Showing 84001 words to 87000 words out of 101986 words

Chapter 29 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15653

mata baya.

A kullum tana ƙara son sa tana ƙara ƙaunar babyn su dake tare da ita sai dai tun abin baya damin ta har ya kai ya kawo abin ya fara ɗaga mata hnkl..

Kishi ne me zafi yake cinta, A ganin ta ba komai Saheeb ke nuna mata ba sama da tausay,dan tana ganin yanzu matar sa ta dawo so bai da lkcn ta ita sai na matar nasa,dan har a wurin cin abinci yana kafa kafa da Muhibba wannan dalili ya sa ta rage zuwa wurin cin abincin dan kar ta rinƙa ganin abinda zai riƙa ɗaga mata hnkl..

Takan zauna tayi kuka ta roƙi Allah ya yaye mata wannan damuwa nata haka zalika takan zauna ta rinƙa tmbyr kan ta ko laifin me tama Saheeb ɗin da ya daina kulawa da ta sosai haka..?

Sai yanzu take gane zafin son da baida amfani,ciwon dake cikin kyaliya sharewa juya baya da wahalan dake cikin nuna fifiko wayanda ta saba da sabanin su tun farin rayuwarta..

Wani lkcn zataji kishi sosai, zuciyar ta kan bata amsa da ai tunda kin fara nauyi hala shi ya sa ya daina sauraron ki dama fah kar ki manta auren haɗi aka maku ke da shi ba soyayya kuke yi ba..

A kullum in ta tuno hakan sai ta ji zafi a zuciyar ta ta kuma rinƙa ganin laifin zuciyar ta da ya bar ta tana makahon soyayyar da bata san kansa ba..

Dai dai da rana ɗaya Saheeb bai taɓa yunƙurin zama da fifi dan sanar da ita komai ba musanman akan current health situation ɗin Muhibba,dalili kuwa shine shi yana da miskilanci da ganin in mutum ya ga abu ya faru ai ya san da dalili ba sai ya bi mutumin ya mai bayani akan abinda ya farun ba kuma,sannan yana ganin shi ɗin ba yaro bane da zai yi ta bibiyar yara kamar bai san me yake yi ba..

So duka waɗannan tunanin su suka taru suka bada gudunmawa mai ƙarfi wurin nesanta muamalr su sannan zargi mai ƙarfi ya ɗarsu a zuciyar ta ta yadda take ganin kamar yana so ya ci amanar soyayyar ta ne dan ta daɗe da gane ƙarya yake mata ba son ta yake ba wani abu yake so a tattare da ita da ya janyo sa gare ta...

Duk kuwa yadda su Ammy da Hajja ke bata kulawa da kariya daidai gwargwado hakan bai ishe ta dan duk daɗin ka da mutani in har kana da matsala da gidan auren ka toh babu wani daɗi..

Tana nuna jin daɗin hakn amma aranta ta fi buƙatar shi mijin nata kusa da ita sama da kowa da komai sai dai hakan bai yiwu ba dan ganin sa ma sai yana so ya zo ya zame mata da ƙyar.

Rannan tana zaune a garden ɗin gidan tana aikin kullum wato tunanin sa da rayuwar su sai hawaye ya fara zubo mata dan bata saba da rashi ba,kamar tana son abu amma ta rasa sa,sam bata saba ba komai take so ana mata shi saidai a yanzu auren da tayi tana buƙatar abubuwa da dama daga cikin sa amma an kasa sama mata shi ta kasa samin waɗannan abubuwan dama da gaske in har mace tayi aure gatan ta ya ƙare dole ta fuskanci gidan ta ita kaɗai?in haka ne ita zata bada lbrn faruwar hakan dan dai gata iya gata babu wanda bata samu but cikin gidan ta ya zame mata kamar wuta bata iya kashe wutar sai dai in guje mai da ta yi dan komawa sashen su Ammy da zama tayi ba kasafai take zuwa nan nata sashen ba sbd gudun ɓacin rai...

Hannu ta ji a kafaɗar ta sai ta ɗago ta kalli hannun sannan ta kalli fuskar mamallakin hannun take ta kawar da kan ta tana cigaba da zubda kwallar ta..

Ta gaban ta ya zago ya zo ya zauna a kujerar dake fuskantar ta haɗe da riƙo hannayen ta yana murzawa..

Tana jin abin amma ta ƙyale sa bata tanka mai ba shi kuma bai hana ta kukan ba dan a ƴan kwanakin nan yana ɗan lura da halin rashin natsuwar zuciyar da take ciki sai ya daure ya binciko ta inda ya gan ta a nan garden ɗin ya kuma ƙudirta sanin matsalar ta..

"Me ke damin ki"?tmbyr da ya mata kenan sai ta kalle sa irin u are bluffing ɗin nan sai ta kawar da kan ta tayi shiru.

Juyo da fuskar ta yayi suna kallon juna for a while sannan ya furta
"Am sorry"a hnkl abin sai ya bata mamaki wato ya san ya mata laifi kenan..

"I truly am".ya kuma maimaita mata sai ta cigaba da yin shiru har dai dan kan sa ya fara rarrashin ta da alƙawarin making up mata da haka dai ya kalailaye ta a sannu har ta sauko daga dokin fushin ta saurare sa.

Tsakanin Mata da miji sai Allah,kalau suka shirya ranar haka tun safe har yamma fifi ta kasance cikin annashuwa da farinciki duk da bai zo inda take ba hakan ma yayi tunda ya bata tym da attention ɗin sa a ranar...

Sannu sannu rayuwa ke ta tafiya ahakan Saheeb yayi ta disappointing fifi kullum tana saka shi abu bata samun yadda takeso haka zata gaji ta cire tunanin a ran ta shi kuma bai taɓa tunanin ya take ji ba in bai nuna mata komai ba..

A ɓangaren su Hamida da Muhibba kuwa abubuwa sai gaba suke yi kamar ba za a daina numfashi ba dan kullum sabbin abubuwa suke ƙarawa akan na da sun yi nisa basu jin kira kuma duk wannan abin babu wanda ya san suna yi daga su sai su..

A kwanakin nan ne Muhibba ta fara jin wani irin abu a jikin ta kamar dai bata lfy,tun tana ɗan daurewa da kawar da kai har abin ya fara fin ƙarfin ta dan kuwa matsanancin ciwon ciki ke tasa ta gaba ba kaɗan ba amma bata da yadda ta iya dan dole ta kuma samin attention ɗin mijin ta wanda hakan ya kuma datsawa a rayuwar auren Saheeb da fifi

abubuwan sun kacame ma fifi ta yadda hakan yake nufin tana buƙatar attention ɗin wani da shawarar wani,but wa zata fuskanta ne bata sani ba..

Tana zaune wata ranar alhamis sai ta ji tana son ganawa da ƴar uwar ta duk munin naka naka ne ko da korar ta zata yi zata tafi ta faɗa mata damuwar ta maybe ta sami mafita..

Fita tayi zuwa sashen Hamida inda da ƙyar ma ta sami attention ɗin Hamidar,abu na farko da ta fara shine kuka mai tsanani da ratsa zuciya sai Hamidan ta natsu ta fara sauraron ta inda ta rinƙa karanto mata damuwar ta..

Gwanar tausayi Tace "Hamee am not happy wit my marriage,rayuwar aure na bai min yadda ya dace komai nawa ya fitar min a hannu na rasa ya zan yi,yaya Saheeb baya bani lkcn sa,bana samin kulawar sa,Hameda ban san makoma ta ba ban san laifi na ba,haka tawa jarabtar take ni kuma?fixing aure na kan sa na kasa yi?am pregnant but the father of my baby isn't ready to take care of me and our baby ya zan yi hakan ni kaɗai?bani da uwa i don't have any one sai ke" bzan iya kai damuwata wajen su ammy ba hamida,Hamida ki taimaka min dan Allah..
."da kuka mai taɓa zuciya fifi ta ida mgnr..

Sosai jikin Hamida yayi la'asar ta kasa haƙuri har ta janyo ƴaruwar nata tayi hugging nata tightly tana petting bayan ta cikin tsananin tausayi tana fidda sautin
"shhhh" a hnkl..
Kuka sosai fifi ke yi kuma kukan na ɗan taɓa ta a zuciyar ta ba kaɗan ba sai dai abinda bata sani ba shine,shin ta taya ƴaruwar ta yaƙin samin natsuwar mijin ta gare ta ne ko dai a'a ta bar ta ta cigaba ne ita kaɗai ba tare da ta taimaka mata ba?
#Mamuh
******34*

Murya ƙasa ƙasa kamar mai tsoron yin mgn Hamida ta fara yiwa ƴar uwar nata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya dan ba ƙaramin tausayin ta ta ni ba duk da yadda take ji a game da fifin bai sauya ko kaɗan ba a zuciyar ta but tana ganin kamar in ta ƙyale fifi cikin damuwar da take ciki akwai matsala..

  Ɗagowa fifi tayi tana kallon Hamida dake ta rarrashin ta,mantawa tayi da Hamidar tana fushi da ita sai ta kuma faɗa mata wani sashe na halin Saheeb wato rashin kimanta adalcin da yake yi a cikin gidan tsakanin su matayen sa..

  Hamida da hnkl ta ya koma kan ƙulalliyar da suke yi ita da Muhibba akan yadda zasu takura fifi sai ta ji gaban ta ya faɗi ta rasa inda hnkln ta ya tafi kawai sai ta ji ruwa ya ciko mata a ido sai dai ta danne bata bari ya zubo ba ta kuma rungume fifi tana ce mata
"Na maki alƙawarin taya ki addu'a da samin ƴancin ki a gidan mijin ki i promise u"

Ba ƙaramin daɗi Mufida ta ji ba sakamakon jiyo waɗannan kalamai daga bakin ƴar uwar ta after many months of shunning her..
  Da kalamai masu daɗi Hamida ta kwantarwa fifi hnkl har ta raka ta zuwa bakin gate ɗin sashen ta ta komo ciki ta zauna tana ta tunani ita kaɗai akan abubuwa da dama..

  Fifi kuwa ɗakin ta ta nufa dake sashen su Ammy ta kwanta shiru tana shafa cikin ta,cikin ya fara girma har ya bayyanu ta yadda duk wanda ya gan ta ya san mace ce mai juna biyu..
  Sanyayyan hawaye ne ya zubo mata a kumatun ta ta saka hannu ta goge tana gyara kwanciyar ta,a ran ta take ayyana dama zata iya juya hannun agogo baya da ta juya ba dan komai ba sai dan ta goge sashen Saheeb dake cikin shafukan rayuwar ta.

"Ina ma a ce zan iya,ina ma a ce ni Mufida zan iya goge ka gabaɗaya a rayuwa ta yaya Saheeb,ina ma a ce zan iya ciro zuciya ta in wanke inda sunan ka ya taɓa a zuciya ta sannan a mayar cikin ƙirji na,ina ma a ce ina da iko da zuciya da zan bata umarnin daina haska min kai da take yi a kai a kai,da da yadda zan yi da na yi ko dan in yaye ka a rayuwa ta dan ni kaɗai ke iyo a zurfaffen ƙaunar ka kai baka yi,ni ke soyayyar ni ke ƙaunar haka ni ke fuskantar hukuncin _Ƙaunarmu_ isn't it too much for me all alone"?ta ida mgnr tana mai fidda kuka mai sautin gaske da tsantsar tausayin kan ta..

  Tana ta kukan har bacci ya ɗauke ta mai tsanani,Hajja dake bakin ƙofar ta tana ta jiyo shesheƙar ta haka tana sauraron maganganun ta ta turo ƙofar ta shigo a hnkl ta isa inda fifi ke kwance a kaikaice. 

  Kallon tausayi ta ma fifi sannan ta matso dab da ita ta mata addu'a ta gyara mata kwamciyar a hnkl gudun kar ta tashe ta daga baccin kar ciwon kai ya dame ta...

******
A ɓangaren Hamida abubuwa babu sauƙi dan ranar a wani yanayi ta yini har mijin ta ya dawo ya same ta a haka nan ya tmby ta damuwar ta but ta kasa ce mai komai sai langaɓeai da take ta yi a jiki,duk ta yi sanyi hnkl ta baya jikin ta halin da ƴar uwar ta ke ciki ba ƙaramin takurawa zuciyar ta yake ba..

  Haka dai Khalid yayi ta fama da matar nasa hatta da abinci sai da ya karɓo masu a cikin gida dan kasa aiwatar da komai tayi,kkrin da tayi na girka abincin sai da ya ƙone ƙaurin sa ya cike gidan kaf da rana shi ya sa da yamma ya shiga wurin su Ammy ya karɓo dinner...

*****
kamar ƙiftawar ido cikin Fifi ya kai wata shida gab da na bakwai,babu abinda ya sauya a zamantakewar ta da mijin ta Saheeb,alƙawarurruka kam ta sha ta har ta gaji har ma ta daina yarda da shi da kalaman sa dan faɗa yake yi baya cikawa..

  Sashen Muhibba kuma rashin lfy sai daɗa gaba yake yi ciwon ciki matsananci kullum cikin ta take na yau na ɗare na jiya,sannan depressant da ta karɓa tana sha bata daina sha ba..

  Gani take kamar duk sakamakon damuwar da ta ɗorawa kan ta akan raahin haihuwar ne,ta kasa gane illar maganin da take sha ne ke haifar mata da ciwon cikin sai ta rinƙa ƙara yawan maganin madaɗin biyu a rana sai ta maida shi huɗu a rana ta sha biyu safe biyu yamma..

  Saheeb kuwa ya kasa samin natsuwar sa dan in ciwon cikin ya motsa mata sai ta yi kamar zata tafi tayi ta juyi haka zai ta kula da ita..

A lkcn da ya nemi Khalid a abin sai Khalid ya mai nuni da su tafi asibiti a duba mata mahaifar nata ƙememe Muhibba ta ƙi yarda dan ta san blackmailing Saheeb da tayi kuma take kanyi in ta tafi asibiti za a iya sanin gaskiya ita kuma batajin zata iya karawa da Mufida..

  Haka nan Saheeb ya bar ta dan ta ce ita gynaecologist ɗin ta zata tafi ta gani in ta shirya..
  Sosai take cikin matsala amma ta ƙi zuwa asibitin ga ciwon na daɗa gaba amma taurin zuciya irin na Muhibba bai bar ta ta tafi ganin likita ba ta yi ta managing kan ta..

Wani rana haka da dare misalin ƙarfe tara bayan Saheeb da Muhibba sun sami sa'insa da junan su sai ya fitar mata a ɗakin ya koma nasa baidai sami kwanciyar hnkl ba sai ya fita ya bar sashen ma gabaɗaya ya nufi sashen su Ammy..

  Ko da ya shiga duk sun kwanta sai ya nufi ɗakin fifi dan dama niyar sa washegari ya zo duba ta but yadda Muhibba ta ɗaga mai hnkl haka ya sa baya jin ya cigaba da zama a sashen dole ya zo ya ga fifi duk kuwa da ya san yaata laifi but he want to impress her today ta hanyar nuna mata sincere apology ɗin sa...

  Da fari da ya shiga ɗakin sai ya ga duhu ya mamaye ɗakin so yayi switching wutar ɗakin,ga mamakin sa sai ya hango ta jingine da gadon ta ta haɗe kai da gwiwar ta,hasken da ya mamaye ɗakin ne ya saka ta ɗago kan ta..
  Tana ganin sa sai ta zuba mai ido kamar bata taɓa ganin sa ba sai yau,shi kuma ya ƙarasa shigowa ciki a sannu,idanun ta na kan sa haka shima nasa idanun na kan ta..
  Da ya ƙarasa shigowa ya zo dab da ita sai ya zauna kusa da ita,sunkuyar da kan ta ƙasa tati ta mai shiru,bai san ta ina zai fara ba amma yana so yau ya kasance tare da ita ya faranta mata ya saka ta jin daɗi kamar yadda ya dace..

  Hannun sa ya saka ya riƙo nata,bata ce mai komai ba tana bin sa da kallo har ya kwantar da ita tana kallon sa ya dawo ta dama ya kwanta haɗe jawo marufin gadon ya lulluɓe su..
  Mamakin sa sosai ne ya kama ta ganin yadda yake mata abu kamar kurma,jan ta zuwa jikin sa da yayi ne ya saka ta lumshe ido dan dole ta kasa buɗewa..
  Kunnuwar ta ne suka jiyo mata sautin muryar sa yana bata haƙuri kamar kullum,ran ta a ɓace ta fara jan jikin ta amma ya matse ta dan ya fi ta ƙarfi ta ko ina..

  "Ki kula kar ki bige min baby".dakatawa tayi daga fizge fizgen da take yi ta natsu tana numfarfashi kamar tayi gudun tsere..

  Hannun sa ya kai kan cikin ta da ya fara girma sosai,zagayawa ya shiga yi da hannun nasa bisa cikin ta ba tare da ya ce komai ba..
  Da ya gama yayi ƙasa da kan sa ya sumbaci cikin nata sannan yayo sama ya rungume ta tsam a jikin sa,ƙala bata ce mai ba sai da suka share wasu lokuta a haka sannan fifi ta fara yunƙurin raba jikin ta da nasa amma ta ji ya kuma riƙo ta ƙam..
  Bata ankara ba ta ji ya fara janta a sannu ba da zafi zafi..
Tun bata biye masa har ta sauko ta biye mai abu kamar wasa sai ga fifi manne da Saheeb ana zuba love abin gwanin burgewa..

A nan ɗakin nata ya kwana bayan ya gama cika mata brain da alƙawarurrukan daga yanzu bai kuma yin nesa da ita ya mata alƙawarin tare zasu raini unborn baby ɗin su..

Tare suka yi wanka da asuba suka yi sallah tare suka kuma komawa baccin safe again bayan yayi showering nata da salon soyayyar sa mai ɗauke hnklin ɗiya mace...

****
  A sashen Muhibba kuma tun safe da ta farka ta duba bata gan sa ba ta shirya hnkl tashe ta fito,kamar ta fara tsayawa a sashen Hamida sai kuma ta fasa ta wuce zuwa sashen su Ammy..
  Babu wani walwala sosai a tattare da ita so bata wani jima ba tare da su ta tmby ƴar aikin gidan ko Saheeb ya shigo amma ta ce mata bata sani ba.
  Hnkl ta na bata Saheeb na nan tare da fifi kamar ta je kamar kar ta je sai ta miƙe ta haura saman gabab ta na ɗan faɗi..

Bata san me zata gani ba in ta shiga ɗakin fifi but bata dai son ta ga abinda ran ta ke raya mata..

Da isar ta ɗakin ta ɗora hannu a handle ɗin ta murɗa ta tura a hnkl ta sa kai..

Wani faɗuwar gaba ne ya riske ta ba dan komai ba sai ganin Saheeb

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login