Showing 45001 words to 48000 words out of 101986 words

Chapter 16 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15647

itama fuskar ta jiƙe yake da hawaye sakamakon tuno da irin rayuwar ƙinci da tayi a baya all because of Mufida..

Numfasa fifi tayi tana kuma matsawo kusa da Hamida ta kawo hannu ta riƙo ta tana tambayar ta murya a karye.
  "Hamida yaushe duk waɗannan abubuwan suka faru?ban sani ba baki sanar da ni ba ban taɓa gani ba,Hamida all these happened amma baki tsayar da ni kin sanar da ni ba?why"?fizge hannu Hamida tayi ta amsa mata.
  "Yaushe na sami lokacin sanar da ke?kina da lokaci na ne?soyayyar family ɗin mu ya mamaye ki baki da lokaci na baki taɓa lura da yanayi na ba ta yaya kike tsammanin zan iya tsayar da ke in nuna maki wannan abin?already akwai third party a tsakanin mu Mufida tell me how did you think i have been feeling lately all those years"!!kuka sosai Mufida ke yi Khalid kan sa a ƙasa Hamida kam hawayen ne kaɗai ke fitowa amma babu kuka tsantsar ɗacin da ran ta ke mata...
  Mufida bata haƙura ba ta kuma matsowa ta riƙo hannun Hamida tana kallon ta ta fara magana da sansayyar murya..

"Amma Hamida for once kin taɓa tunanin kira na ki faɗa min ni da ke?Hamida all my life na yi sa ne ina so maki farincikin rayuwa kamar yadda kike so min Hamida ban taɓa kawowa a rai na wannan kulawar da ake ba ni yana taɓa maki zuciya ba,ban san ana treating ɗin ki a haka ba,zuciya ta da tunani na bata taɓa kawo min ana ɓata maki irin haka ba tun yarintar mu har girman mu,Hamida ban san irin rayuwar da nake yi kike so ba believe me i swear,Hamida kina ganin kamar da niya nake ɗauke kai na akan ki??no, Hamida ban san halin da kike ciki ba,har zuciya ta ban san kina jin zafin wannan abin ba,Hamida ban taɓa lura ba Allah ne shaida na ban taɓa lura da yanayin rayuwa ta mafarkin ki bane,Hamida komai nawa naki ne komai naki nawa ne,ki yafe min na maki katsalandar a rayuwar ki soyayya da kulawar daddyn mu Ammy da Hajja duk na tara a kai na ni kaɗai ban bari kin mora ba Hamida ki yafe min am so sorry and i promise to make it up to you Hamee tun yanzu zan sanar da su Ammy da Hajja su canza su daina saka ki jin irin wannan feelings ɗin am coming"!!?duk a ruɗe take maganar zata juya Hamida ta wani finciko ta a hasale ta ce
"Stop this i don't like it,ki daina wannan pretence ɗin i hate liars and pretenders,Mufida duk wata so da zai fito daga wurin su Ammy,Hajja da daddyn mu a ƙarƙashin alfarmar ki bana so ki je ki cigaba da more goodies ɗin ki all i want is you to leave me and my husband alone na roƙe ki Mufida ba dan hali na ba na haƙura da jin daɗin family ɗi na dan na san ba zan samu ba sai a dalilin ki ni kuma bana so dan haka ki rabu da rayuwa ta da na miji na please Mufida"!!!a yanzu sosai kukan Mufida ya fito sarari ta kasa ɓoye sa,zafin da take ji a zuciyar ta ya sa ta kasa tsayawa ta juya da zumar kawa sashen Ammy amma sai me..

Ammy ce da Hajja ke share hawaye suna jan hanci abinda ya kuma girgiza Mufida kenan dan ta tabbatar suma sun saurari abinda ya faru sai kawai ta ƙarasa ta faɗa jikin Ammy tana matsanancin kuka tana kuma nanatawa Ammy abinda ya faru Ammy ba abinda take yi sama da kuka mai sauti,hankalin ta in yayi dubu ya tashi bata taɓa kawo maltreating Hamida suke yi ba da soyayyar da suke nunawa Mufida..

Hajja da tayi making attempt ɗin rungumo Hamida jikin ta bayan ta ƙarasa shigowa cikin parlor kawai Hamida ta ture hannun Ammy ta haura sama abin ta Khalid kam ya tsaya ya rinƙa ba su Ammy haƙuri tunanin sa basu ji daɗin maganganun Hamida bane sai da Ammy ta tura sa ya je ya lallaso Hamidar kafin ta kai fifi ɗaki dan kan ta har ya fara sara mata jikin ta na ɓari...

Jiki sanyaye Hajja da Ammy suka koma apartment ɗin su da nadama mai tsanani duk rayuwar da suka yi da su Hamida a gidan nan basu taɓa sanin suna zaluntar ta ba sai yau da ta furta da kan ta..
Abu kamar wasa fifi zazzaɓi ya rufe ta tun safiyar nan har dare haka Hamida sai da ta ji sauyi a jikin ta dan zazzaɓi ne mai tsanani ya rufe ta amma taurin zuciya ya sa ta ƙi yarda Khalid yayi nursing ɗin ta..

Kamar wasa kwana biyu kenan da faruwar wannan abin amma komai ya taɓarɓare Ammy da Hajja ba yadda basu yi ba akan Hamida ta sake jiki da su suna jawo ta jiki amma sam Hamida ko sauraron su bata yi dan ta san fake affection suke nuna mata ba dan son ran su ba..
Rannan Hajja ta ga abin ya fi ƙarfin ta ƙiyayyar kamar ta gama ginuwa a zuciyar Hamida game da ƴar uwar ta sai ta kira daddyn su Hamida tana sharɓe kuka tana mayar mai da abinda ya faru sannan tayi requesting ɗin sa da ya dawo Nigeria ya zo su haɗu su gyara wannan ɓarakar...

****
A rana na ukun ne da faruwar hakan Hamida ta fito farfajiyar gidan ta tana nemar wanda zata aika ya karɓo mata saƙon mijin ta a sashen su Ammy dan ko sashen ta daina zuwa sbd zafin da zuciyar ta ke mata game da su..
Rasa samin ɗan aika ya sa ta fito zuwa farfajiyar gidan dan nemo ko da driver ne ko mai gadi dan aiken sa..
Tana tsaka da dube duben ta idanun ta ya hasko mata wani mutum daga baya yana taaye hannun sa riƙe a ƙugun sa sanye da sport suit yana bada direction,tsayawa tayi tana kallon mutumin daga baya dan bata san waye shi ba a gidan bata taɓa ganin sa ba..
A sannu mutumin ya juyo a natse cikin kamewa ya fuskanci hanyar ɗaya apartment ɗin dake kusa da nasu
Atake kwarjininsa da haibarsa tareda wani kamewarsa da tsantsar kyawun fuskarsa da fatarsa dake bayyana tsantsar hutu da dukiya data gama kamesa ya cika gurin hartana Dan sauke kanta qasa sbd cika idanuwansa
yana tafe yana amsa waya kan sa direct yana kallon hanyar da zai shiga..
Sbd cikin Daren Koda ya iso baa shiga da kayansaba sai yanxu da safen

Wani irin suman tsaye Hamida tayi ta ƙame tana bin wannan mutumi da kallo da bata san ko wa nene shi ɗin ba,gaban ta ne ke faɗi da ta rasa dalili,ai kuwa tana tsayen sai ga Khalid ya fito da ɗan sauri yana dube dube sam bata san da zuwan sa ba sai ji tayi yana
"Luv kin ga min Marshall ba a ta nan wurin"?

dum ta ji gaban ta ya faɗi jin sunan da ya kira kasa kallon sa tayi sai sashen da take kallon an wuce ɗazu..

Tunowa Khalid yayi akan Hamidar fah bata san Marshall ɗin ba sai yayiwa kan sa murmushi ya ce
"Na manta Luv baki san shi ba am sure ya shige part ɗin sa dan yanzu na hango sa yana wucewa ina kiran sa amma yana waya bai ji ni ba am coming bari in duba shi"!!

tsinkewa zuciyar Hamida yayi jin an kira wannan mutumi da Marshall kenan yaya Saheeb..
"Inalillahi wa'inailaihir raji'un"!!shine kalmar da Hamida ta rinƙa nanatawa a zuciyar ta tana tsaye Khalid ya wuce ta zuwa apartment ɗin dake next to them batareda ta iya motsawa ba..
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*19*

Jiki sanyaye Hamida ta nemi hanyar komawar ta sashen ta gaban ta na cigaba da faɗi tana cigaba da nanata innalilahi wa'inailaihir raji'un idanun ta na mata mugun hasashen..
Da shigar ta parlorn ta zauna daɓas akan kujera tayi shiru tana kallon gefe ɗaya tana tunanin yadda tayiwa kan ta tuwon tulu gashi a yanzu ta rasa marar kwashe ta..

Me idanuwanta keson nuna Mata???
Mijin Fifi yafi nata??
Ko yanxuma kenan Fifi ce ke gabanta??

Hawaye ne ya hau zarya a fuskarta fuskarsa da haibarsa na sake cika idanuwanta..

Share hawayen tayi ta hau jujjuya kai tana girgiza ƙafa rasa madogara tayi kawai ta tashi ta shige ɗakin ta bata jira komai ba ta saka lock ta rufe ɗakin ta faɗa kan gado ta saki kukan raɗaɗin zuciya da zafin rai..

Kimanin mintuna arba'in da wani abu Hamida na rufe a ɗaki tana sharɓe kuka tsakanin ta da Allah wanda ita ta san dalilin yin sa,tana nan tana kukan har bacci yayi nasarar cin ƙarfin ta bata ankara ba sai ji tayi ana tapping bayan ta ana kiran sunan ta..
Ɗan buɗe idanun ta tayi ta sauke akan fuskar Khalid dake kan ta fuskar sa cike da damuwa ƙarara..
Tashi tayi ta zauna ta zuba mai idanun ta da ya sauya daga farare tas zuwa rage red..
Shima ita ɗin yake kallo yana tunanin me ya ɗaga mata hankali har haka da idanun ta suka sauya suka kumbura sannan jikin ta yayi zafi kamar wacce fever ya ma kamun sauri..
Kawo hannu yayi ya taɓa jikin ta ya ji zafi rau sai yayi saurin kai hannun sa goshin ta nan ma zafi rau,hankali a tashe ya hau tambayar ta me ke faruwa amma kasa amsa mai tayi sai bin shi da wani irin kallon tsarguwa take yi wanda ya fara bashi tsoro shima..

"Luv me ke damin ki ne i hope ba zazzaɓin ne ya kuma dawowa ba"?ya tambaye ta a ruɗe sai ta kawar da fuskar ta daga kallon sa ta ɗau wasu seconds sannan ta girgiza mai kai sai ya kuma yunƙurowa zai tambaye ta amma ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga mai hannu sannan ta ce
"Bacci nake son yi"!!gyaɗa mata kai yayi sai ya kwantar da ita a kan gadon ya jawo duvet ya lulluɓe ta yana manna mata kiss a goshin ta ya tsaya yana kallon ta..
Ganin bai da niyar fita ita kuma a matse take tayi nazarin ta sai ta lumshe idanun ta dan dai ya ga tayi bacci ya fita..
Shi kuma ganin ta fara bacci ya matso ta ya zauna kusa da ita duk tana jin shi ya hau kwararo mata addu'ar samin lafiya har da na fatar Allah ya sa albarkar sa ne a tare da su..

Tana gama tabbatar da cewa ya fita ta tashi da sauri ta je ta rufe ƙofar ɗakin da double lock ta dawo ta zauna..
Ji tayi kamar zafi na mata yawa alhalin akwai air split a bedroom ɗin but zafin da take ji ko mutumin dake cikin kango sai haka..
Cire kayan jikin ta tayi ta nufi toilet ta kunna shower ɗin wanka dan ba zata iya zama cikin bathtub ɗin ba tsabar rashin natsuwar zuciyar ta..

Wankan nan ana iya kiran sa da wanka baƙin ciki because the more the water is dropping on her skin the more her mind is leaving her soul..

Fuskar mijinta ya fado Mata tareda duk wani abinda ya shafesa ta lumshe idanuwanta cikeda so da qaunarsa saidai tsananin kishin yar uwarta da irin mijin data samu Wanda a gani na ido yafi nata Yana yaqi gurin danne son nata mijin,

Bayan ta gama wankar ne ta fito ta shirya cikin simple abaya ta wuce kitchen ta haɗa masu lunch..

Bata kira Khalid a waya ba bare ta sanar da shi abincin su is ready,rather tayi zaman ta ta ci nata ta bar mai nashi ta tashi tayi ficewar ta zuwa zuwa garden ɗin gidan tayi zaman ta a nan
Ita wato ko yanxuma Bata sauya Mata ba Fifi is always ahead of her,
Meyasa su hajja suka zabarwa Fifi Marshall???
Hawayen tsananin kishin fifin suka gangaro mata tanajin wani irin nauyi cikin ranta.

****
"Baby ki ci abincin nan mana kin taɓa ganin inda mutum ya warke garau kuma baya cin abinc?ana haka"?shiru fifi tayi,tun ranar da ƴar uwar ta ta mata confessing abinda ke ran ta ta kasa natsuwa haka ciwon da take ji a zuciyar ta har yanzu bai warke ba yana nan yana daɗa yaɗuwa,ita dai ta san har ga Allah zuciyar ta ɗaya take yiwa ƴar uwar nata so amma ta rasa yadda aka yi tana raye tayi witnessing irin wannan blast ɗin ta yaya ma aka yi duk waɗannan abubuwan suka faru amma basirar ta ya shafe bata lura ba..
Ko a mafarki bata taɓa kawo rana irin ta ranar nan zata zo ta riske su a rayuwar su ba mostly a labarai take jin ana irin hakan amma ashe it has been designed for her tuntuni ranar da abin ya faru ne dai Allah yayi zai zamo mata eye opener..

Hawaye ne ya fara bin fuskar ta sai hankalin Ammy ya kuma tashi dan a kullum sai dai in fifi bata farka daga bacci ba amma in har idanun ta biyu daga silent tears sai kuka mai sauti hatta da abinci in aka mata maganar sa sai ta saka kuka dan tunowa take da yanzu Hamida na nan na mata kallon selfish person...
Da ƙyar Ammy ta rarrashi fifi ta tashi ta ci abincin dan har an kawo mata ɗakin..
Zama tayi tana kallon abincin sai ta ji appetite ɗin ta yayi ceasing sai ta kalli Ammy ta girgiza mata kai alamar ba ci zata yi ba..
Girgiza mata kai Ammy itama tayi tana faɗin
"Baby not now again rabon ki da abinci tun daren jiya kuma shima liquid sips ne ta yaya zaki warke baki ci abinda zai saka maki ƙarfin jiki ba?uhum?amsa min?ki mana adalci Hajja na can na zaryar sashen Hamida tun ɗazu amma bata same ta ba duk dan mun gyara kuskuren mu amma ke baki son yarda ki taimaka mana why"?jan hanci fifi tayi sai ta kalli Ammy ta ce
"Ammy kina ganin Hamida zata yafe min laifin da na mata kuma yafiyar har abada"?tausayin ta ne ya mamaye Ammy sai ta rungume ta tana amsa mata da eh Hamida zata yafe mata mana ai ba da sanin ta hakan ya faru ba..

Sai da fifi ta ɗan natsa sai ta kuma kallon Ammy muryar ta na rawa ta ce
"Ammy exams ɗin mu saura kwanaki kaɗan,bana concentrating a karatu na ina so in ɗan zaga gidan maybe in sami ikon tuno wasu abubuwan"..
Ɗaga ta Ammy tayi bata ce ƙala ba ta rako ta har main parlor sai fifin ta ce mata ta huta ita kaɗai zata tafi..

Fita tayi ta fara tafiyar ta a hankali tana yi tana tuno irin rayuwar ƙuncin da ƴar uwar ta tayi duk a dalilin ta,a ko da yaushe in ta tuno wannan abin takan yi takaicin irin rayuwar da take yi ta yaya ƴar uwar ta jinin ta ta girma tun yarinta har auren ta a irin wannan baƙin ciki ba tare da sanin ta ba,abin na taɓa mata zuciya..

Tana tafe tana tunanin ta bata san har ta zago zuwa hanyar garden ba sai ji tayi kamar ta jefa ƙafar ta a wani soft place,hakan ya sa ta dawo hayyacin ta ta kalli ƙasa sai ta ga grass carpet alamar garden ta zo..
Ɗan kalle kallen ta tayi ta hango wani kujera sai ta ƙarasa nan ta zauna tana mai haɗe hannun ta da goshin ta wuri ɗaya..

Bata ɗago ba sai da ta ji hawayen idanun ta na nemar tado mata da matsalar zuciyar ta mai wuyar sha'ani sannan ta ɗago ta kalli garden ɗin for a while..
Juya kan ta da zata yi ta hango ƴar uwar ta zaune tayi crossing ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon anterior view ɗin ta..

Ai bata tsaya wani tunanin ba ta tashi da gudun ta dan dama ta jima tana son ta gana da Hamidar amma bai faru ba sakamakon rashin lafiyar da ya lulluɓe ta tun ranar da abin nan ya faru..
Hamida dake zaune a zahiri amma a baɗini duniyar tunani ta dulmiya,kawai sai ta ji an faɗo mata from no where..

Ɗago kai tayi sai ta ga Mufida a jikin ta tana kuka tsakanin ta da Allah

Wani irin tsananin so da kewar fifin ya taso Mata harta daga hannu zata rungumota sai kishinta ya motso Mata mai qarfi ai kam bata wani jira ba ta ture ta daga jikin ta tana kakkaɓe jikin ta haɗe da jefawa Mufida wani irin mugun kallo..
Ita dai bata damu da kallon ba ta kuma zuwa dan rungume ta amma nan ma ta ƙara datse nufin Mufidar tana gargaɗin ta akan kar ta kuskura ta matso ta..

Abin bai ɓatawa Mufida rai ba dan ta san zafin laifin ta ne ya sa Hamidar yi mata hakan.
"Hamee ki saurare ni,i am ready to receive your punishment ko ta ya nene na yarda zan karɓi hukuncin ki in dai zai goge baƙin tambarin da na dasa nawa a zuciyar ki kin ji"?wani dirty look Hamida ta aikawa Mufida da shi kafin ta ja tsaki ta wuce Mufidar tana tafe tana maganganu ciki ciki ita kaɗai ke jin sa..

Durƙusawa Mufida tayi a wurin tana kuka mai taɓa zuciya a duk lokacin da ta tuno irin raɗaɗin da ta sakawa ƴar uwar ta a zuciya sai ta ji kamar kukan nata kaɗai bai isa ba..
Sai da tayi kukan sosai sannan ta tashi tana tangaɗi ta koma sashen Ammy inda da zuwan ta ta sami wuri ta kwanta,forcing kan ta tayi dan bacci ya ɗauke ta kar damuwar ya mata yawa..

Ko da Ammy ta shigo ta gan ta a haka bata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login