Showing 66001 words to 69000 words out of 101986 words
sai dan damuwar ƴar uwar ta d ta sakawa zuciyar ta gashi tayi auren da bata san ma'anar sa ba,a haka ne rashin lafiyar ta ke ta tashi a hankali a hankali amma bata bari a gane ko shi Saheeb ɗin da take kwana tare da shi a apartment ɗaya bai sani ba..
Iyakar sa da ita shine gaisuwar safe abincin sa ruwan wankar sa sai wasu ayyukan sa da ya zama dole akan ta sai dai in tayi zaman kukan ta ya zo ya same ta ta rinƙa tmbyr sa ko tana da aibu ne shi kuma sai ya kalle ta kawai baya amsawa..
A iya zaman su fifi bata ƙara marmarin komawa sashen su Ammy da zama ba sai dai ta je ta gaida su a ɗan yi hira kaɗan da bai wuce mintuna goma zuwa goma sha ba daga haka zata tashi ta koma dan ta sakawa ran ta bata kuma nemar shawarar kowa dan inganta rayuwar ta tunda ta yi hakan a baya bata sami nasara ba..
****
Yau tana zaune a parlor sai ta ji taba sha'awar kwana a ɗaki dan duk wannan zaman nasu a parlor take kwana bata wuce nan ko dai dai da rana ɗaya Marshall bai taɓa yi mata tayin ta zo ta kwanta a bedroom ba ita kuma bata taɓa tmbyr sa ba amma yau ta ƙudiri kwanan ɗakin..
Akwai ranar da yake nuna mata wasu kayan coffee da ya sa aka siyo mai akan in zata rinƙa haɗa mai ta rinƙa amfani da su,a ranar take jin wai matar sa tayi extending dawowar ta zuwa lkcn da ta kammala abubuwan da take son yi..
Haka kawai Ta ɗan ji wani abu a ran ta da ta tuno cewa yana da mata,dan dama ita kam shaf take mantawa,yau da ta tuno sai abun ya mata wani iri,badon tanajin tana son sa ko zata so sa ba,tunani take ita wa zai so ta ya bata kulawan aure da kowacce mace take samu?babu khalid ga hamidarta ma ta juya mata baya.
Wani irin damuwa ne ya shigeta sam bata san dalilin wannan abubuwan dake faruwa da ita ba..
Tana zaune a parlor tana tunane tunanen ta sai sallamar Marshall ya doki kunnen ta,ɗagowa ta yi ta dube sa sai ta mai barka da dawowa kamar kullum shima sai ya mata barka da zama..
Saɓanin da yau sai ya zauna tare da ita a parlorn a kan wani kujera yana kallon ta sai ta ɗan tsargu har ta kasa yin shiru ta ce
"In kawo maka coffee ɗin ne yanzu"!!shi dai kallon ta yake bai ce ƙala ba har ta tashi dan halin ƙyaliyar sa ya rigada ya zame mata jiki tuntuni.. .mikewa tayi zata fice yace
"Dawo ki zauna mgn zamu yi"
..juyowa tayi ta dawo ta zauna a natse..
Sai da ya ɗau lkc sannan ya mata tmby kai tsaye.
"Me ke damin ki da kullum kike zama kina kuka ke kaɗai?
Sai yau ma ya san da haka?take ta ji hawaye na son cika mata ido,bai ce mata komai ba sai ta girgiza mai kai tana faɗin
"Ba komai"kallon mamaki ya mata wai har ta iya zurfin ciki tana ɓoye mai abu?ɗage kafaɗun sa yayi alamr abin bai dame sa ba ya ce ta je ta kawo mai coffee zai kwanta..
Zuciyarta na mata nauyi ta tashi Haka ta je ta haɗa mai tana tunane ta dawo ta miƙa mai a rayuwa tunda take bata taɓa fuskantar damuwa da shiga tashin hankali ba irin wannan,ta saba zama cikin mutani masoyan ta amma yau daga ita sai ita kamar marar hali mai kyau,wa zai fahimce ta ta sami yafiyar ƴar uwar ta...
Da miƙa mai ya tashi ya wuce ciki abin sa ita kuma ta jingina da kujerar tana tunanin ko ina rayuwar ta zata juya aƙala Allah ne kawai masani..
Lokuta ta asarar a tunanin nata har sai da ta ji ta gaji da zaman sannan ta tashi haɗe da kashe lights ɗin nan parlor ta wuce zuwa ciki..
Bed room ɗin is a luxurious one komai yayi daidai toh addu'ar ta ko a ƙasan ne ya bar ta ta kwanta ba sai lallai a kan gadon ba dan ta san wannan gadon ko ranar da ta hau bai mata tsawaba sakamakon rashin lfyr da yake yi ne so bata so ta fuskanci ƙasƙanci ko wulaƙancin sa akan wannan gadon ta san matar sa ce ke da damar hawa gadon..
Mamaki sosai ta yi da ta gan sa zaune saman kujera da table yana aiki ga papers nan birjik gefe ga laptop a side kaɗan ga kofin coffee ɗin sa nan..
Rasa abin yi ta yi sai ta hau kame kame shi kuma sallamar ta na fari a kunnen sa haka ya sa ya ɗago yana kallon ta sai ya tmby ta,da ƙyar ta iya furta..
"Bacci nake ji"!
funny,ya faɗa a zuciyar sa sai ya dube ta ya ƙara yana maida hankalin sa ga aikin sa kamar ba zai ce komai ba sai kuma kamar an fizgo mgnr ya ce mata
"Toh sai da safe"
da sauri ta faɗa mai a nan ɗakin take son kwanciya ba akan kujera ba batare da wani tunani ba tayi mgnr shi kuma sai yayiwa mgnr nata bahaguwar fahimta ya tsaya da ayyukan sa cak ya maida hnkl sa ga kallon ta daga bisani yayi wani tunani ya ce da ita
Ke Bazaki kwana min daki na ba
"Ga ɗakin ki nan can wannan kina iya zuwa can ki kwanta"!!
gyaɗa mai kai ta yi dan dai dai da rana ɗaya bata taɓa dunfarar ɗakunan dake site dinsa ba iyakar ta parlor
kitchen,bedroom ɗin sa in ta kai mai coffee ko in ta tafi gyarawa sai guest toilet da take buƙatun ta a ciki..
Ganin ta fita bata mai gardama ba sai ya taɓe baki yana goge bahaguwar tunanin da ya fara yiwa mgnr ta ya cigaba da aikin sa..
Ita kuwa da fita bata tsaya ko ina ba sai ɗakin da ya ce nata ne,tana buɗewa ta ga daki ne mai kyau sai ta tsaya mamakin tsaruwar ɗakin nata wato har ita ke mallakar ɗai irin wannan amma take kwanciyar parlor kuma shi bai taɓa sanar da ita ba?lallai miskilancin sa ya kai matakin izgilanci dan yayi yawa..
Abubuwan ɗakin sun yi ƙura sai dai bata jin zata iya gyara sa da daren nan ko dan sbd kar ya ce ta dame sa haka ta je ta yaye bedsheet ɗin gadon ta buɗe wardrobe ta nemo wani babban blanket ta shimfiɗa kan expensive cream colour royal bed ɗin ta ta ɗau wani na lulluɓe jiki sannan ta sauya night gown ɗin jikin ta zuwa wani daga haka ta kwanta akan gadon ta lulluɓe jikin ta da blanket ɗin..
Bazata iya tuna rabonta da ta kwanta a kan gado so yau bata jima ba baccin ya ɗauke ta
*****
Kusan makara ta yi da safe yayi sai da ya ga bai ga giftawar ta ba a gidan sai yayi tunanin ya duba ta haka ya tura ƙofar ɗakin..
Hango ta yayi kwance saman gadon tana bacci hnkl kwance ƙarasawa ciki yayi ya tsaya a kan ta ya rinƙa kallon ta ya tada ta ne ko dai ya ƙyale ta ne bai sani ba,it was 7:10am sai da ya ƙare ma fuskar kallo sannan ya saka hannu ya fara yaye mata blanket ɗin dan shi dai bai taɓa jin ya kirata da sunan ta ba daga ki min kaza sai kai min kaza ko zo ko zauna,shidai sunan ta dai bai shiga bakin sa ba..
A baccin ta ji ana ja mata abin rufa sai ta riƙe wani gefe,kallon hannun ta yayi ya girgiza kai ya yaye blanket ɗin baki ɗaya.. .
Ganin surar jikin ta yayi,doguwar rigar bacci ce mai tsantsi kusan komi yana gani sai ya ɗan ɗaga idon sa daya kasa ɗaukewa daga jikin ta yana yi yana kallon fuskar ta sai da ta buɗe ido suka yi ido huɗu da shi..
A firgit ta tashi tana janyo blanket ɗin tana rufe jikin ta shi kuma ya kawar da kan sa a ɗan daburce ya juya yana faɗin
"Are u mad?..Ki tashi ki yi sallah lkc ya tafi"
daga haka ya fita ita kuma kunyar sa ya gama kama ta sai ta rinƙa jin nauyin haɗa ido da shi..
yau gaba daya haka ta rinƙa kauce mai dan kar su haɗu,ita me ya sa ma bata rufe ƙofar ba,shi kam gudun kar ta mai wani kallo sai ya rinƙa ɗaure mata fuska abinda zata ce ta jima rabon ta da ganin sa yana yi tun haɗuwar su ta fari sau biyu zuwa uku da ya rinƙa tamke mata fuska bai kuma ba sai yau..
Tana kitchen tana girkin ta har da saka lock sai ta ji ana juya handle,juyowar ta ke da wuya ta ga har an buɗe ƙofar an shigo..
Sumewar tsaye tayi ganin wani irin ƙerarriyar kaftan da ya saka,she can't judge wen it comes to kayan maza amma ko ma wani iri ne wannan ta san mai tsada ne..
bayan ƙamshin da yake yi suturar ta zauna mai hular da ya saka matching colour da kayan sai ya fito da shi a asalin magidancin kamilin namiji,gabaɗayan sa sai ta ji kamar tayi capturing nasa tayi ta kallon sa.. .
Ƙwarjini ya mata ba kaɗan ba ai tuni tsoron haɗa fuska da shi ya ɓace mata sai ta shagala da kallon sa har sai da ya ɗan girgiza mata keys ta dawo duniyar mu ta fara kame kame sai ya miƙo mata yana faɗin
"Ga keys ɗin sashen nan ki rufe in na wuce in kuma zaki shiga sashen su Ammy ne fyn ni zan tafi wni wuri ba zan dawo da wuri ba kar ki yi abinci da ni,sai na dawo"!!.
da salon gentle man ya mata bayanin sai ta ji wani abu a zuciyar ta bata san ma ta furta ba sai ji ta yi ya ce
"Amin"!!wai ashe ce mai ta yi Allah ya tsare shi kuma ya dube ta sannan ya amsa ya fita...
Bayan ya fita ne ta fara leƙen sa ta windown kitchen ɗin tana kallon sa ya shiga motar sa ta Land cruiser asalin silver colour yayi horn aka buɗe mai gate ɗin nasu ya saka kan motar ya fita aka maida ƙofar aka rufe..
Abinda bata taɓa yi ba yau ta yi wato haurawa upstairs ɗin gidan,da sauri ta haura ta tsaya a balcony inda ta hangi yadda yake tuƙin sa so gently and maturely har ya ɓacewa ganin ta sannan ta dawo ƙasa dan duba abincin ta da niyar komawa duba upstairs ɗin in ta kammala girkin ta..
Duk tunanin sa ne ya rinƙa faɗo mata ta dai ƙarasa girkin ne amma hankalin ta na ga tunanin da bata san dalilin yinsa da take yi ba,bata san matakin da zata saka wannan abinda zuciyar ta ke ayyana mata ba akan Saheeb,so ne, shaƙuwa ce ko kusanci irin na ma'aurata?..
#Mamuh*26*
Tana aiki tana jin wani sanyi yana shigarta saheeb ne yake yawan fado mata arai haka dai ta kammala aikin nata da kyar ta koma ta gyare ɗakin ta ta gyara mai nasa har bed wears ta sauya mai zuwa wasu maroon colours.
Da ta gama ayyukan nata sai ta ƙi zaman cin abinci ta nufi upstairs ɗin dan binciken me ke wurin.
Da zuwan ta ɗaki na farko ta shiga sai ta ga girman su kusan iri ɗaya da nata sai dai wannan ya fi nata girma kaɗan,komai na ɗakin mace yana nan a wannan ɗakin..
Taɓe baki tayi tana tunanin hala na matar sa ne,da haka ta kuma duba wani ɗakin nan ma ta ga kaya kamar na ɗakin farko colour ne ya bambanta su..
Dakin karshe dake saman ta je buɗewa sai ta gan sa a rufe,hararar ɗakin tayi ta sauko ƙasa abin ta zuwa kitchen..
Abinci ta ɗeba ta zauna ci amma kasa ci tayi,fitar duk sai dawo mata a kai yake yi,ɗan awowin da tayi bata gan sa ba ta rasa meya sa duk taji ta dame,da ƙyar ta tuttura abincin ba dan tana jin taste ɗin sa kamar yadda ta so yayi ba...
Sai da ta kammala cin abincin ta saka hijabin ta mai tsayi ta saka flat slippers ɗin ta ta fito,rufe ƙofar tayi ta nufi sashen su Hamida..
Sallama tayi sai ba a amsa mata ba dan haka da hannun ta ta tura ƙaramin ƙofar ta shiga.
Babu kowa a farfajiyar gidan ƙarasawa ciki tayi sai ta ga Hamida kwance ita ɗaya tana riƙe da remote tana ta sauya tashoshin tv..
Tabbacin babu kowa a gidan kenan daga ita sai ita,hakan ya ma fifi daɗi dan zasu fi samin lkcn juna sosai..
"Assalmu alaikum"kafin ta juyo ta fara amsa sallamar sai kuma da ta juyo ta ga Mufida ce sai ta ƙi ƙarasa amsa sallamar a bayyane ta amsa a ran ta.
Ɓata fuska Hamida tayi,tayi kicin kicin tana kallon fifi daga bisani ta ɗaga mata murya tana faɗin
"What?me kike so"?shiru Mufida tayi tana kallon ta,tsaki ta ja tana mai yi mata wasu irin kalamai marasa daɗin ji dake taɓa fifi ainun saidai ta san ita ta kawo kan ta dole ta jure duk abinda Hamida zata mata..
Matsowa kusa da Hamida tayi tana sauke murya ƙasa game da bata haƙuri amma Hamida ta riga ta hau dokin fushi marar dalili kuma kishin fifi ya rufe mata ido da yawa dan har ta daina jin tausayin fifin da take jin in ta zo tana bata haƙuri,ga mijin ta dake lallaɓa ta yana ririta ta amma duk lkcn da ta ga fuskar fifi sai ta ji kamar duk ririta da Khalid ke yi bai isa ba dole sai ya kara dan gani take fifi is receiving a more intensive care a wurin mijin ta akan wanda take samu sai ta rinƙa jin haushin fifin sosai..
"Kar ki ƙaraso gare ni tashi kawai ki fitar min daga gida,a kullum ke ce abin so komai naki mai kyau ne mijin ma sai da aka zaɓar maki mai kyau sannan aka baki ko ba haka ba?toh ki koma wurin waɗannan da suka tsara maki rayuwar ki suka rinƙa bi maki rayuwar daki daki suna nuna maki yadda zaki yi ki ce su samar maki abinda kika rasa yanzu dan ni kam kin ishe ni na gaji da mitar ki da kike zuwa kina min kullum,Hamee kaza Hamee kaza Hamee kaza,duk kalaman bakin ki Hamida ce ciki sbd kina da manufa da ni,in ba dan haka ba ta yaya ni ko zuwa sashen ki ban taɓa yi ba amma ke kin zo min ya fi a ƙirga,what are u up to?huh?fifi kin nemo soyayya da attention ɗin kowa a family ɗin mu kuma kin samu amma ki sani,lkc ya ƙure maki da zaki kirkiro wata soyayyar ƙarya dan ki sami nawa soyayyar,i can't believe u coz u are always pretending.
haka kike haka kika taso kuma haka kike cigaba da rayuwar ki amma ki sani not any more in dai da ni ce Hamida,lies and pretence ɗin ki ya tsaya haka dan ban da lkcn sauraron su a kunne na bare zuciya da kai na
dan haka ina baki shawara da kin zauna a inda kike kin yi rayuwar ki kamar yadda aka tsara maki tun kina yarinya kin zauna da masoyan ki zai fi miki,dan ni nan da kika gan ni,,ba zaki taɓa samin yadda kike so daga gare ni ba ki koma ki yi rayuwar ki da waɗanda suke son ki dan ni ban da damuwa a baya neda ban da kowa damuwar ki ke dami na amma yanzu da nake da miji na ya ishe ni ya maye min gurbin komai,bana buƙatar kowa a rayuwa ta ki manta ma kina da wata ƴar uwa a duniyar nan dan ni na manta da ke...
na manta da an haife ni rana ɗaya nida ke daga jikin mutum ɗaya,awanni ɗaya sai bambanci mintoci biyar,kema da zaki yi hakan da ya fiye maki Mufida coz i will never ever accept u in my life anymore kin taka taki rawar for long so yanzu nawa lkcn ne my husband is all i got i don't need u"!!
tana kaiwa nan ta wuce fifi dake tsaye cikin shock kamar an dasa ta..
Bayan Hamidar ta gama daddasawa fifi maganganu son ran ta ta haura sama faɗawa kan gadon ta tayi ta yi shiru tana tunanin irin kalaman da ta gasawa fifin ko sun dace ko basu dace ba..
Wani sashe na zuciyar ta ke faɗa mata tayi dai dai wani sashen na nuna mata rashin dacewar abinda ta yi sai dai mafi rinjaye ɗin ya fi nuna mata ai daidai tayi dan fifi ce ta jawo wa kan ta hakan..
Fifi dake tsaye tana halin shock ta ɗauki lkc a haka tana tunanin anya wannan Hamida ƴar uwar ta ce ko wata,kasa cigaba da daukar maganan fifi tayi sai ta tare hawayen da ya zubo mata da yatsar hannun ta ta juya ta bar sashen..
Hira suke yi suna dariya as family kawai ta turo ƙofar da ƙarfi ta shigo haɗe da yin jifa da wayar ta a ƙasa da ya faɗi ya tarwatse a wurin..
Take hankulan su ya dawo kan ta sai suka hango ɓacin rai mai tsanani a tattare da ita,take hankulan su ya tashi sai Ammy ta zo da sauri dan tmbyr lfy..
Ɗaga mata hannu fifi tayi cikin ƙunar zuciya da zafi rai ta kuma ɗaga ɗaya hannun ta dan ta san Hajja ce zata zo ta nan..