar ta da suka taimaka wurin haddasa sa a zuciyar ta..
Maimakon ta tsanesu suda sukai komai Amma yar uwarta ta tsana.
****

Kwanaki uku kenan a tsakani Hamida da Mufida babu fahimtar juna sai sabuwar ƙiyayyar juna tun abin na faruwa a tsakanin Hamida da mijin ta a sashen su har ya fito fili Mufida ta gane son ta ne ƴar uwar nata bata yi already ƙiyayyar da take mata ya rinjayi soyayyar da take mata dan haka ta sakawa zuciyar ta haƙurin dole akan bayan wasu lokuta zata kuma komawa ta roƙi yafiyar ƴar uwar nata maybe by then ta huce..

Ana jibi monday exams ɗin su Mufida Ammy ta rinƙa ƙarfafa mata gwiwa dan dai tayi ta kammala lafiya ta dawo gida ta natsu dalilin da ya sa bata sanar da ita dawowar mijin ta ba kenan kar fargaba ya hana ta concentrating a karatun ta,duk yadda zata yi kar su haɗu for now tana yi because bata san ya reaction ɗin Mufidar zai kasance ba in har things turn out to be in a negative way...

****
Da sanyin safiya ta fito zata tafi inda ya fiye mata daɗin karatu wato garden,tana tafe tana nazarin abinda ta karanta a daren jiya..
Tana tafe tana karatun tana ɗan rausayawa unknowingly kawai ta juyo tayi ido biyu da wani mutumin da bata taɓa ganin sa cikin gidan ba..
Cak ta tsaya a wurin hannun ta dogare da ƙirjin ta littafin ta riƙe a ɗaya hannun ta idanun ta akan wannan mutumi sbd sanin Babu wani Wanda ke rayuwa a gidan bayansu..
Shi wannan mutumi dama morning workout ya fito yi as usual kuma yanzu ya kammala zai koma cikin gida..
Gama juyowar sa ke da wuya fifi ta nemi natsuwar ta ta rasa hatta da handbook dake hannun ta saura ƙiris yayi slipping daga hannun ta ya faɗo ƙasa sbd tsananin faduwar da gabanta yayi lokacinda idanuwanta suka hadu da nasa wanda yasa jikinta Neman daukar rawa..
yana zuwa zai wuce ta kuwa ta ƙara girman idanun ta ganin kamar ta so sanin sa amma kamar ba shi bane..
Da zuwan sa zai wuce ya ga mace tsaye ta ƙame kamar soldier tana kallon sa sai ya buɗe baki ya furta
"Excuse me if you wouldn't mind"!!ja da baya tayi ta matsa mai ya wuce ta da ɗan gudu gudu in form of jugging..
Sumewa ne kaɗai ya rage fifi bata yi ba da ba a germany ta taso ba inda nan ne ƙarshen masu workouts,
Maza masu abs sune best mazan datake tsananin so da birgewa tagansu kala kala Amma Bata taba ganin Wanda jikinsa yayi building kamar wannan ba,
Zufan dake gangara daga jikinsa kawai was very neat and shiny,
But waye wannan ɗin!?
Who is he????tambayar da tayi wa kan ta kenan amma babu amsa sai ta cigaba da bin sa da kallo..
Ko me ta tuno kuma oho sai ta taɓe baki ta ɗage kafaɗar ta ta ƙarasa zuwa garden ɗin tayi zaman ta da zumar yin karatu sai dai karatun nan bai yiwu ba because tana yi rabin hankalin ta na ga tunanin wanene wannan gentile good looking man ɗin..

Ƙarshe tashi tayi ta ƙarasa sashen su Ammy na mata tambayar ya karatu amma kasa amsa ta tayi sai shiru da ta mata..
Suna nan zaune suna halin shiru ita da Ammy sai aka doko sallamar da sai da ya shiga ciko cikin kunnuwar Mufida ta ji nan take natsuwar ta ya fara yunƙurin barin jikin ta...
Bata gama alhinin wannan sallamar ba ta ji muryar Ammy na faɗin
"Yau da wuri ka shigo,na ga baka cika fitowa da wuri ba hope babu wata matsala"!?hankalin fifi sai ya dawo ga conversation ɗin su har suka gama magana tana kallon bakinsa a sace yanda yake magana cikin cool and matured tune dinda ya gama kashe jikinta musamman dataketa son tantace wane mizani zata kallesa sbd bata gama sanin wayeba.
yana fita fifin ta rufe idanuwanta ahankali ta bude ta yaqi da shaqar kamshin turarensa na Armani daya gama kame sanyin AC na dakin ta kalli Ammy a hankali ta ce
"Ammy waye shi wannan ɗin"?murmushi Ammy ta mata tana shafo fuskae ta a hankali sannan ta amsa mata
"Baby kin ga illar rashin sani shi ya sa na matsu ku dawo,yanzu jinin naki ma baki san shi ba sai an nuna maki,toh dama ban so ku haɗu tun a yanzu ba sbd jarabawar ki amma tunda Allah ya ƙaddari yau zaku haɗu ina ga sai ki kai mai gaisuwar barka da dawowa kusan 4 days kenan da dawowar sa"!!shiru fifi tayi tana jiran cigaban sharhin Ammy sai kuwa kamar Ammyn ta sani ta cigaba..
"Yayan ki ne baby SAHEEB ne"!!, gaban Mufida ne ya faɗi at once..
"What did Ammy just said?yaya na Saheeb ne?what"?tambayar da ta yiwa zuciyar ta kenan tana ƙara hasashen yanayin sa..
Tashi tayi ta sallami Ammy wanda sallamar ya ɗan tsorata ta tunanin ta ko Saheeb ɗin bai yi ma fifi bane...

Da shigar fifi ɗakin Ammy tayi wurgi da littafin hannun ta ta warware mayafin kan ta ta zo gaban mirror ta tsaya tana ƙarewa kan ta kallo daga sama har ƙasa,sai da ta share mintuna biyar tana kallon kan ta a mirror sannan ta jijjiga kai tana furta
"Ya salam,
"wani irin reaction ne ya riske ta ta kuma kallon kan ta sai ta rainawa kyawun ta da wayewar ta da zamanancin ta dan in aka tsaya aka yi comparing nata da wannan da Ammy ta kira sa da yayan ta Saheeb wanda kuma a addinance shine mijin ta for now toh ita ɗin mummuna ce abinda ya ɗaga mata hankali kenan ta rinƙa tunanin anya Ammy ba tsolanar ta take yi ba kuwa ta yaya mutumin da suka ji labarin sa suka kuma daɗe da tagging nasa old man zai yi turning out to be a gentile,handsome and well kept man like this har ma kyawun sa na nemar ɗare nata kyawun,anya ba tsokanar ta Ammy ke yi ba kuwa..

Kasa samin kan ta fifi tayi sai da ta ga in fah ta cigaba da wannan tunane tunanen da ba lallai bane gaskiya ne ba toh zata yi biyu babu because ba zat sami cikar burin ta ba sannan tayi causing mistrust a zuciyar family members ɗin ta akan ta..
So tun ranar wanda ya kasance saturday fifi bata kuma bi ta kan tunanin wanda aka ce mata yayan ta bane dan ta san hasashen Ammy ne ba asalin wanda take jin sunan sa bane is not even possible a ce shine wannan..
Ranarda taji hajja tayiwa ammy mgnar tarewar Fifi din gurin saheeb hankalinta ya tashi matuqa Amma taqi nunawa
Hankalinta bai sake tashiba Saida taji ammy na cewa abari aji ta bakinsa idan matarsa ba yanxu zata dawoba.

Concentrating tayi a karatun ta har ranar litinin da tayi shirin ta na musamman dan fara zana jarabawar ta,good wishes Ammy ta mata ta fito driver ya wuce da ita zuwa makaranta dan attending exams ɗin ta...
#Mamuh*20*

Yau kimanin kwanaki takwas kenan da fara jarabawar fifi kuma ana saka ran gobe zata kammala da hukuncin ubangiji.
  Yanayin jarabawar ya sa bata da isasshen lokacin zama tayi hira da su Ammy bare har ta sami lokacin tunanin wani abin..
  A wannan tsawon kwanaki tara zuwa goman abubuwa da dama sun faru a gidan wanda fifi bata da masaniya akai..
  Cikin wadannan abubuwa akwai wasu halayyar Hamida da ba a san ta da su ba amma ta rinka yin sa a boye,wannan abin ba komai bane sai salon da ta dauko wurin ganin ta sami wani abinda take so..
  A natse cikin kamun kai da wayewa take haduwa da Saheeb a garden kullum safe in ya tafi morning workout ɗin sa ita kuma sai ta tafi ta zauna tayi concentrating akan wani pamphlet da take yawo da shi a hannun ta kullum da sunan dubawa take yi..
  Haka kawai ta ji duniyar nan babu wanda take son gani kullum safiya zuwa yamma sama da fuskar Saheeb,abin mamaki kamar mantawa tayi ƴar uwar ta Mufida ke aure da shi kuma ita ke da wannan dama da ikon ba ita dake auren ƙanin sa ba..

  Kamar kullum yau ma tana zaune tana duba pamphlet ɗin nata sai mijin ta ya zo dan dama yana ta nemar ta bai gan ta ba sai yayi tunanin zuwa nan dan tun rana da idanun ta ya mata tozali da Saheeb ta fara sauyawa Khalid abincin da suka saba ci tare ta yanke sai dai ta ci nata ta bar mai nashi,wankan da ake yi tare shima ta datse,hirar dare da ake yi kafin a yi bacci nan shima ta yanke sa dan bata da lokacin sauraron hirar lokacin ta na wani abu ne chan daban,toh shi kuma bai ɗau abin da muhimmanci ba ya fi alaƙanta sa da ƙila conflicts ɗin da ya faru ne tsakanin ta da ƴar uwar ta..

  Da zuwan sa ya zauna kusa da ita haɗe da ɗora kan sa a kafaɗar ta yana lumshe ido sai a sannan ta san ya zo dan idon ta na kan Saheeb a kaikaice..

Harga Allah cikin ranta batada wata soyayyar 'da namiji bayanta mijinta khaleed Saidai Sam takasa dauke idanuwanta daga kan Marshall ne sbd son gano wani aibunsa dazai nuna mijinta yafi na Fifi Wanda shine yasa zuciyarta Sam kasa sukuni da walwala.

  Ko da ta juya ta ga shine sai tayi saurin ɗaga kan sa daga jikin ta tana ce mai
  "Miye kuma haka Kuma ka manta a waje muke?shagwaɓe fuska yayi ya kalle ta ya ce
  "Luv Ina ruwanmu da waje tunda Babu kowa a gurin?sai ta bi shi da wani look tana ja da baya kaɗan kafin ta tashi rai a ɗan jagule dan ya hana ta ƙarasa abinda ya kawo ta..
  Yana kallon ta ta tashi ta wuce dan bata yarda kowa ya san da wannan abinda take yi ba iyakat ita da mahaliccin ta..

Yana kallon ta tana wuce sa ya jiyo kiran yayan sa sai ya maida hankalin sa wurin itama ta tsaya a inda take dan jin muryar sa..
  Ƙarasawa Khalid yayi zuwa wurin da yayan sa ke tsaye,da zuwan sa ya gaida Saheeb cike da ladabi da biyayya dan akwai tazara sosai tsakanin su kuma baya da haka tarbiyar gidan dole na ƙasa ya ba na sama da shi mutuncin sa..
  Tana jin yadda Khalid ɗin ke gaida Saheeb tattare da mutuntaka sai kawai ta ja wani tsaki ta wuce ran ta na ɓaci idanun ta na kawo ruwan hawayenda ke sulala zuciyarta ganin mijinta shine yake qasqantarda Kai ga mijin Fifi.

Tare suka ƙaraso Saheeb ɗin na sanar da shi yana so yau su tafi site wato wani ginin da ake yiwa Saheeb a nan cikin Abuja..
  Da murna Khalid ya ce ya yarda zai bi shi har driver ɗin sa zai zama yau dan sun daɗe basu haɗu ba kasancewar ranar da ya kamata su haɗu aka sami akasin ɗaurin auren nan sai ta waya suka cigaba da magana dan ya koma toh yanzu da ya dawo ne Khalid ɗin ke son faranta mai dan ya san yayi laifi kuma shi yayan nasa ba mai damuwa bane yana iya yiwuwa yana da matsala  amma bai furta ba ya barwa kan sa..

Hamidar da yanzu ta ƙarasa cikin sashen su kunnuwan ta suka jiyo mata inda Khalid ke faɗin ai har driver ɗin Saheeb zai zamo a yau,wani baƙin cikin ne ya kuma turnuƙe mata a zuciya wannan karon kasa dannewa tayi tasaki wani irin kuka Mai qarfi tana zubewa kan kujera da qarfi

Ko da ya shigo ya sanar da ita abinda yayan sa ya ce sai ta mai banza kamar bata jin sa sai da ya kuma maimaitawa sannan ta kalle sa a karkace ta ce
  "Ai na ji kuma na fahimta ba kurma bace ni da zaka faɗi magana ka kuma nanatawa duk dan in ji ka ba"!!a yanzu wannan amsar da ta bashi sai ya ji abin wani iri bata taɓa responding mai magana a haka ba sai yau bai san dalilin ta ba amma ko menene dalilin ai bai cancanci irin wannan kalamai daga gare ta ba...

Miqar da ita tsaye yayi cikin yanayi na tsananin damuwa da kulawa yace"

Luv menene please tell me sbd Sam nakasa gane kanki
Please tell me meye matsalar?
Idan maganar Fifi ne inaga mun wuce gurin right?

Kallonsa tayi da sauri hawayenta na sake saukowa cikin rawar murya tace"

Fifi is always ahead of me,
Meyasa bazaa daina qina da wareni ba acikin family na sbd Fifi?
Meyasa mijina zai zai zama bawan mijin fifi sbd mijin Fifi yafi nawa..

Kallonta yayi da wani irin zallar mamaki da tsoro yace"
Hameeda me kike fada?
Meye ruwanki da mijin Fifi ko Kuma wani Abu kaman hakan tunda dai mijinta baifi nakinba......

Cikin fita hayyaci tace"

Yafi nawa tunda yafisa komai
Dukiya,ilimi, wayewa hutu, kyau soyayyarsu ammy da hajjo da komai da komai ma.....meyasa mijinta yafi nawa zuciyata quna takeyi I can't take ita Kun taru kun hainceni Kun boyemin Asalin wayene Marshall sbd tun farko baaso ya aureniba.....

Cikin kaduwa khaleed ya girgiza ta Yana cewa"

Hameeda ki daina wainnan zancen kishin Fifi ne ke cinki zai gurbata tarayyarki da yar uwarki please stop wannan kaman kina Mata hassadane...

Ture hannuwansa tayi tana kuka tace"

Kaima da kake nawa bayanta kakebi,
Harda Kai aka taru aka boyemin baa fada min gskiyar waye saheeb ba you lied to me khaleed....you hid this from me..

Daskarewa khalid yayi agurin cikin tsananin firgici da tashin hankali tareda tsananin tsoro idanuwansa suka ciko da wasu irin hawayen nauyinda zuciyarsa ta dauka ya kasa furta komai sbd nauyinda bakinsa yayi.

Atake tadawo mutsuwarta tareda Dana sanin maganarta cikin sauri ta riqo hannunsa tana hawaye tace"

Baby I'm
I'm sorry ba abinda nake nufiba kenan plea....

Bata qarasaba ya janye ya nufi daki da sauri haryana buge qafarsa da kujera ko gani bayayi sosai.

Jininsa daya buge qafarsa ta durqusa agurin tareda fashewa da sabon kuka tana cewa"

Da gaske hassadar Fifi nakeyi???

Ni meyasa ko yaushe Fifi ce abakin kowa?


Daqyar yayi wanka yafito ya wuceta a palon jikinsa duk a sanyaye Saidai zuciyarsa acike takeda damuwa da bacin Rai Saidai kamar yanda yayi alqawari hameeda itace farin cikinsa zai tsaya tsayin daka Dan ganin bai Bari wannan halinda aka jefata ya Bata rayuwartaba zai zame Mata bango Kuma abokin rayuwa na qarshe.

Basu dawo gidan ba sai dare lis dan yawo ya rinƙa jan yayan nasa yana gargaɗin sa shi kuma yana mai nuni da ai faranta mai yake son yi dan rabon su da juna shekaru da dama,toh sai Saheeb ɗin bai ja ba ya ƙyale Khalid ɗin har sai da dan kan shi ya bar su suka dawo gida...

  Har sashen yayan nasa ya raka sa ya kira sashen su Ammy da a kawo wa yayan nashi abinci,sai da aka kawo ya tabbatar yayan nashi baya buƙatar komai sannan ya mai sai da safe ya nufi sashen su..

Bai yi mamaki ba ganin an kashe light ɗin parlor dan ta saba sai ya ƙarasa ciki ua hango ta kwance tana danna waya..
  Da sigar zolaya ya ce da ita
"Luv ba sai kin kira ni ba na san kewa ta kika ji kuma kin ga ban dawo da wuri ba shi ya sa kike son kira na right"!?ya ɗage gira ɗaya sama sai ta taso da sauri tafada jikinsa tareda qanqamesa tana fashewa da qaramin kuka batareda ta iya furta komaiba.

Sake shigarda ita jikinsa yayi Yana sauke numfashi ahankali.
 

Haka suka cigaba da yin rayuwar zaman shiru a gidan nan sam Hamida bata da lokacin Khalid kullum safe tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login