Showing 42001 words to 45000 words out of 101986 words

Chapter 15 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15644

tana cewa Ammy tana zuwa sai suka bi ta a da kallo har ta haura saman abin na basu mamaki..
  Bayan tafiyar ta ne Ammy ta labartawa Hajja abin da ya faru a daren jiya tsakanin ta da fifi,abin gwanin ban dariya sbd wautar fifin..

Shigar fifi ɗakin Ammy dan ɗauko wani handbook ɗin ta sai kuma kamar ta hango wani dan haka ta dawo da baya ta ɗan yi facing window,nan ta hango clear view ɗin abin da idanun ta ke hango mata a nesa..
  Tsayawa tayi tana kallon sa almost months kenan rabon da ta gan shi,ta dai san last time da Ammy ta mata magana akan sa shi da matar sa shine wai sun tafi honeymoon apart from ranar wata magana mai ƙarfi da ta shafe su bata kuma ji ba..

Ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da kan ta ta ɗau handbook ɗin nata tayi zaman ta a ɗakin bisa kujerar karatun ta ta buɗe tana duba abin da ya faɗo mata ɗazu da take cin abinci har ta kasa haƙura ta tashi..

Kimanin mintuna talatin tana karatun ta bata tashi ba sai da ta kammala sannan ta mayar da littafin ta miƙe ta sauko zuwa ƙasan..

Da zuwan ta Ammy da fara'ar ta ta sanar da ita dawowar su Khalid har sun shigo sun gaida su amma lokacin tana sama so presently Ammy is directing to go and welcome them since da kan sa shi Khalid ɗin yayi requesting Ammy ta bar fifin ta zo dana akwai wani muhimmin abu da yake so ya mata,toh ita dama Ammy tun ranar da ya sanar da ita tafiyar su ta ɗau sassauto da zafin ba dan komai ba sai dan yanayin rayuwa da ganin shi ɗin jinin ta ne...

At first fifi was like scared ne ko fargaba ne na haɗuwa da su dukan ko ya nene bata sani ba,so tana ta son shashantar da zancen amma wani iri tsananin kewar 'yar uwarta na damunta tundaga qasan ranta sbd tun haihuwansu Basu taba yin nesa da junaba ko banxatar da junaba sai yanzu Wanda tasani kowannensu abin na qwaqwalar zuciyarsa da radadi mai zafi.
tashi tayi ta fita cikin faɗuwar gaba ta nufi apartment ɗin su Hamida tana addu'ar samin sanyin zuciya dan kuwa har ciwo ciwon kai take ji..

Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga main entrance ɗin sashen amma shiru sai ta kuma kimtsa kan ta tayi sallama ta shiga asalin parlor ɗin,this is her first time na shiga sashen haka ta rinƙa bin sashen da kallo tana yaba kyawun wurin tana takawa zuwa ciki a natse..
  Bata san daga ina magana ke fitowa ba amma ta ɗan ji hayaniya da alama ƙaramin sa'insa ne ya kaure a inda hayaniyar ke fitowa..
 
Tsayawa tayi a tsakiyar parlorn tana ƙare ma parlorn kallo a hankali,duban ta ta maida ga wall ɗin parlorn sai ta ga wani babban enlargement mai ɗauke da hotuna kala uku na Khalid da Hamida suna murmushi cikin yanayin jin daɗi..
  Rintse ido tayi cikin faduwar gaba kafin ta juya ta kalli ɗayan nan ma sun yi kyau,haka ɗayan da ta kalla nan ma sun kyau ba kaɗan ba,idanun ta na kan wannan last photo sai ta ji muryar Hamida na faɗin
"Mine ba fah zan yarda da wannan sigar ba fah,na ce wannan nake so amma baka ganewa,hankali na kuma ya biya me ya sa kake son haramta min"!!.daidai sun fito parlorn kenan ana jayayya Khalid na saka wani abu cikin aljihun sa yana ƙarasa fitowa cikin parlorn Hamida kuma na turo baki cikin shagwaɓa da ɗan ɓacin rai..

  Basu san fifi na parlorn ba sai da Khalid ɗin ya gama maganar sa da Hamida cikin ɗan ɗaure fuska.
"Luv amma kin san wancan bracelet mai haɗe da wrist watch ɗin nan na farko da na siyo kin ce kina so,na damƙa maki right?wannan bai maki ba yet this one da na faɗa maki mai shi shima kika ce kina so and you knew ba naki bane,wannan ma ba naki bane duk na mutum ɗaya ne amma na baki ɗayar so why still insisting on this one again?haba Luv be just akan wannan lamarin i just can't give this one to you"!!rai ɓace Hamida ta ƙaraso cikin parlorn da nufin saka mai rikici da rigima duk dan ya bata dan bata ƙaunar ya mallakawa wacce yake da nufin mallakawa ɗin..

Har ta buɗe baki da zumar fara yi mai rikici sai kawai tayi tozali da fifi dake tsaye tana sauraron conversation ɗin su tana wondering rigimar nasu ko akan menene..
  Wani haɗe rai Hamida tayi ta aikawa fifi wani irin kallon da sai da ya ƙarawa fifi fargaban ta a zuciya amma ta ɗan kawar da fuskar ta ta buɗe baki ta gaida Khalid..
"Yaya Khalid ina kwana"!!nan take ya juyo ya gan ta tsaye sai ya ji nauyin ta hakan ya tabbatar mai da cewa lallai ta ji duk conversation ɗin su dan haka ya sake fuska ya tunkare ta yana amsawa..
  "Zo ki zauna mana kina tsaye yaushe kika shigo"!!wani takaici ne ya mamaye zuciyar Hamida kawai tayi folding hannuwar ta a ƙirjin ta tana bin su da kallo..
  Kasa zama fifi tayi ta tsaya a tsaye tana girgiza mai kai akan ba zata zauna ba idanuwanta nakan hameeda datakejin kaman taje ta rungumeta sbd take taji kamar zata fashe da kukan kewar hameeda din

Khalid ɗin ya rasa ya zai fara yi mata magana akan haƙurin da ya jima yana son bata but sai tayi cutting tunanin sa off ta hanyar ce mai
  "Yaya Khalid Ammy ce ta ce in zo wai kana nema na shine na zo"!!gyaɗa mata kai yayi yana saka hannun sa dan fiddo da agogon hannun da ya ɓoye ma Hamida.

Ai kuwa Khalid na fiddo wannan ƙaramin packed gift box ɗin nan ɗan madaidaici da zumar miƙawa Mufida a matsayin tsarabar da ya siyo mata Hamida ta waro idanun ta,rai ɓace ta ƙaraso gare su ta fauce abin kafin ya gama miƙowa Mufida..
  Rai ɓace tana kallon Mufida cikin tsananin baƙin ciki da kishin dake cin ranta na fifin tsawon shekaru tace'

  "Wallahi a'a,ba zan yarda ba akan wani dalili zaɓi na zaɓin rai na ka ɗauka ka yi ƙudirin damƙawa wata shi alhalin ka san ina so kuma yanzu na gama yi maka magiyar ka bani amma ka ƙi but ka ɗauka zaka damƙawa fifi akan me"!??tsayawa kallon ta Mufida tayi haka shima Khalid ɗin ya bi ta da kallo bai taɓa tsammamin Hamida zata iya bada wannan reaction ɗin ba akan mere wristwatch da bai kai nata da ta karɓa da fari tsada ba..

Bakin sa cike da magana da niyar hana ta cigaba da fiddo maganganun dake zuciyar ta dan wannan maganganun ya san zai yi leading ma wani matsala ne babba dan yana gudun in bai dakatar da Hamida ba yadda ran ta ya fara ɓacin nan toh komai na iya faruwa..
  Bai gama nazarin sa ba ya jiyo muryar Hamida cikin tsantsar ɓacin rai daya fara karya muryanta tana cewa'

  "Ka daina yi min haka rai na na ɓaci a ce kana nawa ɗin ma amma ban da iko da kai ban isa in mallaki abin da nake so ba daga gare ka sai an raba min shi da wata,ta yaya kake tunanin ba zan yi fushi ba?meye hakan"?Mufida na tsaye na kallon yadda ta rufe ido tana faɗa kamar bata san gaban wa take ba..

Hamidar da ta fuskanci jimami fifi ke yi akan maganganun da ta gama faɗa yanzun nan sai ta ƙara fuskantar ta rai ɓace cikin haɗe fuska ta ce
  "And you,,na yi ƙarya ne?ba gaskiya na faɗi ba kike kallo na?komai ba so kike ki mallaka ba a duniyar nan?ko ina kowa kina so ya zama naki mijin nawa ma ban isa in mallake sa ba ni kaɗai sai na raba sa da ke,abin hannun sa da nake so nake kuma da iko akan sa shima ban isa in mallaka ba ni kaɗai sai an ƙidaye min wanda ya cancanci zama nawa all because of you"!!da zuwan Khalid gaban su da jawo Hamida jikin sa bai fi blink of an eye ba..
  Abinda yake gudu ne ke gab da faruwa dan babu irin kishin da Hamida ke yi akan Mufida da Khalid bai sani ba,komai akan irin kishi da haushin Mufida da matar sa ke ji dan haka yayi saurin janyo ta jikin sa sbd kar ta cigaba da maganar amma ina tayi nisa sai fizge jikin ta da tayi tana hana sa kuma riƙo ta dan ba ƙaramin ɓaci ran ta yayi akan wannan abin da,duk da ta mallaki Khalid ɗin amma bata da cikakkiyar iko akan sa akwai abinda ya fi wannan ciwo a ce mijin ka na ɓare ɓaren ba wata da ba matar sa ba kyautar abinda ita da take matar sa ke muradi,ai wannan masifa ce,kenan in ta cigaba da yin shiru shikenan tana zaune tana ji tana gani shi kan sa mijin zai zamo under control ɗin Mufidar kenan since she is the ƴar so...
  Mufida na ƙare mata kallon mamaki dan bata san musabbabin wannan maganganun ƴar uwar nata ba..
  "Ai sarai kin gane me nake nufi kuma me nake magana akai,komai ke jawo sa and you should be asked for that"!!cikin mamaki da fargabar kalaman Hamida Mufida ta ce
  "Me ya faru Hamida"??wani irin kallon banza ta aikawa Mufida da shi sannan tayi ƙwafa ta ce..
  "Tambaya ta kike ko?ok yanzu zan sanar da ke,Mufida you are a thief asalin ɓarauniya mai kwashewa mutum komai,you are a thief who steals what is rightfully hers and not hers,baki da wani abin da ya zama mallakin ki duk sacewa kika yi kika maida sa naki kuma baki da ranar daina satar,you are a thief Mufida"!!dum dum gaban Mufida ya bayar cikin ƙaraje da rashin natsuwa Mufida ta kasa haƙuri ta tari numfashin ta
  "Hamida me na maki da kike aibata ni haka kuma ki rasa irin kalmar da zaki yi amfani da shi wun aibata ni sai da ɓarauniya?me na maki da tsauri haka Hamida"??datse mata maganar Hamida tayi ta hanyar ɗan ɗaga muryarta dake rawar kukan takaici da bacin Rai tace'

"Ai dama ba zaki sani ba Mufida,in tambaye ki mana?ina sbd jin daɗin da kike yi har kasa tantance abin da ya dace ki mallaka da wanda bai dace ki mallaka ba kika kasa zama ki tantance?tukunna a lokacin da kike jin daɗin ai baki san akwai abinda ba naki bane da bai kamata ya zamo naki ba right?everything ke everything ke sbd ke ce fitilar kowa"!!

kuma datse ta Mufida tayi cikin tashin hankali Khalid kam na gefe yayi yayi tayi shiru amma ta ƙi sauraron sa instead ta taso mai da ɓacin rai akan ko ya bar ta tayi maganar ta ko a ji su a gidan yau ɗin nan..
  "Hamee wai meke faruwa ne na kasa samo ma'ana a cikin kalaman ki"!!..dakatar da ita Hamida tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tana fashewa da kukan mai tsananin radadi tanafaɗin'
  "Save that name for someone kar ki kuma kiran wannan sunar dan baki cancanci kiran sa ba,tsakanin ki da Allah kin taɓa zama kin lura da wasu abubuwan dake faruwa da ke a rayuwar ki?am sure baki taɓa ba dan baki da wannan lokacin you are so occupied da soyayyar family ɗin mu,duk wasu jin daɗi a kan ki ya ƙare ɗiyar so,i cried all years duk a dalilin ki ke kaɗai Mufida,you stole everything komai"!!a ruɗe Mufida ta ce
"Me na sace maki Hamida"!?a tsawace Hamida ta amsa mata rai ɓace
  "Komai Mufida,kin sace min komai da nake mafarkin samu,komai da ya dace in mallaka Mufida you own it,can you believe that you have been leaving my dream?

Ni marainiyace gaba da bayana Banda kowa aduniya tunda na rasa mahaifiyata sbd nasan ita kadaice tasan ciwo da zafina bazata taba wareni kamar Mara galihuba,

Banda kowa Banda komai I have no other choice than to fight for myself Kota wace hanyace Koda kuwa ta hanyarda bai dace bane sbd kune kuka bani wannan choice din,

ohh Mufida kin gama sace min komai na duniyar nan kin ƙwace min komai na rasa me na tare maki kika zaɓi yi min haka"!!a ɗan tsawace Khalid ya kira sunan ta
  "Hamidaa just shut up"!!itama a tsawace ta mayar mai da
  "No ba zan yi shiru ba,gata nan Mufida ce silar faruwar komai da yake faruwa da ni a rayuwa ta,she stole everything for me and i don't want to forgive her"!!hawaye ne cike taf a idanun Mufida jin zafaffan kalaman da Hamida ke faɗa mata..
  Ƙarasowa kusa da su tayi ta tsaya suna fuskantar juna ita da Hamida sai da Mufida ta sauke wata nunfashin kukan zuciya mai nauyi sannan ta ce cikin tsananin rawar murya da rashin ƙarfin gwiwa ta ce
"Hamida ina son sanin asalin abinda na maki a iya rayuwar mu da zaman da muka yi ni da ke"!!wani irin kallo Hamida ta bi fifi da shi sannan ta hau yi mata magana cikin faɗa da haushi..

"Yanzu zan fayyace maki asalin abin da kika min a rayuwa wanda bai da bambanci da baƙin taɓo duk da na so _Ƙaunarmu_ ta ɗore amma kika san yadda kika yi kika datse wannan ƙaunar tamu"!!kuma yi mata wata tambayar fifi tayi gaban ta na faɗi
  "Hamee ta yaya na datse _Ƙaunarmu_"?..
"Ta ko ina Mufida,Mufida kin mamaye min komai,soyayya,kulawa,rarrashi d ƙauna duk kin mamaye komai kin riƙe,ni ba mutum ba ce?ban dace a so ni bane?ban da ƴancin samin gata ne?ke kaɗai ce mutum mai jini a jiki da kika cancanci gata?Mufida tun da muka taso da zuciya ɗaya na riƙe ki a matsayin ƴar uwa ta ta jini ba ƴar uwar dangantaka ba,tun yarintar mu Mufida kika fara ƙwace min abinda nake so,attention ɗin daddyn mu duk ke kika samu ni ban samu ba ban yi complaining ba,karatu ni ba a maida hankali akan nawa ba ke har special classes ake baki a gida ni kuma ko oho dan an fi ƙarfi na ni ban da gata,abincin ki sai an ɗanɗana kafin ki ci gudun kar ki ci ya maki illa ni kuma kai tsaye ake bari na na ci abincin haka,sutura sai wanda kike so kike sakawa kan ki tsaye ba a maki gyara bare a hana ki ni fah?idan zan saka wanda rai na ke so toh sai daddy ya maida ni in canza zuwa wanda ran sa ne ke so i never complained,soyayya da kafa kafa da ake yi da ke kar ran ki ya ɓaci Mufida ni bana samu ni ban taɓa ɗanɗanar sa ba,kaf su Ammy da Hajja da ke suke magana in suka kira a waya dan ke ce tasu ni ko daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin kiran su ba ni ba mutum ba ce?ranar da muka iso ƙasar nan imagine wai hankalin kowa akan ki ya komo ni dake tsaye an manta da ni ba a san ni ba sai ke,wai fah har wucewa aka yi da ke aka shige mota za a tafi a bar ni ana ta maki wasa da dariya ana gwada maki soyayyar da family ke nunawa ƴaƴan su da ƴan uwan su,mun dawo gidan nan aka kai ni wani irin pit wai ɗaki aka ce shine nawa naki kuwa kamar ta princess Cinderella komai an tsara maki dan ke ce kaɗai aka sani ake considering a matsayin ɗiya,abinci sai an tabbatar wanda ran ki ne ke so sannan za a girka kuma ba a ci sai an tabbatar kina nan za a jira ki sai kin zo sannan a ci ni fah?wa ya damu da ni wa kuma ya san ina raye bare a ba ni abinci,dawowar mu ƙasar nan ke kaɗai ce kika rinƙa experiencing soyayya da ƙaunar family ɗin mu ni ban samu ba,masoyi na abin alfahari na da nake muradin aure kafin in aura shima aka nemi a baki shi dan ni ban dace da shi ba sai ke tunda ke ce kika nuna soyayyar ki gare sa a fili,auren namu ma a sace aka ɗaura sa dan kar soyayyar ki da kulawar ki ya sami tangarɗa we ran away,muka dawo muka yi bayani a tunanin mu za a yarda da auren amma sai aka juya mana baya aka ɗau fushi da mu dan mun yi tempering da tunanin ki,babu wanda ya damu da mu a gidan nan daddy,Ammy da Hajja duk babu wanda ke sauraron mu akan karon farko da na tashi nayi standing ma right ɗi na,ni ce wacce bata dace da jin daɗin rayuwa ba aka ɗau wani a matsayin wanda za a ba ni tsoho mai mata wanda ni da ke duk mun san irin mijin da nake so,a lokacin da aka ce za a haɗa ni aure da yaya Saheeb Mufida kika maida ni abin tsokanar ki safe rana dare baki tunanin negative impact ɗin da tsokanar ki ke min a ƙwaƙwalwa ta kawai ana nuna maki so and you think ke ɗin angel ce that deserves everything right?muna nan ni da ke Ammy ta aika aka kwashe duk kayan ki dake sashe na aka maida maki ni kuma aka kwaso nawa aka kawo min,ni da ke ɗin ba abu ɗaya bane?ba uterus ɗaya muka zauna ba?ba rana ɗaya aka haife mu ba?komai naki ba nawa bane?Ammy ta kawar da fuskar ta akan hakan ta min abinda ta min dan ni ba mutum ba ce i never complained,now miji na ya siyo abu na gani na ce ina so ya bani amma ya hau jayayya da ni akan abinda nake tunanin ina da iko da shi ashe still ban tsira ba Mufida kina nan kina bibiya ta da farinciki na kina yunƙurin ƙwace min,for goodness sake Mufida me zan maki ne a rayuwar nan dan ki rabu da ni hakan nan in ji daɗin sabuwar rayuwa ta??uhum?tell me please"!!hawaye ya gama ɓatawa Mufida fuska kaca kaca haka Hamidar mai magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login